89
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*FOLLOW UP-TILL DATE post Via myWATTPAD*
*@SURAYYAHMS*
*Musamman wanda suke nema daga farko kuje chan zaku samu komai a saukake.thanks*
*Page▶89*
Jasmine kuka take yi ta rasa yadda zata yi musamman data ga hankalin zahida a tashe yake itama ba ta hayyacin ta ko kadan
Tsoron ta ma kar itama ta harbe ta ne yarda ta harbe kamal mercilessly.
Don haka ta cigaba da jero adduoi kala kala a bakin ta zahida batace uffan ba sai kuka take tana tuki da uban speed.
A lokacin zuciyan ta ya riga ya bushe yanzun zancen ya dawo sabowa bata ta kan ashraf
don ganin tania yau ya sa ta soma tunanin lallai akwai wani boyayyen al'amari game da su
Shiyasa ta ga dole me ma ta rike jasmine
Don dan tasan zai biyo ta kuma dole tasan gaskiyan lamarin sa.
Yau jamal ya diro nigeria bazata amma bai sanar da kowa ba sakamakon yana so yayi ma yan uwan sa surprise musamman ma ashween da ya sanar da shi matar sa yai zata tare.
Tun daga bakin kwana da ash ya dosu yake ganin taron mutane ga motar kamal a bude anyi cirko cirko ga ambulance.
gaban sa ne yayi wani irin faduwa ya kara sauri suka iso dai dai wajen, salma ne aka sa sai kuka take yi duk ta rude ana kokarin sa kamal a mota da gagggawa zasu tafi
asibiti
Wani sarawa kansa yayi a haukace ya yo kan kamal din ya soma kiran sunan sa cikin zafin nama'
Nan bada bata lokaci ba ya bisu asibiti shida jabieer aka yi da kamal emergency
Da kyar Ashween ya ke iya tsayuwa don tsaban tashin hankali gaba daya ya kasa zama sai leke yake a operation room din ya ma kasa bin takan labarin meya faru.
An shafi kusan minti 40 a haka Can salma tace yaya har yanxu banga jasmine ba fa?sai ya juyo a hargitse ya kalle ta
Ya lumshe ido yana cewa innalilhhi wa enna ilahi rajiun,..
Jabir da tun tuni ya manne ma police report yana bin diidddigin labarin ai yana ji ance ba aga jasmine ba kuma eye witness yace mace ce tayi harbin a ransa sai yace
Tabbas mrs hidayat ce ta ci nasara akan zahida ta gurbata mata tunani
Don haka ya sulale ya kama hanya bai sanar da kowa ba ya nufi neman mrs hidayat a gidan ta don ya ci uban su ya karbo jasmine.
Zahida dake kukan fitan rai ta rasa ma me zatayi ma da jasmine din
Haka kawai ta ajiye ta kan kujera ta daure hannun ta da kafan ta tace zauna nan don in kika motsa sai na harbe ki...
Nan ta rufe ta a dakin tayi waje abun ta
Daga nan bata tsaya ko ena ba sai ta kama hanya gidan mrs hidayat anan ma ta gama buguwa da cocaine kanta ya dau chagi sosai...tayi rigingine akan seat din motar ta idon ta sun yi ja kamar garwashi
Tace daga farko zan fara da wacce ta fara kawo matsala a rayuwa ta ni duniyan nan ya ishe ni haka.
Don haka Tana yin parking ta shiga gidan zaune ta samo mrs hidayat wacce daga ganin yadda zahida ta shigo take rawa da kanta tana jajjan iska tasan tana cikin radadin kunci da tashin hankali matuka
Mrs hidayat tace zahida lpya kuwa,
Ko amsa ta bata yi ba sai ta fito da bindiga tayi nuni ma kan mrs hidayat din anan ta fashe da wani kuka mai tsuma zuciya..
Kafin Tace...ki sake fada min waye Ashween kuma meya kawo shi rayuwa ta?
A tsorace Mrs hidayat tace pls zahida ki kwantar da hankalin mana put d gun down sai muyi magana.
Zahida kam tayi nisa bata jin komai sai ma ta dada rikewa da kyau cikin kuka tace wallhy bana jin bazan iya kashe ki ba ,, ki fada min me kika sani akan sa yanzun nan.
Cikin dauriya mrs hidayat tace zahida meyasa kike so kiji maganan yanzu bayan da har inda kike na kai miki amma kika ki?
Zahida ta sake daka mata tsawa tace ni bana son surutu
I just want to know, nasan tunda kika tafi baki sake dawowa da gaske ne kin barni ne nagani da ido na.
So Tell me now ta fada cikin kuka da rudani.
Nan Mrs hidayat hawaye ya chiko mata ido don yau kam tasan zahida na matukar bukatar taimako a rayuwan ta
Sai tace mata da gaske ne Ashween shine lateef zahida wallhy shi ne.
Bayan labarin dana fada miki na malam na koma nabi diddigi na gane cewa wata hamshakiyar mace ce ta raine shi aka masa surgery aka sauya masa kama ,har ta masa aure da ita yarinyar da yakawo mana a matsayin cousin dinsa
Yana tare da mu ne yana gwara kan mu duk abunda kikaga ya faru dake dani da jabir da jamal duk shirin sa ne.
Nasan da da chan zan gaya miki wannan ma bazaki yarda ba shiyasa kawai naja baki na nayi shiru
Gashi Bani da shaida akan sa sannan ashween yana da kudi ninkin banin kin wanda kike da shi bare ni, tayaya zan tunkare shi da wani hayaniya?
Zahida sai ta tsaya durus jikin ta na karkarwa ta najin mrs rod kamar mafarki take yi ba a duniyan ma take ba.
A hankali taji gabbobin Jikiin ta suna mutuwa sai tayi kamar wancce babu jini a jikin ta hawayen ma bata san suna saukowa ba
A hakan har ta rusuna kasa kan gwiwarta tana sobbing cikin radadin kunci da zafin rai,
Ganin hakan yasa mrs rod ta ji wani shaukin tausayin ta ya kamata .
Tana kaiwa hannu zata dan taba ta zAhida ta haukace ta wani irin tsala ihu da wani murya na daban mai figitarwa sai ta dago tana bori tana dukan mrs rod tana ture ta kusa da ita ..
Cikin kuka da tashin hankali Tace duk ke ce duk ke ce ke ce kika lalata min rayuwa ta hidayat
Allah zai tsine miki bazaki taba shiga inuwar yafiyar ubangiji ba ta cigaba da kuka
Abun ya ma mrs hidayat zafi kam amma sai ta danne tace zahida pls stop blaming me,ki tuna kinada Lokaci har yanzu zaki iya daukar fansan ki akan sa Tunda baisan kin san shi waye bane yanzu
Zahida sai ta mike tsaye a zafafe tace kikace mene?
Na dauki wani fansa akan sa?ke asuwa? Wai a matsayin shawara ko me kike fada min?kin cuce ni hidayat, kin koya min munannan hali ,kin shayar dani mugunta Da da kyamAr mutane, mutane nawa na kashe a rayuwa ta nawa kika sa na tozarta?
And yet ke ce kika kashe min uwa da uba ,ke kika sa ni muka salwantar da rayuwan lateef da lailah..
and now look at me
Ki duba iirin rayuwar da kika jefa ni aciki,
Kinsa nayi soyyaya da wanda nafi tsana a duniya, monster da kika haifa acikin ki ,kanin kanin baya na kinsa na so shi na mutu masa,
nayi masa biyayya ya wulakanta ni na tayyara rayuwata akansa kinsa ya wulakantamin zuciya hidayat i was truly in love with ash ko baki sani bane..
Sai ta durkusa kasa ta cigaba tana kuka muryqn ta na rawa tace
Ya zalunce ni kinsa na dandana zafin soyyayr da bata da riba har abada kin jefa ni A kazama kuma kaskantacciyar rayuwa.
Kin sa Tun tuni yana kallo na a matsayin wawiya mahaukaciya. duk ke kika jawo min"
Ke ce ke ce kika fara komai kece.. tayi nuni da ita da bindigan a zuciye tana kuka tana karkarwa
Mrs hidayat sa da ta riga ta firgita ta karaya gaba daya da yanayin zahidan amma ganin a lokacin zuciyan zahida yayi weak sai tace just shut up and mind ur words ki dena gaya min haka zahida ke ya ta ce, kuma duk abunda nayi nayi ne don na kare ki,
Wato Har Kin manta lokacin da kike kuka baki so kije prizon na tura dana lateef at young age don nayi saving din ki ko?
kafin nan ma sau nawa ena ceto rayuwar ki daga fada wa kasa don naka sa miki wannan ? Wani irin hali ne ban shiga ba don na daga rayuwar ki ta yi kyau a duniya
Naji nayi miki rashin adalci akan mahaifiyar ki
Amma ni sadaukrwa nawa na miki a rayuwa zahida?
Yayan ciki na ne fa ance miki ban ji zafin kashe min yata da kikayi bane? Ko sadaukar da rayuwar lateef danayi akan ki ba komai bane.
Zahida ta cigaba da kuka a kasa batace uffan ba
Duk jabeer na labe najin su,
Mrs hidayat tace,look i know we hurt each otther Alots,amma toh ki sani don nace ki dauki fansa akan ashween ena nema miki sauki ne
don nasan nikam bazaii taba yafe min ba im har kema kina so ki zauna lpya a rayuwar ki ki kashe sa ki huta in munje lahira sai ayi mana sharia,.
Cikin kukan zahida da ta fashe da wani irin mahaukacin dariya mai dauke da kunci da bakin dacin rai... tace a duk inda yake yanzu nasan yana neman matar sa don kuwa tana hannu na na daure ta a gidan gonan sa gadon sa daya sa na tono asirin ki da shi..
ta sake fashewa da dariya tace ma mrs hidayat
Na gode da shawarar ki my dear wicked mom.
Amma ki sani lateef dinki yau ne zai yi asalin tafiya lahira ya sami lailan sa achan don kuwa in yazo sai na kashe shi.
Ke kuma ki saurare abunda zan miki don bazan barki ba .
Bana kaunar ki bana kaunar ki sake numfashi mai dadi a duniya prizon anan zaki wulakanta sannan ki mutu kaskantacciya.
Nan jabeer ya sullube ya bar gidan a hujajan ya nufo hanya a guje yana danna kira ma ashweenn
Shikuma Lokacin wayar sa na mota yana tare da jamal wanda tuni yazo wajen da aka sanar da shi halin da suke ciki da kamal
Sai shi ash yayi zaman jira kamal ya farafado tare da salma shi kuma jamal ya bi police aka shiga neman jasmine..
Ita kanta salma tasan hankalin sa a tashe yake matuka amma sam ya kasa nuna mata ya nace sai ya jira yaga abokin sa ya tashi kafin ya je neman matar sa dakan sa.
Jamal kuma ana chan ana zaga gari ana bincike da shi ko za'aji labarin jasmine
Da shike lokacin rana yayi an fara hada hadan dauko yara daga makarantu sai Mummunan Traffic ya rike jabirr a hanya
Gashi baisan da zuwan jamal ba bare ya kira shi ga wayar ashween na ringing a mota amma sam ba ayi picking ba
sam sai basira ta dauke masa ya kira jummai wacce take tare da su tuntuni
Don Yagama shiga qani yanayi hankalin sa yayi mummanan tashi.
Zahida ta daga bindiga kan mrs rod ta nuna ta dashi tace kar kiji komai zan tura details din kisan saminu da kika zo kikayi
Confessing da bakin ki a office dina
yanzu ma yan sanda zasu zo su kaiki gidan ki na gaskiya.ta fashe da dariya abun tam
Mrs hidayat ta rusuna kasa ta sake wani irin Kara ta dauka ko zahida zata fahimci abun su juya kan Ashween tare amma sai taga daban ne yanzu
Ko ajikin zahida cikin sauri sauri ta juyabta shiga mota ta bar arean gidan baki daya
A cikin motar ma kamar mahaukaciya take sai ta shiga tura sakon voice note emergency direct ofishin SSpolice..
daga nan ta kashe wayar ta gaba daya ta nifi inda jasmine take.
Shirin ta tsaf tayi cikin bakaken kaya ta daure kanta da bakin dankwali yau kam babu kwalliya don revenge ne zallah a zuciyan ta,
Jasmine ta wahala ga yunwa ga tsamin da hannun ta yake mata ga bakin duhu
Tayi kukan har ta gaji tayi shiru
Cikin haka ne zahida ta zo ta bude ta ta kwance mata baki,
Nan jasmine sai da ta sake wani numfashin wahala tare da hawaye
Wani murmushin takaici zahida tayi tana binta da kallo sai ta dauko ruwa mai sanyi ta bata ta sha
Tace yau zaki ji abunda nake ji jasmine.
Yau zaki ji zafin dafin soyayyar da Mijin ki kuma kani na ya dan dana ma zuciya ta
Ba ya dauki SO MAKAMIN CUTA ba?
Ya cuna ma zuciyata wutar soyayyan da har na mutu bazan mallaka se ba.?
Yau sai na sake kashe masa soyayyya a rayuwar sa kamar yadda na masa tun da chan akan wata banzar yar uwan sa da yake ikirarin ita ta fara son shi a duniya.
Cikin kuka jasmine tace kiyi hakuri dan Allah,
Wallhy yaya ba hakan yake nufi dake ba dan Allah ki nemi gafarar sa ku sasanta junan ku nasan zai yafe miki
Pls dont hurt him kiyi hakuri.
Zahida ta mayar mata da dan karamin murmushi tace jasmine kenan na san kina son shi sosai nima haka.
Ke In har zaki iya zama dani a matsayin gf dinsa a gidan sa kina gani yana ce miki ke cousin din sa a gaba na kuma kika zauna dashi hakan kiyi tunani
Wani irin sace zuciya kike ganin ashween bai iya ba?
He fooled me,ke ai yarinya ce ba a wasa da feelings so bazai taba zamowa makamin cuta ba jasmine,
can you believe dat har yanzu enajin ena son shi a raina?wannan natural ne saboda feelings ne...
wani irin wulaknci yayi ma zuciya ta duk akan na kashe masa soyayyar sa na farko a duniya?
Jasmine ta dago ta kalle ta kalar tausayi tace,kinyi gaskiya yayi kuskure aunty,a duniya kar ka taba dawowa da so makamin cuta wanda ya so sai ka so shi da gaskiya.
amma ki sani ke fa babba ce ke ce agaba da shi dan Allah ku sasan ta kanku, you can still make it..pls pls dont hurt him na roke ki dan Allah kiyiii min rai kar ki kashe min shi shika dai nake da shi a duniya kiyi hakuri.
Zahida tayi shiru tana saka wani abun aranta don harga Allah ta so ta kyale jasmine ta fuskan ce shi
Amma ena Tayi tayi ta dena jin diigon zafin abun aranta amma ta kasa
ji take kamar komai karya ne har yanzu ashween nata ne ita kadai.
Ji take in ma ta bar komai ya wuce ta rusuna don a shirya ta sani sarai
Ba zata iya cire shi arai ba soyayyar sa tamkar ubangiji ne ya dasa mata ita kanta bata iya control
Gashi duk da abunda yayi har ila yau a zuciyan ta ba abunda ya sauya na son shi
tasan kuma soyayyar su zallan cutarwa ne har abada shiyasa take ganin ba wani mafita sai dai wannan din da ta zaba a ranta
Kawai sai ta tashi ta cigaba da zuqan cocaine dinta saboda ta cire sauran imanin dake damun zuciyar ta akan maganar da sukayi da jasmine din yanzu..
Anan ma ta bugu ta bugu ta cire makanta hankali sosai sai ta shiga ta fito da hot acid da tayi niyyar zata watsa ma jasmine din tun da chan.
Sannan ta sa a ranta sai tayi hakan kafin ta kira ash tace ya zo ya gani da idon sa da ganan sai ta kashe sa ta huta.
*hmmm SO MAKAMIN CUTA ,So mugun wasa😂*
*Leeme hear your views please👂🏻👂🏻👂🏻👂🏻👂🏻👂🏻*
*surriem*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top