BABI NA SITTIN DA TAKWAS
Sati daya har ya wuce, in kaga Sakina da Habiba bazaka taba cewa sun dauki tsawon watanni batare da sanin inda junansu suke ba. Tun kusan last two days Habiba take damun Sakina akan ita tanaso taje gida wajen Inna da Baba, saboda zuwa yanzu Arhaan ya fada masu cewar rehabilitation camp yasa aka kai Ya T, inda ake saka ran Insha Allahu idan ya fito duk wani shaye shaye zai daina zai natsu ya kama sana'ar yi.
Sakina tanaso taje gidan amma tsoron irin tarbar da Inna zata mata yasa ta kasa zuwa, dan haka Arhaan ya saka driver dinshi yaja motar Habiba ya kaita har Kaduna kafin ya hau mota ya dawo gida. Koda Habiba ta tsaya bakin kofar gidansu tafi five minutes batare da ta kara taku koda daya ba. With a heavy heart, a hankali ta fara taku daya daya har ta shiga gidan.
As usual, muryar Inna ta jiyo tana sheka masifa cikin gidan, wai ta shanya dussa awakin Maman iliya sun cinye mata. She put it in mind, zata siyawa iyayenta gida, atleast they owe her that. Daga muryarta tayi ta kara kwada wata sallamar, kamar daga sama Inna ta jiyo sauti kamar na Habiba. Juyowa tayi kafin ta tsaya shekeke tana kallonta.
"Innalillahi! Habiba kece nake gani haka?! Allah mai yadda yaso, Habiba ina kika shiga tsawon lokacin nan ko waya bakiyi?" Tunda Inna take sai yau ta bari damuwar rashin sanin inda Habiba take ta fito fili, dan koda Maman iliya ke cewa sunje sun saida yarinya bata taba bari abun ya dameta ba.
A hankali Habiba ta tako har inda Inna take kafin tayi hugging dinta sai kuka. Baba yana jinsu cikin daki, dan yau bayajin dadin jikinshi ko kasuwar baije ba, koma yahe baida karfin da zaiyi wani dako. Jin shashekar kukan Habiba tanawa Inna magana yasa a takarkara ya fito daga dakin, ilai kau ita yagani tsaye, hannunta cikin na Inna suna magana.
"Beebalo?" Her calls her that sometimes, wani sa'ilin har Sakina ta rika mata dariya wai ita dai duk yanda akayi da sunanta bai taba yin dadi. A hankali ta saki hannun Inna kafin ta karasa wajen Baba, she missed him.
Saida komai ya lafa kafin take fada masu ai ga inda aka kai Ya T su daina damun kansu abun alkhairi ne insha Allahu. Ta fada masu cewar daga gidan Sakina take kuma tanaso zasuje wani waje da ita. Kafin yamma tayi ta samo number din dillalin gidaje, nan sukayi magana akan gobe zataje taga gidan ta siya.
Washe gari da safe haka ta daukesu cikin mota suka nufa inda dillalin ya turo mata address, cikinsu babu wanda ya tambayi inda ta samo mota ko kuma kudin da suka lura tanada shi, saidai ta lura Baba yana san yayi magana amma yana tsoron masifar Inna, dan abu kadan daya fada zatace nema yake ya takurawa yarinya.
Gidan sukaje suka gani, gida ne flat me kyau daki uku sai falo daya da kitchen, kowane daki kuma da toilet dinshi, tsakar gidan kuma ba laifi tana da dan girma. Juyawa tayi ta kallesu tace gidan yayi? A tare suka daga mata kai, da murmushi tabi dillalin kafin taje ta mishi transfer, akayi signing aka bata takardun gida. Motar suka koma kafin ta dauki hanyar rehabilitation center dinnan, dama Arhaan ya bata address din wajen.
Waje ne mai kyau inda sai dan wane da wane ake kaiwa, ba kananun kudi ake kashewa duk wanda aka kai wajen ba, dan kuwa har karatun boko dana addini ake koya masu a wajen. Shiga sukayi suka cika bayani kafin aka kaisu wani waje suka jira bada dadewa ba saiga Ya T an fito dashi, hankalinshi kwance babu alamar wahala a tattare dashi, sai ma wani hankali daya fara yi.
Har kasa ya duka ya gida Baba da Inna kafin Habiba ta danyi hugging dinshi, she missed him. Dan dukan kanta yayi cikin wasa, "Ke kuma wannan yarinyar mara magana yaushe kika dawo?" Dukansu sukayi dariya.
Hira suka taba ba laifi har sunzo zaus tafi yace "Ina wannan rigimarmiyar? Ita bata zuwa ta duba ni ko? Ko dan mijinta ya kawo ni nan? Kice ina missing dinta." Dariya suka karayi kafin Habiba ta tabbatar mashi da ttabbaszata isar da sakonshi wajen Sakina.
Gida ta maidasu kafin ta kallesu tace, "To Inna ku kwaso kayanku, amma dan Allah wanda kadai zamuyi amfani dasu, komai da ake bukata zan siya." Hakan kuwa akayi, kayan sakawa kadai suka dauka suma banda tsummomi. Dillalin daya samar mata gida shi ya samo mata interior designers sukaje suka cika gidan da furnitures, kayan kitchen da kuma sauran kayan kwalliyar gida. Ita kanta batasan kudin dake account dinta ba, all she knows is karamar kyautar kudin da ake mata itace ta five mil, dan akwai wata minister data taba bata 20 mil nan take. Kuma bayan wadda ta daukota duk wacce tayi wani abu da ita sai tayi mata kyautar kudi, it's dirty, she knows.
Dare nayi suka yiwa su Maman iliya sallama suka koma sabon gidansu. Dukda taurin zuciya irin na Inna amma saida taji babu dadi, koba komai dai an dade ana tare. Saida sukaci abincin dare kafin ta zame ta zauna kasa. "Inna, Baba, nasan baku nanku cike yake da tarin tambayoyi a kaina, ni daku munsan kudin aikatau bazai taba yiman wannan hidimar danake ba. Inna zan baku labarina, abunda ya faru dani bayan barina gida." Tiryan tiryan ta fara basu labarin irin rayuwar data tsinci kanta ciki, wani abun takanji nauyin fadinshi gaban Baba amma koma miye su sukaja masu daga ita har Sakina, she's not blaming them, amma kuma sune sila. Data gama kuma ta dora da ainihin labarin Sakina har saida ta kawo karshe.
"Ba zamu dora laifi a kanku ba, most especially, ke Inna. Munsan cewar wannan kaddarar mu ce, kuma no matter how bawa yakai wajen wayau bazai taba kaucewa kaddarar shi ba. Haka Allah ya rubuto mana, koba aikatau ba dole zamu bar gida. Sauran kudin dake account dina, Baba zamuje a nemi shago Babba a bude maka, motar hannu na itama zan baka. Inna ke kuma, zaa saro maki laces da atamfofi sai ki rika saidawa cikin gida. Shi kuma Ya T idan ya dawo, zan maida shi makaranta kuma a tambayeshi sana'ar me yakesan yayi sai a bashi jari. Inna burinki ya cika ko? Zaki daina wahala ko? Da wannan fadan da kikeyi dasu Maman iliya da safe. Ina dai komai ya kare? Ko akwai aabundakike bukata?"
Ko Baba da yayu shekara aru aru tare da Inna bai taba ganin tayi kuka irin wanda takeyi yanzu ba, shima bawai dan bayaso yayi kukan bane, amma yadda take kukan ba karamin tada mashi da hankali yayi ba. Kuka ne take har kasan zuciyarta, babu inda baya rawa a jikinta. Abu daya take furtawa, "Babu wanda yaja masu wallahi sai ni, duk nice naja." Nadamar duniya babu irin wacce bata shiga ba.
Lallashi babu irin wanda Baba da Habiba basuyi amma Inna saida tayi kukanta har ta gaji, murya a disashe ta kalli Habiba tace ta kira mata Sakina zasuyi magana. Dialing number din Sakinar tayi, saida ta kusan tsinkewa kafin ta jiyo muryar Sakina a hankali, cike da damuwa tana furta, "Beeba to yaya? Inna masifa taita maki ko? Koma kina hanyar Abuja already? Nasan da kin bata labari saita koreki."
Hawaye Inna ta kara sharewa, kome sukace bazata ga laifinsu ba. "Sakina gulma ko? Ba na hanaki gulma ta ba?" Nan da nan jikin Sakina ya dauki kyarma, ita batama gane muryar Innar a dasashe take ba.
"Inna dan Allah kiyi hakuri. Ina yini? Dan Allah Inna karki daki Habiba, wallahi bata da laifi, asiri suka mata. Kinji Inna?" Sai kuka kuma, nan Inna ta kara fashewa da wani kukan, wato yaranta har sunsan she will never understand them. Kaico ita.
Kamar a mafarki haka Sakina taji Inna na kuka tana bata hakuri, kuma ta roketa akan gobe tazo dan Allah ta ganta. Saida suka gaisa da Baba kafin Habiba ta kashe wayarta. Kowa dakinshi ya nufa ya kwanta, dukda dai bawai an ida kowa kayayyakin gidan bane, amma sun kawo gado da curtains. Cikin dare saida Baba ya rinka bawa Inna hakuri kafin ya dora da nasifa yana nusar da ita akan dalilin wadannan abubuwan yasa baiso sukaje ba amma ta kafe. Shi kanshi saida ta roki yafiyar shi.
Sai bayan Azahar Arhaan ya dawo daga wajen aiki kafin suka nufi hanyar kaduna, Sakina had never been this eager taga Inna kamar yadda takeji yau. Dan cikinta har ya fara tasawa kadan ba laifi. Address din da Habiba ta basu shi sukabi ya kaisu har gidan.
Da Sallama suka shiga Sakina na rike da hannun Arhaan, Habiba ce ta fito fuskarta dauke da murmushi. Gidan yanzu babu inda baa gama kammalawa ba, dan tunda safe masu aiki sukazo suka ida, dan har girkin rana yau a gidan sukayi ba siya akayi ba. Iso ta musu cikin gidan tana ta jan Sakina akan wai ita dai ko kasan teku zaa kaita tayi rayuwa bazata taba yin haske ba. Dan zungurinta Sakina tayi kafin tace "Haba Yar Baka, ke har kinada bakin magana?"
Habiba ji tayi kamar ta kurma ihu, a haka suka shiga. Saiga Inna ta fito da hijab jikinta, har kasa Arhaan ya fuka ya gaidata ta amsa cike da jin kunyarshi, dan ta tafka abubuwa a gabanshi. Baba ne ya fiti shima sukayi musabaha da Arhaan kafin yace ya zauna. Sakina dai tsaye tayi tana kallon Inna, dan gani take kamar yaudarar ta zaayi.
Har inda take Inna ta karasa, "Zo nan yar banza, badai gulmata kike yi ba?" Dan dukanta tayi cikin wasa kafin tayi hugging dinta, farin cikin da Sakina bata tabaji ba shi taji a wannan lokacin.
Cikin gari aka aika aka siyo ma Sakina su zogale da abubuwan gargajiya. Sai janta suke wai yau Sakinar nan mara jin magana da tsabar masifa itace keda ciki. Kunya duk ta kama Arhaan, Sakina kuwa ko a jikinta. Nan sukaci abinci sai gab da maghrib kafin Baba ya takura akan su tafi, suna barin gidan taga Arhaan yabi wata hanya ba hanyar fita gari ba.
"Arhaan ina zaka kaini kuma?" Ta tambaya tana kalle kallen titi.
"I know you miss him, fada ne kawai bakya yi. Zan kaiki wajen Ya T." Shiru tayi ita dai, dan gani take kamar ba can zasuje ba. Sai kuwa taga sunyi parking a rehabilitation camp din. Dukda yawan fadansu da Ya T, Allah yasani wallahi tana sanshi, kuma yanzu haka ta yafe mashi tun ranar da abun ya faru. She wants to see him.
Sun gama cika duk wasu bayanai, a nan Arhaan ya biya wasu kudin akan a bawa Ya T special care kuma yanaso inda hali a sakashi a makaranta yayi joining KASU, dama WAEC dinshi is not bad yanzu jamb zaiyi kawai ya fara, idan yanayi a gabansu sunga hankalinshi ana iya maidashi gida. Gaban Sakina akayi komai ya biya kudin kafin ya kira Habiba akan ta kawo masu waec result din Ya T.
Basu dade ba wajen aka fiddo masu da Ya T, Sakina tana ganinshi tama manta da wani tanada ciki ko kuma Ya T din haushinta yakeji. She moved forward and hugged him, sai hawaye. "Allah Ya T nayi missing dinka sosai, dan Allah kayi hakuri kaji? Inna ma tace ta yafe man."
Breaking hug dinsu yayi kafin ya kamo kunnenta, "Allah ya soki wancan mijin naki ya kawoni nan, kuma yanzu na daina rashin ji, amma da sai kin fada man ko suwaye. Me nace maki akan ciki? Sakina bakya jin magana ko?" Cikin wasa yake mata maganar yana riko kunnenta. Dariya suka fashe dashi a tare. Gaisawa sukayi cikin girmamawa shida Arhaan, basu wani dade sosai ba a wajen suka tafi.
Basuyi wani nisa ba Sakina ta juyo tana kallon Arhaan, he became uncomfortable, "Anina kallon fa? Ko twin kikeso a samar wa na cikinki?" Dariya yayi ita kuma ta dan dakar mashi shoulders.
"Arhaan tunani nake how my life would've been without you. How crumbled I would've been with no one to lift me up. I've always had hopes for Ya T, babban burina bai wuce ace ya zama that kind of big brother everyone has ba. And you fulfill my wish without me even voicing it out. Ina sanka Arhaan, ina sanka sosaiiiii." She drawled and planted a rough kiss on his cheeks.
Da gangan ya jujjuya motar saman titi ta fara ihu shima yana biye mata, "Anina zaki saka muyi accident mu mutu bamuje munga Mama ba."
Dariya tayi tana riko hannunshi, "Tunda Mama bata barmu ba, mu babu abunda zai samu barta. 15 yaran nan sai na maka su." Hancin ta ya lakata cike da wasa, a haka suna fira suna dariya har suka karasa Abuja.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top