BABI NA BIYU

Tun cikin daren suka fara kaya-kayen kayan dake dakin, suna ware na wanki da wanda za'a maida cikin ghana must go dinsu. Har suka gama babu wanda yace da wani kala, everyone was lost in his own world. Abunda ke damun Sakeena yafi karfin wanda ke damun Habiba, though half of Habiba's problem is what would her sister be going through? She knew her so well, this would lead to something else.

"Sakeena, you have been crying for almost five minutes now, dan Allah ki daina kukan haka," Habiba spoke softly, tana share mata hawayenta.

Sakeena wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya taja, dan ita rayuwarta dukda talaucinsu ta tsani a raina ta, sai yasa duk bala'i bata zuwa wani wajen ta kwana; ko yini gidan mutane bata cika yi ba.

"Biba, you knew my problem, kinsan fears dina. Habiba wallahi bana san wannan aikatau din, duk abunda za'amin wulakanci ba sanshi nake ba," Sakeena whimpered, clutching onto her sister's shirt. She was crying in an agonizing way, she has many dreams and hopes; but it loomed all her dreams and hopes would be shattered.

Breaking hug dinsu Habiba tayi, kafin ta share mata hawayenta; taking all her might not to break down too. "Kiyi hakuri, Sakeena. Ni kaina ba san wannan aikatau din nake ba, I have this bad feeling gnawing at me saboda aikin nan. Kema din Insha Allahu babu abunda zai faru, komai would become a history, Saky," Cikin kwanciyar hankali da lallashi take maganar, hakan kuwa yayi nasara wajen kwantar wa crying Sakeena hankali.

Sakeena hawayenta ta share kafin wani factitious smile yayi curving full lips dinta. "Thank you, Biba. Having you as a sister is the best thing in my life," she slurred, hugging her sister affectionately.

Hugging dinta back Habiba tayi, itama murmushin kwance kan fuskarta. "Allah ya kare abunda zai shiga tsakaninmu, Saky. I love you with all my being," tana fadin haka ta zare jikinta daga embrace din Sakeena. Trying so hard to suppress the tears that were trying to cascade down her subtle cheeks.

Saida sukasha hirarsu kafin sukayi addu'ar bacci ko waccensu ta kwanta a bangare daya na katifar. Sakeena kam bacci yace neman ni a inda kika ajiye. Saidai tayita juyi marar kara, tana gudun ta tada Habiba da motsi. A haka dai tayi kukanta iya kuka kafin wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita.

Da asuba kamar saukar aradu haka suka jiyo masifar Inna cikin gidan, a tare suka saki tsakin takaici, dan kuwa they were used to waking up by her unending shoutings and yellings. They groaned and groggily sat upright, kallon juna sukayi kafin suka kwashe da dariya, dan jin da sukayi Inna ta zagi dayar matar dake cikin gidan.

Sakeena ce ta fara mikewa, "Kinga, ki tashi muyi sallah, ga wanki da wanke-wanke; masifar Inna will never end," tana fadin haka tayi hanyar fita dakin.

Itama Habiba mikewa tayi, saida ta kalli himilin kayansu kafin tayi sauntering out of the room; with a heavy heart.

Suna fita sukaga Inna nata surfa bala'i tana alwalla. "Wai Inna for godsake bakya gajiya da fada ne? Tunda asuba fah, ke ko irin abunnan da mutum yakeyi na rashin san magana idan ya tashi bacci bakya yi, dan Allah ki rage," Fadar Sakeena, dama itace mai bakin, dan ta Habiba to Inna ta kwana tana bala'inta.

Saida Inna ta furzar da ruwan dake bakinta kafin ta kalli Sakeena cikeda masifa "To sannu mai bakin reza, bazanyi shirun ba, kuma wallahi idan baki man shiru ba saina maujeki. Shegen baki kamar gurasa," Inna bellowed, glaring at her.

Sakeena stifling back dariyarta tayi, "Allah ya baki hakuri, Inna. Amma ko ban tambaya ba nasan wallahi koma dawa kike fada shi keda gaskiya," tana fadin haka ta fada toilet tana dariya, dan tasan tabbas reply din Inna wouldn't be sweet.

Kwafa Inna tayi kafin ta wuce dakinsu, Habiba kuwa saida tayi dariyarta sannan ta fara alwalla. Saida sukayi Sallah har suka kwaso kayan wanki sannan Baba ya shigo gidan da yar sallamarshi; gaidashi sukayi kafin ya wuce dakinsu.

Zama sukayi kowaccensu ta tsura ma kayan ido, an rasa wacce zataje ta karbo kudin sabulun wanki wajen Inna. "Sakeena dan Allah kije ki karbo, wallahi kinsan ni dakyar ma ta kulani," inji Habiba, pleadingly looking at Sakeena, whom held a devoid expression on her face.

Saida Sakeena ta saisaita zamanta saman bucket din da take zaune kafin ta fara magana "Beeba, kinsan dai halin Inna, balle yanzu ma na bata haushi, Allah dakyar in bata ci ubana ba ma. Dan Allah kije ki karbo," ai kafin ma Habiba ta bude baki suka jiyo hargowar Inna.

"Wato yarannan ni kuka raina ko? Me nace maku jiya? Ba cewa nayi kuyi wanke wanke da wankinku ba? Sannan yau har gidannan nakeso a shareshi kaf! Tunda Allah ya hadamu da bakaken kazamai cikin gida," Inna ta fada sarcastically, tana harararsu hade da karasowa inda suke zaune; sukam cikinsu ya duri ruwa.

Kamar an mintsine su haka suka tashi "Inna babu sabulun wanki ne," Sukayi stuttering in unison, dan sunsan tazo ta iske a zaunen jikinsu zai gaya masu.

"Kunga abunda nake gaya maku yanzu ko? Kodan hidimun gidannan ai kunje kuyi aikatau, balle kayan dakinku; wanda kanku zaku rufawa asiri," fadar Inna, wacce ke tsaye tsakaninsu, her hands at akimbo.

"Inna dan Allah ki daina maganar nan, yanzu dai bari mu fara wanke wanken, ai akwai sauran omo jiya. Idan gari yayi haske sai a siyo sabulun," Sakeena na fadin haka ta fara bin tsakar gidan nasu tana tsinto kwanukansu.

Aikinsu suka fara, babu wadda tace kala har suka gama; lokacin gari har yayi haske. Yadda sukaji ana buga kofar gidansu yasa suka san ko waye. Hada ido sukayi kafin Habiba taje ta bude gidan; ko kallon wanda ya bude kofar baiyi ba ya bangaje ta ya wuce.

"Ina kwana, Yaya Tukur?" Ta gaidashi cikin sanyin murya. Dukda tasan bawai zai amsa gaisuwarta bane, amma in bata gaidashi ba dole taci na jaki.

Bai kalleta ba saima kallan inda Sakeena take yayi, ganin ko kallon inda yake batayi ba yasa ya kara tunzura "Ke dan ubanki wato kinfi karfin gaidani ko? Kuma banace a rinka barmin gidan bude ba?" He roared, making them shivered in fear. Maganar shi ta yan daba, balle akai ga suturarshi da tsagun dake fuskarshi.

Ganin sunyi shiru yasa yayi wajen da Sakeena take, dan dama itace yar rainin wayon "Ba magana nake maku bane eh?" Ai Sakeena bata jira ya karaso ba ta ari na kare sai dakinsu Inna.

"Ke lafiya zaki fado ma mutane babu sallama?" Inna ta tambaya a dan kidime, shi kuwa Baba hankalinshi kwance yake sauraron radio dinshi, dan inda sabo sun saba, kusan kullum.

"Yaya Tukur ne mana, dukana zaiyi, Inna," Sakeena ta fada tana nuni da kofa; har hawaye sun fara taruwar mata.

"Kina ina dan ubanki! Yau sai na cire maki wannan rashin kunyar wallahi," Tukur ya fada da karfi yana bankade labulen daki.

Zumbur Inna ta mike "Kai wai dan baka da kunya baka kwana gidan ba amma kazo zaka dukarmin yarinya? Fice min daga gani, ai nasan yunwar cikinka ta koro ka!" Inna ta fada cike da masifa, ko Baba da yake mahaifinshi bai isa taka mashi birki ba sai Inna; itama dan masifarta tayi yawa. Wani lokacin ma ita take daukar role din uban gaba daya, dan sanyin Baba yayi yawa.

Karasowa yayi ya tsaya tsakiyar dakin; sending hurtful glares towards Sakeena; whose head was hung low, dan bala'in tsoronshi take, amma kuma she loathes his irritating behaviours.

"Haba Inna! Ya zaki rika mani haka gaban yarinyar nan. Na rantse da Allah bacin ke cikin gidannan da tuni na babballata; dayar can tafi tarbiya," ya fada yana wani basarwa, yadda kasan baima san sunayensu ba.

"Eh naji tafi tarbiyar, fita kabarmin gida, idan na samu kokon da zansha da ya' ya' na, idan ya isa na bada akai maka can wajen shashancin naku. Amma baka zuwa ka tada man hankali da safiyar nan," Inna ta fada tana nuna mashi kofa, dan ko ita wani lokacin tsoronshi takeji, dan ba karamin dan daba bane.

"Yi yadda kike wata magana kamar ni din ba danki bane. To wanka na dawo yi," yana fadin haka ya kalli Sakeena hade da nuna mata wukar dake kugunshi, kafin ya wuce.

Inna na ganin ya fita ta sauke wata ajiyar zuciya. Mauje kan Sakeena tayi hade da fadin "To ai sai ki wuce fitsararriya, daga yau bazan kara cetonki ba. Kuma kodan jarababben yaronnan dole ku tafi aikatau in huta," tana fadin haka ta hankada ta ta fita.

Sakeena nasan magana amma tayi shiru ta wuce, dan idan Tukur yana gidan; kwakkwaran motsi bata isa yinshi ba.

Sakeena na fita Inna ta juyo wrathfully tana kallon Baba, wanda hankalinshi kwance, kamar baisan wainar da suke toyawa ba. "Kai kuma wallahi bansar marabar ka da mace ba, ji yadda yaro yazo yayi wulakancinshi amma ko uffan," yadda kasan danta haka take masifa, amma ko kallon arziki bai mata ba.

Saida suka gama komai, they ate their breakfast with Tukur; that moment was the most dreadful moment of Sakeena's life. It was as if ace mata arr! Ta ruga.

Suna zaune sai ga wata mata ta shigo, daga ganinta Inna ta mike tanata zabga uwar fara'a. Saida suka gama gaisawa, kowa ya gaidata banda Tukur daya ja tsaki ma ya mike yayi tafiyarshi. Baba ma kallan Inna yayi kafin ya mike, he knew what she was planning on doing.

"To Abida Allah yayi an dace. Ita babbar an samu wata mata na neman mai aiki; amma a tudun wada take. Sai karamar kuma akwai mai nema a GRA," fadar matar tanata washe baki, dan itama alheri zata samu, nan take Inna ta fara jero hamdala.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top