BABI NA SITTIN DA BIYU
Dube dube ta farayi, can dai ma ta dage rigarta tana laluben cikinta, ita kam bataji komai ba in ba dan kumburin da yayi mata daga kasa ba, shima ta alakanga shi ne da kila ulcer yake damunta tunda bawai cin arziki take ma abincin ba. "Inna ciki kuma? Ni banda ciki ai, me kika gani?" Gaba daya jikinga babu inda baya rawa, burinta bai wuce ace exaggeration bane kawai irin na Inna. Ta ina ma zata fara yin cikin?
"Ni keda cikin, nace ni keda cikin dan ubanki!" Dungurinta Inna tayi kafin ta juya ta rufe dakin gam yadda ko wani ya shigo bazai iya kwatar Sakina a hannunta ba. Dan yau ta saka ma ranta ko ita ko Sakina cikin dakin nan amma dan dole sai ta fada mata abunda ya hadasu da Arhaan har ya barta gidansu tsawon wata biyu.
Baya baya Sakina ta fara ganin Inna ta nufota kamar wata yunwataccen zaki. "Inna ki tsaya kiji, dan girman Allah karki dake ki, wallahi zan miki bayanin komai. All I know is inma cikin gareni to wallahi na Arhaan ne, Inna ni ba yar iska bace, inma iskancin zanyi bazanyishi da aure na ba Inna, kimun rai dan Allah. Kuma ni banma da wani ciki wallahi." Kuka take sosai tana kara murza cikin da zunmar ta batar da wannan tudun daya mata amma duk a banza.
Maruka biyu Inna ta sauke mata su a jere, ganin yadda ta kara rikicewa sai ta bata tausayi. Kujerar dake dakin Inna ta zauna kafin ta nuna mata kasa kusa da kujerar tace ta zaune. Jikinta babu inda baya rawa haka ta zauna tana kuka har kyarma takeyi. Duk tabi ta fita hayyacinta, babu abunda yafi tada mata hankali kamar yadda zasu kwasheta da Arhaan. Ta ina zata fara ce mashi tanada ciki?
"Sakina ki natsu ki fada man gaskia, cikin wanene jikinki? Kuma karki kuskura kice man ba ciki ne dake ba dan ni ba yarinya bace tun kafin na haifi Tukur nasan wacece mace me ciki dan ubanki."
"Inna wallahi tallahi ki yarda dani, Inna cikin nan na Arhaan ne bana kowa ba. Inna dama zan iya sabama Allah da aure bisa kaina? To me na nema na rasa a wajenshi da zan mishi wannan sakayyar? Dan Allah Inna kiman rai."
"Naji wannan na yarda, amma dan ubanki yau dole ko zaki mutu sai kin fada man dalilin dayasa ya maido ki gida har tsawon wata biyu bai waiwayeki ba, laifin me kika mashi? Sakinah ki fada man gaskia tun muna shaidar juna dake."
"Ni kaina bansan me na mishi ba Inna, nidai nasan Mamarshi tayi accident aka tafi da ita egypt tin daga lokacin ya daina kwana gida ko magana baya mun, ranar kawai yazo yace mu taho kaduna zaizo wani aiki sati daya, shine fah."
"To kuwa indai haka ne dan ubanshi yazo ya dauke ki duk inda zai kaiki yaje ya kaiki, dan bazanyi renon dan wani shegen ba cikin gidana. Maza kirashi!" Ta daka mata tsawa.
Jiki na rawa Sakina ta kara dialing number din Arhaan amma as usual akayi rejecting dan ya riga da ya sakata blocked list. "Inna bazai dauka ba indai da wayata ce, kawo taki na gwada kira naga." Cikin zafin rai Inna ta ciro wayarta daga cikin zani ta mikawa Sakina.
Zuciyar Sakina a hannu haka ta rubuta numbers din Arhaan tayi dialing, sai a third call din kafin ya dauka murya can kasa yayi sallama kamar wanda bayasan magana. Wasu fresh sizzling hawaye ne suka fara cascading saman cheeks dinta, she has missed his voice more than everyone and everything in her life.
"Ar..ha..an.." muryarta har wani daukewa tayi, idea din bai taba kawo mata ba ai da tuni da sayi new line ta kirashi.
Jin muryarta yayi tun daga saman kanshi har tafin kafafuwanshi. Dama yana falonshi zaune shi kadai abun duniya ya isheshi, kamar sabon abun alamari haka yaji abun amma ya dake. Kafin ya kashe call din yaji ta fara kuka tana rokonshi "Dan Allah badan ni ba Arhaan, dan Allah ba dan ni ba, dan Allah kuma dan Mama ka taimaka mun kazo, wallahi Inna zata kasheni bata yarda dani ba, nasan yanzu zaka kashe ko? Arhaan..." bata ida nagana ba taji dut ya kashe call din. Bata san lokacin data kife kanta saman cinyoyin Inna ta fara kuka ba, dan kuwa tasan ko tsafi take bazai kara daukar call dinta ba.
Ranar haka ta kwana tana kuka, abinci kuwa saida Inna ta mata tsaye kafin taci shi. Da safe Inna ta tasa ta gaba suka wuce asibiti domin aga wai shin akwai cikin ko babu? Idan akwai kwana ko watanshi nawa da kuma lafiyar abunda yake cikin. Bayan dukkanin awanni aka gane cewar cikin satinshi tara, that is wata biyu da sati daya. Ita dai Sakina ba yabo ba fallasa, Inna ma dama baka gane cikinta.
Har adaidaita sahu ta saukesu kofar gida babu wanda yace wa kowa komai, Sakinah ce ta tsaya biyan mutumin dan ita Inna har tayi gaba. Tana juyowa kamar almara taga motar Arhaan yayi parking daidai inda ya ajeta ranar daya maidota gida. Ya fito daga motar ya juya mata baya yana magana da wani yaro alamun kiranta yakeso ayi.
Wasu hawaye ne suka zubo mata, daga kadan kadan sai shar shar kuma ta kasa controlling dinsu. A hankali take takawa har takai inda yake tsaye yana wa yaron magana, yaron na ganinta yace ai gama Sakinar nan. A hankali Arhaan ya juyo, suna hada idanu ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciyar da baisan da ita ba.
Kuka ta fashe dashi mai ratsa zuciya, bata jira wata maganar shi ba tayi hugging dinshi hade da fashewa da wani kukan. Shidai baiyi hugging dinta back ba bai kuma rabata da jikinshi ba. Shi kanshi bai taba tunanin haka yake da kafiya ba sai yau. Wata zuciyar naso ya yafewa Sakina wata kuma bataso. Saida ta gaji dan kanta kafin ta raba jikinsu tana kallonshi, har yanzu hawayen sun kasa daina zubowa.
Tausayi ta bashi, ganin yadda duk ta kare ta lalace, he could imagine voice din Mama na mashi magana 'Arhaan haka ka mayar mun da Sakinah? Mugunta ko Arhaan? To nima babu ruwana dakai.' A hankali yakai hannayenshi yana share mata hawayenta.
"To kukan ya isa haka, ba gani nazo ba? Meya faru?" A hankali yake mata maganar, dukda dai soyayyar dake tsakaninshi da Mama tasha bamban da irin wacce Sakina ke mishi, he could imagine yadda takeji akan rashin sa.
Takardar result din kawai ta mika mishi, a zuciyarta kau duk wata addua data taba sani tun yarintarta har girmanta babu kalar wacce batayi ba. A hankali ta fara ganin face dinshi ta chanza, ita dai She's certain cikin nan na Arhaan, but if he wants he can reject it har sai ta haihu a masu DNA test da yaron ko yarinyar.
"I cannot accept this pregnancy, Sakinah. I just can't." Wani irin heartbreaking step tayi taking back tana kallonshi tana girgiza kai.
"Karka hukuntani a haka Arhaan, yadda kamun ma yanzu ya isa wallahi, na horu dan darajar Allah. You and I know it, ni kadai naje gidanka, Arhaan kamun adalci."
"Anything can happen, koda kuwa a gidan nawa ne." Abunda ya furta kenan kafin ya nade takardar ya saka aljihu. Wani part a zuciyarshi yana fada mashi akan ya daga Sakinah sama ya nunawa Allah ya gode mashi dan kuwa shi kanshi yasan baby nashi ne, wata kuma na fada mashi ya zaayi ya yarda da maganar mazinaciya musanman ma akan ciki? He just can't.
Ya T ne ya taso daga inda yake kwana yazo har bakin kofar gida sai yaga motar da bai gane ta ba, cike da tangadi haka ya karasa wajen motar ya tsaya sai can ya lura da Sakina ce da Arhaan. Ganin Arhaan yayi hanyar motarshi zai shiga yasa shima ya juya zai wuce gida dam yau ba daidai yake jinshi babu imani tattare da lamarin shi.
Cak ya tsaya kamar daukewar wuta jin kalmar da Sakina take furtawa Arhaan din cikin wani gunjin kuka. "I was raped Arhaan, months before we got married, shiyasa you met me not as a virgin. Ka yarda dani, cikin dake jikina naka ne ba na kowa ba." Wani irin kukan kura yayi ya cakumo wuyan Sakina tun kafin shock din maganarta ya gama kama Arhaan balle har ayi maganar sakinshi.
Ko saurarar magana daya daga bakinta Ya T baiyi ba dukanta ya farayi ko ta ina, babu alamar imani a tattare dashi. Ciki da Rape? Duk yaushe akayi wadannan abubuwan bai sani ba? This means kafin ma tayi aure she was raped basu sani and yanzu duk irin warning din daya mata kar tayi ciki saida tayi? Na rape din yafi komai kona masa rai dan kuwa na cikin yasan babu yadda zaayi shine baida gaskia.
Tun tana ihu tana rokonshi gafara akan ya taimaka ya kyaleta zata mashi bayani har ta yi shiru idanunta fixed on Arhaan da yake kallonsu ba tare daya furta kalma ko daya ba. Duka jina jina haka Ya T yama Sakinah, zagi kuwa babu irin wanda bata sha ba, masifar da yake bai wuce sai ta fada mashi su ubanwa sukayi raping dinta ba yaje ya hallaka su, to itama bata san inda suke ba ko sunansu bata sani ba.
Kwallo yakeyi da ita tako ina, jikinta babu inda bai fashe ba amma Arhaan ko motsi baiyi daga inda yake ba, yadda take kallonshi shima idanshi ko sau daya bai motsa daga inda take ba. Inna tayi zagin tayi magiyar amma ko gezau Ya T baima nuna yasan akwai mutanen dake zagaye suna bashi hakuri ba, maganarshi daya sai Sakina ta fada mashi wanda sukayi raping dinta.
Wata tsawa ya sakar mata hade da harbi da ita inda kafarshi ta samu cikin nata, wani gigitaccen ihu ta saki ko minti biyu baayi ba sai ga jini ya fara bin kafafunta. Taji damshin jinin, kallon Arhaan tayi hawaye na kara zubo mata. A hankali tayi mouthing "I'm losing my baby, your very first child in the world." Babu sauti, amma ko kalma daya baiyi missing ba, baisan lokacin daya ciro wayarshi ya kira DPO din dake area dinba hade da yan NDLEA.
How about a double update😁
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top