BABI NA HAMSIN

Dedicated to Aysha Aliyu Batsari (Sholeey) Happy birthday dear🥳❤️ Sakinah and Arhaan loves you and wish you a happy birthday with lots of laughter and love.

"Lallai ma yarinyar nan duniya kika samu shine baki nemana ko? To gani nazo yanzu ai." Ya T ne yayi magana hade da dan dukan kanta kafin yayi breaking hug dinsu, janyo hannunta yayi ba tare da ya lura da yadda jikinta yayi sanyi ba, zama sukayi kan kujera yana kallonta "Ke wai dallah gidan naki ba abinci ne? Alquran yau banci komai ba." Yadda yayi maganar cike da dabanci yayi ta, Sakinah yaken dole tayi ta mike tsaye. Har yanzu idanun Arhaan yana kansu, shi bai koma ciki ba shi kuma bai karaso ba.

"Kai Ya T? Kana da kudi fah shine zaka wani ce bakaci komai ba? Nidai yi hakuri bari in zubo maka." Tsoronta daya kar sai taje kitchen din Arhaan ya shigo falon, tasan ko kule yace ma Ya T dan dole zai ce mashi cas cass cassss, kuma tana tsoron yasa a kamashi.

Kamar wacce kwai ya fashe mawa haka ta fara takawa ta shiga kitchen din, "Ke sakara ga tv amma bakya kallo? Lallai yarinyar nan sai na fada ma Inna irin dolancin da kikeyi, ko ina wannan sakarar da ko magana bata san yi? Dama itama auren taje tayi na hutu na fargabar halin da kuke ciki ku duka." Bai kula da mutum yana kallonshi ba, haka yaje ya kunno tv ya dawo dauke da remote domin chanza channels.

Cikin gaugawa Sakinah ta zubo mashi abincin ta dauko drink din ta kawo mashi, jikinta babu inda baya rawa, tsoron Arhaan ne yayi mata wani irin mugun comeback a ran ta. Ganin Ya T ya kunna tv saida taji kamar ta saki fitsari a wajen, kasa kallon inda Arhaan yake tsaye tayi, Ya T ta aje ma abinci kafin ta raba ta zauna gefenshi.

Fira suka fara sama sama yanacin abincin shi, tambayarshi su Maman Iliya tayi, saida yayi wata irin muguwar dariya kafin ya bata amsa. "Ai ki barni da shegiyar matar nan, wai dan uwarta ni zan koma gidan nan inji tana fada ma Inna magana? Ina mata magana akan tayi shiru kuma ta nemi ta zageni wai nine katon banza tsabar banda amfani an aurar dake bana nan ita kuma waccan sokuwar an kasa getting to her. Aikuwa na lakada mata na jaki, muna zaune a majalisar mu sai ga mijinta yana huci yazo wai zai rama mata, nasa su Gatari da Zarto ranar Kusa yana wajen; suka kusa wulla shi lahira. Yanzu shegiyar tana can asibiti jinya suke." Hankalinshi kwance yake bata labari sai dariya yakeyi, murmushin yake kawai take mashi dan tasan yanzu kam Arhaan yagama cika ya batse.

Sama sama ake hirar, ya lura Sakinah bawai san magana take ba kuma yasan ba haka take ba, "Ke wai lafiyar ki kuwa? Naga tun dazu sai juyawa kike kina kallon wajen labulen can. Wai waye mijin ma dan uwarshi bazaizo ya gaida ni bane? Ko wani abun yake maki? Akwai mai takura maki ne inyi maganin ko wane shege? Ina wannan dan iskan yaron da yayi maki iskanci a gidan aikin ki?" Hannu kawai Sakinah ta dora saman kai ganin Arhaan tsaye gabansh eyes dinshi sunyi jaa tsabar bacin ran dayake ciki, kallonta yayi ido cikin ido kafin ya maida hankalinshi akan Ya T.

"Gani, kuma nine mijinta da kake nema." Bata taba tunanin zataga irin wannan confidence and courage din a fuskar Arhaan ba, tayi tunanin the next time da zasu kara haduwa da Ya T kila sai ya kusa fitsari a wando tsabar tsoro amma she saw nothing in his eyes banda rage, he was angry and thirsty for revenge.

Daga zaunen da yake T ya mike tsaye, wani irin ashar ya saki kafin ya maida kallonshi kan Sakinah "Ke dan ubanki da gaske wannan huhu lahun yake? Ta gidan uwar wa kika fara sanshi?!" Jijiyoyin nan sun taso sunyi rudu rudu, yadda yake kallonta tasan inhar bata bashi amsa ta samu sun rabu lafiya ba toh babu wanda zai hanashi ya mata jan bugu kuma ya zane Arhaan din shima.

"Wallahi ban sanshi Ya T!" Tana furta hakan wasu hawaye suka sauko mata, tasan idan tace tana sanshi wani tashin hankalin ne, a hakan ma bawai ta tsira bane ba.

"To kai bata sanka ta gidan uwar wa ka auro ta? Inna dole ta maki ko? Wannan tsohuwar na rantse da mai busan numfashi sai ta gane kurenta!" Ganin ya chakumi collar din Arhaan yasa Sakinah riko hannayenshi gam, kuka take shara shara tana girgiza ma Ya T kai.

Kallon Arhaan tayi with an apologetic look, "Shima baya so na ai, baka so na ko? Fada mashi dan Allah." Bata ida rufe baki ba taji amsar Arhaan "Ina santa." Hannu ta dora a kai ta fashe da kuka, jin wani irin naushi da Ya T ya sauke ma Arhaan din a ciki.

"Ya T wallahi baya so na kawai ya fada ne dan ya bata maka rai, dan Allah kayi hakuri ka tafi dan girman Allah!" Ganin daga naushi daya abun yana nema ya koma duka sosai.

Wata irin shewa Ya T ya saka, wato tsabar wannan yaron ya raina mashi wayau "Kai dan uwarka ni kakeso ka bata ma rai? Uban wa ya baka damar auran mani kanwa bayan bata sanka? Uban wa ya baka izinin aurenta ma? Ke gaya dan ubanki ya taba tabaki? Gaya man nace!" Wani mari ya sauke mata ganin tayi sototo tana kallonshi, taga taga tayi zata fadi Arhaan yayi saurin tareta, jikinshi ta fada ta kara fashewa da wani kukan.

"Kai dan uwarka gabana kake wani rungumeta? Zaka saketa ko sai na chanza maka halitta." Ita tasan cewar brothers are overprotective, amma bata taba tunanin protectiveness din Ya T yakai haka ba. Cikin hanzari ta janye jikinta daga na Arhaan ta rike hannun Ya T tana kuka.

"Ya T dan Allah badan hali na bakayi hakuri, wallahi bazan kara maka abunda nake maka ba. Zan rika gaidaka kullum wallahi, kuma nabar gidan Inna balle na rika fita yawo, dan Allah ka kyaleshi haka nan, dan girman Allah karka ji mashi ciwo Ya T." Kuka take har cikin ranta tana rokonshi, wani wurgi Ya T yayi da Arhaan kasa, har tayi wajenshi kuma ta dawo wajen Ya T din dan tasan tana nuna wani sign of affection yanzu zai cigaba da dukan Arhaan din.

Janyo ta yayi ya zaunar da ita gefen Arhaan yana kallonsu dakunsu, yadda eyes dinshi sukayi ja kai kayi tunanin garwashi ne. "Ke wai dan ubanki saboda wannan kike wani kuka? Da can bake kikace na lakada mashi na jaki ba? Ko dan yanzu yana mijinki? Ohhhh sanshi ma kike kenan?!"

Ya T bai ida rufe baki ba Sakinah tayi saurin rike hannayenshi dan tasan mari ne zai biyo baya, ko ya mare ta ko Arhaan din, "Wallahi tallahi Ya T bana sanshi, dan Allah kayi hakuri ka tafi. Arhaan ai bana sanka ko? Ka fada mashi kaima baka so na, wallahi Ya T ba haka bane." Yasha fada masu bayasan suyi alaka da ko wane da namiji, ashe ashe shi kadai yasan haukan da zaiyi masu idan ya gansu da namiji, ta dauka duk cikin rashin hankalinshi ne, not knowing he meant it.

Wani irin razanannen kallo Ya T yabi Arhaan dashi yana jiran ya amsa mashi tambayar da ba sai ya furta ta ba, "Ina santa..." Arhaan bai rufe baki ba yaji saukan maruka har guda biyu, Sakinah na niyar rikoshi itama ta samu nata.

"Na shiga uku Ya T ka taimaka ka tafi dan Allah, miji na ne fah, inma inasan ko yana so na ai ba laifi bane ko? Dan Allah kayi hakuri, kuma ma wallahi ba so na yake ba." Bata ida rufe baki ba Arhaan ya katse ta "Ina santa" Ya T yakai hannu ta rike tana girgiza kai "Wallahi karya ne Ya T ba sona yake ba." Kuka take har numfashinta yana barazanar tsayawa.

Shago wuyan Arhaan yayi, "Sai ka saketa dan uwar ka, ba da kanwata zakayi zaman aure ba. Saketa yanzu ko kuma wallahi na lahira sai ya fika watayawa."

"Bazan iya sakinta ba." Naushi yakai mashi a chest dole Sakinah ta hugging Arhaan gaba daya tana kuka, which makes her back facin Ya T, kallonta yake cike da mamaki da tarin takaici.

"Ke dan uwarki miye haka? Zaki matsa ki bani wuri ko sai na hada dake na maku dukan banza gara na kaiki asibiti akan in kyale wannan shegen."

Cikin kuka ta fara magana, "Ya T ka taimaka man, wallahi na maka alkawarin idan har yaman wani abun da banaso zan kiraka da kaina na fada maka, yanzu idan kace ya sakeni wallahi Inna kasheni zatayi, koda ka hanata wallahi cikin dare sai ta kasheni, dan Allah ka taimaka ka tafi kafin wani abu ya sameka. Yanzu yan sandan dake mana gadin dare zasuzo, kar su ganka su kamaka."

Cable din daya ciro ya lafta ma Sakinah a baya ta saki wani razanannen ihu amma still tana rungume da Arhaan din; clutching more onto him. "Dan uwarki inga kinyi ciki a gidan nan wallahi daga ke har shi shegen da yayi maki cikin sai na halaka ku, shi kuma dan shegen take tsinanne zanyi da ya dagargaje. Zaki sakeshi ko sai maki jina jina?!" Dukanta ya fara yi babu tsayawa, ita kuma tsoronta ta sakeshi ya dake Arhaan, ganin da gaske T yake indai bata saki Arhaan ba bazai daina dukanta ba yasa Arhaan ya raba jikinshi da nata.

Saida T ya kashe ma Arhaan warning kafin ya wurga mashi cable din ya fita daga gidan yana huci kamar tsohon zaki. Sakinah kuka take kamar ranta zai fita, ga azabar duka ga bakin cikin abunda yama Arhaan sannan fargabar ita abunda Arhaan din zai mata. Dama har yanzu bai mata maganar abunda tasa Ya T ya mashi ba, gashi kuma yazo yayi adding more salt to the wound.

Yana zaune gefenta yana kallonta, saida taci kukanta mai isarta kafin ta mike takai hannu zata taba Arhaan amma ya goce, tashi yayi tsaye yana jifanta da wani kaskantaccen kallo kafin hankade ta ya wuce part dinshi yana dan dingishi. Hannu kawai ta dora aka ta fashe da wani kukan, shikenan ita rayuwarta.



From chapter 48-50, they're wholeheartedly dedicated to my personal girl, my lovely sweetheart Sholeey_ Happy Birthday my dear, Sakinah and Arhaan loves you to the square of Infinity❤️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top