BABI NA SHA BIYU

Kamar daga sama haka taji muryarshi, saurin dagowa tayi tana kallonshi kafin ta tuno abunda ya faru shekaran jiya. Gulping back tears dinta tayi tana share hawayenta, but the tears were so stubborn to abide.

"Can I have a seat?" Ya tambaya, dan ganin yadda ma ta rude ta kasa ma tsaida hawayen balle ta amsa mashi tambayar shi ta farko.

Koda ya zauna Habiba kallonshi kawai tayi ta kauda kai, dan ita kanta batasan what she's feeling in her heart ba, all she knew is she doesn't need any feeling of empathy towards her; she has lost that from the incipient.

Koda ya zauna shi ya rasa abunda yake mashi yawo cikin kai, he is supposed to be angry at her for spilling a drink on him, but here he is; feeling as if a droplet of fire being dripped on his heart with every tear she shed.

"Bazaki man magana ba? Ko tsoro na kikeji?" Shi kanshi mamakin kanshi yake, all he knew is he hates seeing a girl crying, dan kuwa bayasan ma tunanin abunda zai sakata kuka. Babban abunda ya tsana bai wuci ganin mace na kuma ba, dan yasha ganin macen da yafi so a rayuwarshi na kuka; kuma it wasn't a feeling to remember.

A hankali ta juyo tana kallonshi, tana goge hawayen amma stubborn ones din were still streaming in oceans. "Ni bana tsoronka, amma aren't you still angry at me? My feet still hurts uno?" Ta tambaya tana dago kafarta mai ciwo tana dan jujjuyawa, she could welcome hundreds of this pain than what she's feeling in her heart.

Ganin yadda take juyo kafarta tana kallo ga wasu hawayen na zuba a idanunta yasa yaji tausayinta ya kamashi, "Ni bana fushi dake, kece ya kamata kiyi fushi dani; nine silar ji maki ciwo ko? Was that the reason you were crying?" Ya tambaya a hankali, dreading to hear her answer, dan he would be angry at himself if shine silar sakata wannan kukan mai taba zuciya- dan the last abu da yakesan yi a rayuwarshi shine ya saka mace kuka.

Saurin girgiza kai tayi with a fleeting smile on her lips, "Aa fah, wannan ai is a minor pain, I could welcome thousands of it than what I'm feeling in my heart. Kasan irin feeling dinnan, wanda abu yana damunka amma bazaka iya cewa menene ba? But you surely knows that something is definitely wrong with you?" ta fada tana langabar da kai, wasu hawayen na kara zarya saman kuncinta.

Ji yayi kamar ya tayata kukan, he could relate to this feeling more than anyone in this world. Haka kawai yaji zuciyarshi na karyewa, dan yasan irin abun nan babu abunda ya kaisa paining. "I tagged that as the worst feeling one could ever feel. Had it been kasan abunda ke damunka da sauki, I can relate to your pain. But you know what? Idan kikayi voicing out abun zakiji dadi sosai ba kadan ba; I was once a victim," ya fada in a soothing way, yana kallonta-kallo me cike da tausayi da wani feeling da shi kanshi bai sani ba. Sai yanzu yake lura da yanayin skin colour dinta, ga sanyi halinta wanda kallon farko ma zaka iya ganewa.

Leaning back on the chair tayi da dan murmushi wanda yake sabo a gareta, "Sunana Habiba, but you can call me Beeba," haka kawai ta samu kanta da furta sunan da Ramcy ta rada mata.

"Toh Beeba, sunana Saheer. Nasan fadin abunda ke cikin ranki zai maki wahala, why not ki kira gida ki fada masu?" Yayi offering again, dan yasan not everyone like confiding in strangers-he is a testifier on that.

Kalmar gida ta tado mata da wata irin maguwar faduwar gaba, dan ita har ga Allah tasan tabbas dole tanada iyaye, amma dan yanzu ace ta fadi koda sunansu ne bata iyawa balle har tace ga inda suke zaune. Lalube ta farayi cikin kwakwalwarta, amma iyakar tunaninta babu wanda zata iya pointing tace gashi shi dan-uwanta ne; kawai dai tasan ita yar aikin Hajia ce.

Wani kuka ne kawai ya kwace mata, fadin tashin hankalin data shiga bama zai iya faduwa ba. Wani irin zugi zuciyarta ke mata, ga wani tashin hankali da ciwan kai daya ziyarci kwakwalwarta. Girgiza kai ta shiga yi, hawaye wani nabin wani. "Wallahi bansan su ba, bansan kowa nawa ba, Hajia kawai na sani-sannan kuma nasan ni yar aiki ce."

Ganin yadda take kuka tana girgiza kai ba karamin taba mashi zuciya yayi ba. Shi duk a tunanin wani soft spot na zuciyarta da batasan tunawa ne ya famo mata-not knowing tambayarshi ce ta ganar da ita halin da zuciyarta da kwakwalwarta suke ciki.

"Dan Allah kiyi hakuri, bansan maganar da nayi zata zamar maki haka ba. Kiyi hakuri, kowa da tashi kaddarar a rayuwa, ke taki kenan," yayi magana a hankali, yadda ta kifa kai bisa laps dinta tana kuka was excruciatingly painful.

Dagowa tayi da rinanun idanunta ta saukesu a kanshi, kawai sai taji she can call him her family. "Thanks brother Saheer, It really means alot. Bari na shiga ciki," ta furta tana mikewa, dan kuwa she needs to be alone, bata yarda da brain dinta ba, dole ta fiddo mata inda takai iyayenta!

To lessen the tensed atmosphere; ya kalleta with a smile on his lips. "To Yar baka, banda kuka kinji?" Ya furta amiably, yana mikewa tsaye shima.

Yar dariya ta kubce ma bakinta, "Yar baka kuma? Ni ba baka bace. Bye Dan gayu." Tana fadin haka ta mishi smile kafin ta karasa cikin gida, a storm thundering in her heart, as a headache throbbed her head.

***

Sakeena triumphantly haka ta rika yawo cikin gidan, koda Aunty Halima ta tafi aiki saida ta gama share share ta wanke utensils din da sukayi using a breakfast kafin taci nata breakfast din. Koda Arhaan ya fito zai fita suna hada ido ta galla mishi harara, irin kallon zakayi bayani ya mata kafin ya wuce yayi tafiyarshi.

Wajen 1 Aunty Halima ta shigo gidan looking shagged and frazzled. Sakeena ta iske cikin kitchen tana gyaran kayan miya. Wani murmushi tayi kafin ta karaso cikin kitchen din "Kai amma Sakeena nagode maki sosai, yanzu da sai na dawo zan gyara gidan na fada ma girki kuma. Sannu kinji," ta furta gratefully, tana karasowa cikin kitchen din.

Dama ita kam aiki indai tayi niyyar yinshi to fa zata maka me kyau, aikin gidansu ne ta tsana kamar mutuwarta, shima sharar tsakar gidan, dan tana ganin kamar ta share ma kattin banza ne su Maman Iliya.

"Auntynmu sannu da dawowa. Su Kamal ba yanzu ba kenan?" Ta tambaya itama, tana mai jin dadin ganin Auntyn, dan kuwa she felt lonely being alone in this humongous house.

"Su Kamal sai 1:30 suke tashi, Sakeena. Bari nayi maza na dora abincin kafin Baban Shaheed su dawo, dan nasan dukansu da yunwa duke dawowa," ta fada kafin ta fara kiciniyar daura sanwar, dan ita a wani organization take aiki, karfe daya take dawowa gida.

Saida 1:30 ta kusa kafin Aunty Halima tayi gasping, tana mai dafe kanta alamun tayi mantuwar wani abu. "Sakeena, dan Allah ki taimaka kije ki gyara bangaren Arhaan kafin ya dawo, na sanshi da kyankyami; yana iya yaki kwana dakin idan ya sameshi yadda ya barshi. Amma fah sai kinyi sauri, kar yazo yaga ke kike gyarawa," Aunty Halima ta furta cikin girmamawa da sanin darajar dan Adam, dan ita koda wasa bata looking down on wadanda basu da hali.

Ajiye abunda takeyi tayi hade da wanke hannunta. "Gaskia Aunty kinaji da kaninnan naki. Kara man kwatancen wajenshin dan bazan gane ba," Sakeena ta furta with a smile on her lips, dan d'an lokacin da sukayi spending da Aunty Halima har sun saba, kasancewarsu dukansu masu saurin sabo da kuma surutu.

Saida ta mata kwatancen kafin ta tabe baki da yar dariyarta, "Ai bari kawai Sakeena, wani abun hada mugunta yaroncan yake man, dan yaga inaso ya zauna nan-kuma yasan daya fadawa Mama matsala daya shikenan zatace ya koma."

Murmushi Sakeena ta mayar mata a matsayin amsa kafin a ranta tace 'Ai dole, wancan gardin kuke sangartawa haka'.

Koda ta shiga bangaren, itadai duk iya tsaftar da Inna ta koya masu-to babu ko alamun mutum mai rai yana zauna wajen balle a samu kura ko datti. Kyal yake amma a haka ta kara share parlour da dakin tayi moping kafin ta kunna turaren kamshi. Towel dinshi ta dauka daya aje kan gado da niyar mayarwa toilet-sai a lokacin ta tuna bata wanke toilet din ba, gashi Aunty tace tayi sauri kafin ya dawo.

Gulping down lump tayi kafin tayi Adduar kada Allah yasa ya isketa a dakinshi, dan ita ta kawo kanta sai ya mata duk abunda yaga dama, kuma tasan dama da haushinta ya fita gidan.

Arhaan kuwa koda ya dawo har wata lahainiya yake saboda azabar yunwar dake cinshi, dan koda safe tsabar takaici ma haka nan ya tafi on an empty stomach.

Yana shiga direct dakinshi ya wuce, koda ya isa yaga dakin fes baiyi mamaki ba, dan yasan Aunty Halima data dawo aiki bangarenshi take fara gyarawa. Haka nan yaji kawai wanka yakesan yi, direct toilet ya shiga dagashi sai dogon wandanshi, dan kuwa ya cire rigar da vest ya wurgar cikin laundry basket.

Yana shiga kawai ya hangi yarinya budurwa tana wanke toilet din, sai yar wakarta take tana rausaya kadan kadan.

"Keh!!!" He roared, startling himself and her as well, duk sun daburce sun rasa inda zasu saka kansu.



Thank you.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top