BABI NA ASHIRIN

Gam ta runtse idonta, jinta finally ta dira a kasa, dama tasan rikonta da yayi was on reflex, amma da zarar hankalinshi ya dawo dole ya saketa ta fadi kasa, kuma abunda ya faru kenan. Wincing in pain tayi, tama rasa wace azaba zatayi acting upon; azabar ciwon mararta ko kuwa faduwar da tayi? Dagowa tayi da rinannun idanunta tana galla mashi wata irin muguwar harar, long forgetting Aunty Halima's warning.

"Wai kai dan Allah wani irin mara imani ne? Inda kasan bazaka rikeni ba ai basai ka fara ba," ta furta cike da tsiwa tana flashing mashi kallo me cike da rashin kunyar data saba.

"Ke har ni zaki kira da rashin imani? Na rantse da Allah in baki kama kazamin bakinki kinyi shiru ba, sannan kuma kinja dirty body dinki out of this place ba sai na saba miki, idiot," he wasn't yelling, nor was he talking to her in a soft tone-kawai abunda ya fahimta, baida lokacin dazai kara batawa tare da wannan sakaryar yarinyar.

She sat upright and glared at him, "Kai wai nan har zaka iya bude baki ka kira wani kazami? Dallah malam ja gafe kabar masu tsafta suyi magana. Kuma naga dama bani na kawo kaina ba, janyo ni kayi." Har cikin ranta ji take inama ace zata iya lakada wa Arhaan mugun bugun dazai kasa tashi, rainin wayonshi ya fara mata yawa.

Ganin yayo kanta yasa tayi ignoring ciwon tayi hanzarin mikewa, idanuwanta na falling on the floor-taga stains of blood almost duk inda jikinta ya rab'a. Arhaan zaro idanu yayi yana kallonta yana kallon stained floor din, "Ke menene wannan?" He clamoured, tsabar kyama har cikin throat dinshi yakejin wasu kuraje na neman fito mashi.

Kallon kasan tayi kafin ta hadiyi wani yawu me azaba, suppressing vulnerable part dinta tayi kan ta galla mashi wata hararar "Nasan dai kai ba karamin yaro bane, kai ko yaran yanzu ma indai sukaga wannan sunsan menene. Amma considering yadda kake, zan iya yarda idan kace bakasan menene ba. Amma indai haka ta faru, na rantse da Allah dan guntun mutuncinka dake idona har ya zube ya gama. Shagwababbe kawai." Ai bata jira taji me zaice ba kawai tayi hanyar fita.

Muryarshi ta jiyo yana fadin "Ke kizo ki kashe abunnan, dan you won't expect me to eat anything after seeing this trash!" Da alama ma shi maganganun data fada mashi ko registering basuyi a brain dinshi ba, dan ji yake kamar ya rasu wannan abun daya gani.

"Kanka akeji, dama bakin iyayi yasa kaki cin leftover din mutane, kai ala dole ga dan gata!" She yelled back and entered her room-wanka ta fada direct ta gyara jikinta hade da wanke kayan kafin ta fito ta koma kitchen din domin ta gyara wajen, yadda ta fita haka ta samu wajen, saidai ya kashe gas din, amma kuma dankalin yana cikin mai tsamo tsamo.

Wani irin dogon tsaki taja, "Allah wadaran naka ya lalace, sai kace yaga kashi. Yanzu shikenan zai kara rainani wallahi." Daga nan ta cigaba da aikinta tana kunkuni. Dan ita gaba daya alamarin Arhaan ba karamin takaici yake sata ba.

***

Habiba ce zaune saman daya daga cikin kujerun dake zagaye da garden din gidan, hawaye ne ke zarya saman idanunta-ita dai har ga Allah abunda Ramcy take mata bata kaunarshi ko misali, wai haka kawai kullum tana bacci is either taji ana tattabata ko kuma mutum makale da ita. Harma ta gaji da kulle dakin, dan da alama tanada spare key din dakin.

Bata hangoshi ba saida handkerchief din dataji saman hannunta, dagowa tayi da streaming eyes dinta ta sauke su akan nashi, he was intensely staring at her, with his orbs bored into hers. She looked away, for his gaze was too fierce for her fragile heart. She could see something through those plaque orbs of his, something she couldn't decipher.

"Dan gayu," she slurred, tana kai handkerchief din saitin idanuwanta tana gogewa. Ita abun har mamaki yake bata, duk yadda take kuka dayazo take tsintar kanta da dainawa, wanda in da ita kadaice, har sai ta gaji da kokarin daina kukan bacci ya kwasheta. He surely have something different in him.

"Ba wani dan gayu, ya mukayi dake? Ba na hana wannan kukan ba? Kullum ina fada maki Yar baka you can talk to me-say whatever is it dake damunki, I promise idan har baifi karfina ba zan miki maganinshi." Magana yake cikeda natsuwa da kuma tausayinta dake bin dukkan wani sassa na jikinshi, so yake yaji menene matsalarta, menene dalilin zubar hawayenta a kullum? Wacece ita? Dan yasan tabbas babu wanda ya fado daga sama.

Maimakon ta daina kukan kamar kullum, yau maganarshi ta tabo mata wani spot a cikin scorched heart dinta. "Wallahi inaso na fada maka, atleast may be na samu sauki a wani bangaren na zuciyata. Amma duk lokacin danayi yunkurin fada maka wallahi my tongue gets tied. Akwai problem, all what I know is; Dan gayu na gaji da zama anan, banasan nan-but bansan inda zani ba. Ko relative daya I don't know if inada shi....," kukane yaci karfinta kawai ta kasa karasa maganar ta rushe da kuka, ita kanta ta rasa gane kanta, kunci bakin ciki da takaici ne sun mata katutu cikin zuciya. Ya zatayi da ranta?

"Indai wannan ne, Insha Allahu zan maki maganinshi, ki daina kuka kinji? Ina tare dake." Dakyar ya samu ya lallasheta ta daina kuka, but still, she was staring deeply into space-he couldn't want to imagine what she's feeling in her heart.

Bayan sunyi sallama ya dauko Maama suna hanyar zuwa gida, numfashi ya sauke nannauya wadan ya tilasta ma Hajia Hauwa kallonshi. "Lafiya kuwa Saheer? Na lura tunda muka baro gidan Hajia hankalinka kamar baya jikinka," Hajia Hauwa ta tambaya, tana kureshi da idanunta dake cike da zallar kaunarshi.

Saida yasha roundabout, har Hajia Hauwa ta fidda rai akan zai mata magana tajiyo muryarshi, "Wallahi Maama yarinyar nan ta gidan Hajia, kullum nidai zan ganta cikin hawaye nake ganinta, sannan kuma idan na tambayeta meke damunta ta kasa fadaman, yaudai Allah yayi ta furta man cewar itadai ta gaji da zama gidan ne, amma she doesn't have a family. So abun na damuna, bansan ya zan mata ba wallahi."

Wani irin kayataccen murmushi ne yayi gracing lips din Hajia Hauwa. She was an inch close to cikar burinta. "To Saheer ni a ganina tunda hakan ya faru, me zai hana inma Hajia magana akan inaso ta barmin ita a matsayin yar aiki-kaga sai ta dawo nan wajenmu ta zauna, inda babu mai takurata ko?"

Ya dade rabonshi da yaji Maama tayi wata reasonable maganar ta kwanta mashi a rai. Fully etched murmushi yayi "Hakan yayi Maama. Amma dai ai ba aikin zatayi mana ba ko? Saidai irin taya aiyukan da ba'a rasa ba."

"Maida wukar, yar gida zata zama kaji?" Daga haka nodding kanshi kawai yayi, har suka karasa gidan babu wanda ya kara furta wani abu, kowa da abunda yake sakawa a ranshi.

***

Tsaye suke cirko cirko tsakiyan falo, Kamal ne kawai sai Hafsah yau zasu makarantar, Shaheed ya kwana da zazzabi bazai iya zuwa ba. Aunty Halima ta turo Kamal yafi sau biyar akan ya tada Sakina amma taki tashi, sai yanzu a zuwan karshe idanunshi suka yo mashi mugun gani-wanda yayi daidai da shigowar Arhaan cikin falon, dan wata irin azababbiyar yunwa yakeji, jifa kaf dinta kasa digama bakinshi ko ruwa yayi.

"Kai Kamal lafiya naga kuna kus kus? Do you want to be late ne, Hafsah?" Ya tambaya a yayin da yake shirin zama kan daya daga cikin kujerun da suka kawata falon, amma abunda Hafsah ta fada ne in a hushed tone yasashi mikewa tsayen gaba daya.

"Uncle Arhaan, Sakinah ce yau ma ta kara fitsarin kwance, yanzu Kamal ya shiga tadata ya ga katifarta sharkaf da fitsari kuna taba bacci sama." Wani irin joy daya ziyarci zuciyarshi me wuyar fada ne, amma dukda haka ya dake kar yara su kaishi su baro.

"Ke Hafsah bansan sakarcin banza, ku wuce kuje ku shirya," ya dan fada with a stern look.

"Allah muje ka gani Uncle Arhaan," kafin ma yayi protesting, Kamal yaja shi sun fada cikin dakin babu ko sallama balle knocking, dukda ko sunyi uwar gayya baccinta take shara bawai zata san sunyi bane.

"Ka gani ko Uncle Arhaan? Wallahi Amalala ce!" Kamal ya furta cike da jin dadin Uncle Arhaan yaga gaskiyar zance.

Arhaan kuwa toshe hanci yayi, dan wani mugun zarni daya daki hancinshi har kusan amai ya sakashi. Ganin da gaske bil haqqi bacci take yasa wani mugun tunanin darsuwa a ranshi, dama maganganun data fada mashi jiya dan baida lokaci ne da sai jikinta ya gaya mata, amma yanzu cikin ruwan sanyi zata gane kurenta.

Alama yama Kamal da yayi shiru, toilet dinta ya fada ya dauko bokiti cike tam da ruwa, ai ko second daya bai kara ba ya sheka mata shi tas.

Sakinah kuwa da jiya da daddare tasha murkusun ciwon ciki sai gab da asuba bacci ga kwasheta-kamar a mafarta taji saukar ruwan sanyi saman gaba daya ilahirin jikinta, firgigit ta mike tana tunanin kila a lahira take.

Tana bude idanuwanta suka sauka kan nashi, "kan ubancan, amma yau na tabbatar da baka da hankali, uban miye haka wai?" Cikin hargagin masifa da azabar sanyi take maganar har tana kyarma.

"Ina abunda ake ma amalala ne kafin a tadasu daga bacci." And that was when realization dawned on her: Arhaan ya ganta kwance sheme sheme cikin fitsari.


Ya kukejin littafin? Inason naji ra'ayoyinku.

Nagode.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top