77
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*Page▶77*
Gefen Jasmine kuwa duk da abubuwan dake damun ta dan dolen ta
tayi hakuri tana cin abinci normal
kuma ta soma dan sakewa har su dan yi hira sama sama da mamy "inda take fada mata za a soma gyara mata jikin ta tunda ta samu miscarriage,mamy tace ita da kanta zata kaita a dada kimtsa ta sosai ko dan taji dadin jikin ta.
Duk ana yi ne Sai dai zuciyan ta fall yake da son jin dalilin da ya hana ashween bai zago ya duba ta ba yau har sati biyu kenan...
Gefen mrs rod kuma ana neman karfe 8am na safe ba taga an fara kiran sharia'r ta ba sai ya sa ta shiga wajen judge tace ' mr judge dan maliki, ya dai an barni ena ta jira meye ne haka?
Yace calm down mrs rod
Na gaya miki Akwai muhimman abunda nake jira akan case din nan naki ne
Ki bani minti 20 za'a kira
Tace ince dai lpya ko?
Meyasa baka sanar da ni akwai jira acikin harkan nan ba.
Yace mata kar dai kimanta aikina da tsari
Kotun ne ta sauya lawyer mu da mai bincike da tantance case, amma kinsan ai duk munyi maganan wannan dake ba matsala ko?
Tace of cous, yanzu shi ake jira kenan
Alkali yace eh,pls sit down and stay put, kar ace muna hada wani abun dake kinsan ansamin ido..
Ba tace komai ba ta juya ta zauna ta tare da harde kafa.
Ko minti 5 bata yiba da zama saiga shi comitten sharia sun soma shigowa
sai tana binsu da ido tana murmurshii tana Allah Allah minute of success dinta ya zo
Har wani lumshe ido take don farin ciki..
Ana kan shiga sai ga lawyer mai bincike da tantacewa ya dosu,shima ta bishi da ido tabbas wannan bata san shi ba,sannan fuskan sa ba wasa ko fara'a,
tana kau da kai kansa ganin wa zai sake shigowa
Sai Zama ya gagara ta mike tsaye cikin wani razanannen shocking tana bin zahida da kallo,
Ga jamal ,ga kuma jabeer tafe.
Take fuskan ta ya tsatssafo da zufa zuciyan ta yayi bugun tara tara , ta rufe ido gam tana dan bubbuga kai a hankali ko zata tashi a mummunan mafarkin da take
Su kuwa Haka suka zo suka wuce ta gaban ta ba wanda ya mata kallon arziki
Kowa ya zauna aka barta a tsaye durus tana kan waswasin abun
Jin anbuga akalar sharia za asoma ya sa ta dan razana Ta zauna tsuliya a zage .
Gaba daya sai taji gwiwan ta suna karkarwa hankalin ta yakai makura wajen tashi, jamal, jabir zahida ? Kai wannnan ba alheri bane.tace ma kanta.
Ba bata lokaci aka soma shari'a
Sai gashi Tun kafin sharia yayi nisa, notin kan mrs hidayat ya soma kuncewa ta fara hauka.
musamman da aka kawo shaidan cewa tunda lailah ta mutu ,akwai lateef sannan bata da shaidan cewa yana raye ko ya mutu don haka anyi invalidating case din su lateef har sai an samo gaskiyan lamari in aka tabbata ya mutu shima sai azo ayi magana,kotu ta buga wannan,
Nan ma Ta hadiye yawu da kyar tasan wannan ya kubce mata kenan har abada ,
Sai aka cigaba anan aka dago na hanan hrnandez
Nan ne fa lawyer mai tantacewa ya bada korafin Hrod tana da will a karanta a kotu aga arzikin ma waye ne ,
mrs rod bata so haka ba,
Amma kasancewar akwai original will din Hrod a hannun lawyer wanda zahida ta bayar sai ta dakata dan dolen ta aka karanta.
Hauka sai ya kunce ma mrs hidayat aka dawo rike ta ake yi tana kuka.
Nan alkali ya bada izini aka ba zahida dama itama tafadi abunda ta sani akan haka
Zahida ta tashi Ba mutunci,ba kawaici ko kunya tsaf zahida tagaya musu komai, tun daga yadda mrs hidayat ke hana su sanin komai akan hakkin su na mahaifun su, da yadda take sirri da mulki da su akan hakkin sun, da ranar da ta soma ganin key din hrod a offishin mrs hidayat kankat ma har da case din rasa contract din plantation sai da bada bayani gamsashu.
Aka kuma baza proofs gaban kotu aka ga komai hakan ne,
Ga shi yau mrs hidayat ta riga ta fada ma yan jarida a sirri take rike da kudin yayan ta Marayun,
Take sai aka juya wannan maganan nata aka ba zahida gaskiya na cewa eh duk tana hakan ne don ta musu yankan baya da hakkin su.
Mrs rod Tace Allah ya tsine miki zahida uwar ki tayi asarar haihuwa,
zahida tsaban munafurci sai ta sa kuka ma judges akan akarba mata hakkin ta ita tsoro take ji, cewa anyi depriving dinta right na samun wani access da late mahaifiyar,
tace ko a hoto mrs hidayat ta hana ta ganin mum dinta, ita ta an toye mata hakkin ta na dan adam..a taimaka mata
Ta cigaba da kuka sai da
Kowa hankalin sa ya tashii gashi sai dauka ake yi a cameras ba sauki,
Karshe jamal ne ya rungumota ya zaunar da ita yana rarashinta,
Alkali yayi rubuce rubucen sa ,ya ce akwai mai magana? sai jabir yayi saurin cewa eh,
Nan ya roki alfarman kiti da a raba musu gadon su yau kowa ya huta,.
Bisa ga dalilai masu karfi kotu ba bata lokaci ta shiga kasafi aka raba gado chas chas ,batare da antaba na ashween da sisters lailah ba akan sai an bincika anji ko yana raye ko ya mutu duk dama alkalin ya san gaskiya.
Kafin azo wannan matakin mrs hidayat ta suma sau sha takwas
Sai ya dawo rike ta akaye kamar tsohuwar lagwani bata iya tsayuwa da kafan ta.
Asalin will din rod data boye tasan bata da gadon shi kona ficcika gashi da shi akayi shariar ba da fake din ba
Don a fake an nuna tana da 30% alhalin dik ashe karya takeyi..
Kotu ta zo karshe enda aka maida ma zahida dukkan abunda mahaifiyar ta ta bar mata ,,
Sannan da kaso ta na gado
Aka kuma bayyana mrs hidayat a matsayin azzaluman uwa, barauniya,mai danne hakkin marayu,
Ranar Kowa wani shafin jarida da gidan talabijin da kalar sunan da ya kira ta labari ya dawo latest in town
Dadin karawa kotu ta tsare ta tsawon wata uku..
Da likita da hukuma aka zo aka fitar da ita,
A lokacin mrs rod ta zare har tayi kusa yin ma kanta tsirara garin yage yage da fincike fincike tana hauka tana kuka tana zage zage...
Bata tashi sake suma ba sai dai jamal ya gaya mata bakaken magana, jabir ya kara mata da mai zafi sannan zahida ta cinna mata wuta a kirji suka nuna mata ita kadai ce yanzu a duniya, ba su santa ba..kowa kuma yayi hanyar sa.
Daganan mrs rod a motar ambulance aka tafi da ita ga hukuma akan ta suna kula.
Rayuwa yayi ma zahida dadi, duk da ma can kasan ranta taji wani digon tausayin mum din nasu,
A ranar jamal ya bar nigeria yace musu zai tafi mexico ya tada rayuwar sa a fresh,
Shikam jabir da ma ya gama plan dinsa har yakan je ya duba lpyar jummai a gidan gwamnati da suka dauki nauyin ta.
Bangeren ash kuwa yana isa lagos aka masa jagora wajen mr fhadul,
Duk da yaki nunawa amma zuciyan sa ta dan tabu da jin labarin halin da yake cikin
Domin yasan rasa shi wani mummunan rashi ne a gare shi,
Ya zame masa tamkar guadian angel wajen lura da hidimomin sa da sa shin akan hanya wanda shi kansa bai san da su ba,
wata rana yakan yi alfahari da shi yace da bazar sa yake taka rawa,
Mr fadhul kwararre ne mai ilmi da basira nagani na fada,
Dan ko shi ashween mamakin sa yake sha musamman in yana koyaar da shi abubuwa da dama akan harkan business, murde murde,da warware dukkan wani matsala komin girman sa ..
Dan dole ashween ke kiran sa da sir fadhul don dama yasan ya kai ma ya haife biyun sa ,
sai kuma gashi yana bashi kulawa ,so, kauna da girmamawa cikin amana irin na asalin uba.
Ashween ya zo daf ana sa shi a wheel chair alaman an fito da shi daga life surpoting machine ba dadewa ba ,
Sai ya shiga jera masa sannu sannu,yana masa addu'ar sauki
Mr fadhul ya nuna farin cikin sa na zuwan ash sosai , don haka ya sake neman alfarman su akan ya biyo sa suje gidan sa.
mamakin ash ya ke binsu bayan dankarrun motan da suka zo daukan sa ,
Wani anguwa daban yaga anyi da su wato victoria island.
Anguwa ne wanda ko wa ya san ta kafa tarihi wajen ajiye masu kudin gaske har da na barazana a garin lagos.
Cikin wata mansion aka sauke su.
Ashween yayi gum baice komai ba don kansa a daure yake,sai yana bin tsarin gidan da ido ya dan tabe baki ,wato motoci tsadaddu tsaban sunyi yawa wasu a waje aka jera su.
Sai ma da yaga an soma bada mr fahdul girma da gaisuwa na ban gajiya ya dada shiga zulumi
Yace toh lallai in har wannan duk mallakin mutumin nan ne to ba aiki ya kawo sa company na ba,
Haka suka shiga ciki daga shi sai ashween
aka barsu a wani daki suna zaune
Nan ya dubi ash ya ce,kayi hakuri nasan na takura maka yau kuma na shiga hakkin ka,
Ash yace bakomai
Mr fadhul ya gyara Yace masa ba komai bane ya sa ya na kira ka nan illah yau nake so nayi cikan burina na karshe a duniya,
Sai ya soma hawaye,
ash yace ayi hakuri sir Allah ya dada baka lafiyan amin ,
Mr fadhul yace,nasan baka sanni ba sai a companyn ka amma ka sani lallai kai ka kasance da na ne na hakika,
Ash yayi shiru don abun ya soma daure masa kai kuma amma bai tanka ba
Mr fadhul ya kuma daurewa yace ashween da na, nasan bani da lokaci sosai a duniya yanzu.
Amma zanso ka biyo ni na nuna maka wani abu,
Ashween dake shiru ya tashi Ba tantama ya bisa ciki
Enda idon sa suka ci karo da katoton hotan jasmine a manne a bango.
Ash yayi sauri yaje gaban pics din yana nunawa yace mata ce fa?
Cikin kallin mamaki ash ya sake ceawa How comes,ena ka sami hotun matata haka ,mr fadhul baice komai ba
Ya dada buda ma ash ya ga hotunan kala kala manne a bango iya kallon ka,
Sai ya kyale sa har idon sa ya kai kan hoton asalin jasmine din sa wasu na tare da shi wanda sukayi a dubai, uk, har da wanda sukayi a ukraine tun lokacin da ta samu cikin farko,.
Sai aka barshi da tantancewa chan ya dawo ya dada duban na farkon yace kai amma wannan kamar ya baci da jasmine,ya kalli mr fadhul yace isshe ur wife? Sistr or ?
Toh mu kuma meye na mu da sa hotunan nan mu anan sir, ash yayi dan dariyan karfin hali,don ya san shikan sa a birkice yake ya kasa dago mr fadhul har yanzu..
Shi kuwa bai kula ba sai da yagama tattaro abubuwa ya baza a a kasa ya kama hannun Ash zaunar da shi nan ya zauna ya shiga zayyana masa labarin rayuwar sa kaf ba ragi.
Mr fadhul Yana kuka ashween na kuka,Ash tun yana jin haushin sa har ya dawo ya karaya ya soma tausaya masa sosai a ransa yana jin nadaman san har na taba kokon zuciyan sa ,
Duka suka kasa rarrashin juna,
Da kyar ashween ya dago yace yanzu me kake so nace ma jasmine,nace baban ta na raye yana tare damu, yana kula damu all this while amma yaki bayyana mata kansa?
Mr fahdul ya riko hannun ash gam gam cikin jimami yace, i dont know son,nidai bana so na sa jasmine a kuncin rayuwa ne ko da na seconds daya ne.
Kayi tunani en har zata kalle ni wata rana zata tuna da ni nayi sandiyar mahaifiyar ta akan wata ya mace,kuma na barta ta rayu cikin maraici.
Yadda kake son ta ka kuma rike min amanan ta haka nake maka addu'an Allah ya so ka ya kuma rike amanar ka kamar yadda yayi,nasan kanada ilimi,amana da tarbiya da gaskiya ka taimaka min ka sa yata ta yafe ni ko su shahida da yar uwan ta hamida zasu yafe min"
yace Ashween Kuyafe ni, lokaci na ne yazo yau, nima kuma zan baku aman junan ku kar ku rabu da juna ku har abada ku kasance masu hakuri da zaman duniya
Bai bari ash yace komai ba ya kira lawyers dinsa
Da shaidu ,sai ya ma ashween kyautar biron ban girma da ya mallaka a hannun queen elizabeth of england na jajircewan sa da basiran sa.
Yace d'a na,ena fatan duk abubuwan da nake daura ka akai ka na fahimtar su sosai ?
Ashween da kansa na kasa sai Ya gyada akai a sanyaye yace eh,
Sai ya dauko files yace masa yayi signing duka a gaban kowa yana gani.
Ba musu yayi hakan
Sannan mr fahdul ya soma masa bayani yace wannan arziki na ne wanda na bar ma yata jasmine halak dinta ne in kaje ka bata.
Sannan ya sa masa letter a ciki nan ma yace duk abata
Sai ya dauko dayan file din yace wannan shine na rayu akai na kai har enda kake tunani na kai yanzu a kwarewan aiki zan bar maka su a matsayin garkuwa da kariya.ba zaka taba fadi kasa ba har karshen rayuwan ka da izinin ubangiji,
Allah ya maka albarka ya baka farin ciki mai daurewa..
Ash ya amsa yana kokarin tare hawayen sa.
Sai ya bashi wani file kuma yace wannan na jikoki na ne ,nasan bazamu hadu ba amma kace musu su yafe mun ena son su, nan sai ya fara tari mai tsanani..
Ash ya rike sa a birkice duk aka dawo ana saisaita shi,
Sai yayi kokarin conrol da kyar yace ma lawyers ga ashween shine kadai dangin na anan ku tabbata an mallaka masa komai dana bar musu,
Kalman shahadar ma bata kai karshe ba sukaji shiruuu Allah ya karbi ransa...
😪😪😪😪
*surriem*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top