86

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.





*Page▶86*



Suna isa gida mamy tayi cirko cirko a falo tana jiran shigowar su abban ashrf da jasmine

Shikuwa da suka shigo agaba yasa ta yace maza ta wuce site din sa yana kallo har ta lume ba wanda ya isa ya mata magana.

Ranar rayin mamy ya baci don sosai don taso ayira wuta wuta ne komai ya wuce mata.

Jasmine Gaba daya ranar a site din abban ashraf din ta zauna tsaban tsoro yadda mamy ta birkice ta kasa zama waje daya a gidan ita kawai a fada mata waye uban cikin dake jikin jasmine

Anan ma Ta hana ashraf sakat ta sashi a gaba da bala'i ta daga masa hankali sosai sai da ranshi ya baci har sai da yayi mata kuka kafin ta hakura ta kyale sa

Haka Abba kuwa ya tirje yace sam ba wanda ya isa ya taba jasmine har sai hankalin ta ya kwanta ayi maganan cewar sa kar aje a taba masa jika.

Wannan magana ya matukar bata ma mamy rai musamman da ta fahimci abban ashraf  ko ajikin sa bai damu ba..

Shi dai sau daya ya tambaye jasmine din yace mata cikin na waye ne?
Bata ji kunya ba tayi masa bayanin komai sannan tace masa abba wallhy cikin na yaya ne ...
Yace Alhmdullh ,to gobe idan aka tashi magana bana so kiji tsoro ki fada mata komai kinga sai kowa ya huta ko?

Jasmine tace toh,anan tayi zamanta sai chan 10.30 na dare ya sata a gaba yace taje ta kwanta a dakin ta.

sannan yayi kashedin kar yaji wani ya daga ta sai da safe za suyi maganan.
Jasmine kam tun a asibiti data ji maganan a bakin mamy ta gode ma Allah yafi abun a kirga a zuciyan ta .

Yanzun ma Ta so ace ta gaya ma ashween halin da take ciki amma sai ta nemi layin sa iya nema amma shiru baya tafiya

Cikin daren tayi nafila ta dada nuna godiya ma ubangiji tare da dada nuna masa nadamar ta na kuskuren data tafka da kyautar da ya bata na farko

Tsaban murna hannun ta akan cikin tana shafawa ciikin tunanin mijin ta har bacci ya dauke ta.

Tun safiyan Allah mamy ta zo ta turje a bisa dikkan alamu kamar ko bacci batayi ba,
Ita dai duk damuwar ta yau ita mai zata fada ma Ashween game da cikin?

Abban ashraf haka yaki cewa komai ya ringa waina ta har saida aka ci karfe 10  na safe kafin yace ayo zaman..

Jasmine sanye da doguwar riga ta shigo falon abba sai ta zauna a a kasa daf da shi ta sunkuyar da kai kasa.

Mamy sam ta kasa hakuri tace ehem ena jinki ?
Nace Daga ena kika samo juna biyu jasmine

Jas tayi shiru tana tunanin yadda zatayi bayanin satan hanya ta keyi tana fita har aka samu

Sai mamy tace magana fa nake miki ko sai na tashi na miki dukan tsiya zaKi gaya min?

Sai ta soma kuka a hankali, tace kiyi hakuri mamy dan Allah kiyi hakuri

Mamyn ta tashi ta tsaya a tsaye idon ta har sun kawo ruwa don firgici tace ki kace nayi hakuri?ni ban san shi ba, Bayani kawai zaki min uban wa ya miki ciki agidan nan.

Cikin kuka Jasmine tace zan fada mamy amma kiyi hakuri dan Allah

Tace ni baruwa kawai kiyi magana ena jin ki, nan jasmine ta daure ta tsayar da hawayen ta amma sai ta sunkuyar da kai kasa tace mamy cikin nan na yaya ne don ni bantaba fita da kowa ba sai shi..daga nan tayi shiru

Mamy dake jin maganan kamar wani almara sai tace ki kace yaya? Wani yayan?

Jasmine Ta dago boldly ta kalli mamyn tace yaya Ashween ne.

Mamy ta sa hannu akai cikin wani irin shock  tace what? Sai aka bar ta kai a daure ta kalli nan ta kalli nan tace,Ashween!?toh how ,when?nace
Garin yaya?naga dai Ashween baiya ma zuwa gidan nan kwata kwata.

Sai jas ta tari numfashin ta da cewa a'ah mamy ai ni nake zuwa na same shi dama..
nan ma ta sunkuyar da kai cikin wani kukan tayi nuni da ashraf dake wajen shima tace wallhy gaskiya nake fada miki nidai nasan cikin yaya ash  ne
Kuma Yaya ashraf ma yasan komai ko jiya ma maganan da yazo gaya min kenan,yace min har wajen yaya ash din ya taba bina don ya tabbatar...
Sai ta karashe maganan murya kasa kasa  tace mamy ki tambaye shi zai fada miki ko yaya ashraf?

Aka bar ashraf da zare ido yana kallon jasmine din don bai san har zata iya furta magana har hakan ba

Mamy ta sake juyi cikin wani mamakin ta kalle sa shima tace ashraf?wato Kaima Kasan sa cewa jasmine tana fita gidan nan har zuwa wajen Ashween shine baka fada min ba?

Kafin ya amsa Nan abba ya sa baki yace ashraf, ka fadi gaskiya yadda kasan zaka mutu" ba maganan wasa akeyi anan ba haka ne ko ba haka bane?

Da shike duk rashin kunyar sa yana daraja baban na sa hakan don dolen sa ya ma jasmine shaida ya amsa da cewa eh suna fita da ashween
Yace a gidan ammy take samun shi
Ni na sha ganin su tare sai dai kawai bansan abun hakan yake ba ne.

Mamy ta dafe kirji ta sallame ta kwaso salati tana bin kowannen su da kallon mamaki

Wani turirin kunya ke tsatsafo mata tun daga dunduniyar kafar ta har tsakan kanta sai ta dan lumshe ido tana ji kamar a bude mata kasa ta shiga ta boye don wannan abun kunya.

Abban ashraf kam sai yayi murmushi a ransa yace yaran zamani kenan,dama duk wanda ya shiga tsakanin ma'aurata karshen sa jin kunya
don ko da kuwa kanada gaskiya in tayi musu zaki sai a mance da kai.

Mamy ta kasa cewa komai ta nemi waje ta zauna don jasmine ta gama kure mata tunani.

A ranta Tace ohhh, ciki har wata2 da kwana uku agaba na?sai naga kamar yarinyar nan ta sake agidan nan ashe tana chan sake da mijin ta,
Ashe toh an dade ana yi kenan ban sani ba.
Hmmm Lallai yaran zamani abun tsoro ne, uhmmm tohmm ban isah ba ai gwara maza Ashween ya zo ya dauke matar sa kafin ayi nisa..tabbb ni yau naga duniya dan ba kara.

Jin kowa yayi shiru jasmine ta dan kara sautin kukan tana cewa mamy kiyi hakuri wallhy ba laifin shi bane duk laifi na ne kar ki masa fada kinji mamy, ni na yarda barin sake kara fita a gidan nan ban fada miki ba dan Allah kiyi hakuri

Mamyn batace komai ba sai suka kalli juna da abban ashraf wanda ya gama gano kunya ne ya hana mamy sake magana a wajen

Sai tayi boyayyen murmushi tace yi min shiru awajen,yanzu ne kika san da haka?sai da kika dauko min ciki zaki ce min bazaki kara ba? wato har ni zaki na zagawa agidan nan ko jasmine?
Bakomai tashi kije ciki da kaina zan kira ashween din a idon ki kina gani bazaki koma gidan san ba..

Jasmine tuni ta fada kasa ta tsala ihu ta soma bori tana birgima cikin kuka tana cewa mamy dan Allah kiyi hakuri kar kice hakan wallhy ena son shi,ni gaskiya zan koma wajen shi ai yace bazai yi auren ba kuma ni kadai yake so ...

Borin nata abun kunya abin dariya amma mamy sai ta danne tace sai ta dan jijjiga ta yadda ita ma tasa jiya taji tsoro da fargaba sosai ranta
Tace nace ji tashi ki je ciki ,shi zai zo nan ya same ni shima.bani zaku mayar shasha ba..

Jasmine zata kara wani maganan abban ashraf yace mama na tashi abun ki,kukan ya isa haka, ai kema kinga da laifin ki kar ki sake aikata irin haka kinji?
Duk abunda zakiyi kar ki nayi a boye kinga in badon akwai wanda suka sani ba da ba mai yarda da ke..

Cikin kuka tace ayi hakuri abba nasan nayi kuskure,amma nidai dan Allah kar a raba ni da yaya na wallhy ena son shi.
Abban saida ya kasa danne murmushin sa
Yace jeki toh ki kwanta maza tashi..

Mamy dake makale da guntun dariya ,kunya da mamakin jasmine din tace barta kawai,ai jasmine bata jin magana ne kwata kwata musamman ma nawa.

Jasmine Ba musu ta tashi tana kan matse ido tana kananun magana ciki ciki don har ga Allah wani haushin mamyn yanzu take ji take kamar ta yi tsuntsu ta gudu a gidan

Nan Ta haura sama suna binta da ido
Fuskan su dauke da murmushi duka

Sai dai Banda ashraf wanda tun lokacin da jasmine ta sa yayi mata shaidan cikin ashween dan dolen sa ya kamo da wani bakin ciwon zuciya da bacin rai mai daci.

Anan duk idon sa sun gauraye da bakin ciki don haka ne ma bai iya cewa komai ba.

Bai tashi ba ya sunkuyar da kansa yana kan jin hirar su mamyn
Abba yace kingani ko hadiza ai saida na rokeki tum wuri ki maida masa matar sa kika ki baga irin ta ba,?

Mamy tace gaskiya ne alhj yau nima naga kuskure na
Insha Allah kuma na dauko darasi daga dan ba kara.

Yace alhamdullhi,
Tace yanzu ni zan kirashi yazo nan ayi magana sai a maida ta kawai tunda cikin satin nan zamuyi tafiya muma.

Abban ashraf yace wannan yayi dai dai, Allah ya shige mana gaba.

A sulale ashraf ya tashi suna kan hirar su ko takan sa basuyi ba bare su san meya ke ciki

Yana shiga dakin sa ya daka ihu mai dauke da kunan rai yana maka ma katifan sa duka cikin bacin rai.

Yace wallhy ba a isa amun haka  ni kenan na tashi a tutan babu?
Sai ya rarumi wayar da ya dauki videon su yayi screen shoot na wasu wurare suka dawo hotuna
Nan ya tashi a gaggauce ya soma shirin zuwa paris.

A ganin sa wannan ne kawai ya rage masa hanyar da zai hana komawar auren Ashween da jasmine,

Ba yadda mamy batayi da shi ya gaya mata mai ya kawo tafiyar gaggawa ba amma sam yaki yace yana so ya samu wani abun ne akan lokaci shiyasa zai tafi

Tun kafin ace wani karfe
2pm ya bar nigeria ya nufi paris neman zahida abun sa..

Mamy kam shiri ta shigayi na abubuwan da zata tarkata jasmine da shi kafin su sami layin ashween din.
Don daga ita har jasmine 
Din sun neme sa ba su same shi ba

Barin ma jasmine da ta gama rudewa mamy tace zata raba ta da mijin ta.
Karshe text kawai ta tura masa cewa dan Allah ya zo tana cikin matsala.

Har dare jasmine bata fito ba tana kan fushin ta da mamy gashi har yanzu ba wani motsi daga wajen habibin ta.

Bayan isha'i sai tayi wanka ta dauko sabon nightien ta da suka siya kwanan nan da shi da su kaje ukraine zuwan si na karshe

Dark royal blue ne mai tsansi mai dauke da dan fingilin riga mai tsiririn hannu kuma iya rabin cinya ta ciki.

Sai haddaden jacket dinsa na waje anyi masa vneck mai kyau shi sai ya dan zarce daf gwiwar ta ta haska sosai kalar ya fito da farin fatar ta

Tana jikin mirror tana kan masifa aranta cewa duk tsiya wallhy bazata zauna ba sai tabi mijin ta.
Nan Ta kama suman kanta da suka dada cikowa duk sanadiyar shigar cikin tana daurewa sannan sai
Ta juya zata haura gado.

Ko isa kan katifar bata gama yi ba wayar ta yi karar alaman shigar tex
Ta dauka cikin sauri ta bude tsaban murna bata saya wani suturce jikin ta ba ta fice a dakin ba ko takalmi tayi bayan balcony nan hanyar da ta saba fita a sace.

Ba tan tama Shine a tsaye sanye da baki da ash suit mai guntun hannu bisa ga dukkan alamu yanzun dirowar sa nigeria sai yaga sakon data turo masa tun safen shine ya taho kawai bai bi gida ba.

Da uban gudu take saukowa yana kallon ta har ta zo ta fada kirjin sa suka kankame juna

sai kansa ya  dan daure ya dan dago smilling face din ta dake faman jera masa sannu da dawowa,yayi kissing lios  dinta ligthly yana dada kallon yadda tayi matukar kyau cikin kayan baccin yace princess wato kina jin dadin ki dinga birkitamin zuciya na ko?meke damun ki yanzun i saw ur tex wai kina cikin matsala
Ni kuma ena jirgi yau,gashi tun jiya ban samu na zauna ba

Ta dan sake jingina jikin sa a shagwabe tace toh dama bazaka dawo din bane,yayi murmushi ya dan dada riko ta jikin baice komai ba sa sai tace uhmmmmm
Yaya, dama so nake kazo sai mu tafi gida ni na gaji da nan.

Yace kamar ya jasmine? ba munyi magana ba, ai nace zanzo na samu mamy da kaina na sake gwadawa
Nan ta dago tana kallon sa sai ta sa fuskan kuka tace uhm,uhm,kar ka wani same ta kawai mutafi ni yanxu nake so ni wallhy sai na bika.
Ya shiga lallabata amma sam tako ta kuma turje

Sai Abun ya soma damun shi ganin jasmine lallai da gaske take yi ita sam sai dai su gudu.

Ash ya ce ,jasmine hakan bazai yuwu ba
I can't..innna sace ki a gidan nan kenan me nayi? Kinga mamy zata dada jin haushi na ne kinga komai ya sake baci kena ko

Jasmine sai ta fashe da kuka tace wallhy nikam bazan zauna ba kuma ka tafi anan nima guduwa zanyi
Ya kamo hannun ta looking tensed yace meyasa? Wai wani abun aka miki ne.. kifada min mana.

Wani kasallen kallon love ta bishi da shi sai Ta kamo hannun sa ta kai kan cikin ta ,muryan ta mai dauke da kuka ta kafe sa  da ido tace yaya,Allah ya sake bamu baby
I am 2month old pregnant and i want to be with you ta karashe cikin kuka.

Lokacin Ya kasa motsi ya bita da kallo ya rasa a mafarki yake ko a zahiri yaji wannan maganan.

Wani irin kamo ta yayi cikin tsananin farin ciki yace,jasmine kika ce kina da ciki?
Ta dan tauro bakin a sakalce tace ehhh, ya daga ta sama yana juyi da ita sam hausan ko turancin ya dauke a bakin nasa sai ya shiga yaba ubangijin sa yana mika masa godiya da  kyawawan kalamai da harshen yaren turkiya inda suka zauna da ammyn nasa tun yana karami ita jasmine kuma bata ji don lokacin jaririya take bata ma san komai ba..

Tsaban farin cikin data ga ya durmuye sa saida ta yanke kukan ta soma masa dariya yana sauke ta ya jawo ta cikin shaukin jin dadi ya rungema ta tsam tsam a jikin sa yace Nagode jasmine this is one of the happiest day of my life
I love you ,i love you sooo much....
Cikin murmushi ita ma ta dada kankame sa ta mayar masa da i love you more

Duk mamy na tsaye kallon su daga sama kan step don dama ta shirya zata dan zo tayi ma jasmine nasiha ne kafin gobe sai ta tarar ba kowa a dakin shine ta leko don jin noise din su ta baya.

Ash lokacin ya birkice da murna da farin ciki yace tagaya masa duk abunda take so a duniya shi zai bata

Ita ko Sai langwamewa take jikin sa tace,ni kai kawai nake so
Yaya dan Allah ka tafi dani kaji? Bana so a raba mu ne.. ai da auren ka akaina gaka ko Allah bazai kama ka da laifin komai ba..

Ash ya dan yi shiru yana dada gyara mata jacket din nitie daya dan since yana dada bayyana boobs dinta a waje yace"jasmine kiyi hakuri wallhy bazan iya ba ne..
Is kind of disrespectful in nayi hakan ma mamy,
Ai bazata ji dadi nazo har gida na dauke ki haka kawai ba,

Mamyn fa ai kamar mahaifiyar mu ne kin manta ammy tace muyi mata biyayya ko?

Please ki kara hakuri zanzo da kai na dada bata hakuri nasan zata saurare ni ai duk laifi na ne abunda ya faru da chan ma kuma nasan na bata mata rai ne.

Jin hakan ya sa Jasmine kuka don gani take kawai bazata iya rayuwa babu shi ba,,yace
Pls pls wify kiyi hakuri ki bani uzuri let me do the right thing,

Jasmine kam ta rufe ido tace sam bata iya ji ba.

Mamy na tsaye lokacin ta share tears din ta don maganan san ya mugun sosa mata zuciya,
bata san har a yanayin farin cikin daya ke ciki haka zai iya bata uziri ba..
a ranta tace
Lallai shahida bata so ka a banza ba,kanada hankali da biyayya matuka kuma nasan kai kadai zaka iya rike amanan da tabar maka duka a duniya.

Nan ma wani sabon soyayya da girmamawa ta soma bashi a zuciyan ta.

Ganin jasmine na neman sake daga masa hankali sosai a wajen ya sa ta waske ta dan daure fuska sai ta fito sarari cikin muryan masifa
Tace suwaye anan wajen suke cika mana kunne?

A tsorace jasmine din ta koma bayan sa da gudu ta boye ta kankame sa sosai.

Sai Ya dan rusuna kai yace ena wuni mamy, ganin san kawai yasa taji
Kamar ta fashe da kuka don zuciyan ta yariga ya sanyaye

amma sai ta ce ayyo dama kai ne ka sake kawo min shashancin naku har gida kenan ko'

Sai Ta daka ma jasmine tsawa tace ,ke kuma kin wuce ne ko sai nazo wajen

Sam taki ta sake sa sai ma ta dada kankame sa tana hawaye da kyar ya bambaro ta ya dan tura ta kan hanya sannan ta haura sama tana bori tana bubbuga kafa

mamy kuwa tuni ta gama ji mata kunyar yadda taga ta fito almost half naked kafar ba ko takalmi Gaban su

Tana juyowa suka hada ido da shi alaman shima matar nasa yake kallo
Sai yayi saurin Sunkuyar da kai yace mamy dan Allah kiyi hakuri nasan nayi miki laifi, amma wallhy ena son jasmine

Ta dada turjewa tace yi min shiru marar kunya kawai
To dama ena neman ka gobe da safe a gidan nan kar ka bari na sake maimaitawa kuma.

A ladabce yace Allah ya kaimu mamy sai da safe
Ba tace komai ba ta haura sama ta barsa wajen,tausayin sa takeji sosai
Don ita kanta tasan ta shiga hakkin sa bana wasa ba.

Shikam bai damu ba don har yanzun murnan babyn sa yake yi ya najin koma miye za'a sake masa bazai ji
Zafi ba muddin bazai sake shafar jasmine da babyn sa ba.

Gefen ashraf kuwa yana zuwa paris yayi booking ticket nawani hamshakin pool party da za'ayi a cikin daren don an tabbatar masa cewa lallai zahida ma zata ce wajen.




*toh fa ga Zahida versus ashraf wai anyi gamo inji aljanu🤣😸😸*





*Surriem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top