BABI NA SITTIN DA BAKWAI

Zarya takeyi cikin falon gidan, sai kai kawo take ta rasa inda zata saka ranta, masifar da Hajiar take mata ba itace abunda yake tada mata hankali ba, abubuwan da take fada mata sunfi komai daga mata hankali. Kwana biyu kenan da barin Habiba cikin gidannan, amma sam abun bai kawo mata na ta fadawa Hajia halin da ake ciki ba sai yau.

"Haba Hajia hauwa, ban taba tunanin zafin ranki yakai na har ki aikata irin wannan abun ba. Wane kalar kashedi ne ban maki ba akan yarinyar nan? To yanzu dana kira Malam cewa yayi inhar aka bari ta hadu da wani daga cikin danginta to fa asirin mu na kanta wanda zata mance da ko ita wacece zai kare, daga nan kuma wanda kikayi mata dama rawa yakeyi yanzu, har gaba da abada tabar harkar nan tamu. Sai kisan nayi, nidai banda asara, ke kika jiyo." Koda Hajia ta gane cewar Maama ga harkar data saka Habiba ba karamin yaki sukayi ba, dan kuwa Habiba kowa rububinta yakeyi, dan dole Maama ta yanki wasu kudade masu tsoka ta bawa Hajia kafin ta tsaida gobarar.

Maama palming face dinta tayi, duk ta gama rikicewa, "Nasan insha Allahu ma babu abunda zai faru, bazata hadu da kowa ba. Ba kince can cikin garin kaduna aka daukota ba? Inada tabbacin hankalinta bai taba bata kaduna, ko zata buga saidai su lagos ko tabar kasar gaba daya. Yanzu nikam ya zanyi da her excellency? Sai kirana take akan taji in yau din zataje." Hankalinta duk ya gama tashi, taga samu kuma taga rashi kururu.

Wani irin tsakin takaici Hajia ta saki, "Wannan kuma duk mai sauki ce, kice mata yarinyar ce bata jin dadi, ta turo maki kudin jirgin da komai zaki idan taji sauki zaki turota da kanki. Harda new tips duk zaki ma koya mata." A haka sukayi sallama, nan take Maama ta kira matar ta shaida mata, bata nuna rashin jin dadinta ba nan take ta turo ma Maama makudan kudade akan a kaita asibiti da kuma sauran expenses siyayyar da takeso kafin tazo.

Daya daga cikin yaranta dake lagos ta tura ma picture din Habiba akan ta saka a fara bincika mata ita, a nan kaduna ma ta tura, hankalinta kwata kwata bai taba kawo mata Abuja ba. Dama gidan wata hajia zataje, nan take ta sabi gyalenta ta fice. Dukda yanayin da Saahir yake ciki yana damunta, amma she has nothing to do about it.

A bangaren Habiba kuwa, kwananta biyu a cikin Abuja amma kullum cikin gararamba take, ita bata yarda da hotel ba, gani take idan har taje ta kwana a hotel to tabbas dole wani ya alakanta ta da mummunan aiki. A ga budurwa kamarta, ga mota kuma ta shiga hotel? Ita kanta bata yarda da kanta.

Cikin mota take kwana, kuka kuwa babu irin wanda batayi ba, burinta bai wuce ta tuna ita din wacece ba? Dan tawa kanta alkawari ko a kufai iyayenta suke zataje ta zauna dasu. Saidai ta shiga wannan eatery taci abinci ta koma wancan taci.

Wajen 9pm ta tsaya bakin wani eatery, ta sayi abincin amma bata ma iya cin abincin, duk wata damuwar duniya babu irin wacce bata shiga ba. Dakyar taci lomar da bata wuce biyar ba kafin ta biya kudin abincin ta fita ta shiga motar ta. Yau a nan zata kwana, dan she thinks of no where but there.

Ganin yanda mutane ke shigowa suna farin ciki da annushuwa, wasu families ne, wasu newly weds ne, wasu kuma saurayi ne da budurwa, wasu ma friends ne ko abokan kasuwanci, na families din yafi tsaya mata a rai. Haka kawai taji duk wani tarin damuwa ya dawo mata cikin rai, kuka ta farayi kamar da bakin kwarya. Jikinta babu inda baya kyarma. Saahir takeso tayi magana dashi amma ba dama. Duk tunaninta bai wuce inda zata samu matsugunni ba. Babu wanda xai taimaketa a haka yanda take dan kowa zai kawo ma ranshi yar iska ce. Idan tace ta kama gidan haya kuwa nan ma bazata tsira ba, idan tace ta saida motar tayi basaja akan bata da arziki ina iya cutarta tunda ba wai kan dukiyar ta sani ba.

Bata da madafa, haka zalika bata da kowa sai Allah sai kuma Saahir, shi kuma yanzu ya juya mata baya. Ana haka taji an hasketa da fitilar mota, a hankali ta dago rinannun idanunta ta saukesu akan wacce ke gaban motar da kuma namiji wanda shi yake tukin alamar mijinta ne.

Fitilar ya kashe ita kuma ta cigaba da kukanta, no one in this world cares, dan haka itama bata damu da abunda kowa zaice a kanta ba wai dan an ganta tana kuka. Kowa dai tashi ta fisheshi.

Tunda Sakina take a rayuwar ta bata tabajin faduwar gaba ba irin wadda taji a yau. Parking sukayi Arhaan mistakenly ya haske matar dake cikin motar, alamu sun nuna kuka takeyi because she can see the illumination.

"Arhaan bazamuje mu duba matar can ba? Kodai wani abu ya faru bata da mai taimaka mata?" Abunda Sakina ta furta kenan bayan sun fito daga cikin motar. Tun da tayi sallar maghrib gabanta ke faduwa, hakan yasa tace ma Arhaan suyi zamansu a gida suci dinner ba sai sunje restaurant ba amma yace shi Aa, he's going to treat her like a queen, because she deserves it.

Hannunta ya riko in a soothing way, "Anina mutane can be conniving, kiga mata cikin waccen luxurious motar kice taimako take nema? May be dai family issue ne ko? Allahu a'alam, koma miye Allah ya kawo mata mafita." Ameen ta furta can kasan ranta, a haka sukaje sukaci abincin, hira yake janta dashi a hankali amma Sakina gaba daya hankalinta yana kan matar dake cikin motar can, dan kuwa yanzu da suke zaune cikin restaurant din she gets a clear view of her. Kalar kukan da takeyi kuka ne irin wanda yake kunshe da dukkan bakin ciki da tarin damuwa. Kukane da bawa yakeyi a lokacin da yakeji a ranshi baida kowa kuma baida komai.

A daddafe suka gama cin abincin, har sunzo zasuyi hanyar motarsu Sakina ta kalli Arhaan tayi rau rau da idanu, "Arhaan dan Allah naje wajenta? Five minutes yayi yawa. Dan Allah Arhaan, I've once been in her situation, it kills to know you have no one in this world. I know her pain, dan Allah naje?" Hawaye ne ke barazanar fitowa daga idanunta.

A hankali Arhaan yayi hugging dinta yana patting bayanta, "I know you've been through hell, but you have me now, Anina. Cry not, muje tare dake nima na ganta." Hand in hand haka suka taka har gaban motar nan.

A hankali Sakina tayi knocking glass din, ssaidatayi knocking sau biyu, with each knock kuwa bugun zuciyarta yana karuwa. Kamar bazata budeba sai kuma ta bude, ganin matar da namiji ya tabbatar mata da mata da miji ne. Glass din ta sauke gaba daya, a take sukayi four eyes da Sakina, wani irin horrific look sukewa juna.

Sakina ce ta fara girgiza kai, tana kara damke hannun Arhaan da yake cikin nata. Wannan bazata taba zama Habibar ta ba, wannan ba Habiba bace. Habiba bata da mota, Habiba bata shiga irin wacce ke jikin wannan matar. Yes it's not a bad dress, amma kayan dake jikin matar nan ba na Habiba bane. Kuma if she can remember a matsayin yar aiki aka kai Habiba ba matsayin matar gida ba.

"Anina, meya faru?" Abunda ya furta kenan, ganin kallon kallon da sukewa juna, tashin hankali karara saman faces dinsu.

Sai a lokacin Sakina hankalinta ya dawo jikinta, kuka ta fara iyakar karfinta, "Arhaan Habiba ce, Habibah ta, my one and only sister. She's the only one I have. Tell me I'm hallucinating, because Habibah doesn't look like this, she doesn't have all this luxury." Bata jira amsar shi ba taje ta bude kofar mota, inda Habiba take zaune saman drivers seat babu abunda yake motsi a jikinta face hawayenta da suke zubar da ruwa, she was stilled. Wasu fresh memories ne ke dawo mata cikin kai kamar an kunna film. Faces dinsu take hangowa time din da suna yara har lokacin da ta tafi aikatau.

Cikin kuka Sakina ta fada jikinta, sai a lokacin Habiba ta saki wata irin atishawa kafin tabi jikin Sakina luuu... Dakyar Arhaan ya lallaba Sakina ta koma mota kafin ya samo matan restaurant din suka kama mashi Habiba suka sakata bayan motarsu. Duk abunda ke cikin motar na Habiba saida ya daukoshi ya kuma biya daya daga cikin masu aiki wajen ya tuko mashi motar Habiba zuwa gida.

Tunda suka kama hanya Sakina take kuka, ya dade dajin labarin Habiba, tunda ta dawo gida kusan kullum sai tayi kuka akan ita dai Habiba, abun is getting out of hand, ko wata kasa aka kaita aikatau yaci ace ta dawo balle cikin kaduna. Duk wani memories dinta dana Habiba babu wanda bata fada mashi ba, and he knew how she means to Sakinah.

Koda suka isa gida Sakina ta kamawa Arhaan suka shigar da Habiba har cikin dakin baki dake part din Sakina. Tanaji ya gama shigo da kayan amma ko kyafta ido batayi ba daga jikin Habiba, hannunta cikin nata. Sai after almost an hour kafin Habiba ta fara farkawa, a lokacin babu abunda bata gani cikin idanunta, kuka ta fashe dashi a time din data ganta kusa da Sakina, because she thought it was all a dream.

"Baby Sakky..." sunan da take kiran Sakina kenan duk ranar da sukajin annashuwa. Dakyar Arhaan ya lallabasu suka daina kukan kafin ya fita yabar masu dakin. Sakina ce tasa Habiba ta shiga tayi wanka, saida tayi wanka ta rama sallolinta dake kanta maghrib da isha kafin suka zauna, kowa has alot of questions to ask.

"What kind of life have you lived? I can see, you've changed, everything has changed." Abunda suka furta kenan a tare, kafin aka fara wannan ta fada wannan ta fada. Karshe akayi settling akan Sakina ta fara fada, sunsha kuka har sun godewa Allah. Habiba couldn't believe all that happened to Sakinah, can tayi shiru kafin ta tuna ranar da sukaje ansar dinki tabbas sunga mace bakin shagon, had it been she knew, da basu wuce ba.

She can't believe Sakina har tayi aure hada ciki wai, dariyar hauka suka fara, sai su rungume juna, ayi kuka ayi dariya sai can kuwa suyi ihun jin dadi. Sai bayan Sakinah ta hado masu custard sunsha kafin ta kamo hannun Habibah.

"Habibah what happened to you? Tell me the life you lived, you don't look like your old self."

"I forgot who I was the moment I stepped my legs cikin gidan matar nan Sakina, I can remember bayan ta kawo mun wani lemu nasha from then, saidai naga sunana Habiba Abdullahi Bello amma bansan waye haka ba..." tiryan tiryan ta fara bawa Sakina labarin rayuwar da tayi da kuma irin kasashen da taje, da irin kayan data siyo masu tare dukda cewar batasan tanada yar uwa ba a lokacin, she just felt that akwai wani missing part of her.

Cikin labarin zata tsaida ta bude akwati ta fiddo mata kayan suyi dariya suna admiring kayan with tears in their eyes. Har karshe inda Saahir ya koreta da kuma two days da tayi a Abuja tana yawo har Allah ya hadasu. Kuka suke suna rungume da juna. Babu wanda yaja masu irin wannan rayuwar face Inna, amma they believed kaddarar su ce, koda sunso ko sunki dole hakan ya faru.

Tun suna kuka har abun ya koma labari, sunyi dariya sun kara shedding wasu tears din kafin da bala'i Habiba ta kora Sakina wajen Arhaan wai she wants to sleep. Sakina na fita dakin ta shiga toilet tayi kuka harta gaji kafin tazo ta fara sallah.

Sakina a hankali ta turo kofar dakin Arhaan ta shiga, a zaune ta ganshi kan gado ya tasa laptop gaba daga gani aiki yake. Koda taje inda yake hawa kan gadon tayi kafin ta dora kanta saman laps dinshi. Kamar yadda yake al'adarsu haka ya sunkuyo yayi kissing lips dinta softly before he uttered "You don't have to talk about it if you don't want to. Just get some rest, I love you kinji Anina?" Da murmushi kan face dinta, a tare hands dinsu suka kai saman cikinta suna fondling a hankali. They love themselves, most especially, the child between them.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top