BABI NA SITTIN DA TARA
Tunda ta tafi ya nemi kwanciyar hankalinshi ya rasa. Yafi awa uku zaune cikin office dinnan amma sam baya gane wake shiga da kuma wake fita. Tun ranar daya fara ganinta a gidan Hajia yake tariyowa, da irin maganganun da take mashi, kukanta, yadda hawaye ke zuba saman cheeks dinta, how he body vibrates as she cries. Karar ringing tone dinshi ne ta katse mashi duk wani tunanin shi, dan karamin tsaki yayi, yana duba wayar yaga Maama ce.
Dauka yayi ya kara a kunnenshi, gaidata yayi kamar yanda ya saba kamar yayi shiru alamun ta fadi abunda yasa ta kirashi. "Saahir zaka kai nan da three hours baka dawo gida ba?" Abunda ta tambaya kenan, ta saba mashi wannan tambayar duk in baya gida, shi bai kawo komai a ranshi ba.
Agogo ya kalla yaga 12pm har ta dan gota, baya tunanin zai iya kaiwa har wajen 3 cikin office dinnan, "Eh Maama zan kai, fita zakiyi ne?" Haka nan yace mata zaikai, dan yanzu idan yace baijin dadi zai dawo gida ta dinga takura mashi da questions.
"Aa ba fita zanyi ba, saidai ka dawo din. Kaci abinci kaje Saahir?" Da toh ya amsa mata kafin ya kashe wayar. Wata duniyar ya kara lulawa, abubuwa ne suke kara dawo mashi kamar lokacin ake yinsu. Duk wasu suspicious abubuwa.
Bai kara cikakkar one hour ba cikin office din ya kulle ya fita, restaurant ya fara biyawa ya siya snacks yaci, dan tunda Beeba ta tafi yake kasa cin abincin kowa. Dama can ko tayi yan tafiye tafiyenta saidai ya girka da kanshi yaci, to yanzu ba karfin da zaiyi wani girki balle.
Gida ya nufa direct, koda yayi parking dakinshi ya fara zuwa yayi wanka yayi sallah kafin ya dade yana addua, shikam baima san abunda yake damunshi ba. Kamar wanda aka ja haka ya fara takawa har zuwa dakin Habiba. Yana shiga ya iske shi a yanda ta barshi, kamar ya kurma ihu haka yaji. Sai yaji kamar one of those moments da zai shigo dakin yace "Yar Baka yau baza'a mun girkin bane?"
Wani sa'in sai tayi kamar bata jishi ba har sai ya shigo ya zauna kan kujera kafin ta kalleshi tace "Dan gayu indai har bazaka ansa ka fada kogin nan ba to fa ji babu girkin da zan karayi maka."
Kullum ansar shi indai baice shi yana bakin gabar kogin ba tofa zaice "Saidai kece kika fada Yar baka, amma ni har yanzu ko hanyar kogin ma ban kama ba." Da haka zai lallaba ta ta fito suje suyi girki, ranar kuma da bayajin yan girki saidai ta girka shi yana zaune yana mata hira.
Kauda tunanin yayi a ranshi, dan inhar ya fara tunanin memories dinsu to wallahi sai ya shekara wajen. Direct bed side drawer dinta ya nufa, yana janyowa kuwa idanunshi suka fada kan passport dinta, jikinshi na rawa ya dauka ya buda yaga kuwa sunanta ne. Visas ya fara gani daga wannan kasa zuwa wannan kasa, hankalinshi bai kara tashi ba saida yaga dan madaidaicin photo album dinta.
It's a tradition to her, duk kasar da taje sai taje gaban wani monumental place nasu tayi picture, not only picture din waya kuma, picture ake fiddo mata dashi. Tace ita bata yarda da picture din waya ba, saboda wataran wayar na iya bacewa, sai tayi yaya kuma?
Pictures dinta yaita gani tururu, wanda ciki kashi 100 ko kashi 5 basu kai ba wanda tayi a nigeria. Ranshi yakai kololuwa wajen tashi, hankalinshi babu inda bai kaiba a gushewa, jikinshi rawa yake. Album din da passport din ya fito ya nufi dakin Maama, yasan tana nan tunda ya shigo yaga motar ta is parked.
A bangaren Maama kuwa, tun ranar data kira Hajia suka gama magana ta nufi gidan wata kawar huldarsu, a nanne ta iske an kawo wata tsaleliyar budurwa. Yau aka kawo mata ita gida, dalilinta kenan na kiran Saahir taji in har zai kai 3 hours bai dawo ba. Akayi dace kuma yace eh, dan da yace Aa tabbas to saidai suje hotel. Hankali kwance suka lula duniyarsu ta alfasha.
Suna cike da alfasharsu taji an banko kofa, duk duniya bata taba tunanin zataji tashin hankali irin wanda taji ba a time. Ita ba ganin da Saahir din ya mata ba, tunano kalmomin malaminta tayi "Ki kula Hajia hauwa, koda wasa karki bari ya kamaki cikin wannan siga. Dan kuwa a yanzu aikinmu da yake kanshi ko duk duniya zata taro tace mashi ga halin da kike cike bazai taba yarda ba, ke koke da bakinki kika fada mashi bazai yarda ba, amma the moment idanunshi suka gane mashi, to fa babu sauran boye boye."
Da Album din, da passport din, da shi kanshi Saahir din, a tare suka fadi ragab a bakin kofar. Idanunshi kan Maama ko kyaftawa bayayi, a hanzarce ita da yarinyar suka suturta jikinsu kafin yarinyar tayi sumsum ta fice daga gidan gaba daya. Kamar wacce kwai ya fashewa a jiki haka ta fara takowa tazo itama ta zauna a inda yake har yanzu, hawaye kawai ke fitowa daga idanunshi.
"Maama why?! Meyasa zaki man haka?" Kuka yake kamar karamin yaro, ji yake kamar ranshi ya fito ya huta da irin wannan bakin cikin.
Girgiza kai ta farayi, kafin daga baya ta saduda ta fara bashi ansa. "Saahir tun kafin na rabu da Babanka nakeyi, bansan ya zanyi ba. Bai bani time, ko ya dawo kasar baya kulani, I can't resist the urge of my desires, so I asked Hajia...ita ta sakani a harkar. Saahir, kayi haku..." bai bari ta idasa ba ya tsayar da ita.
"Bayan kin rabu dashi din fah? Meyasa bakiyi aure ba, Maama? Meyasa? Wannan wace irin kazanta ce? Ki rasa abunda zaki bi sai mata, Maama? Yar Baka...you gave her this life too. You ruined her. Idan kince after kun rabu baki da niyya, daya rasu fah? Bayan duka abunda ya tara ya dawo karkashin ikona wanda ke kike juya komai fah? Wanda idan kinso zaki iya auran wanda bai kaini shekaru ba. Maama, just tell me why?!!" Da akwai yadda mutum zai fiddo zuciyarshi tayi koda seconds ne bata cikin kirjinshi kafin ya maidata, da Saahir yayi. Komai ya tsaya mashi cak, gani yake to tunda Maama haka take kowa ma zai iya yin komai.
Hannu takai zata tabashi yayi hanzarin janye jikinshi, "Just answer me, why?!"
Kukanta ne yayi intensifying, "Nasan I have no excuse. Duk wanda ya lalace shi yaso, na dauka. Koma me zakamun kamun, amma dan Allah Saahir karkayi fushi dani, ka gafarta man." Roqon gafara babu irin wanda batawa Saahir ba amma ko gezau.
Har yazo zai fita daga dakin ya dawo, "Nayi alkawarin zan yafe maki, amma bisa sharadi biyu."
Da hanzari ta fara daga kai "Na yarda, koma menene wallahi tallahi na yarda, ka yafe man Saahir, na maka alkawari bazan kara ba." Shi bai yarda da alkawarinta ba, kawai dai she has to do all he says.
"Na farko, zan maki aure. Nasan eh ke mahaifiyata ce, amma a musulunce zan iya zama waliyyin ki. Kowa na aura maki Maama zaki zauna dashi babu wulakanci. Na biyu, idan yana da yara zaki rikesu kamar yanda kika rikeni, Maama idan akwai mace cikinsu kika lalata Allah ya isa ba..." bata bari ya karasa ba tayi hanzarin riko hannayenshi, duk fadin duniya da abunda ke cikinta babu abunda takeso kamar Saahir, haka zalika babu abunda bazata iya yi mashi ba.
"Na yarda, wallahi na yarda Saahir. Ba sai kamun Allah ya isa ba, na maka alkawari bazanyi ba." Kuka take tana nadamar rayuwarta. Babu irin nadama da bakin cikin da bataji a cikin zuciyarta.
Fita yayi bai ko kara kallonta ba. Direct dakin gateman dinsu yaje, he took him as a father tun tasowarshi. Kuka ya farayi yana hadashi da Allah, babu abunda ya boye mashi kafin ya fito mashi da bukatarshi. Dakyar ya aminci ganin yadda Saahir din ke kuka yana rokanshi, kuma shima practically shi yayi raising dinshi, dukda cewar tun mahaifinshi na raye suke tare. Matarshi shekarar ta biyu da rasuwa. Yaranshi 7 duka mata ne. Yar autar yanzu she's 13 kuma ita kadai ce a gabanshi tana gidan dan uwanshi. Sauran duk sunyi aure.
Bayan sallar maghrib a masallacin unguwarsu Saahir ya bukaci a dauren auren, nan take kuwa aka daura auren. Koda ya shigo gidan ya fada mata kuka ta fashe dashi, bawai dan auren da ya mata ba ko kuma dan wanda ya aura mata ba, Aa, ganin tsana da kyamarta data gane cikin idanunshi.
Dakin dake kusa da nata shi ya gyarawa Malam Musa da kanshi, kafin kuma ya kara tunasar da Maama alkawarin data daukar mashi. Ranar cikin gidan Malam Musa ya kwana, kafin da safe Saahir zai bashi driver suje kauyensu ya taho da diyarshi Kausar.
Dare ya tsala, babu abunda yake motsi face karar ac din dake busa mashi iska. Ya kasa bacci, yasan what he did is right, amma there is one wrong da yakeso ya gyara. Yar Baka. Kamar dan koyo haka ya fara dialing number dinta. Yanda take gurinshi itama ta kasa bacci, kullum cikin dare sai tayi kuka harta gaji dayi kafin bacci yake daukarta.
Kamar a mafarki taji wayarta na ringing, har saida ta kusa daukewa kafin tayi picking. A hankali ta kara wayar kunnenta. "Dan Gayu..." ta furta a hankali, dan gani take kamar mafarki takeyi, after two whole months.
"Yar Baka. Na fada kogin, zaki fidda ni?" Maganar daya fara mata kenan, shi kanshi ya rasa yadda akayi of all the things he wants to tell her.
Ta gane ya gano gaskia, wani kukan farin ciki ne ya hadu da dariya, "Sai yanzu ka fada kenan? To ka bari ka dan wahala kadan sannan sai na fiddo ka."
"Aa nidai, ruwan kogin suffocating dina yake, ko so kike ki rasani gaba daya? Yar Baka I miss you kamar na fiddo zuciyata na huta for some minutes. Ina zan ganki?"
"To ni banyi missing dinka ba akace? Kullum fa sai nayi kuka tunda bana ganin Dan gayu a nan."
Kamar wasa suka fara magana, a hankali ya fara bata hakuri saboda he caused that life on her, baisan halin mamanshi ba da bai kaita ba. She apologised for insulting Mamanshi kafin ta bashi address din gidansu. Kusan kwana sukayi suna waya. Washe gari kuwa after zuhr ya kirata yace mata yana gida, tasha ado iya ado tazo ta tarbeta ta shigar dashi, dama sunyi da Baba zai dawo after zuhr su gaisa da Saahir din. Inna kuwa sai haba haba takeyi dashi.
Bayan yaci abinci sun danyi fira ne yake fada mata abunda ya faru da kuma hukuncin daya dauka, ita dai batace mashi komai ba, dan ta gama sarewa da alamuran Maama. Akwai tambayar dayakeso ya mata, dukda dai yasan amsar amma it breaks his heart. He could remember tace Mamanshi ita ta bata ta, does that mean sun aikata alfasha da mamanshi? He knows the answer, amma he doesn't want to be believe. Kuma bayaso yayi asking dinta because he's definitely going to break his heart.
Har bakin motarshi ta rakashi, sai dariya takeyi kamar wacce ta tsinci hakuri. Ita kanta batasan tana san Saahir da gasken gasken ba saida suka rabu. Har zai shiga mota ya juyo, "Yar Baka na turo a saka mana ranar aure gobe?" Dariya ta fashe dashi, duk tunaninta wasa yake.
"Eh ka turo, Ina nan ina jiran dangin Dan gayu."
As he said, goben saidai ya kirata yace mata ga brothers din babanshi nan sun taho. Duk iya rudewa ta rude. Haka ta fada wa Inna nan suka fara shiri cikin gaggawa. Baba ma ya kira brothers dinshi. Sunzo sunyi tambaya kuma an basu, amma sai suka roki alfarma akan a saka bikin wata daya dan kuwa yaran kudu yakeson komawa da aiki babu bukatar wani jinkiri, dan ko cokali bazasu bukata ba.
Dakyar Baba ya yarda, haka aka saka rana ana jiran tazo. Tunda aka saka ranar kullum sai Habiba ta kira Sakina suna shirye shirye, Inna kuwa batayi kasa a guiwa ba wajen gyara duka yaran nata biyu, dan gani take yanzu dukansu zata hadasu ta musu auren.
Rana bata karya, saidai uwar diya taji kunya, yau aka daure auren Habiba Abdullahi Bello da angonta Saahir Mukhtar Maigida. Babu kalar mutanen da basuzo daurin auren ba, mostly friends din baban Saahir ne da kuma business partners dinsu.
Sakinah karshen rudewa tayita, daga Baba har Inna kowa kanta yake, aike taje nan taje can. Ya T ma ya samu halarta, dan kuwa Arhaan da kanshi yaje ya daukoshi daga camp din, san cewa yayi, yayi missing bikin Sakina bai kamata ace yayi na Habiba ba. Cikin Sakina yanzu yana cikin wata bakwai zuwa takwas, tayi nauyi amma hakan bai saka ta zauna taki taya yaruwarta hidima ba.
Wajen 5:30 jirgin su Habiba da Saahir ya daga zuwa garin ikko, wato Lagos. Apartment ne hadadde na gani na fada a valley estate. Driver dinshi yazo daukarsu, koda suka iso gidan key ya bata ta bude ta shiga kafin ya shigo masu da akwatunansu. Tanaso ta tambayeshi ya Maama amma ta kasa, but da suka sauka taji yana waya da Maama yana fada mata cewar sun sauka har taji sun gaisa da Kauthar, alamar dai komai lafiya.
Wanka sukayi sukaci abinci kafin sukayi sallah kamar yadda kowane ma'aurata sukeyi. Hugging dinta yayi ta gefe yana sauke numfashi. "Yar Baka I can't believe this, wai kece matata. Dan Allah tell me it's not a dream." Dariya tayi kafin ta kwantar da kanta saman shoulder dinshi.
"It's not a dream, Dan gayu, no matter how unreal it looks. We're married now." Sunkuyowa yayi da niyyar yayi kissing dinta amma ta zille tana dariya.
"Ai kace baka fada kogin ba ko? Ka bani sai kaga babu sarki sai Allah zama ka fada kogin ne." Binta ya farayi tsakar dakin.
"Yar baka nikam bazan iya ba, nagaji. Okay naji, na fada kogin, nayi iyo har na gaji, ki saka kugiya ki fiddo ni." Wata dariya suka fashe da ita a tare kafin ta dawo inda yake, da kanta tayi merging lips dinsu waje daya, ans gradually, they become one.
•
Dukda irin gajiyar dake jikin Sakinah amma haka bai saka Arhaan ya kyaleta sai washe gari ba, wajen 6 ya kirata akan ta shirya kayanta tama su Inna sallama tazo su tafi. Tayi mitar tayi magiyar amma duk a banza. shi gani yake indai ya barta gidan nan to bazata taba hutawa ba.
A gajiye lis suka isa gida, ko akwatunan su basu dauka ba suka shiga gidan. A tare sukayi wanka sukaci abincin da suka siya a hanya. Kwance take kan gadonshi daga ita sai yar rigar bacci, duk ta dage saboda tudun da cikinta yayi.
Kafafunta yake matsa mata a hankali, har bacci yanasan daukarta. Wayarshi ta fara ringing, kuma wayar na kusa da ita. Dauka tayi yace ta saka a speaker. Number din Baba ne, yasan ba abunda zaice mashi sai fadan baya kula da company sosai.
Tana sakawa a speaker yace "Hello, Baba."
Kamar daga sama sukaji sauti, murya ce kamar ta Mama, ko daga bacci aka tashesu zasu gane muryar Mama. "Dan Mama? Mama ta tashi kaji? Ya kake? Baka rame ba ko? Sakinah bata bari kayi kuka sosai ba ko?..." Baba yasan halinta sarai surutu zataita yi, karbar wayar yayi. "Arhaan, nasa an maku renewing visa dinku, tickets dinku suna hannun driver na, gobe karfe 9 jirgin zai tashi, zaizo ya daukeku by 7 insha Allah."
Ihun da suke ya hana daga Baban har Maman su samu wata amsa daga wajensu. Ihu suke kamar wasu kananun yara, tsalle sosai sukeyi tsakiyar gadon suna rungume da juna. Bacci da ba'ayi ba kenan, kaya suka fara hadawa, kowannen su bakinshi yaki rufuwa. Mama is back! Sound and safe! Cairo, here they come!
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top