76

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*🌹🌹AMARYA PRINCESS na cikin group din SURAYYAHMS fans page,Allah ya bada Zaman lpya ya kuma sanya Dubun Alkhairi cikin sabon Auren ki,Allah ya kawo juria na gari,ameen*


*Page▶76*



Alkali baiyi kasa a gwiwa ba ya shiga aikin sa, ganin alert daga ashween tun acikin daren sai ya sa shi kira ya sanar sa mrs hidayat akan yana da muhimman baki kuma zaifi dacewa su daga case dinta sai nan da 14 days in sun tafi kar su jangwalo musu wani abun..

Ba musu ta amsa ta amince don dama a private conference room za'ayi ba asalin kotu ba enda daga shaidu sai shaharrarun newsmen da yan jarida na kasa.

Awajen in kotu tayi mata licenced  ta mika mata transfer of will na zahida da  su lateef sai ta sa a watsa a labarai cewa rodriguez ta dawo da kafarta ga abubuwan da kuma ta mallaka

Ta dade tana shirin wannan rana don haka bata son wani obstacle ko kadan ya shiga tsakanin ta da cimma burin rayuwar ta.
Tace na jira shekaru dayawa ma sai dan wannan kwanaki?

A gefe kuwa Zahida ta sha mamki ita da saminu don bata yarda an daga karar ba saida saminu yaje ya jiyo musu gulman da kansa.

Nan tace yanzu mun samu damar tara wasu evidence akan mrs rod kenan
Saminu yace gaskiya zai yi wahala kice zaki nuna papers kawae as shaidun mu, karki manta mrs rod bata fara harka sai ta sayi bakin shugaban harkan

Nan ma saminu ya sake sata cikin zullumi sai ta koma gida ta zauna ita kadai tana tunanin duniya...ta tsorata sossai amma sai ta sa aranta
Ta ce ko mutuwa zatayi bazata bari a karbe hakkin ta tana raye ba..

Wani bin kuma tace to how can she do it,? Gashi shi kansa saminu baida idea bare ita..

Cikin haka wayar ta yayi kara ganin ashweeen ne ya sata sauke smiles dan dole.

Nan Ta sanyaya murya tace sai yau akayi lokaci na ko?
Yayi murmushi mai sauti yace my lady,
Me kike yi ne ya dan shagwabe.

Cikin nishadi da ya ziyarce ta bazataTace enaa zaune ne so lonely.

Yace oya kizo ki sameni a yola yanzu ena jiran ki a gida
Tace are u seRious
Har ka koma ne?amma shine kamal yace kana abuja.
To bari dai na zo ta daka tsalle dan murna ta katse wayar,
Nan ta tattara komai tayi shiri that moment tayi hanyar airpot.

Ashween Ya iso karfe 1.30pm na rana ita kuma ta iso karfe 4pmsaura  ta shigo garin

Ba laifi yau ashween ya sauke mata kai sukayi hira sosai kamar ba shi ba.
Taji dadi sosai ta kuma dada jin ta yadda da shi can cikin kokon ranta,

Sai dai Tai ta yi yafada mata meke damun sa taga bandage akai yace sam
Bazai fada mata ba sai ta gaya masa meyasa ta takura tana son magana da shi.

Nan mood dinta ya sauya, ta  ce masa tana cikin babban matsala and she needed somone to talk to..
Tace kai kadai na yarda da shi a duniyan nan yanzu
Kaine kadai garkuwa na ash
Yace bangane ba?ko Ki kina samun matsala da project din ki ne?
What happen

Sai hawaye suka soma sauko mata ta riko hannun sa tace mumy ne kawai,

Yace  ohhhh maam,

tace ehh, azzaluman nan,bakar muguwan ma yaudariya,ta ci amana na..ta cigaba da kuka,
Sai ya budi baki in xtreme suprise yace subhalllah zahida me kike cewa haka? Fada kukayi da ita,

Ya san komai amma sai ya fita nuna damuwan ta gaya masa meya faru a lokacin ,

Nan ta zuba masa labari komai da komai har maganan shiga koto abu daya da ash bai ji ba shine hidiman ta saminu
Sosai ta boye sai ta nuna masa yanzun ta rasa yadda zatayi ta kwaco hakkin ta ne .bata san ya zatayi ba

Cikin yanayin damuwan da bai kai zuciyan sa ba ya shiga salati yana sallamewa
Ya nuna mata abun ya dame sa matuka har da cewa baisan haka mum take ba,
Sai ya shiga bata baki yana ce mata komai ya kare insha Allahu shi zai taimake ta kuma ya bata assurance zata karbi hakkin ta ..

Ta dago tace but how ? Bani da shaida a kanta mai karfi

Yace, kince ance miki harda wil din plantatiom din ku ko?

Ta ce eh har da shi,
Yace to bari na baki shawara sai ki duba ki gani

Ta nitsu ta share hawaye tana jinshi

Yace tunda arzikin rodriquez duk na yayan sane ,kinga ko za'ace will din wanda suka mutu ne, ba ma ita za'a tranfering ba, ya kamata ma yayan rod ne wanda suke raye am i right?

Ta gyada kai,,

Yace good kinga kenan tunda kina ganin ure not eligible enougth ki tsaya akan dukiyan maman ki kuma kiyi fighing akan na baban ki.

Ni zan iya taimaka miki mu fitar da brothers dinki  a prison

Kinga Ranar sharia sai kawai sai ku taru kuyo defending hakkin ku,

I think yanzu ai kun girma da zaku rike arzikin ku da kanku
Sai aba kowa gadon sa na tun asali
Kefa kaso biyu kenan, sai ki karbi na mahaifiyar ki ki karbi kason ki na mahaifin ki kuma.

And i trust my baby nasan zaki iya handling dukiyar ki ba tare da taimakon wani wanda zai cuce ki ba..

Tayi shirruuuuu tana saka maganan tana hadawa tana jerawa  a brain din ta
Tace tabbas wannan zaifi mata ciwo in mukayi haka,
Kaga ko a haka na rama abunda ta min
Shikenan A garin neman hadamar ta sai mu karbe komai kowa ya rike nashi a kyale ta da halin ta .

Ai nagani a asalin will din mahaifin mu bata da komai, ashe duk karya take yi baita ba
Sai ta sa aka yi fake duk nagani..

Ash ya jinjina kai yace,
Kar kiyi gaggawa kuma ni shawara kawai na baki
Atleast kinga kema kinyi adalci ko?

Tayi murmushi ta taho zata rungume sa ta hada masa kiss sai yayi saurin kaucewa gefe:

Tace baby,haba dan Allah ni kenan kullum haka?
Kamar zatayi kuka ta kuma cewa I tot yanzu mun zama daya ni da kai tamkar jini daya ne,
Kasan sirri na baby meyasa bazaka bari naji dumin jikin ka ba? dont u think we need some sexual connections, baby aure fa zamuyi

Sai ya sauya mood ya mata shiru tana ta magana ita kadai, sai tace yawwa ya kamata ma kace wani abu akan weding din, like yaushe zamu soma shirye shirye
Don nifa ena karban hakki na wajen wancan shegiyar sai muyi auren ko?

Ash ya saukar da kai kasa kamar wanda yaci kudin aika still yana shiru

Nan ta sha jinin jikin ta ta dago sa a hankali ta ga fuskan sa a murde,kamar mai shirin yin kuka sai alaman damuwa sosai ya bayyana,

Tace meya faru Ashween yanzun nan muna magana lpya lpya,sai ka kuma sauya fuska ?
Ko na nafadi wani abu ne
Marar dadi.pls tell me

Ya marairaice kalar tausayi ya rike hannun ta yace,tsoro nake ji zahida im scared baby, ina son na fada miki wani abu amma ena tsoron rasa ki a rayuwa ta, i want to be with u ,bana son ki rabu dani

Tuni tom and jerry suka soma mata zanen flower so a brain din ta, tsaban dadin words din nashi da ta ji har wani iska mai dadi ne ta zuka ta hanci cikin kula sai tace tell me mana dan Allah ,meye matsalar
Kaima kasan A duniya  banga mai rabani da kai ba,dan Allah ka fada min ..

Yace uhm uhm zahida, gaskiya ena tsoro musamman ma yanzu da muka sa maganan aure agaban mu,i dont want to loose u,ena ganin maybe kice bazaki aure ni ba.

Nan hankalin ta ya soma tashi sosai don ta dauka ko zaice mata ance daga gida  ya auri jasmine ne tunda tana da cikin Sa sai su zauna tare.
Tayi shiru Batace komai ba
Sai ya dago ya nuna mata shatin canula dake hannun sa alaman Yayo kwanciyar asibiti sai da bandages din Kansa daya ki cirewa.

Yace baby na miki karya tun ranar, accident nayi bana ma abuja ena lagos

Pls Kar kiga laifin kamal ni nace ya gaya miki hakan

Cikin terifyn mood Tace o my god, haba baby shine nake tambayar ka bandages din meye ne  kaki fada min?

Sai ya dakatar da ita ya dada sauya fuska yace
Ba haka bane zAhida, bana so na daga miki hankali ne,

doc ne yace ,.ya..ce

Sai tace yace me..sai ya dukar da kai kasa.

A sanyaye yace i lost my potency sanadiyar hatsarin danayi,zahida bazan iya komai da mace ba.

A hargitse ta mike tsaye tana kallon sa tace what?me kace?

Sai yayi saurin riko hannun ta yace "Amma Kuma yace zan warke sai  dai ba da wuri ba sai nan da 6-9mont,ya marairace yace
Kuma kina son auren da wuri ko?.kinga ba amfanin mijin da bazai iya biyan hakkin wife dinsa ba
Im sure u wont like it..

Ta dan ja da baya ta kalle sa taga duk ya nuna damuwar sa ,ta dauki mint 3 tana shiru
Chan  tayi ajiyan zuciya ta dawo ta zauna ta dan ja karan hancin sa tace har ka tsorata ni wallhy,

Na dauka zakace an aura maka wata ne ba ni ba, don gaskiya kishiya ne kawai bazan iya zama da ita ba.
Dum da ma still bazan bar mata kai din ba.

ya dada sunkuyar da jai abun sa ,kalar tausayi

Sai tace hey baby, ka gani
Kar ka damu da wannan maganan, ko shekara ne zakayi baka warke ba ni zan jira ka ,kar ka manta i love you alot damuwar ka ai nawa ne.
So stop worying urself am ok with it kaji?

Yayi takaitaccen murmushi yace ,nagode zahida har kinsa naji sanyi a raina"

A ranta tace wow ashe haka Ash yake so na?im so stupid da na kasa fahimtar sa tun da chan,
 
Yace  na yarda yau,kuna nagani baby na tana so na.and i promise u zan tayaki figthing akan koma waye a duniya da zai takura rayuwar ki, im here for u.

Tsaban dadin kalaman san bata iya bude baki ba ..sai murmushi kawai takeyi, irin yau ni ashween ki zuba ma wannan kalamai?..its a dream come true to me.

Tace to sai muje muci abinci ko naga 6 ya wuce

Yace ah a sallah zamuyi baby,

Tayi saurin cewa toh shikenan, sai ta haura sama don ma kar yace taje ita ma tayi sallah

Don bata son hakan ko kadan,ta tsana. gani take alwala takuri ne bare kuma rufe jiki da sa  goshi akasa yin wani sallah.

Tun daga ranar komai ke tafiya mata dai dai
Don ashween yana kula ta ya kuma sa mata hannu sosai akan hidiman fitar da su jamal

Abune mai wahala kwarai amma sai ya nemi taimako daga chan sama aka sa baki Aka sake musu brothers dinsu ana washe garin shiga kotu da mrs hidyat.

Ranar da su jamal da jabir suka fito Sunyi murna kwarai suka gode ma ash,

Nan zahida ta gaya musu komai abunda ake ciki,
Duk da ma ba suji mamaki ba

Jin an dago maganan lateef da lailah yasa jamal ya sake shiga wani hali,yace  yayi nadaman yadda suka salwantar da rayuwan su yana daya daga cikin abunda ya ke damun sa sosai a ran sa yanzu.

Ash yayi shiru yana kallon sa don har ransa yaji dadin jin haka, sai jabir ne ya rarrashe sa shima cikin nadaman rayuwa,

Jamal din yace dama baida niyyar komawa ma familyn rodriquez rayuwar sa kawai zaije yayi sabo,
amma kodan ya hana a sake aiwata wani zaluncin da hakkin su lateef zai amince ya bada hadin kai aje da shi kotu a tarwatsa mum din su.

Jabir yace kayi gaskiya, nima ya zama min dole saboda ni kaina bansan eya adadin yayan ciki na da aka kai ophanage homes ba.samun saukin kawai yana da tabbacin duk na garin nan ne ba a fitar da su ba , sai ya yanke hukuncin in ya karbi kudin gadon sa zai raba biyu ya kai gidan marayu,

sannan yace yana so ya auri jummai tunda ance yanzu tana dauke da cikin sa kuma ta kusa haihuwa,

Ashween kamar zaiyi kuka jin wayannan kalmomni a bakin su.
Yace ko bai gaya musu shi waye bane a wajen su lallai nadaman su ya biya shi.

Zahida kam murmushi take binsu da shi, tana kaunar su sosai kuma taji dadin sauyawar sun amma ita kam yanzu take jin zata fara cin duniyar ta don haka zuciyan ta bata nan yake ba ,

Bata furta ba kam amma ko kadan cikin ranta ba damuwar ta wani hakkin lateef ko lailah bane,
Damuwar ta sabon rayuwan arziki da zata shiga ciki, ga masoyin ta Ash ,sannan ga shi ta na jin zata dau fansa ma mahaifiyar ta ta hanyar wulakanta mrs rod bayan sun karbe dukiya a hannun ta gobe..

Da safer rod ta riga kowa hallara ,taci kyau iya kyau sai hotuna media suke daukawa

Tsaban farin cikin dake balbale a ranta har dan takaitaccen hira tayi da media ana dauka

Anan tace musu tayi aiki tsawon lokaci cikin sirri da jajircewa wajen rikon amana kudin marayun yayan ta, sannan yau zata nuna ma duniya ita kanta mai ta mallaka, kuma duk abunda ake zargin familyn ta dashi yau zata wanke.

anan a wajen su jamal kaf An gama shiri, zahida ta karbo komai a hannun saminu, sannan suka shiga mota su ukun suka kama hanya..

Ashween bai samu damar halarta ba saboda anyi masa kiran gaggawa daga lagos cewa dattijo mr fadhul na cikin wani hali, kuma yayi umarnin ace masa ya zo akwai muhimmiyar magana da zai gaya masa.



*Good morning people, ni dai nace im a woman and i lost my potency irin na Ash🤣😸😂 amma nasan kawayen zahida ne kawai zasu yarda*







*surriem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top