BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
Ku gafarta mani na rashin jina da kukayi, biki mukayi nayi rashin lafiya kuma, sai sauran hidimomin rayuwa. Amma yanzu I'm fully back!
Slow beats taji yana tashi, kuma from all indications the person inside the kitchen is rhyming the song and swaying a little, for she could hear the soft smacks of his leg on the floor. Tana bude kitchen din taga Saheer da apron sai yanka carrots yake da walwala kan fuskarshi, murmushi tayi kafin ta karasa inda yake.
"Dan gayu kawo na tayaka," Ta furta da muryarta mai sanyi, tana zama kan kujearar dake opposite tashi a kitchen island din.
"Yar baka you should've rest, na saba ai," Girgiza mata kai yayi alamar bazai bada ba kafin ya cigaba da yankar carrots dinshi.
"Dan Allah ka kawo, ni idan kaga nayi baccin rana to banda lafiya, or do you want me to fall sick ne?" Yadda take maganar with a cute voice yasashi kasa mata gardama, baisan lokacin daya mika mata chopping board din da sauran carrots dinba.
"Yar baka ba lafiya kuma ai zance ya baci, gashi nan ki yanka toh." He chuckled and stood up, yaje yayi stirring girkinshi kafin ya dawo ya zauna, ganin yadda ta hade girar sama data kasa yanka carrot din kawai take.
"Ba zaka koma wajen aiki ba? Tunda nazo yanzu I think sai ka daina girki ai ko?" Dagowa tayi cikin nutsuwa tana mashi magana, amma ganin yadda yake kallonta yasa taji gabanta ya fadi kuma ta sauke idanunta kasa.
"I'm done for today ai, kuma girki we can be doing it together ko?" She kanshi yadda yake magana mamaki abun yake bashi, dan bai taba expecting zai zama soft towards mace ba.
"Babba dakai da girki? Dan Allah ka daina," yadda tayi maganar kawai ya bashi dariya, baisan sadda ya fashe da dariya ba ya mike ya koma wajen cooking gas din.
Murmushi tayi tana tambayarshi dalilin dariyarshi, amma bai ansa ba saima dariyar daya karayi. Carrots din taje ta wanke kafin a tare suka cigaba da girkinsu suna fira cikin kwanciyar hankali, duk abunnan da ake Momma tana daki tana barci, saukowarta kenan taga suna hada dining table din, Beeba sai dariya take tana girgiza kai, shi kuma Saheer ya kureta kawai da idanu, everything about her appeals his eyes.
***
Koda Sakinah taje masallacin asibitin sallah tayi kafin ta roki Allah akan ya rufa mata asiri kar a gane itace silar saka Arhaan cikin wannan hali, koda ta gama sai ta tsinci kanta da zama ta rungume guiwowinta ta fada duniyar tunani.
Tunanin rayuwarta ta baya takeyi, kafin dawowar Ya Tukur daga makarantar poly kano dayayi, ta kasance mai yawan tara samari, saboda Sakinah baka ce, amma akwai kyau da diri.
Dan ita ko abincin gidansu ne baiyi mata ba to ta gwammace taje shagon Ilu ta ranto garin kwaki ko na hamsin ne, in cikin samarin nata wani yazo fira sai ya bata taje ta biya. Duk wani kwaleman yan unguwarsu babu wanda bai santa ba, amma dawowar Tukur komai ya tsaya chak, su kansu samarin tsoron zuwa suke wajenta balle ita da Ya T ke nakada mata na jaki, kuma Inna bata taba cemashi kala, dan itama bawai samarin takeso ba.
Tanasan ta koma gida, amma idan ta tuna irin rayuwar da zata koma mawa sai ta tsinci kanta da rashin san hakan. Yanzu babban burinta bai wuce taga ta shiga makaranta ba, ta nemi ilimi, dukda waec dinta bawai tayi kyau bane, amma tana saka ran koda FCE ne zata iya samu.
Ta taimaka ma iyayenta, taje ta dauko Habibah suyi zamansu tare, Baba ya daina aikin kwadago, Inna ta daina masifar rashin kudi, ta chanza masu gida ta rabu dasu Maman Iliyu, dreams dinta yawane dasu.
Sauke numfashi tayi kafin ta mike ta koma dakin, tana komawa ta iske har Baban Shaheed ya kawo masu dinner, gasu Hafsah nan duk sun zagaye Mama, Aunty Halima kuma tana bawa Arhaan abinci a baki.
Aunty Halima na ganinta ta mike tsaye "Yauwa Sakinah, dan Allah zo ki tayani bashi abincin nan, zanje in gaida matar abokin Baban Shaheed an kwantar da ita nan asibitin ta haihu." Ko jiran amsar Sakinar batayi ba ta mike hade da mika mata cup din kafin tawa Mama sallama dake bawa su Hafsah harda Kamal abinci a baki ta wuce.
Sakinah zama tayi gefenshi amma kuma sai ta kasa motsi, dan tunanin datayi na rayuwarta yasa jikinta duk ya mutu, ganin she has a very long way to go.
Arhaan kallonta yayi yaga tunani ma take abunta bawai tashi take ba, kunu ne bawai wani abu ba, shima saboda ya warware mashi intestines dinshi ne daga flour din dayaci.
Tsaki yaja dan siriri wanda is only audible for her, firgigit ta dawo hayyacinta, saurin kanga mashi cup din tayi a baki batare data jira komai ba. Kona bakinshi yayi, amma a haka ya daure ya hadiye kunun, zare fuskarshi daga cup din yayi yana jifanta da wani irin mugun kallo.
"Ke azzalumar ina ce? Bakisan kunun yana da zafi ba? Kuma a garinku haka ake bawa mutum a baki without care and all?" Cike da masifa yake maganar, amma kuma muryarshi can kasa take gudun kar Mama ta jiyo rigimarsu wacce bata karewa.
"Arhaan kake ko wa? Dan Allah I'm not ready for your drama yanzu cikin daren nan, in zakasha kasha, in kuma ka koshi ne tafi nono fari, tunda dama naji ance duran abinci suka maka," Ai bata ida ba sai kawai ta fashe da dariya, bataga halin da aka kawoshi ciki ba, amma she couldn't help laughing at just the image of him laying lifelessly ga uban abinci an dirka ma cikinshi.
Wani irin tukukin bacin ciki ne ya ziyarci zuciyar Arhaan, a zuciye ya karbe cup din daga hannunta, amma kafin ya karasa bakinshi dashi cup din ya subuce kunun kuma duk ya zube mashi a chest, kasancewar hannun bawai su Ya T sun raga mashi bane.
"Asssshhh!" He wailed, sai cije lebe yake, dan kunun maganar gaskia yanada zafi, saukinshi ma akwai riga me dan kauri a jikinshi. Da vest ce daya shiga ukku.
Duk abun Sakinah tanada tausayi, firgigit ta mike ta dauke cup din daga gefenshi ta ajiye kafin zaro tissue tana goge gefen gadon daya baci. A haka saida tayi clearing wajen kafin ta dawo kan chest dinshi, ba wani tunani a ranta ta fara gogewa, ganin yadda yayi shiru kawai ya runtse ido, trying to relish on the scorching warmth seeping into his chest.
Takai daidai saiting heart dinshi ya bude ido, jin wani irin electrifying spark that he felt, not only him, ita kanta she shuddered. Yana bude ido eyes dinsu suka hadu, it was an intense look that made the toes of Sakinah curl up into her, she felt like a cheese butter being engulfed by heat_and slowly, she started melting under his eyes.
Dakyar ta dauke idanunta, sai kuma bata saukesu ko ina ba sai daidai saitin heart dinshi, wanda wajen was bare, rigar ta dan bude, saboda irin hospital gown dinnan ce. Kasan farin mutum, balle ga abu me zafi ya taba wurin, gani tayi yayi ja alamar kafin kuna zata tashi.
Saurin dukawa tayi tana hura mashi iska wajen, ita with all sincerity takeyi, ba wani tunani. Motsawa yayi alamar da zafi, hakan yasa ta dago idanunta, ignoring how he has his eyes unshaken on her face.
"Ka tsaya kaji? I'm trying to help relieve the pain, if ba haka ba kunar zata tashi, balai goma da ashirin." Tana furta hakan ta duka tana tofa mashi addua kafin a hankali ta ida goge wajen kafin ta dago tana kallonshi, ganin ya runtse ido yasa tayi tunanin ko bacci yake.
Shi kuwa Arhaan tunda tayi maganar nan, she didn't speak to him with only her mouth, her eyes spoke to him, dole ya runtse idonshi relishing on the warmth of the air blown upon him from her lips.
Tana gamawa ta sauka kasa kusa da Mama. Mama ta sakata zuba abincin, a hankali ta zauna tana ci, domin wani irin abu takeji yana bin ilahirin lungu da sako na jikinta. Bazata iya tantance menene ba, amma ta tabbata wani sabon alamari ne.
Koda ta gama cin abinta lum tayi saman guiwowinta that were brought up to her chest. Shiru tayi ta natsu domin jin inda wannan abun da yake mata yawo cikin jiki zai tsaya, dan kuwa tanajin motsinshi.
Aunty Halima ce ta shigo dakin tare da Baban Shaheed, saida suka zauna suka danyi hira kafin yace su tashi su tafi gida saboda yara zasu school gobe.
Har Aunty Halima tace Mama taje ita da yaran da Sakinah, sai Mama tace Aa taje ita da yaran, su ita da Sakinah sun kwana da Arhaan din.
Haka akayi, sallama suka masu kafin suka tafi, dayake dakin is spacious, dama Baban Shaheed ya kawowa Mama katifa, sai ta shimfida ta kwanta, ita kuma Sakinah denied kwana kan katifar, cewar she'll just sleep on the carpet, amma a zahirin gaskia gudu take a samu matsala saman katifar nan.
Dayake jininta kan fingers yake, dan ko motsi taji cikinta yayi sai taje toilet taji ko fitsari ne, karar wayan Arhaan taji, shiru waya nata ruri amma baa dauka ba. Mikewa tayi taje ta dauki wayar dake gefenshi, sai kuma ta rasa yadda zatayi ta tada shi, dan alamu sun nuna yanajin dadin baccin.
"Ka tashi ana kiran wayar ka." Shiru bai motsa ba.
Saitin kunnenshi taje gudun kar ta tada Mama "Arhaan ka tashi budurwarka na kira!" Ta furta da dan karfi, shi kuma ya farka a razane.
Thank you!
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top