90

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Wannan shafin SADAUKAR wa ne ga Dukkanin masoya na da yan uwa da abokan arziki na cikin wayannan groups din da zan lissafo da ma wanda bansa ba*
*wayan da Dake jigilan re -posting littafin so makamin cuta a ko ena, comments,muhawara da discussions masu dadi masu ban dariya da abun tausayi*
*nagode gaskiya kusan kowani page from 1-90 nan ana iya kokarin tantance shi da comments ba abunda zance sai SAKALLAH fil jannat al fiddaus Allah ya so ku kamar yadda kuka so ni,nagode kwarai*

*ALL members na👇🏿*

*▶SURAYYAHMS fans page*
*-SURAYYAhms fan group 2 ,3*
*-HAUSA NOVEL females only*
*-BRiiliant writers fans 1.2.3.4*
*-MATA UKU Gobara fans1,2*
*-Asmeenat Zeeyan's fans2*
*-Novel and make up group*
*-JAMEESHA fans 1,2*
*- INDABAWA novels*
*-DOKIN karfe fans*
*-SUREEHERNY novel*
*-Habieba luv and Anfa novels*
*ALFAH fans*
*-Ummu ahmad fans*
*Habeeba Hausa novels*
*-HOME Of novels*
*-BK fans*
*Hausa novels group*
*Leemah novel fans*
*Asmaluv cuisuine and novel*
*Asma luv fans*
*Haske novels*
*Yar mutan arkillah fanz*
*Hakuri da masoyi fans*
*Kainuwa fans group 1,5*
*Sadnaf Group of novels*
*Sadnaf group 5*
*Samy Luv Novels*
*Mata Masu Duniya*
*Matan Arewa*
*Hikima novels*
*Duniyar littafai*
*Dr zains novel*
*nagartattun littafan hausa group*
*KAI AYI HAKURI bazan iya kaiwa kan kowa ba wanda dai nafi ganin tattaunar wa ku kusan kullum akan SMC bana mantawa da ku na gode sosaii*

*Wayan da na fita a groups din su da chan saboda korafin shugabanin su akan yawan coments din su ma littafin SMC dama sauran groups da abun ya shafa ayi hakuri fatan wayanda aka turo su na karba waje na suna kai mu ku lpya, naji sakonnin wasun ku na alhairi na kuma nagode sosai Jazakha Allah khairan*👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻❤



*Page▶90*

Mrs hidayat ta tuni tasan nata ya kare cikin minti kadan za'a bazama neman ta akan kisan saminu sai tace kafin taje prison sai ta hallaka zahida kowa ma ya huta

Atleast koma yaya ne tunda har zahida zata iya juya,bayan mata baya duk bayanin da ta mata to lallai ita ya cancanci ta kashe in yaso ita yayan ta su rayu a duniya..

Daga nan itama ta kama hanyar gidan gona tanayi tana tsoro kar polisawa su kama ta

Don haka jeji ta yanka ta shiga tsaga hanya tana tafiya a rude don ta samu ta kashe zahida kafin ta cimma burin ta akan danta Ashween don tasan ita kam dole ta tafi prison.

Anan ne jabir ya samu shigowa asibiti harbyana haki kamar ranshi zai fita

Lokacin kamal ya tashi duk ya daga musu hankali akan su tashi anemo jasmine da babyn su.

Ba yadda ash baiyi dan ya hakura ba amma kamal tsakani da Allah ya zage yana kukan a warware masa hannuu shi zaii tashi ya nemo ta tunda sun bar ma jamal ne da police  su kayo zaman su don shi

Already an sanar da su jamal cewa kamal ya ce zahida ce ke rike da jasmine

Shi yasa ganin ash zaune akansa ya dada sa shi kasa kwantar da hankalin sa don Allah kawai yasan meke gudana a zuciiyan ashween a lokacin game da zaman jasmine a hannun zahida.

A gigice Jabir yace ena ta kiran ka ena ka ajiye wayar ka ?sai suka tashi a tsaye yace brother meke faruwa
Jabeeer yace jasmine tana plantation u have to go therre zahida ta haukace zata cutar da ita
Zahida ta san kai waye ne naji kaffff abunda mum tafada mata akan ka..

A rude Ashween yace innalihhi wa enna ilahi rajiun sai ya juya ymtare da jabir zai tafi
Kamal shima ya soma yunkurin tashi zai bisu
Ash ya ma salma ido akan ta kulle kofar ta hana shi binsu don ko motsi hannun bai fara yi ba tukun.

Ba tantama ta tashi ta aikata hakan aka bar kamal da ihun kiran sunan ashween don a duniya baiji zai iya barin Ashween ya shiga wani mummunan hali baya tare da shi ba.

Kafin polisawa suyi hade haden su

Zahida ta taso tana tangal tangal kamar zata fadi tsaban buguwar da tayi da heavy drugs tana kan gauraya acid din gaban jasmine tana cewa am sorryy kinji? Kiyi hakuri babyn baby.
Ke kadai ce wanda in nataba yanzu zan taba zuciyar sa kamar yadda ya chakuda nawa
Kiyi hakuri kinji?

Jasmine ba abunda take in banda kuka da addua ko Allah zai shigo wannan lamarin da gaggawa ya cece ta.

Anan cikin haka mrs hidayat ta shigo ta baya a hankali lokacin zahida ta riko acid tana shirin tinkaro kan jasmine

nan mrs hidayat tayi wuf ta damko zahida ta wanka mata mari sukayi gefe da acid din a hannun ta dam
Suna kokuwa itama mrs rod ta damke hannun ta mai dauke da container acid din ta hana ta motsawa da shi

jasmine na daure sai fifficekwa take ko zata kunce kanta amma ena

Achan kan hanya kuwa an baza ana neman hidayat adebayo rodriquez for the murder of famous lawyer barister saminu

Jamal da poliisawa sun debo hanya haka shima ashween da jabeer sun debo hanya su duka zasu je plantation.

Anan aka shiga kwabzawa tsakanin zahida da mrs hidayat enda kowa ta rike bakin ruwan acid din suna dada tona makan su asiri

zahida na kan zagin ta akan irin rayuwar data daura ta akai.
Har aka kaiga acid ya soma diga kadan kadan a kafan mrs hidayat sanadiyar tankwara shi da sukayi acikin kwabzawan na su

Mrs hidayat tana magana tana kukan ga radadin zafin acid da har ya soma dage mata kan yatsun farcun kafafun ta duka
Tana jin wani irin zafi mai tsanani

Zahida kuwa sai wani mahaukacin dariya take
Ta na ce ma jasmine ,duba nan ga wicked mother inlaw dinki wanda ta haifi munafukin mijin ki wanda na tsane sa fiye da kowa kuma nake son shi fiye da rayuwa na.

yau zaki gode min in na kashe ki kika je chan gaban Allah kiyi zaman ki if not kema zata lalata miki rayuwar ki kamar yadda ta lalata nawa dana yayan ta gaba daya.

Ita kam jasmine duk ta gama rikicewa don tsoron yanayin su
Sai kuka take yi a razane

Anan mrs rod tayi wani wawan yunkuri ta ture zahida kasa ta kwace roban acid din da karfin bala'i
ganin zahida na yunkurin
Wawuso bindiga zata harbe ta ya sa ta watsa mata ruwan acid din daga fuskan ta har jikin ta baki daya

Wani firgitaccen ihu jasmine ta tsala ganin yadda zAhida ta sullebe gaba daya cikin jini tayi kasa bata ko numfashi

Mrs rod ta mugun tsorata sai ta shiga temporary shock bata ma iya sake container acid din a hannun ta ba bare ta gudu a wajen

Wanda yayi dai dai da shigowar su jamal da police sai ashween na biye da su shida jabir

  Shikam Da gudu yayi kan matar sa ya riko ta duk ta firgice ta rufe idon ta gam tana karkarwa tsaban tashin hankali, sai ya kunce ta ya dauko abunsa chak a hannu suka bar wajen bai kula ya sake duban kowa ba

Anan aka kama mrs hidayat da ko motsi ta kasa yi don sam ba acikin hanklin ta ta ma zahida hakan ba.

Jamal na tsaye wajen yana ma ambulance jagora aka zo aka dauki zahida da sunan ta kawai za a fada kace mutum ce awajen
don ko ena ata bangaren gaban ta tun daga fuska  ya sullebe ba aganin komai sai jini

Jabir kuma tuni suka tafi da su Ashween yana jan motar ash, shi kuma ya rungumo ta a sit din baya yana calming dinta sai kuka take yi...

Ba bata lokaci akayo sharia mai tsafta inda aka yanke ma mrs rod hukunci zaman rai da rai a prison

Sannan aka kai zahida asibiti ana mata emergency treatment karshen ta haka aka hakura aka barta under skin therapy saida aka shafi kusan wata 3 bata samu kanta ba.

Lokacin komai ya fara dawo musu normal jamal dake dan kula  da ita har ya koma mexico shirye shiryen auren sa next week

Lokacin jasmine da Ash sun koma yola cikin ta na neman shiga watan sa na biyar kenan.
Sai uban soyayyar su suke sha cikin arziki da wadatar rayuwa.

Washe garin laraba na satin
Shirye shirye aka somayi na tafiya bikin jamal
Don jabeer da jummai sun riga sun tafi tun ranar lahadi

Shima ashween kamal kawai yake jira akan zasu hadu a abuja sai a tafi chan tare.

Jasmine ta dada yin bul bul da katon cikin ta da ya mata bala'in kyau
Ta gama dawowa da Ashween abun wasan ta don ba irin waina shi da bata yi musamman da taga yanzun abu kadan na samun ta sai yayi hawaye.

Ranar da safe suka tafi abuja anan suka jira su salma daga chan lagos 

junior na hannun ash suka je gaida mamy don tunda abun ya faru ya sanar da ita komai da komai bayan sun dawo daga hutun su

Har da abunda ya faru tsakanin shi da jasmine da zahida komai saida ya warware mata

mamy taci kuka harta gode ma Allah..
Da kyar maganan ya wuce a zuciyan ta suka ci gaba da rayuwan su.

A mexico gaba daya aka taru aka sha hidima biki ya sha biki anyi pics kala kala.
Jasmine kuwa ba irin gatan da bata samu wajen yayun mijin nata
Sosai ta dada sakalcewa tamkar ita ce musu kanwa na karshe a duniya haka suka dauke ta.

Sai dai duk abunda ake yi acikin ranta bata iya mancewa da zahida musamman yadda ta ganta a asibiti tamkar rubabben gawa.

duk iya kokari anayi amma sam kamar ba ayi don kuwa wani wajen ya burme wani wajen a fuskan ta ya fice gaba daya tayi loosing shape din ta na asalin mutum

Gashi har yau Ash bai taba amsa maganan da ya shafi zahida ba ma bare ya je asibitin da aka ajiye ta yaga halin da ta ke ciki

Jamal shike kokari akan ta tunda yanzu shine babban su ya kuma yi alkwarin bazai kyale ta ba a ganin sa duk tarbiyan mahaifiyar su ya kai zahida wannan matsayin.

Tsawon wannan lokacin ashraf na zaman sa akasan wajen ganin baici nasara ba sai ya kasa dawowa nigeria.

Ranar da su Ashween suka dawo the same day kamal da salma suka wuce lagos abun su
Su sai suka tsaya a Abuja. 

mamy na zaune aka danna mata kira ta dauka a nitse sai taji maganan ba irin na mutanen mu bane da alaman wani a kasar ce ta da ban don english din su ya banbanta.

anan aka koro mata bayani hannun ta na karkarwa ta ajiye wayar bata iya cewa komai ba sai ta tsala ihu tana innalillhi wa enna ilahi rajiun,
timm ta fada kasa wajen sumammiya.



*KARMA is real friends do good and see good,.what goes around must surely turn around*
  I love u🌹





*surriem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top