BABI NA SHA BIYAR
With glassy eyes, haka take kallonshi, dan jikinta har rawa ya fara; ganin yadda ya murtuke fuska-tasan koda ace azara'ilu ne yazo daukar ranta kila ba haka zai daure fuska ba. Baya baya ta fara ja, tana kallonshi idanunta cike da tsoro.
Shi kuwa kallonta ya tsaya yanayi, idan akwai abunda yafi bacin rai to tabbas yau ya shigeshi. Kallon yadda idanunta suka cika taf da hawaye yake, ga jikinta yana rawa ta kasa koda motsa baki.
Da kyar kwakwalwarta ta tuna mata abunda ya kamata tayi, for she fell into a hiatus; after colliding into the Lion-as she named him. "Dan Allah kayi hakuri, wallahi bansan kai bane ba," she stuttered, a daidai lokacin da bayanta ya bugo da bangon dan corridor din; that means ta zo karshe kenan, amma tasan babu halin guduwa tabar wannan zakin me gurnani-dan definitely sai ya biyota.
Yadda kasan da bango haka take magana, fuskar nan kuwa hade kamar an turo mashi mutuwa-kwakwalwarshi tunani take akan abunda ya kamata ya mata, bacin baida lokacin batawa yau da sai ta gane kurenta; kuma saboda Halima bazai iya korarta ba-dan yaga san yar aikin take.
"Dan Allah Baban Shaheed kayi hakuri, na rantse da Allah wallahi bansan kai bane-nayi tunanin wannan dan...," sai kuma tayi shiru, dan tunanin she would've spilt that to this roaring lion before her.
Sai a lokacin yayi gulping lump din da yake throat dinshi kafin yayi magana "wanene dan rainin wayon? Dan naga kafata da inda kika daka bai maki kama dana yara ba balle kice Kamal ne ko?" Shi kwata kwata ma hankalinshi bai kawo wajen Arhaan ba, dan ya dauka raina mashi wayau kawai zatayi.
"Aa wallahi ba haka nake nufi ba, nidai kayi hakuri dan Allah," duk ta rude, dukda a nutse yake maganarshi amma ba karamin kada mata yan hanji take ba.
Ko kala bai kara ce mata ba, dan a ganinshi kaskantar da kai ne ya tsaya yana magana har haka da yar aikin gidanshi, amma dole yama Halima magana domin taja mata kunne-dan shi if it's possible ma-she should make herself oblivious idan yana nan.
Yana wucewa-Sakinah heaved a sigh and cleared the line of sweat that formed on her forehead, with a relief smile adorning her full lips.
"Na tsira yau, Allah ka kara kareni nan gaba," daga haka ta shiga ta cigaba da aikace aikacenta, amma dukda haka duk wani motsi da zataji sai tayi tunanin duk shine ya dawo domin ci mata mutunci.
***
Zuwa yanzu ciwon dake jikin kafarta ya warke kamar ma baayi shi ba, amma duk karin second dinta daya a duniya-ciwon dake cikin zuciyarta yana kara linkuwa linkin ba linkin ne. Normally, a well functioning heart beats 80 beats per minute, to her-with each beat-the pain in her heart intensifies itself into millions.
Kullum cikin dare sai tayi kuka, gashi kusan yanzu kullum Ramcy tana nanike da ita-but what baffles her was she couldn't even say no to whatever Ramcy does to her body, dukda dai she never exceeded her limits, amma dukda haka it was over exceeded to her frail heart.
Tunani akan iyayenta kuwa, tun tana lalube cikin zuciya da kwakwalwarta-har ta daina, dan kuwa it causes nothing but a throbbing headache to her already thudding brain. Iyaka idan ta gama dan lalubenta cikin brain dinta ta kasa ganin information daya-to zata zauna ta dizgi kukanta har ta godewa Allah.
Phone-was her only companion, dan it's the only thing she used in taking off her mind from this hideous world. Kamar ko wanne marece a kowacce rana, dolene kafin Ramcy tabar gidan zatazo ta dan lulubeta kafin kuma hakan idan ta dawo da daddare-amma bata taba wuce iyakarta ba. A cewarta, sai ta gama koya mata dadin abun tukunna. Allah ya tsaremu.
Tana zaune cikin dakinta tana game sai wayar ta fara ruri, sliding answer button tayi before ta amsa da "Toh gani nan" kafin ta wuce kitchen. Yadda ta saba hadawa Hajia Hauwa kayan motsa baki idan tazo haka ta hada kafin ta wuce hanyar main living room.
Tana shiga ta hango Hajiar Saheer zaune saman kujera tana nunawa Hajia wasu hotona; kallonsu tayi kafin ta duka ta ajiye tana mai gaida Hajiar.
"Ahh Beeba, Hajia Saude jiman yarinya sai gogewa take, fatarta har ta fara chanzawa wallahi," Fadar Hajia Hauwa kenan, tana bin Beeba da wani kallon kurilla; wanda yasa dole Habiba ducked her head down and began fidgetting with her long sculptured fingers.
"Hmmm bari kedai Hajia, ai taji dadin zama ne-gashi bata da matsala ko kadan wallahi, tanada ladabi yarinyar," Hajia spoke, her lingering stare scrutinizing Habiba's curved body-which was fitted in an ankara skirt and blouse.
Saida suka gama complimenting dinta kafin Hajiar Saheer ta dauke idanunta ta saukesu kan tray din refreshments dinnda aka ajiye mata. "Amm...Beeba nace ko? Kuna dan wani abu mai nauyi kamar snack haka? Saheer baici abinci ba wallahi, dawowarshi kenan nace ya kawoni," ta tambaya tana kallonta.
"Eh Hajia akwai, amma snacks ne gaskia; saidai ko na dora mashi girki yanzu sharp sharp," ta fada tana niyyar juyawa domin kama hanyar kitchen, but muryan Hajia Hauwa halted her at the doorstep.
"No, the snack can do, help him with some dan Allah." And with that, Habiba nodded with a smile and walked to the kitchen, dan itama ta kwana biyu bataga dan Gayu ba-as she named him.
Saida taje dakinta ta dauki hijab ta saka kafin ta wuce da tray filled with scrumptious snacks and a drink. Tana zuwa direct dan garden din ta wuce, saida ta ajesu kafin ta nufi hanyar motan-can ta hangoshi zaune saman driver's seat ya kifa kai saman steeeing wheel-he might be asleep or ruminative.
"Assalamu Alaikum," she spoke softly, standing inches away from him.
Dago lazy and bloodshot eyes dinshi yayi, dan he was knackered to the extent that he couldn't even move a finger-and famished? That's what he doesn't even want to think about, as a growl escaped his intestines.
"Ahh Yar baka, yau kece a garin?" Ya furta da wani irin wahalallen murmushi, yana kallon yadda duk ta rame ta fada cikin kwanakin da basufi biyar ba, from the last time he saw her.
"Kaji wani hausa da kayi kuwa? Wai a garin, ba gidanmu kazo ba?" Haka kawai ta tsinci kanta da yin dariya, she doesn't know why-but seeing him lifted up her forlorn soul.
Saidai ya danyi dariya, irin dariyar daka gani kasan mai yinta ya gaji ko kuma cikinshi na bukarta lodi. "To what do I owe this visit zance ko me?" Ya furta amiably.
"Abinci na kawo maka, gashi can a garden kazo muje," ta furta tana kara matsawa gefe dan bashi wajen da zai fito.
Wani irin murmushi ne ya subuce ma lips dinshi, this lady here deserves to be given some accolades-kamar ta shiga ranshi. "I wasn't the inventor of the idea, Hajia tace na kawo maka," haka ya jiyo muryarta na yawo cikin kunnenshi.
Scrunching up face dinshi yayi jin tace hajia, kafarshi daya fara fiddowa waje ya maida hade da harde hannayenshi saman chest.
"Kai Dan gayu, Hajiarka nake nufi fah, ka fiya zafin rai Allah. Fito toh," and she giggled, he heard the giggle lingering in his earlobes like an adorable child's giggle.
Wani murmushi ya saki kafin ya fito cikin motar, yadda ta karkata mashi ya wuce yasa rana reflecting saman face dinta, making her looked radiant and ravishing. His breathe almost hitched, yadda ta kulle idanunta-probably being blinded by the rays of sun inflicted on her orbs. Her long eye lashes casted beautifully on her cheekbones.
Wani gauron numfashi yaja kawai ya fara takawa har garden din tana binshi a baya, sai wani yamutsa fuska take tana kare fuskar da hannunta; saboda ranar da tayi casting directly on her face.
Suna zama tayi thrusting plate din gabanshi saman dan table din dake tsakaninsu. Kallonshi tayi da murmushi kafin tace "Kaci mana, Dan gayu," tana mashi nuni da ido akan tray din.
Bai musa ba ya dauki snack din ya fara kaiwa baki yana ci cikin hankali da nutsuwa kamar dai dan gayun da take kiranshi dashi. Har ya kusa rabi sai ya tsaya yana kallonta, ya lura da tunda ya fara cin abinci she was deeply staring into space, dan bata ma lura da yana kallonta ba.
"Kinsan ma?" Ya katse masu silence din.
"Hmm?" Abunda kawai ta iya furtawa kenan; dan she was physically there, but her mind was kilometres away.
"Tunda nake ko? Ban taba zama da wata mace a haka ba, like har muyi maganar da tayi tsayi sosai," ya fada da dan fleeting smile dinshi, yana girgiza kai alamun shi bai taba ba.
Wani murmushi ne ya subuce ma bakinta, ta rasa yadda akayi dukda tana cikin damuwa-ganinshi kadai take off her worries in a fleet. "Ahhh kace na ciri tuta kenan," she uttered, followed by an amazing chuckle that adorned her chapped lips.
Dariya ya fashe da ita, ganin wani triumphant smile a lips dinta. Sai can maganar da tayi yayi registering a barin dinshi, sobering up yayi kafin ya furta, "Eh to, badai ki kai ga ciro tutar ba-amma har kin bude kofar da zata sadaki da tutar; Yar Baka."
Baku enjoying story dinne? You guys aren't voting nor commenting😭💔
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top