BABI NA SABA'IN

A gajiye suka iso asibitin, jikinsu babu inda baya rawa, burinsu bai wuce suje suga halin da Mama take ciki ba. Baba ne ya juyo ya kallesu, dama shi yaje daukosu asibitin. He wanted it to be a surprise, tun last month ta farka, amma kasancewar jikin nata time din bama gane mutane take ba yasa babu wanda ya fada mawa. Bata fara magana ba sai last week, maganan ta na farko was ina Arhaan? Tun Baba yana gani kamar zafin ciwo ne har dai ya kira mata Arhaan din, lokacin har ya musu booking din flight and all.

"Arhaan kodai na kaiku masauki ku huta anjima kun dawo? May be itama baccin take yanzu." Ba dan komai yace haka ba saidan Sakina, yaga abun ciki shi baima san akwai cikin ba, kuma kullum sai sunyi waya da Mommy amma bata taba fada mashi ba.

Sakina ce tayi karaf, "Aa Baba dan Allah zamu jirata har sai ta tashi," gani take ita tafi Arhaan kosawa suga Mamar nan, she has alot to tell her.

Baba yar dariya yayi kafin yayi leading dinsu hanyar dakin da Mamar take ciki, "Sakina ke nake tausayawa, naga kinyi nauyi da yawa. Kai Arhaan shine ko ka fada man na fara siyayyar kaka ko?" Left kunnenshi ya kamo ya murza cikin wasa.

Kunya ta lullube Sakina, shi kuwa Arhaan ihu ya fara, "Baba kayi hakuri to, ba gashi ka gani ba yanzu? Kyautar me zaa bawa baby?"

"Kaci gidanku! Kyautar kaina zan bawa dan, dan gidanku mara kunyar banza!" Duka ya kai mishi daidai time din da suka bude kofar suka shiga dakin.

Da dariya fuskarsu, amma dukansu tsayawa sukayi suna kallon Mama wacce nurse take bawa magungunanta. Sakina bayan Arhaan ta boye, dan wata irin kunya taji ace Mama ta ganta da uban ciki haihuwa gobe ko jibi.

"Dan Mama..." Mama ta furta da murya mai rawa, daka ganta kasan dauriya kawai takeyi amma kuka takeso tayi.

Kamar karamin yaro haka ya fara takawa har inda yake, hannunta da take miko mashi ya rike a hannunshi sai hawaye, hugging dinta yayi gaba daya. Ita kuka shi kuka kamar wacce ta shekara dari ba lafiya. Sai can cikin kuka ya fara magana.

"Mama I thought you're going to leave me, Mama I thought bazan kara ganinki ba, your hands, your voice, your laps, everything about you Mama. I kept dreaming About Aunty Yo, she's laughing at me saying that dama tace zata rabami dake har karshen rayuwata, yanzu bazan kara ganin ki ba." Aunty Yo matar Baba ce wacce suka rabu tun Arhaan bai kai 10 years ba. A lokacin suna zama Lagos, Mummy kuma na Kaduna. Kudirat sunanta, bayerabiya ce, kamar wasa ta fara kai tallar abinci wajen aikin Baba a nan dai tasan yanda tayi har ta aureshi. Muzgunawa babu irin wacce bata yiwa Mama dasu Arhaan ba, yakai Baba ko magana baya masu. Karshe dai saida tasa akawa Mama saki daya, kafin ranar da dubunta ta cika asirinta ya kare Baba ya saketa.

A zaman da sukayi da ita, Arhaan babu kalar rayuwar da bai gani ba, har takai da dukda Mama ta dawo gidan kullum da daddare sai yayi mafarkin Aunty Yo tana azabtar dashi. Mafari kenan duk idan ya fara bacci tofa jikinshi ya mutu kenan, dan har yau gani yake Aunty Yo zata dawo cikin rayuwar shi. Shi da Aunty Halima suka saka mata Aunty Yo. A cewarsu she's Yoruba, gashi Mama tace su rika ce mata Aunty. Hence the name, Aunty Yo.

Breaking hug dinsu Mama tayi, "Haba Dan Mama, ba nace maka babu kai babu Aunty Yo ba har abada? Ka kwantar da hankalinka kaji? Maza daina kuka kar Sakina ta maka dariya. Naji kamar ka dan rame, kuka ka rikayi ko?" Jikinshi ta fara dubawa kafin tayi cupping face dinshi, kuka yake har yanzu, ita kuma she's trying all she can do ta danne nata kukan amma ta kasa. Dukda watannin da tayi a kwance she can feel his absence a tare da ita.

"Nayi missing dinki Mama, I almost gone crazy wallahi. How are you feeling? Thank you for coming back to me, to us, and your little Arhaan as well." Yana fadin haka yayi breaking hug dinsu kafin ya janyo hannun Sakina ta dawo gabanshi.

Kallon mamaki Mama ta bisu dashi, ido sake take kallon Sakina, wacce hawaye sun gama wanke mata fuska tas. A hankali eyes dinta suka sauka akan cikin Sakina, dole ta saki hawayenta suka zubo. Sakina ce ta karasa jikinta tayi hugging dinta.

"Mamaa..." ta furta da muryar kuka, she was beyond happy. Here, was the woman that did all the best thing for her. She couldn't thank her enough. She owes Mama all the best things in life as well.

"Sakina am. Ikon Allah." Sai kuma ta fara dariya. A hankali ta fara tattaba face din Sakina kafin ta shafo cikin cike da soyayya.

"To Sakina yaya? How did it went?" Ta kara tambaya, tana kallonsu daga ita har Arhaan din.

"It was rough, I cried kamar na mutu Mama, but everything is fine. You're fine, Alhamdulillah. I couldn't thank Allah enough." Abunda Sakina ta furta kenan cikin kuka tana kara hugging Mama.

Dan dukan wasa Mama tawa Arhaan, "Mugunta ko Arhaan? Naso ina nan ai, da duk muguntar daka mata sai na rama mata."

"Kuma Mama kamar kinsan I kept saying, Mama ce shaidata, amma zo kiga ruwan mugunta, kamar ba Arhaan dinki ba."

"Sakina sharri zaki ja man? Ni babu wata muguntar dana maki."

Dukda cewar Baba baisan inda maganarsu ta dosa ba, amma ganin Mama cikin farin ciki shima ya sakashi cikin annashuwa. "Indai mugunta ce akazo kan Arhaan kuma ai an gama magana. Rainon Aunty Yo ne fah, kema dai Maman yara kinsan abunda kika hada Sakina dashi."

Dariya dukansu suka kwashe dashi, dan itama Sakina tasan labarin Aunty Yo. Fira suka fara yiwa Mama, daga wannan yace wannan sai wancan yace wannan. A haka mijin Aunty Halima ya kira Baba akan gobe flight din Safe zata biyo, shi babu halin zuwa yara kuma makaranta.

Aunty Halima ba karamin dadi taji ba ganin Sakina living well in her house. Sunyi fira, dan dakin da Aunty Halomar ta sauka can Sakinar ta koma. She told her everything, and thanked her beyond words. Bayan zuwansu da sati biyu aka sallami Mama, a gida kuwa fadin irin murnar da sukayi ma baa magana, dan har Inna da Baba saida sukazo jiwa Mama ban gajiya.

Tunda cikin Sakina ya kusa cika wata tara cif Mama taje da kanta gidan ta daukota, gida ta maidota. Amma ganin irin zaryar da Arhaan yake mata cikin gida yasa ta hakura ta mayar da ita part dinshi dake gidan, dan da cikin dakinta Sakinar take. Wani time din sai suna hira da ita da Sakina da Arhaan din sai ta kalli Arhaan tace "Arhaan duk ina cika bakin wai?" Yasan maganar me takeyi, akan shi fa bazai taba san Sakina ba.

Saidai yayi dariya yace "Kai Mama." Dukansu dariyar sukeyi. Dan yanzu daya kwantar da kamshi kan cinyar Mama tadashi take, saidai tace yanzu kuma ai saidai danshi ko yarshi.

Ranar kuwa da daddare Sakina ta fara nakuda, tun tana tunanin zata iya daurewa har ta tada Arhaan, dama baccin ba wani na arziki yakeyi ba duk kar ace Sakina ta tadashi baiji ba. A hanzarce ya mike ya taimaka mata ta chanza kayan jikinta kafin ya kaita mota. Part din Mama ya shiga, suka fito ita da Safiyya dan tunda Mama ta dawo Safiyya taki matsawa kusa da ita.

Asibiti suka kaita, tun suna tunanin zata haihu cikin dare har suka fidda rai, suna jiyo kukanta daga labour room din, Mama dai da lallashi ta samu ta lallaba Arhaan yaki shiga dakin nan. Sai wajen 7 na safe kafin Allah ya bawa Sakina iko ta haifo diyarta mace sak Arhaan.

Wajen 12 aka sallamo su suka koma gida. Dangi daga ko ina suke zuwa suga Babyn dan Mama. Inna da Baba sunzo amma ranar suka koma. Arhaan ganin har dare na niyyar yi bai samu yaga Sakina ya kira Safiyya yace ta taimaka mashi shidai ta fito mashi da Sakina. Haka kuwa akayi. Ya kusa five minutes yana kallon face din babyn ya kasa cewa komai, Sakina ce ta kwanto da kanta saman shoulders dinshi tana murmushi.

"1 down, 14 remain." Ta fada cikin sigar wasa.

Kallonta yayi yana dariya, he can't believe wai yau shine da Sakina har da babynsu. Like yarinyar nan dai that brings the best and bad out of him. Kan Sakina yasan cewar ya iya masifa da fada. Kan Sakina yasan cewar mutane sun iya bada haushi har kaji inda hali zaka iya shakare mutum ya mutu ka huta. Kan Sakina yasan zafin bakin ciki da damuwa. Akan Sakina yayi dariya irin wacce bai taba yi ba. Akan Sakina yayi kukan da bai taba yin irinshi ba. Akan Sakina yasan mecece soyayya da ma wai yarda akeyinta. Akan Sakina ya koyi hakuri da daukar kaddara. Sannan kuma a cikin kaddarar Sakina yaga tashi kaddarar shima. At some point, he can say he's the nemesis of Sakina, saboda kome ya faru da ita is linked to him, and it brought her to him.

Ranar suna Baby taci Sunan Mama suna kiranta da My Mama. Har Aunty Halima saida tazo, saboda dama kwananta hudu a Egypt ta koma Sudan din. Habiba ma tazo, dan wannan karan har Kaduna zasuje wajen Maama. Washe garin Suna Saahir yazo ya dauki Habiba wacce itama yanzu she's pregnant, saidai idan ba ta fada ba babu wanda zai gane tanada shi.

Tana shiga motar ta kalleshi gajiya cike da face dinta, "Dan Gayu nagaji, take me out dan Allah."

"Your wish is my command Yar Baka, nidai karki haifa man lazy baby dan Allah."

"To karbi cikin mana, in yaso sai babyn ya zama as strong as you are."

"Idan na karba kuma wazai taya wani fitowa daga kogin? Ke you're lazy, ni kuma I'm pregnant. Urgh, gross, wai pregnant. Abun ko dadin ji." Dariya ta fashe dashi, a haka ya tsaya ya siya mata snacks da ice cream kafin suka kama hanyar Kaduna.

Kamar babu abunda ya faru haka Maama ta tarbe su, dan kuwa tun suna can suna waya da Habiba babu laifi. Kauthar kuwa an goge an zama yan gayu, lafiya lau suke zama cikin kwanciyar hankali babu wani matsala.

Saahir ya lura da yadda Maama har wata yar kiba tayi, "Maama wai nikam ban gane ba, da haka kike? Kinyi dan haske da yar kiba fah. Maama wai kodai?" Wata irin mazga ta kai mishi ya kauce yana dariya, Habiba ma dariyar tayi dan duk sun gani abunda ke faruwa da Maamar.

Dakin Saahir suka sauka, bayan tayi wanka ta chanza kaya shima yayi wanka. Tana tsaye bakin gadon sai kawai ta fada kan gadon, "Ahh! I've been dreaming to do this, gadonka is so inviting Dan Gayu, I can finally sleep on it."

Dariya yayi kafin ya kwanta gefenta, "Let's sleep together then, Yar Baka."

A dakin Mama kuwa, Sakina na zaune tana hada kayan My Mama cikin akwatinta, dazu Safiyya ta kawo wankin data mata. Kuka My Mama ta fara tana kwance kan gadon Mama, Sakina naji amma tayi shiru dan ita kan tana jin nauyin Mama sometimes.

"Arhaan wai bakajin takwarata na kuka?" Suna zaune dashi suna fira, saima langabar da kai yayi saman shoulder dinta.

"Ina wajen Mamata, kowa ya tafi wajen Mamarshi." Abunda ya furta kenan.

Cikin wasa Sakina ita ma ta mike, "Mama zanje Kaduna, tunda ance kowa ya tafi wajen Mamanshi." Daurewa takeyi karta yi dariya, ganin irin kallon da Arhaan yake mata alamar 'Anina sharri zaki ja man?'

Har tazo bakin kofa ya rikota ya maidota cikin dakin, Mama kuma ta bige kanshi dake kan shoulder dinta taje ya dauki My Mama dake faman tsangara kuka, takowa tayi har inda Sakina take, "Karbarta ko in mammakeku duka biyun, yara biyu amma nema kuke ku haukata ni wai?!" Dariya sukayi kafin Sakina ta karbeta ita kuma Mama ta bar musu dakin.

Dukansu ya hadasu yayi hugging dinsu, Sakina tayi planting kanta saman chest dinshi. My Mama kuwa kamar tasan abunda akeyi tayi shiru tana wasa da design din rigar Sakina.

"Anina ina sanku." Arhaan ya furta in a dreamy voice.

"Tohm Dan shagwaba nima ina sanka, muna sanshi ko My Mama." A tare suka duka sukayi pecking both cheeks din yarinyar.






Alhamdulillah!!!

Nan mukazo karshen wannan littafin na THE NEMESIS OF SAKINAH...KADDARAR SAKINAH.

Na fara rubuta littafin nan on 28th May, 2018. Yau, 28 October, 2019, Allah ya bani ikon gamashi.

Duk kura kuren dake ciki Allah ya yafeman, durussan dake ciki kuma Allah ya bamu ikon amfani dasu. Ina fata mun koyi darussa daga Rayuwar Sakina, Habiba, Mama, Inna, Ya T, Maama, Saahir, har da shi kanshi uban gayyar, Dan Mama; Arhaan.

Nagode maku sosai. Sai mun hadu a littafi na nagaba. Mai taken 'Sarauta...A jini na take.'

Bissalam.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top