My name is Nala Khalif, the daughter of the head district of Heliwa district, which is among the authoritatively districts of Mogadishu castle in the southeastern Somalia.I'm known to be Amiirad Nala, the first daughter and most beloved to Boqor Khalif. I used to pity how my maid Sahra, lives her life as a slave and be contented with that. Only if I know what life has in store for me. The prones I were to perch on.The Mogadishu castle was known to be the white pearl of the indian ocean. Could it be realized anymore? When all is left would be a BURNT CASTLE.Would you give your girl the chance? It's Ayshatou! You all know I love heart breaks! Well; this has more than just the word "Heart break."…
Littafinnan Ingausa ne; wato hadakar turanci da Hausa.Shin ko ya rayuwar yan mata guda biyu zata kasance, a yayin da iyayensu zasu turasu aikatau; wanda ta hanyar iyayen keso su yiwa kansu kayan daki idan hidimar bikinsu ta taso.Shin wannan hanya da iyayen suka dauke zata bulle kuwa? Bayan dukansu yaran ba so suke ba?Me zai faru ga Sakeena wacce take fitsarin kwance, gata da rashin hakuri? Shin zaman gidan aiki zaiyi mata sauki kuwa?Habeeba fah? Wanda hakuri da juriya sune halinta. Shin aikatau zai chanza mata halayenta?Ku biyoni domin kuji yadda tafiyar zata kama.Aysha Malumfashi ce.…
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi.Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai.Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu._______Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?…