50

.

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Allahu ya ba jaafar lpya,a taya mu da sadakan ameen yan uwa dan mu ba lpya*😪



*Page▶50*




Haka rayuwa ta kasance
A gidan yau  fari gobe baki

Ashween da abun nasu ya ishe sa tattara nashi yayi ya tafi abuja a cikin satin jasmine bata sani ba.

Kwana biyu Duk hankalin ta ya tashi sosai saboda bata gansa  ba ,

don tunda suka soma gwabzawar su da su zahida ta soma fahimtar kamar dagangan aka mata wannan abun dan yanzu ankai ga ido da ido zahida ke mata dariyan da ba dalili

Hakan ya sake jefe ta cikin ruda nin tunani akan abun Sai dai ta kasa fahimtar yanayin data gansa a lokacin da abun ya faru

A hankali ta soma musu labe itama tana bibiyan su tana dan jin hirar su
Nan har ta fahimci ashe zahida bada zuciya daya ta dawo gidan ba,
Abun ya mata zafi sosai yaci mata rai.

gashi ba yadda zata iya tona ma zahida asiri  ta riga ta nisantar da oga daga jikin ta bare tace zata neme su tsokana a sake kora su

  Haka dai tayi hakuri ta bar maganan azuciyan ta amma na ciki na ciki.

Kafin ya tafi, takan tsaya window ta baya kullum tana kallon sa im zai fita aiki ko dan hankalin ta ya kwanta
Amma sai gashi yau ana neman kwana hudu kenan ba shi ba alaman shi a gidan.
Zuciya tayi sosai, tayi fushin da ita kanta ta rasa dalilin sa.

Zahida ko hankalin ta na kwance da shike ta san mumyn ta ne ta kira shi,
Ya tafi.sai baza mulkin ta take yi a gidan tana sharholiya iya son ranta

Sati daya na neman gaucewa har da kwana uku
Ashween bai dawo ba,

shikuma achan cook nana yakan kira ya bata odas yadda zata na kula da jasmine din batare da ta sani

Gashi anan din ma Ko abincin bata iya ci sosai don inda zata samu chance  din kurma ihu da tayi don taji saukin abun dake yawo a ranta
Ta kan zauna tayi kuka ko wani dare kafin tayi bacci..amma stil haushin san nan na nan aranta

Ranar jumu'ah da yamma lis wajen karfe 5 saura tana zaune ta rafka tagumi bayan ta gama tunanin ta itama taga yafi dacewa itama ta cire sa aranta tunda tafiya yayi ya barta baiko damu ba.

yau din ashween  zai cika 1 week 5 days da tafiya abuja.
tasha  kwalliyar ta mai kyau amma saita sa simple english wears riga da straight skirt wanda ya mugun fito da shape dinta,

Nan ta tsaya normal kamar yadda ta saba bakin window  tana kallon wajen daga sama

Jim kadan tasoma ganin motoci har biyu na yunkurin shigowa daga harabar gidan,

Bata dai san duka motocin sa amma tana gani ta san duk yadda akayi yana daya daga cikin wanda suka shigo yanzu

Ji tayi zuciyan ta yayi sanyi, hankalin ta ya kwanta
Har ta juyo cikin sauri zata sauko sai ta tuna ashe ma basu shiri sai ta sake komawa sama jiki a sanyaye chan ta tsaya fuskan nan a murde ta harde hannu.

  Kallo takeyi kamar da wasa taga kamal ne a dayan motar ya sauko
Sai dayan kuma ashween ya fito yana magana da wata amma bata ga da da waye yake maganan ba

Dariya kawai take gani a fuskan sun musamman kamal
Chan ta hango kamar mace amma bata ga waye bane sai ta dada kaiwa kan step ta dada lakewa da kyau ai tana hango salma tayi wani irin juyi ta sa gudu ta fito

Wani uban ihu ta tsala ta na saukowa kasa tana dariya a hankali ita kadai kamar zararriya,

Sun jero su uku ashween yana amsa waya ,salma na gefen kamal suna tahowa
Kamar an cillo ta ta bayyana a wajen da dan gudun ta suka kankamae juna da salma  suna murnan su

  Shi dai ashween dauke wuta yayi ya kara da gaba  saboda haushin ganin yadda gaba daya ta fito ahakan yaji ga shape dinta yayi mugun bayyana
don har shatin pants din ta har na neman fitowa jikin skirts din ,kamal shima daya gaji da shirmen nasu yayi gaba yabi bayn ashween ya barsu.

A falo suka same su har sun zauna ,ta shigo rike da hannun salman duknsu fuskn su dauke da annuri

Wani kallon daya mata ne ya sa ta soma tsarguwa tuni ta gano abunda yake nufi sai ta soma jin kunya.

Kamal yace amarya wato, kin ga kawarki kin mance damu ko,
Ta sunkuyar da kai cikin jin kunyan tace yi hakuri yy kamal
Ena zuwa toh,nan ta ja salma a kunyace suka haura sama

Shiko ashween Sai binta yake da mugayen kallo.

Suna lumewa kamal ya dube sa ya fashe dan takaitaccen dariya  yace wallhy kanada matsala ash kasan dai sun jima basu hadu ba ne ko,

Yayi tsaki yace uhm, kar ka ma bata min rai lets just go
Nan suka tashi suka fice

Duk wannan hidiman zahida bata nan don tun safe ta fice abun ta.

Mai aiki ta gama ajiye kayan salman dai dai suna karasowa cikin daki.

Dariya duka suke yi na farin ciki jasmine ta juyo ta dada kallon salman data cika tayi bul bul ta da yin kyau,tace i missed you, nan sukaa dada rungume juna sai kuma kowacce ta sa kuka

Da kyar suka rarrarshi kan su
Salma tace am sooo sorry jas, ki yafe min kinji?

Ta gyada kai alaman bata yarda ba sannan
Tace " ena kika shiga nayi ta neman ki salma har aka mjn aure baki nan,wllhy i misses u alots

Ta ja kumatun ta tace ai nazo lokacin baki da lpya ne jasmine

Nan salma ta bata labarin yadda auren su ya faru da kamal
Da kuma rashin lpyar umma don tun bayan auren suka kai umma india suna hidimar jinya.

Jikin jasmine yayi sanyi don bata so ta ji ance mahaifiyar mutum ba lpya sai gaba daya ya sata tuno ammyn nata.

Salman ta cigaba da cewa ai naso na kira ki kamal ne ya ce na dakata
Kar na daga miki hankali kice zaki zo,

amma duk abunda kike ciki ena sani aminiya ta kin yafe min?

Jasmine ta danyi shiru Duk da ma abubuwa da yawa sun bata mamaki game da auren salman da ciwon umman sai tayi murmushi nan ta dan share hawayen ta tace to ya na iya, ai dama har na tsora ta na dauka wani abu ne ya same ki ..wato shine yaya kamal yake wasa da hankali na ashe ya angwance ko

Salma tayi dariya tace
Hmm bazaki canza ba jasmine, na dauka aure zaisa ki daina dan iskan shagwaban nan naki

Tace ai ke kika koya min,
Ai Naji haushi da ba ayi dani na chobare a bikin na naki ba,
shikenan yanzu ya wuce ni kenan

Salma ta ce ai sai kiyi ai
Gashi yanzu kamar bake ba ,aure ya karbe ki jas lallai yaya ash ya na wuta yaji huduba ta.

Jasmine ta gwalo ido tace, ke baki kalli kanki ba sai ni
Salman tace ai ni ciki ne dani ke ma cikin ne ?

Tayo saurin rufe ido ta ce ni baruwa na tashi kawai ki kimtsa mu ci abinci i know ure tired.

Nan suka zauna suna ta shirmen su ..hira kala kala
Ba wanda salma bata sha ba

Salma Duk tana lura da ita ,don ahakan sosai ta soma fahimtar abunda ke tafiya

A gefen su ash kuwa kamal  ya riga ya handling masa files din case din su jabir da jamal gaba daya

'Anan ashween yake sanar masa da akwai makarkashiya akan will din da mahaifin su ya bari akwai abunda ke boye.
don ranar da mrs rod ta turo sakon documents din plantation din su a computer sa ranar ya fahimci  cewa
Ba su kadai bane ke da hakkin kudin uban su akwai third party amma baisan waye bane.

Suna cikin hidiman tattaunawar su ,
Zahida ta iske su as usual ta sha kana nan kayan ta  wandon jeans da top sai ta barbaza suman kanta kamar brazillian hair...

Smiles ta sakar musu ta dan jingina jikin kamal tace dan ganin dama sai yau ka zo mana ko?

Yay murmushi ya riko hannun ta ya zago da ita ya zaunar da ita

Ash ko ya kalle ta bare ya ga abun da take yi sai ma ya maida hankali kan wayar sa yana kallon fiskan princess dinsa

Kamal Yace ,ai gani na zo sai kuma akayi yaya

Bata amsa shi ba tayi smiles

Nan ne ta dube ashween daya tsime tace baby baka ganni ba ko?

Ya dan yi tsaki yace pls kutashi muje gida am so tired,

Duk da bataji dadin abun dayayin ba sai ta bari kawai akan ya gaji ne baison magana don tasani sarai in yafara  bada attitudes baya son disturbancess ne

 
Tare suka nufi gida dan tsaban wulakanci
Sai ya kane a baya
Ya bar kamal na jan su
Zahida na gaba suna hiran su su biyu baisa baki ba.

Shikan sa kamal wani lokaci har tausayin zahida yakeyi
Don ash haka kawai in borin shi ya tashi  ya dinga wulakanta ta kenan yana yarfa ta ba gaira ba dalili.

Gefen su salma da jasmine kuwa ko ena suka ruda da surutun su a gidan
Sun sake wanka tsaf ,nan ne jasmine ta sanya riga da skirt na lace baby pink
Itamaa salma ta sa dogon rigar atmfa mai kyau
Sosai jasmine ta haska don gaba daya ji take farin cikin yau na daban ne tunda ga salma.

Hatta cook nana saida ta fahimci haka don gaba daya suka ruda waje da suruutu wai tana ma salma girki.

Ba laifi sun kammala komai suka jera akan dinning,
Nan suka yi zaman su falo
Wanda yayi dai dai da shigowar su zahida su ukun su

Tana gaba ta bi ta ishi kamal da zance

Tuni jasmine ta dauke wuta jin muryan zahida sai aka bar salma da bin su da kallo,don wani irin kallon banza zahidan ma ta musu duka a takaice ta dauke kai kamar bata gan su ba

Ashween Ne last din shigowa a baya 
Ya dubi salma ya sakar mata murmushi

Dan ledan hannun sa ya ajiye daf gefen ta
Wanda ke dauke da fresh pure grapes wanda shi kansa kamal baisan aena ya siyo su ba

Yace kina lpya ko?
Tace sannu da dawo yaya ash na gode...

Nan ne zahida ta kyale kamal ta dawo da hankalin ta kan su duka
Ba kunya ta ce baby waye wannan kuma,?

Cikin mamaki salma ta kalle ta

Kamal yace ' baby sai ka fada mata.

Ash yana kallon salma yace my wife,

Zahida Ta galla masa
Wanda ya sa kamal dariya sosai

Yace to maida wukar kar ki cakke min shi.
She s my wife ya tallafo salma ya janyo ta jikin sa yace itace mata na da nake fada miki

Nan ta mika hannu ma salma suka gaisa bayabo ba fallasa

Jasmine kuwa tuni ta harde karamin tsaki taja ta tashi ta haura sama abun ta.




🤐🤐.....🖊 mon amour my ppl kuna coments ana kari ❤..zahida na gaishe ku harda kari😊😸


*surriem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top