74

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.




*Page▶74*





Tun tafiyar ashween mamy ke kuka sosai a dakin ta dama dauriya kawai tayi don  aganin ta hakan ne kadai zaisa ta karbe ma jasmine yancin ta nan gaba.

Abban ashraf ya shigo baice uffan ba ya dawo gefen ta ya zauna.

Dama yana cikin masallaci ake hayaniyan amma da shike itace ke da alhakin su duka biyu sai ya zuba mata ido yaga kalar nata hukun cin.

Kuka take yi kanta a kasa kamar wacce tayi laifi sai yace kiyi hakuri hadiza kukan ai ya'isa haka

Its so obvious that u cant hurt sumone witout hurting urself,
Ni aganina hadiza anya harshen ki baiyi tsauri akan yaron nan ba?

Wai Duk akan ya kawo wata mata cikin hidiman ...gaskiya banji dadin kalaman  ki ba .
Na dauka zaki bi abun a sannu  ai  ashween yaro ne
  na tabbata ko shahiida na raye yau bazata taba furta masa haka.kiyi tunani dai

Nan ta dago murya a sanyaye tace nasani alhj,na sani.

Amma kuma hakan nayi niyya nafi so nagaya masa hakan shyasa kuma na fada.
Kaiwa nan ta tashi ta fuce abunta

Girgiza kai kawai yayi yace toh Allah ya kyauta

Gefen ashween kuwa  a lokacin Ya turo kofar ammyn ciki  da karfi idon sa sun rufe baya ma ganin gaban sa sai ya soma tahowa enda shimfidar ammyn yake nan ya zube gwuwir sa a kasa yana kan kuka mai cin rai.

Koran sunan ta yake Tamkar a gaban ta yake.
  Yace" dan Allah ki dawo ammy nasan zaki saurare ni,come bak to me mother i ne..e.d you.
Nan ya cigaba Ya fada ya sake maimai tawa

Har ya kife kansa akan gadon"bai fasa ba can kasan makoshi yake cewa ke daban ce ammy nasan ba zaki taba rabuwa da ni ba har abada kina so na ,ke kadai kika san ena kaunar ku baki daya kuma bazan taba butulce miki ba bare na ci amanan ki,

Bakin sa  har na rawa yace i love her ,ena son jasmine ammy ki zo ki fada musu, pls come bak bazan iya rayuwa na a hakan ba
.
Babu ke babu jasmine banda farin ciki
today i feel so guilty an scared
Ki taimaka min ki dawo mana

,.. sai ya lumshe ido yana dada matso zafafan hawayen sa yana jan katifan da hannun sa cikin tsananin tashin hankali da firgici bai masan meya keyi ba

A Brain dinsa Ya rasa  maganan wanne daya cikin jasmine da mamy zai dena tunawa don ya samo sauki ma zuciyan sa.

Duk da ma yasan maganan mamy yafi masa ciwo amma har yanzu yana jin tsananin bakin ciki kufcewar jasmine a rayuwar sa.

Wani Bacci mai nauyi ne bazata ya dauke shi a wajen a tsugune kan gwiwar sa.

Cikin baccin yake jin yadda ake shafo suman kansa ana calming dinsa amma Allah baiyi zai iya juyawa ya ga waye ba ne
Tsaban yadda yake jin dadin yadda ake calming dinsa sa shafowar kan ya sa shi jin dama dama a ransa.
Amma  sai ya shiga  cikin zulumi to waye yake rarrashin sa haka.

Sai ya budi baki yace ammy na ke ne?shiru baiji an amsa ba.ya dan ja ajiyan zuciya yace pls come back to me mother ki zo ki saurare kice mamy ta bani mata ta wallhy ena son ta ... Bayan nan shiru yayi kamar wanda aka ce masa yayi

Chan kuma sai komai ya dauke masa kamar film firgit ya bude idon sa yaga sarari ashe shika dai ne ba kowa

Wani perfect silence ne ya dada ratsa dakin aka barshi da rarraba ido a tsugune a kan kafar sa,

Nan wani mummunan Jiri ne ya debe sa ya zube kasa a take baya ko
motsi.

Kamal na jirgi amma sam hankalin sa bai kwanta ba
Yayi iya kokarin yaga ya samu wani information akan meke faruwa sa ash amma shiru

Gashi Tun karfe 6 yake jirgi  daga chan yankin antactica daura da north america wurim akwai nisa sosai da africa sai ana neman 5.30 pm ya diro nigeria

  Layin ash still Ya kira ya kira amma shiru ba a dagawa
Nan ya dada birkicewa jikin sa yayo sanyi yasan ba lpya ba.

Inda salma take ya soma zuwa ya danyi refreshing kansa ,ita ma duk ta sa abun arai daurewa kawai takeyi take masa smiles don karfin hali

Yana cin abinci a gaggauce yace mata ki kwantar da hankalin ki, zan je na dubo sa yanzun
Na san endai har jasmine bata saurare shi  yau ba bazai hakura ba and i know where to find him

A sanyaye Salma tace pls do,
Allah kadai ya san ya yake ji yanzu na tausaya ma yaya ash baka yadda yake ba ne dazu.

Koma meye ne i dont think jasmine zata tsawwala wannan hukunci akansa its so unfair.

Kamal yace, hakane mine..ya muka iya?ai ku din ne sumtimes zuciya baya barin ku.
Ya tashi tsaye yace"Let me be going in na same shi zan kira ki ko?
Ta gyada kai ya mata light kiss ya fice.

Ba tantama ya nufi hanyar gidan ammy lokacin daf 6pm na yamma.
Ganin motar sa a parker ko rufewa ba'ayi ba ya sa yayi ajiyan zuciya tace thank God

  Shima Yayi saurin parking ya shige cikin gidan.

Ko ena ya duba a kulle sai ya rasa to ena ash ya shiga,chan sai wata basira ta zo masa ya biya ta site din ammyn

Da shike a bude ya bar kofan Tun daga step na haurowa na karshe ya gansa a kasa baya ko numfashi bare motsi

Da gudu ya iso ya tsuguna gaban sa yace Ashween ya girgiza sa..
A hujajan ya tallafo sa da kyar haka ya ringa yi har suka fito waje ya sashi a mota sukayi asibiti

Emergency aka shigar da shi likita ya akai awa 4 akansa yana duba shi
Kafin nan salma har ta zo tana taya kamal zaman jira har ana neman 9pm na dare,
Nan doc ya fito ,ya ma kamal izini suka shigo office:

Kamal yace ya jikin nasa meke damunsa doc?

Doc yace, yanzu dai da sauki sosai amma zai bukaci kulawa na musamman
Tunda sunada home doc i advise ace ta matso kusa da aikin ta kar ciwon yayi nisa.

Kamal yace ban fahimce ka ba ciwon me?
Ash is perfctly fine baida wani ciwo..

Salma tace calm down mine pls doc kamana bayani

Doc yace kanada gaskiya, sir Ashween  baida wani ciwo amma yanzu an samo wani abu da yake so ya dago wani tsohon miki  dayake fama da shi da chan"

as a child, late hijy shahida ta bamu medical records dinsa kuma mungani ya taba fama da emotional trauma a brain din sa.

It was a succesful treatment gaskiya amma yanzun naga wajen  na neman ya sake tabuwa shiyasa nace
U have to be careful pls

Kamal ya dan dafe kai yace la hawla wala kuwwata illa billahi tuni salma ta shiga taro hawayen ta dakw shirin sauka da hanu cikin ranta tace jasmine mahaukaciya ce Allah kadai yasan me aka masa yanzun..dis is so unfair.ta karashe tana dada share hawayen nata

Cikin dauriya kamal ya ma likita godiya suka fita suka taho da ashween zuwa gida
Cikin motar Baice komai ba ya jingina kai a kan seat an nannade masa da bandage wanda ya ji sedative 'anxiolytic" sai cannula dake manne a jijiyan sa alaman Bai gama shan ruwa ba.

Kowa da abun dake ji aransa kamal ya taimaka masa suka ajiye sa agida
Aka kawo nurses biyu maza masu lura da shi kafin doc ta iso.

Da kyar ya kwakwulo murmushi ya musu sabida yaga hankalin su sam baya jikin su..

A haka kamar ba zasu barshi ba amma ya sa su dole suka tafi.

Zahida na chan bata damu ba ,dama burin ta daya ne taga an soma maganan aure kuma tunda ash ya yi proposing bata da case da kowa

Yanzu hidiman ta da saminu take so ta karfafa don ta sa arai kafin tayi aure zata karbi dukiyan ta tas,so that she wont have to give saminu any sex in da auren ash akanta.

Jamine na daki na kwance sai yanzu ta samu tayi shiru fuskan ta har ya haura sai dai jikin nata yayi zafi sosai

Taso ace mamy bata fito ba lokacin da yake ce mata i love you,
A ganin ta ba tantama zuciyan ta zai iya saukowa ta bishi taji me zai fada matan da ya dage ta saurare shi.

Tayi juyi kan pillow nan aka sake yin sallama da abiinci
Mai aiki tace hajiy mamy tace na sake kawo miki wannan ko kina bukata?

Batare da ga meye bane tace na koshi, ki debe sauran ma ki mayar kitchen ni bacci zanyi..

Ba musu mai aiki ta aikata hakan
Inda suka CI karo da mamyn

Sai Ta bude taga abincin rana dana dare duk ba ataba zu ba ga sauran na safe da baifi 2 spoon tayi ta ajiye ba

Tace ma mai aiki me takeyi ne dakin haka
Tace bacci tace zatayi hajya

Cikin damuwa mamy  ta karbi cooler daya ta koma da shi amma still haka fir jasmine ta ki tashi  sai ta cigaba ma da baccin karyan don kae ace za'a sata dole ta ci

Washe gari da safe kamal ya zo daf asalin doc ta gama duba sa

Tace ma kamal ka taimaka ka taya ni pls is getting worst
I think he need to relax kar ya jawo ma kansa matsala
Kamal yace bakomai doc i got this.

Sai Ya raka ta har waje ta fice ya dawo
Baice ma ashween komai ba tukun duk da ya lura da silent tears dake bin kuncin sa

Sai ya hada masa abin ci ya sa shi dan dole yaci
  Cikin masifa da rarrashi yace haba ashween zaka kashe kanka ne?
To bismillah ai sai kayi gaggawa ga fili

Murya a dishe Ash yace wallhy bazan iya bane  kamal
Nakasa cire abun da suka ce min araina.

Nan kamal yace pls share  it with me zaka samu relieve kar ka bari  a ranka c'mon
ba musu ash ya shiga bashi labari komai da komai nan ma yayi kuka sosai gwanin tausayi yace kamal i cant do this anymore,jasmine is my life, bansan ya zanyi na samu ta sauko ba i felt so alone.

Kamal Ya riko hannun sa cikin radadin zuci yace kayi hakuri ash, na lura dukan su da bacin rai a tattare da su but thy dont mean to say this words to u.

Ash yace kana ganin haka ne ko? Niko ena ganin
Na riga na bata rayuwa ta ne.

Kamal yace stop it, ya isa haka kanaji ai ance maka
Baka da lpya sosai ko?
Meyasa kake ba da zuciyan ka waje ta na dada raunana ne ash ,

cmon stop it, be a man nasan zaka iya kuma ena tare da kai
Even if the world are againts ni u nasan zaka iya fighting wannan challenge din
Yanzu Ka nitsu musan yadda zamu shawo kan al'amarin komai ya daidaita

Ash Ya sauke ajiyan zuciya yace  but i dont have any idea
Me zanyi yanzun, atleast na raba zahida daga cutar da jasmine har abada shine kadai gain dina.
So whats there to think of?

Kamal yace "many things,
Like dawo da matar ka ku zauna na har abada .
As long as kana kwance anan kana kuka,kana blaming kanka bazaka gama abubuwan dake shiga tsakanin ka da farin cikin ka ba ash

Pls get up and stop all dis.

Ya lumshe ido yace toh naji,ure right
Amma i think i need some space to think

Kamal yayi ajiyan zuciya yace yanzu naji magana.
Insha Allahu komai zai daidaita u will have ur wife bak  ok?

Ya gyada kai yace ok boss,
Kamal yayi murmushi juya ya fuce ya barsa

A hankali ya ke kawo komai a ransa tun daga farko yana tacewa.

Wani bin yayi hawaye wani bin yayi murmushi yadda zai ajiye maganan jasmine a gefe yayi dealing da su zahida ya ke masa wuyan yanke wa

Har ga Allah yasan abu ne mai wuya yayi rayuwa babu jasmine kusa da shi
Amma yana ganin dole ya karbi hakan don yanzun shi kadai ne masa mafita

Ya kai minti 40 a haka
Sannan ya tashi yace a taimaka masa yaje waje ya sha iska.

Nan kan steps ya tsaya yayi murmushin karfin hali yace ,bakomai i know what to do

Amma sai na fara komawa ma matata na gani ko zan ci saa ta saurare ni.im not letting her go this soon .



*Ur coments are🔥💪🏻👆🏻*
*Jazakh Allah khairan If ure reading this*



*surriem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top