91

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*ENA MIKA GODIYA TA NA MEMBERS Na SURAYYAHMS fans page musamman enda aka shirin musan juna jiya your beautifl words of prayers, love and encouragement is what keeps me blowing Allah ya sada ku da farin ciki da kwanciyar hankali All members of my fans groups 2.3 ena kaunar ku sosai nagode.*

*Sadaukarwa na musamman ga👇🏿*

*Maman khayr tawaje na my admin*
*Saffah one*
*mom khadija ena mika sako ma dan baba*
*Haulat bawa Allah ya dawo dake lapya ya bada ladan aikin hajj*
*ummu farhan na cikin asmaluv fans*
*Maimunat muhammad na sureehrny fans*
*fatima tijjani*
*Hurul aynn my admin*
*Real maryam noble*
*Da rukayyaht BB*
*And lastly my*
*Meenah luv meenaauwal marubuciyar sanyin idaniya ke da members din ki*



*Page▶91*


Mamy bata bude ido ba sai a gadon asibiti anan ma da wani irin kuka ta tashi
Yar uwan Abban Ashraf dake gefe itace kawai ke faman danne mamy tana cewa kiyi hakuri insha Allah komai zai zo da sauki ashraf bazai mutu ba.

Mamy tace na shiga uku,wannan bala'i da me yayi kama?  zaynab na dade ena gaya masa ya gyara halayen sa musamman akan biye biyen matan nan amma sam ashraf yaki ji na
Yau ba ga irin ta ba,yaje garin neman ido gashi an rasa gira?

Ga mata nan na sha kawowa ya zaba acikin su amma ya ki
Sai ya zabi wannan rayuwa gashi tana neman raba shi da duniya baki daya,yanzun ya yake ciki?

Gaskiya ena so naje na duba sa sunce min an sashi a emergency plane an dawo da shi kasar nan

Zaynab tace eh, kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki ,ai case din ma da yar gidan wani senator ne shiyasa ma iyayen ta suka kashe maganan tun akasan waje aka dawo da komai nan gida don ance yarinyar ta masa raunuka munana ajikin sa.

Dole muma muyi hakuri mu karbi wannan kaddara don Bamusan gaskiyan labarin ta ba
Ta dai ce ma media yaje raping dinta ne shiyasa ta cahhaka masa wuka ta kuma sokale masa kwayar ido da shi don ta samu ta kubutar  da kanta daga hannun sa

Mamy ta dada sunkuyar da kanta ta cigaba da kuka

Yau ana neman kusan sati biyu kenan ga media sunyi rububin labarin cewa famous  dan kwalisan nan Ashraf musaddik yayi atempting raping din mace har ta cire masa ido daya.

Yawancin yan matan da ya tayyara rayuwan su su suka dada azzala abun a shafukan su na media 
Su Suka dada bada shaidan ashraf zaiyi abunda yafi haka

A hakan nan mamy ta kasa samun nitsuwa tsaban bakin ciki, jasmine ce ta kasance kullum tare da ita tana sanyaya mata rai

Shi kuma ashween yana tsaye akan case din ashraf ana nema masa saukin jikin sa
gaba daya ashraf sai ya dawo shiru shiru baisan yin magana tsaban takaici,wayar sa ma ya kasa budewa sabida sakonnin mutane wanda mafi yawancin su na gwale ne.

A haka asibiti Sai kusan bayan sati biyu aka soma yunkurin sallamar sa lokacin akayi sa'a wutar fitanan yana neman ragowa kadan kadan.

Duk hankalin sa bai jikin sa musamman da ya lura  cewa albarkacin roko da magiyan da ashween yake yi yasa abban sa yake kula da shi

Doc ya tabbatar musu da cewa aahraf ya rasa karfin ido daya dole sai dai yayi amfani da ido daya

Ga raunaukan da yar senator ta ji masa 'a kullum in ya tuno yadda yarinyar ta masa  sai yaji ya tsani kansa.

Musamman daya tabbata karya take yi bai ce zaiyi raping din ta drugs kawai ta debo ta tsula masa rashin mutunci amma sai gashi
Ta juya magaman a media,girman shi da mutuncin shi gaban iyayen sa da mutane ya girgiza..

Yace hmmm duniya budurwan wawa yanzu ni ribar me naci?
Ni ban aikata ba amma ya shafe ni gashi narasa komai har da kyaun halittar da nake rigima da shi.

Sosai abubuwan ke damun sa, ga mamy bata ko amsa gaisuwan sa
A takaice Ashween ne kadai ke sake masa fuska yana tare da shi

Amma kuma yana mugun jin kunyar sa
Ta ena zan fara ? Tambayar kenan da ke hanasa tabuka komai gaban Ash don shi kansa ya san gaban da yake yi da Ash tun suna kanana ne.

Shikuwa ash ba ruwan sa tausayin sa ma kawai yake ji
Shiyasa ma yake nace masu mamy suna kula dashi kar ya shiga wani hali duk da fushi suke yi har yanzu

Haka rayuwa ta cigaba ma ashraf ba aikin yi gaba daya abba ya kwace ya rike abun sa

Sai ya zamo in ya zauna ba abunda yake tunawa sai kazamar rayuwan sa
Ga ido dayan nan shi yake asalin damun sa gani yake ba wacce zata aure shi a hakan kullum sai yayi kuka yana neman mafita wajen uban giji .

Da kyar ya soma samun sauki ya rusuna sosaii wajen neman yafiyar iyayen sa.

Kafin wata daya ya sake zagowa har ya dan sake ya soma fita sai dai yawon ba ya wuce gidan su jasmine anan ma Ash ne kawai yake kula sa.

Jabeer shi yayi sanadiyar zaman su jazmine na dan lokaci a abuja akan Ash zai taimake sa ya tada plantation din daya bar musu kyauta.

Anan su kanje asibiti a duba lpyar cikin jasmine sai dai kullun akaje sai ta turje masa akan lallai aje aduba zahida..

Duk da yanzu kam ta bude ido amma sam bata san ena take ba.
Gashi jamal da jabir sun gama shirye shirye akan za'a akaita chan babylon a cikin kasar iraq ayi mata special body surgery
Wata kila hala ayi dace ta dawo asalin siffar mutum

A asibitin nan duk sunyi signing din files dinta amma
Ashween ko ajikin sa hakan ya matukar damun jasmine

Ranar din ma da kuka aka koma gida yana driving baice komai ba don abun na mugun bata masa rai yadda take neman daga masa hankali akan zahida

Shi baisan meyasa jasmine ta damu da zahida ba shikuma gani yake zaman ta achan yafi tunda bazata taba barin komai  ya wuce ba.

Ga ba daya ranar haka taki kula shi, ko magana bata son amsa masa
tun yana kau da kai har ya sauko ya fara yar lallabi amma sai abunda ma ya karu.

Chan dare Tana kwance a kan bed da katon cikin ta a gefen sa ' yayi lumui yana kallon ta
Sai chan yace, jasmine ki fada min ya kike so nayi miki ? Ni kenan bazan yi abunda zai kawo min kwanciyar hankali a rayuwa ta ba 
Nan ma ta shiga matso ido tace yaya ba haka bane
Ni dai nafiso ace kana kula da ita kaima ai yar uwar ka ce,
Ka duba fa kaga yaya jamal da yay jabir thy are doing alots kaifa? In don nine wallhy na yafe maka
Kasan ba wanda ya isa ya kare ni sai Allah,.. ko da yau ta warke bata shiryu ba in Allah bai qaddara zata min wani abu ba bazata yi ba

Yayi shiru abunsa bai kula ba ta cigaba da jero masa bayani har dai ya hakura yace ,to shikenan in aka kammala surgrey zasu je su ganta tare

Duk da ma jasmine ta dan ji dadi amma ta so ace yanzu ne yaje don surgery zai iya daukar wani 4-5month kafin ta tashi gar gar kamar kowa.

Amma da shike tasan halin ogan nata sai ta amince kawai magana da ya kare tunda yace zai je.

Wata uku aka dauka ana ma zahida komai da komai har ansa ta a layin observation ana so aga wani irin kalar depigmentation jikin ta zai sake bayar wa

Ko ena bandages ne a lullube a jikin nata amma tana magana warau da muryan ta, tana kuma cin abinci sama sama

Sannnan ana koya mata yadda zatayi amfani da wasu gabobin jikin nata da yadda zata na motsawa

Zahida Yadda take jin ta garau ta ciki gani take tamkar in aka bude bandages din nan zata dawo normal kamannin ta.

Ana saura wata na karshe lokacin ashween
Yayi rakiyar jasmine makaranta don da kyar take motsawa ciki na watan shi na takwas.

Haka yayi jigila da ita ta kammala classes dinta sannan ta sa shi agaba sukazo babylon city don ganin zahida kamar yadda yayi alkawari

Already jamal da jabir sun iso kowa ya taru a asibiti tana zaune akan gado za'ayi unveiling bandages din agaa sabon kaman da zahida ta koma

Kowa na tsaye aciki yana jiran agama banda jasmine data manne masa ta rike hannun sa dam tana lafewa jikin sa don tasan sa sarai aiki kadan ne wajen sa ya zame ya bar musu wajen

Jamal ne ke dan amsa maganan zahidam kadan kadan ga dai muryan ta real kowa naji

Ana kaiwa karshe kowa yayi shiruuuuu awajen ganin yadda gaba daya ta dawo ba ita ba ce.

Wani halitta ce daban ,bakar fata mai madaidaicin hanci da baki sannan da kananan idanu

Ba yabo ba fallasa ba za ace mummuniya bace amma ko kadan baza a jera ta a layin kyawawan mata ba.

Hawaye ne suka sauko kam fuskan jabir ,jummai na rike da dan su Saleem tana dan calming dinsa a dabaran ce kar zahida ta fahimci wani abun

Shi kansa doc ya kasa nuna mata madubi ta kalli kanta don yasan bazata iya daukan wannan  qaddaran ta sauki ba.

She lost her beauty  ga shi ta dawo baka yanzu tsabanin kalar ta na da.

ganin yadda sukayi tsit suna rarraba ido ya sa ta danyi murmushi tace jamal im back
Ya mayar mata da smile din yace yes ure sis ,

Nan ya ma doc ido akan ya nuna mata kamannin ta kawai ta gani don basuda iko ko wani dabara sama da na Allah.

Ash sai ya dada kankamo matar sa suna tsaye suna kallon ikon Allah..

Ana bata madubi bata jira ba tasa akan idon ta,
Sai hannun ya soma karkarwa

Ta kalli kanta ta dada kallon kanta , a hargitse ta dago ta kalli doc tace wheres is my face?

Doc ya ce am sorry maaam we cundt bring it back this is the best we can
Tayi wurgi da madubin ya fashe a daburce tana cewa a bata fuskan ta wannan ba jikin ta bane.

Har abun ya fi karfin doc ya zame ya fita kowa  na kanta  ana daddane ta ana bata hakuri

ashween ne kadai bai kara ko one step ba abun na taba shi kam amma ya rasa me zai mata in ya ma je kusa..

Ita kuwa Cikin kuka mai razani Tace wallhy gwara na mutu dana zauna da wannan fuskan
Wallhy ba ni bace wannan

Ta riko Jasmine gam gam a haukace cikin kuka ta ce dan Allah ki ce su bani fuska na ni na gaji hakan nan im tired

Kuka awajen ba wanda baiyi ba sai jamal da Ash..

Karshe ma data ga hakuri kawai ake bata sai ta kori kowa ajikin ta kamar mahaukaciya ta sa su a tsakiya tana kukan fitan rai tana maganganu

Ganin zahida na neman fita a hayyacin ta abun naso ya zame mata tabon hankali ya sa shi isowa daf da shi..

Sosai jikin su yayi sanyi ganin yadda komai yake tafiya ma zahida kowa awajen idon sa ya kada yayi ja don tausayi.

Yana isowa kusa da ita ya riko hannun ta softly kan yace zai yi magana sai ta fada jikin sa tana faman karkawa tana kuka
Tace pls help me kace su bani fuska ta i cant live like this pls pls..

Ash ya dan soma tapping bayan ta a hankali har ta soma  yin shiru sannan ya dago ta yace ,kiyi hakuri zAhida
We cant change ur destiny

Kar ki manta dukkan mu anan munzo ne don ke
We are not complaing don baki dawo mana yadda muke so ba.

We stil remain family  zamu so junan mu a duk halin da muke ciki..

Sai ta kalle sa ta danyi murmushin takaici tace.
Rayuwa na kenan
Maybe abubuwan danayi ke dawo min
Gashi na rasa abunda nake tinkaho da shi har abada,

Ku din da naki kune kawai kuke kusa dani
Amma ena ganin da yau bazan iya kara kwana daya ba
Don Wannan ba ni bace ba halitta na bace sai ta cigaba da kuka a hannun sa tana cewa pls forgive me lateef na cuce ka na cuci kaina..pls say it kace ka yafe min ko Allah zai dube ni ya tsayar min da wannan azaban dana ke gani a duniya

Im so scared don Allah ka yafe ni lateef.

Ash baice komai ba don sai yanzu tausayin ta ya soma shigo masa
Sai kawai ya cigaba da calming dinta ko don ta sassauta kukan

Cikin dabara jamal da jabir suka karaso wajen suma suka shiga rararshin ta ,
kowa yana fahimtar da ita ya yafe mata ba laifin ta bane ,..

Sannan suka mata alkwarin bazasu taba rabuwa da ita ba

Don zahida ta sa aranta sosai hala yanzu da ta dawo wani halittan daban itama za'a tsame ta a cikin rodriquez

Amma sai taga ba hakan bane ,gaba daya sun bata assuarance zasu kula da ita kuma suna tare da ita

A haka har ta samu tayi shiru ,sannan aka soma shiri aka koma masaukin su.

Da shike yanzu ne lokaci na farko da dukkan su suka hadu a waje daya

Sai jamal ya kawo shawaran su dan yi hutun musan juna a babylon city tunda waje ne na tarihi da abun mamaki masu girma

Anan suka yada zango ,jabir da familyn sa jummai da salim
Jamal da new wife dinsa sarah
Sai ashween da jasmine da kuma zahida

Duk waje daya suke awani katon estate na shakatawa sai dai part daban daban 

Zahida ta kasance har yanzu ashween kawai ke iya controlling din ta
Ko kuka takeyi idan ya zo ya bata hakuri da kanshi sai ta tsinci kanta da jin sauki a ranta
haka ma abinci muddin bai sa baki ba bata iya wani ci sakamakon kullum tana fama da tunanin yadda zata fuskanci rayuwanta a yanzu da bata komai sai arzikin ta da yan uwan ta .

Don haka ne ma jasmine ta yanke hukuncin su dawo da zahida kusa da su sosai cikin flat din su ita da ash
saboda tafi sakewa kuma shivkadai ne ke sata samun nitsuwa daga jefa kanta cikin wani halin tunani

Yau ana sati na biyu kenan Ba laifi zaman zahida da su jasmine a flat daya ya sa ta soma mancewa da abubuwan dake damun ta.

Musamman da jasmine ta ke janta a jiki suna hira  wani lokaci abun dariya
Wani bin duk neman gafara ne.

A haka suka soma sabawa sosai sai dai zahida kullum ta kanyi fighting da abunda ke damun ta akan ashween

Ji take kamar shi kadai ne ruhin ta,
Ta kasa zama ita kadai tasan presence dinsa da kulawar sa ne ya sa ta soma samun sauki har haka ba wani abun ba.

har cikin zuciyan ta bata son haka don tasan hakan halaka ne mai grima

Allah ya riga ya haramta mata shi amma zuciyanta yaki ya barta

Ranar ma haka ta kasa bacci gashi ana neman wajen 1.30 na dare
Amma tana fitowa cikin daren sai tayi gamo da su A sitting room

yasa white 3qrt  ba ko riga ajikin sa yana kwance jasmine tana tsakiyar kafar sa da wani guntun bomshot na jeans iya rabin cinya da dan fingililallen vest sharara wanda yake bayyana katoton cikin ta kanta na kan kirjinsa
Sai ta mike kafa suna hirar su cike da so da kauna sai kissing din face dinta,da neck ko ena ma yake suna dariya gwanin sha'awa

Kallon su a hakan yasa Sai taji wani iri sosai ta koma dakin ta a sulale basu lura ba.

Kuka ne ya kufce mata amma ta rasa na meye ne
Ta yi makanta gargadin ashween haramun mata har abada amma ena tasan vazata iya denaying har yau tana jin zafin ganin shi da wata ba
musamman yadda yake nuna rayuwar sa gaba daya na jasmine ne yanzu.

Zahida tayi kuka sosai tana tausaya ma kanta
Gashi bata iya sallah ba bare addua oi
Sai abubuwan suka taru suka mata yawa a zuciyan ta

Anan a kasan dakin ta ta kwana tana kuka daga karshe sai ta yanke ma kanta wani hukunci wanda take ganin hakan ne kadai mafita a gare ta.





*Ku biyo ni muji hukuncin da zahida ta yanke*






*surriem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top