BABI NA ASHIRIN DA DAYA
Tunda tayi wayau a rayuwarta bata taba shiga cikin bakin ciki da tsananin takaici da jin kunya irin na yau ba. Kaskantaccen kallon da bai taba mata ba shi yake flashing mata with so much disgust, ita kuwa gata tsamo tsamo cikin fitsari da kuma ruwan daya sheka mata.
Wani irin tukuk'in kuka ne ya kwace mata amma ta danne shi, dan yadda ya wani dode hanci yana kallonta ji take kamar ta ta shakeshi ta kwakulo idanuwan kowa ma ya huta. Wulakancin Arhaan yau ya kaita makura.
"Amma kasan ko a cikin mara imani kai na daban ne ko? Na tabbata idan na leka jahannama ban hango ka ba to wallahi garwashin azaba ne ya rufe ka, bakin mugu kawai azzalumi wanda baida digon imani ko tausayi a zuciyarshi. Kuma wallahi bazan taba yafe maka wannan tozarcin daka mani ba, Allah ya isa!" Tana kaiwa nan dole hawayen suka zubo, dan itadai a iyakar sanin data ma rayuwarta, bata taba jin kunya da takaici irin na yau ba, dan yanzu ba Kamal kadai ba, har Hafsah da Shaheed suna dakin sai kyalkyala dariyar ganinta cikin fitsari tsamo tsamo sukeyi.
"Laah! Uncle Arhaan, Malam yace babu kyau kace ma wani dan wuta fah-and Sakeena called you so!" Hafsah ta furta tana zare idanu alamar taji tsoron kalmar, kasan yara da tsoron ace wani zai shiga wuta.
"Na rantse da Allah na bude idanuna na ganku cikin dakin nan sai naci ubanku! Zaku fice ku bani waje ko kuwa!" She thundered! Tana zaro masu idanu kamar zata cinyesu.
Jiki na rawa sukayi hanyar fita amma Arhaan wanda zuciyarshi ta gama tafarfasa kan maganganun da Sakinar ta fada mashi ya tsaidasu-yadda ta kona mai rai dole itama ya kona mata.
"Kai ku dawo. And you all should repeat after me! Amalala mai fitsarin kwance! Ta tsula ta kuma tsulawa, tabar mamanta da wankewa, mamanta da wankewa....Babanta yana bulala!" Yadda kasan dan cikin gari haka yake wakar harda tone din wakar, dan bai tabajin dadin koyan abubu kamar yadda Allah yasa ya iya wannan wakar ba a yau.
Aikuwa su Hafsah tafi suka fara suka cigaba da rero waka yana tayasu idanunshi kyar cikin nata yana mata kallon yarinya yanzu kika fara ganin bakin ciki.
"Amalala...mai fitsarin kwance!" Tafi suke sosai harda yar rausayarsu. Can kuma ya tsaidasu, "Kids, ku shiga toilet kuyita debo ruwa kuma zuba mata, let's wash her up!" Kamar dama jiran umarni suke, suka fada toilet din, daga mai debowa da mug din toilet, wai cup din brush and toothpaste wani kuma da buta-haka suka zo sunata juye ruwan nan suna komawa ga waka suna rerawa.
Ita kuwa Sakina kai kawai ta hade da guiwa tanata kuka, duk zubar da ruwan zaiyi a jikinta sai taji kamar yankar fatarta sukeyi, ga yadda wakar ke shiga kunnuwanta da wani amo da ke iya tarwatsa dodon kunnenta. Tsanar Arhaan kuwa a hankali take bi tana cika ko wane sassa na jikinta!
"Kamal kad'o klin cikin bucket dinnan ayi mata proper bath! Oya let's continue; Amalala mai fitsarin kwance, ta tsula ta kuma tsulawa, tabar mamanta da wankewa. Mamanta da wankewa; babanta yana bulala!" Katuwar ledar klin dake toilet dinta Kamal ya juye cikin ruwan bucket din kafin suka cigaba da diba sunata tsalle tsallensu suna watsa ma jikinta-shi kuwa Arhaan kallansu yake with a satisfied look on his face. Yau ya rama abunda yar rainin wayon yarinyar nan ta dade tana mashi.
"To yanzu mama ta wanke fitsarin, saura baba yayi bulala. Ku dauko viels dinta dake can wurin ku fara dukanta! Oya! Amalala mai fitsarin kwance, ta tsula ta kuma tsulawa, tabar mamanta da wankewa, mamanta da wankewa babanta yana bulala!" Su yara dama abinso ne ya samo, dan kuwa ci gaba sukayi da jibgar Sakina, wacce zuwa yanzu hade zuciyarta ne kawai batayi ba-banda sanyin ruwan da suka jikata dashi, azabar zafi da santsin klin, dukan da suke nata kadai ya isa ya farfasa fata da kuma zuciyarta. Ga wani uban rushing da takeyi, tasan tabbas ta gama bata wannan katifar.
Aunty Halima ce daga kitchen ta jiyo kamar hayaniya a falo, saida tayi jiimmm taji dai da gasken kamar ma waka yarannan suke suna wasa sun barta nan tana ta uban jiransu, babu su babu Sakinar. Tsaki taja mara adadi kafin ta nufi falon, tana shiga taji shiru amma kuma hayaniyar na fitowa daga dakin Sakina, tunani tayi kila acan Sakina me masu wanka suna yan wakokinsu da suka saba.
Shiga tayi kawai tayi magun gani. Ga Arhaan tsaye hannu cikin aljihu da wani satisfied look on his face, sannan kuma yaranta harda Shaheed wanda bata da masaniya akan lokacin daya tashi sunata jibgar Sakina-ita kuma kanta hade kai da guiwa banda rawa babu abunda jikinta keyi, ko ina sharkaf da ruwa da wani abunda bata da shakku klin ne aka jika.
"What the hell is wrong with you?! Arhaan menene haka?!" She clamoured, tana karasawa wajen gadon da Sakinar har yanzu bata dago daga duken da take ba-su kuwa suna ganinta suka ruga suka boye bayan Arhaan sunata dariyar jin dadi.
Batace komai ba ta kamo Sakina ta dagar da ita-sai kuma ga jini lame lame a kasan katifar yayi amalgamating da ruwa and klin. Tare suka saki wani disgusted grunt, shi kuma Arhaan budar bakinshi kawai yace "Sakina is a dirty girl iya iya wo! Shame shame shame, shame!!!" Aikuwa yara suka dauka harda tafi suna tsalle.
Wata irin hirgitattar tsawa Aunty Halima ta sakar masu, "Wai baza ku fita dakin nan ba sai naci ubanku?!" Ai basu kadai ba, har Arhaan saida yabar dakin dan yasin ran Aunty Halima ya gama baci, kuma bata da kyau idan ranta ya baci.
Batace wa Sakina komai ba haka ta kamata suka shiga toilet ta hada mata ruwan wanka, da kanta tazo ta yaye bedsheet din ta kaisa wajen laundry kafin ta dawo ta fara tsane ruwan daya kusa cika tsakiyar dakin-tama rasa irin tunanin da zatayi. Yau ta tabbatar da Arhaan ba shagwaba kadai ke damunshi ba harda iskanci.
Sakina na fitowa wankan ta iske Aunty Halima har ta gyara dakin ta kawo mata breakfast. Har yanzu hawaye ne ke zarya saman fuskarta, kuka takeyi na bakin ciki da kuncin rayuwa. Bata taba tunanin duk talaucinta wannan cin mutunci zai taba iskarta ba, wacece sila? Duk Inna ce taja mata, had it been batazo gidannan a matsayin yar aiki ba babu yadda zaayi a taba mata irin wannan cin mutuncin.
"Wallahi sai na dauki fansa!" She avowed, wasu hawayen na zarya saman cheeks dinta. Tasan duk abunda zatayi bazata taba ci mashi mutunci kamar yarda yaci mata ba, dole ta nemo mafita.
Kamar mahaukaciya haka ta nufi ghana must go dinta ta zazzage kayan tas ta tud'o ta baibai, idan har bazata manta ba, sun taba rubuta number din Yaya T itada Habiba jikin wannan ghana din, ilai kuwa! Sai ga dankareren rubutun Habiba da number. Wani irin magun wahalallen murmushi ta saki kafin ta kwashi number din jikin wayarta, wacce Aunty Halima ta bata koda zata sakata wani abun idan tana wajen aiki.
Saida ta kira sau biyu a na ukkun ne ya dauka, kuma daga jin muryarshi a buge yake wanwas! Hakan yasa taji kamar ta kurma ihu dan dadi. Dukda dama akwai bakin cikin, amma haka ta kakalo kukan munafurci ta fashe dashi. "Yaya T!" Abunda ta iya furtawa kenan, dan tasan tabbas shi kadai zai iya ladabtar mata da Arhaan.
"Ke wacece cikin ku ne? Kinsan ni bawai na cika gane murya bane eh! Sakina ce ko Habiba?" Ya tambaya, dan shidai yasan duk duniya su kadai ke ganinshi da mutuncin kiranshi yaya, suma din dan ya musu mugun bugu ne.
"Sakina ce Yaya T, wallahi anan inda nake aiki wani ya wulakantani, dukana yayi kamar raina ya fita yaya T, ya jikani da ruwan klin yaita kwallo dani tsakar gida...," duk wani tuggu da tasan zai harzuka Tukur saida ta fadeshi tanayi tana kuka harda ciccijewa kamar ranta zai fita.
Wani irin ashar ya dura yana mikewa tsaye, "Uban waye shi dan uwatai! Ke dan ubanki bar kuka fadaman wane dan shegiyar ne kuma yana iya!" Har wani zillo yake yana layi.
Wani murmushi ta saki ganin hakarta ta cimma ruwa. Nepa bill din da aka kawo ta dauko ta duba address din gidan. Hango Arhaan tayi whistling while gamboling towards his black sleek Mercedes. "Ya T ka tsaya kaji, banaso su gane ni zan tura ka, amma fa karka kasheshi, kawai kai mashi dukan da ko zai tashi sai yayi wata daya kwance, sannan kuma kar ka fada mashi ni na turoka_ni zansan yadda zanyi ya gane kai yayana ne." Address din gidan ta bashi da kuma motar da Arhaan din ya fita da ita, tana jaddada mashi akan kar yazo yanzu sai daidai lokacin data fada mashi Arhaan din zai tashi daga wajen aiki sai ya tareshi hanyar gidan.
"Ke dan ubanki babu wanda ya isa ya tabaki ya kara shakar wani numfashin na rantse da Allah! Dole yau barzahu tayi sabon bako, kuma billahillazi sai na chanza ma dan shegiya kamanni kafin in sai mashi ticket din kabari!" Yana fadin haka bai jira ta furta komai ba ya latse wayar hade da kasheta gaba daya! Take yayi wajen addunansu ya dauko daya ya fara wasata, dan yau aikin na daban ne.
Yau naji dadin shafin😂😂😂 kowa zai gane kurenshi💃
Kuyi voting da comment dan kara mani gwarin guiwa😊
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top