85

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.


*Page▶85*



Haka jasmine tayi zaman ta kwana kin ba abunda take tunawa sai babyn ta.
Duk ta sa abun a ranta amma sam ta kasa nuna masa in suna waya.

A ranta She can only imagine wani irin zafi yaji a zuciyan sa da aka fada masa tayi hakan a lokacin..
Tadan yi murmushi ta goge hawayen ta a ranta tana cewa lallai yaya yana so na sosai.

Ranar sunan salma haka ta sake fita suka tafi da Ash dama ashraf shima abunda yake jira kenan ta sake fita ya tabbatar mata cewa ya ganta ba sau daya ba.

Anan ma gaba daya sai tana jin wani iri aranta duk ta rikice musamman data ga uban gata da Ash suka ma babyn
Sunan was grand anci an sha anyi shagali one in town.

Wani sabon jerin set din akwati aka sake ma wa salma ga kyautukka masu tsada data samu
Daga wajen mutane har mota sai da aka siya mata.

Duk wannan bai dame jasmine ba damuwar ta ace itama yanzun tana da ciki ne ko zata sanyaya ma mijin ta rai shima ya ga nasa a duniya.

Daf zasu tafi ummah tayi musu nasiha dukan su
Ta kuma yi ma jasmine addu'a Allah ya basu rabon su suma .
haka kawai ta kasa daurewa kuka take yi  a hankali amma sai tana boyewa ba wanda yasan halin da take ciki.

Around 7pm na dare Ya dauko ta  suka kama hanya
Sai dai duk yadda take danne damuwar tan sosai ya fahimce ta
sai ya dauke kai kamar bai san me take ciki ba ya cigaba da satan kallon ta.

Tana shiru sai Ya dan riko hannun ta daya yana kan driving yace baby tell u what?
A kasale tace what,

Ya dube ta yace uhmm dama ena so na fada miki zan yi tafiya ne zanje mexico.

Sai tayi saurin kau da kai wani hawaye mai daci ya soma saukowa batace komai ba
Yace jasmine daga magana sai kuka wai meya haka ne kam?
Tace babu komai yaya
Yace toh kiyi hakuri ai nafada miki mum tasan nine dan ta (not in details) ya fada
So, na yanke hukunci zanje na sanar da brothers dina gaskiya kawai mu fahimci juna don ban san me zata iya yi ba kar asake tafka wani mistakes din.

Cikin dauriya tace ok,hakan yayi Allah ya sa ku fahimci juna da su sosai atleast we have peopl we can call our family now

Ya amsa da haka ne tare da yunkurin parking  a inda suka saba tsayuwa.
Sai tace to yaushe zaka dawo ince dai bazaka dade ba ko yaya na? Ta dada shagwabewa idon ta acike tace i cant miss u for soo long kar kace zaka zauna achan

Ya dan ja karan hancin ta yace ,me zanyi achan din bayan kina nan ,karki damu bazan dade ba wify kiyi hakuri kinji ?

And na miki alkwari ina dawowa zan sake zuwa na same mamy ko zata amince mukoma gida kawai.

Nan ta danyi smiles tana dada jin sonshi na balbale ta sosai.
Ana Ganin idon sa kasan yafi ta jin baya so yayi missing din nata amma da shike yaga yanayin data ke ciki sai yana daurewa don ya ga hankailn ta ya dan kwanta

don tafiyar ta zamo masa kamar dole ne
Ash na matukar so ya kawo karshen duk wani abu da zai takura rayuwan su nan gaba.

Ganin itama bazata iya daurewa tana kallon san ba ko magana bata iya yi ba ta juya zata sauka a motar tare da sake wani shakuraren kuka"

Yace ya salam jasmine sai shima
Yayi saurin fitowa ya zaga waje ya tare ta tsaye gaban door din motar tana kuka kan ta akasa.

Kaf abunda ake yi ashraf yana kallon su
Don baiya minti 10 cikakke baizo bakin gate ba muddin in yasan jasmine bata gidan.

Ash sai ya shiga rarrashin ta suka rungume juna so tight tana rokon sa dan Allah ya dawo da wuri su tafi ita kam ta gaji

Abun na taba sa sosai shima ba yadda ya iya ne da hawayen sa shima sun sauko.
Yace ,ai alkwari nayi ko? ta gyada kai a hankali yace to kukan ya kare haka kijira ni kawai zanzo mu tafi
Pls ki daina kukan kinji?

Nan ta dago ta kalle sa ta gyada kai sai ya dan matso kusa da ita suka shiga bada juna mahaukatan kisses

ba su ko hankara ba direct and clear agaban ashraf wanda ke kallon su tsaf ya harde hannu yana gefe da bakin gate

Hasken mota daga chan ya fargar dasu yayi saurin cewa shiga gida princess ena ga abban ashraf ne  yake zuwa
Ni zan tafi.
Ta ce ok bye ta wuce a gaggauce.

Nan ma Ashraf ya bita da dan karamin dariya yana bin bayan ta kamar wanda tare suka dawo
Ba tace masa komai ba don gaba daya bata jin kanta dai dai..

Bai fasa bin tan ba Har saida ya ga secret hanyar da zata shiga yana kan dariyan ban haushi don ya dada tabbatar mata da ya ganta ya kuma san me take ciki.

A hanyar sa na fita daga anguwar Ashween bai iya wuce wa ba saida ya sauka ya gaida abban ashraf akan hanyar
Amma sai ya kasa fada masa asalin me ya kawo shi anguwan,

Shikam abban ya fahimta sosai shiyasa ma bai takura ba sai sukayi sallama.

Kwance tashi sai ya kasance yau kwana  biyar kenan da tafiyar Ash

jasmine kuma laulayin ciki kamar dama jira yake ta shiga wani tashin hankali kadan sai ya soma bayyana sosai a jikin ta.

Yanzun takanyi zazzabin safe da yamma ga nonowan sun dada cika sun tsaya sai ciwon mara kadan kadan da ciwon baya da take wuni da shi kamar mai jin alaman period..

Mamy ta kai makura wajen tashin hankali ganin yanayin jasmine kwana biyu amma sai ta cigaba da lazimin karya ne ba ciki ne a jikin jasmine ba.

Mai aiki kam saida ta kasa hakuri ta ce madam wani lokaci sai naga kamar kina da ciki
Jasmine sai ta waske tace  ita ba Ta jin komai a ena zata sami ciki? don ita kanta bawai ta yadda bane

Shiyasa ma bata damu ta gayaa masa duk abunda take ji a jikin ta ba a ganin ta yawan sex da sukeyi kafin ya tafi shine ya sauya mata hidimomin jikin ta har ake mata kallon mai ciki.

*Flashback*

Asali zahida ita ta kira ta sanar da Ash jamal yana so yayi aure amma basu da wanda zai musu jagora
Akan jabir ne kawai kuma tana ganin kamar bazai iya ba,

Anan sai kamal ya bashi shawaran cewa tunda zasu hadu awajen sai yayi amfani da wannan daman ya sanar da su gaskiya kawai.

#:
Hakan kuwa akayi A chan mexico ashween shi yayi ma jamal jagoran neman aure tare da jabir har akaci nasara.

Da shike duk yanzu sun  dawo wasu mutanen da ban sun shiryu sosai na ban mamaki
Ash bai sha wahala wajen kawo maganan cewa shine lateef din su ba

Sun razana kam iya razana don jabir tunda aka fara maganan yayi tsuguno kasa yana kukan fitan rai dukan su suna neman gafarar sa

Shikam bai damu badonn dama tuni burin sa ya cika tunda ya fitar da su da ga hannun mrd hidayat

anan ma  maganan fahimtan juna sukayi sosai da bro dinsa jamal da jabir
Har ya gaya musu halin da yake ciki da mrs rod da zahida..

Tun alokacin Jamal da jabir sai suka sha alwashin kare kansu da dan uwan su,
suka kuma nuna masa zasu taimaka masa kota wani hanya ne ko don su wanke abubuwan da suka sashi ya fuskan ta a rayuwa.

  Bayan kwana biyu jabeer ne ya fara komawa nigeria ya barsu da kyar aka rabu saboda kaf zuciyan su ya jike da shaukin so su tarairaya little bro dinsu su shagwaba sa da kulawar da da chan basu bashi ba.

Ash sai yaji wani sabon dadi da sanyi a ransa sosai
Nan Jamal ya sashi dole suka dan zauna a mexico bond din family na dada karfafuwa tsakanin su..

Washe garin da ash ya cika 2 weeks a mexico jasmine ne a daki ta kammala wanka tana shirin komawa tayi kwanciyar ta
Don sosai ta gaji da yadda ake mata kallo da tambayar kure a gidan

Ashraf kuma ranar ne ya gama shirin sa akan zaizo mata da magana
Don haka ba ko sallama ya shigo dakin nata ya tsaya durus yana kallon ta.

Tana tsaye jikin mirror fully dressed tace yay Ashraf lpya kuwa?

Bai amsa ba tukun sai da Yayi wannan shu'umin dariyan nasa yace "ke zan tambaya ai yanzu
Lpya kuwa, naga shi dadiron naki baizo ba ne kwana biyu?

Tayi wani irin shegen murmushi mai sauti tace yaya ashraf ai yaya Ash miji na ne.

Yace ohh i seee amma a gidan sa kike yanzu?ke dai kawai kice iskancin sa ke fitar da shi ke kuma jaraban tsiya gindi ba zip bazaki iya hana sa ba, hmmm kin shiga uku jasmine
duk da ma yana da karuwa a waje kuma kin sani sarai kike kai kanki wajen sa wai ance miki shi kadai ya iyayi da mace ne? Yana shirin yace mata gashi anan a gidan yaji in tace zata wulakan tasa sai yace zai gaya ma mamy komai

Amma Sai Tayi saurin tsaresa da tsaki mai sauti tare da cewa what eva,nidaii wallahy ka sake ce miji dan iska zaka ga abunda zan maka anan"sannan
in ka gama sai ka fita min don bana son cika Kunne.
Daganan bata sake cewa komai
Ta haura saman gado ta ja bargo ta rufu half
Waya ta shiga latsawa tana ready in yace zai mata wani abu ta kira mamy.

Shikam Bai daddaraa ba ya cigaba da zubo munanan kalaman batsa akan su gaba daya yana gwada mata ba abunda bai sani game da su ba.

Sai dai yana magana ne ammaa kamar da gawa bata ko motsawa bare tayi magana Abun ya mugun bata masa rai

A dan haukace ya karaso kan gado daf da ita zai mata tsawa tuni ta zugo qamshin turaren sa

Wani jiri ne ya daga ta da sauri a daburce tana tangal tangal ta rasa me ke mata dadi
bayi take so ta shiga amma sai tayi hanyar waje tana jan numfashi kamar mai jinnu

Anan fa shraf ya rude ya rasa meke faruwa da jasmine din
Ai kuwa  tana dafa kofar dakin ta rusuna ta zube gwiwa ta soma kwaza amai akasa tana kuka

Ba jira ya yo kanta yana mata sannu don harga Allah ya tsorata da yanayin ta

A sukwane ya soma kiran mamy ,ya hargitsa gidan da ihun kiraye kiraye.

jasmine kuwa kamar ana hura mata wutan aman ne don jin sa akusa da turaren na dada tunzira ta

Kowa ya fito abban ashraf ne kawai baiya kusa
Mamy tun daga ka step da ta hango jasmine idon ta suka ciko  da hawaye aranta tace wayyooooo ni hadiza na shiga uku kar dai Jasmine ciki ne da ita?
Take sai ta soma karkarwa ta kasa yin komai idon ta nakan jasmine tana bata close look

Alokacin brain din mamy ya birkice tunanin ta kar dai ace mata ciki ne da jazmine.
Tace To me zan fada ma Ashween?

A birkice ta karaso ta rike ta da kyau lokacin mai aiki na faman taya ta daga jasmine din dake kan amai tana kuka at the same time.

A dan razane mamy tace sannu jasmien wai meke damun ki,malaria ko?jasmine ko bata ko iya amsawa ba ta fada jikin mamy sumamiya.

Anan akayi da ita asibiti ruwa ruwa dukan su suka tafi aka bar mai aiki tana kimtsa wajen

A mota mamy na so ta tambayi ashraf me ya ma kaisa dakin jasmine
Don yanzu komai  a zargin sa take yi

Amma sai ta kasa tana dai so a tabbatar mata eh hakan ne ko ba haka bane..

Da aka shiga da jasmine din ma
Suna zaune a asibitin zuciyan ta na kan rudani tace kar dai hana yaran nan zaman auren su ya jefa jasmine wani damuwa har ta bada kanta ma ashraf...

Ta runtse ido ita kadai tace noo.nooo yah Allah kaji kaina yau no
Me zanje ma yaron nan in ciki ne da matar sa da yabaro a hannu na
Wayyooo na shiga uku..

Tana cikin wannan yanayi bata sani ba har doc ya fito
Wanda yayi dai dai da zuwan abban ashraf wajen shima

Sai ma kawai ya fuskan ce sa suka gaisa yana cewa alhamdullhi Alhj,

Ai an Samu karuwa yarku tana dauke da juna biyu na tsawon wata 2 da kwana uku kenan.

Abban ashraf ya ce masha Allah tubarkallah  sai yayi murna sosai ya gode ma doc

Lokacin mamy tayi suman tsaye haka shima ashraf.

Sai ta juya a gagagauce  ta shiga dakin  don ta same ta
Sai Tayo tsaye kan jasmine dake tsuru tsuru da ido kamar ba ita ba

Tace jasmine ena kika samo ciki?

Cikin sanyin muryya tace mamy ciki nake da shi da gaske?

Nan mamy ta daka tsalle ta mata wani ihu saida ta razana ta ja gefe tana bari

Abban ashraf ya kamo ta dam dam yace kull hadiza, kar ki sake kice zaki daga mata hankali ko baki ga halin data ke ciki bane?

Mamy Ta fashe da kuka mai dauke da rudani tace alhaji na shiga uku  mena aikata da kaina?

Sai Ya jata shikam har waje ya damka ta ma ashraf yace suje gida kawai shi zai taho da jasmine

Mamy tun a mota take hada ashraf da Allah ya gaya mata gaskiya in shine yayo cikin nan.

Iya rantsuwa yayi amma mamy sai kuka takeyi tana jimami

Bata ma san shima ashraf din a hargitse yake ba
Don gani yake plan dinsa nakan gadan zare saura kadan ya tsinke

don shikam yasan ba tantama cikin ash
Ne a cikin jasmine

Itama jasmine a motar abban kuka takeyi sai yana dan rarrashin ta ba tare da ya tambaye ta komai ba

Don aransa ma dadi yaji koda bai sani ba yasan jasmine dole cikin mijin ta ne a jikin ta ba na wani ba.






*Gud morning people we are pregnant👯🏻‍♀*







*surriem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top