5

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

'''GODIYA''' na *musamman wa yar' uwa ZAYNAB FARUQ,Allah ya bar zumunci ya bar kauna..brilliant gaba daya muna miki fatan alkhairi*

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

'''
Hip hip hip hurray🎂🎂🎂🎂🎂💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
happy bufday my kakus ummufarhana
Allah ya karo shekaru masu albarka'''



*Page▶5*


Bayan kwana biyu'zahida zaune take tasha make up cikin shigar ta manyan yan mata

Gaba daya ta sa hankalin ta kan wayar ta sai murmushi take har tana kada kafafun ta
" beauty?
Nikam me kika samu haka ne
Ive been here ko noticing dina bakiyi ba, madam hidayat wato mahaifiyar su jamal da jabir tace.'

Da sauri ta mike ta karaso
Mummy'ki ga wannan gayen'ta soma viewing hotunan ashween tana nuna mata

Ras taji kanta ya sara da ganin sa amma sai tace "uhumm yayi" sai naga kamar na sanshi a wani waje but i cant remember

Bata ko kula ba tace
Zai iya yiwu ai saboda yaro ne shataf da kudi '
i mean real papers mummy..cikin dan takaitaccen dariya ta karashe

  " nice ,mrs rod tace
To kike kuma Me gamin ki da shi ?

Wani murmushi ta sake sakarwa ta ce
Shi zan aura kwanan nan mummy"
He is d one.

Gyra tsayuwa madam hidayat tayi da kyu tace"What?aure kuma?
Na nawa kenan? tare da galla mata harara tana jiran amsa,

  It Dosnt matter mum..ni dai zan aure shi
Ta karashe tare da tamke fuska

   To waya hanaki..? Ai dama abunda kika gadama shi kikeyi agidan nan zahida

Juyi ta yi cikin rashin jin dadin zAncen!! Mummy?
Ba dama kenan na yi abunda ya dace dani

Whateva .cewar mrs
rod cikin daga murya 
Ni dai ki sani Kuma kiji ni da kywu zahida
ba zan taba yarda bibiyar mazan ki ya sake jawo mana dumbin asarar dukiyar gidan nan kamar kia jawo mana last 2 years ba
are we clear?

' tsaki mai sauti ta ja ta wuce  sama da sauri vatare da ta sake tankawa ba

Zirga -zirga zahida ta shigayi ita kadai a dakin ta rai a bace
Lallai an raina min wayo a gidan nan' yaran ta sumin ita ta min? Hmmm
Zan baku mamaki my co- rodriquez "zahida is coming for you.
Ta karashe dai dai lokacin kiran kamal na shigowa
Ohh thank god " tace saida ta dan nitsu sannan ta dauka ta manna kunne  nan taji
Bae of life kina lpya? Yace cikin dadin sautin muryan sa

Wani juyi tayi da ido sannan tace
Ai ena fushi da kai"
Wato nice zanta kirar ka kana ignoring dina ko kamal? Baka ganin kira ta ne?

Shhhhhhhh ya mata a saukake yana cewa Uhm, uhm,kar kice haka zahida
haba sarauniyar kyw na"
Kinsan babban uzuri ke sawa a mance da phone ko
Nayi tafiya ne.

Nan tace"Ok shikenan yanzu ya ake ciki
Ya maganan mu ?wallhy na matsu kamal please do sumting

"Hey calm down bae kin matsu fa kika ce

Cikin kin jiran wani kalman sa tace" No,dont tel me dat" baka san me ke faruwa ba
kar kaga jamin aji da guy din nan yake kamar karamar yarinya haka yake so ya maida ni
Ko chats dina sama sama yake amsawa
Pls do sumting kamal bazan boye maka ba na  kamu da son shi and i mean it

Dariya ya danyi yace "Oh wow ,kaji lover girl Allah zai baki shi  just calm down

Dan karamin tsuka ta ja tace haba kamal, ba maganan Allah nake anan ba 
bana samaun sukuni tunda ya shiga rayuwa ta i want ash ni shi kawai nake so


Dan shiru yayi ganin ba wasa taken ba sannan yace amma yasan kece kuwa?

   Ya sani mana
Nifa har bibiyan sa nayi cikin kwanakin nan
Ka tambaye sa zai gaya maka
mun hadu a mall sau biyu wajen cin abinci sau daya
Amma sai wani jan aji yake min
Dont really get his attention ..kataimake ni
Bazan iya rasa shi ba kaji kamal
Pleasss
Ta karashe a marairaice

Huhhh?yay xclaming  cikin mamakin yadda take sounding so desperate kamr ba itace mai ji da kantan nan ba

ok yanzu kinsan ya za'ayi?
Zansa shi da kansa  ya  aiko miki ivn welcome partyn sa sai kizo
Daga nan sai ki san yadda zaki yi kin fahimta

Ba tan tama tace
Na fahimta but are yhu sure zan samu karbuwa wajen sa ranar din? kasan fa banda hakuri sosai

Trust me bae abokina na ne fa..me kike ci na baka na zuba
In yabaki Kizo kawai, kafin nan nagama miki komai trust me

Wani kayataccen murmushi ta sake
Tace shikenan to" done !Ure such a durling kamal
Sai naji ka

yh Bye yace tare da katse wayar sa

Dariya suka fashe dashi suka tafa da ashween dake jin komai cikin conversation din su da zahidan
Hmm lallai bata da kunya

Barta kawai kamal'the game has just started.




  Ana saura kwana biyu kacal a soma welcom partyn  ashween
Cikin gidan su ba masaka tsinke
Kowa na harkan sa musamman jasmine da take famar kure adaka din kawai tagwada ma ashween tafi tania kywu ranar
  Salma dake gefe sai kallon ta take tana murmushi..ta kalle ta tace
" ya dai
Me nayi kuma?

Ba komai
Kawai ena imagining ranar auren ki ne  jasmine
Gaskiya bansan wani irin kywu zaki yi ba"

Murmushi ne ta kufce mata tasa hannu ta rufe idon ta alaman taji kunya

Dariya salma tayi tce
Sai dai bansan waye angon ba har yanzu ?in babu fa kinsan yaya fadil ya dade da fadawa ciki ke kawai yake jira

Dan tura baki tayi tace ahhh wani yaya fadil"?
Chab yaimin
Girma ai wannan sai ku

Sosai avun ya ba salma dariya amma saita danne
Tace " toh shi prince din namu ya yake in har kamr yaya fadil ya miki girma

Ohhh my' cewar ta cikin sanyin murya har da
Wani lumshe ido
Ke dai bari,,gani ya kori ji zan baki mamaki salma
Wata rana zaki ganshi

  Uhm i cant wait..ranar ai baki na bazata rufu ba

Allah ko ? Ta fada tana dariya
Hirar su suka cigaba dayi
Har five o clock na yamma kafin salma ta yi niyyar tafiya gida

" suna sauka kan steps na farfajiyan gida  suka ci karo da shi ya sha kananan kaya as usual yayi kywu
A ladabce duka suka gaishe sa
Ya amsa ba yabo ba fallasa daga cikin motar sa  alaman yanzu ya shiga bai tayar ba ma
Ba tare da ya kalle ta ba " yace 'Ena zaki je jasmine?

Uhm dama salma ne zata wuce shine nace Zan raka  ta waje
Dan shiru yayi tare da kure su da ido dukan su kafin yace Ok "
Susu shugo na ajiye ki a gidan toh
Ware ido waje salma tayi tana sauri sauri ta shige inda ya tsaya da  motar ba musu
murna take tana ma jasmine kwalo
Wanda ya sa ta mutsine ta da karfi saida tayi kara  auchhh
Haba jasmine
Shi dai baice uffan Ba amma l yana lura da duk abunda suke yi
Nan salma ta bude sit din baya ta zauna 
Ita kam jasmine Tsaye tayi wajen bata motsa ba don harga Allah bata jin dai dai a zuciyanta muddin akwai mace a  gefen yaya ash cikin tunanin ta har ya kunna motar ya yo kwana ta gefen ta" dan lekawa
Yayi yace mata get in"

Kamar ta hau sama don murna dan haka da wuri ta bude gaban motar  ta zauna a dabaran ce ta maida ma salma kwalon itama
Shiru ne ya ratsa motar kowa da abunda ke ransa
'gefen Wani tafkeken
shoprite sukayo parking sukam basu damu ba.
Kamar bazai ce komai ba
Daga bisani ya juyo yace ma salma" u care for some ice cream?
Sauri salma ta gyada kai tana dan yake mai dauke da kunya

Oya ku sauko muje sharp sharp dare yayi... kaiwa nan ya sauko
Yana gaba suna biye sa shi sai kicin kicin sukeyi suma murna

A ciki " baiyi nesa da su ba kuwa
Haka ko wacce ta zabi choices din ta
Da sauran kayan cime cime ma cikin su

Sam jasmine ta kasa sakewaa duk da ma ranta tas yake yau gata ga yayan ta wajen icecream" dama kullum inta fito waje haka takanyi imagining dama ace da shi ne ,
Hankalin ta yayi nisa cikin tunani bata hankara ba tana sake juyowa sai bata gansa ba

' ena yake ?
Tace a marairaice tana jawo hankalin salma dake famar surutu da attendance

Dan dube dube suka
Shiga yi tuni har zuciyan  ta ya soma kadawa

Gashi chan salma ta nuna chan sama da dan yatsaa
   karamin
Ajiyan zuciya tayi
Tace ohh "alhamdullhi har na tsorata

Salma da tuni kallon ta bai ishe ta ba tace"  Tsorata?
Toh sannu guardian angel din yaya ash

Yeah wateva cewar ta tana turo baki,

Cikin minti 30  suka kammala komai lokacin ana neman karfe 6.20 na yamma 
haka ya dauki hanya da su
Ba wanda ya tanka har suka kai Dai dai kofar gidan su salma
Kuje sai kiyi sallah kafin nima na idar yanzun  nan banda bata min lokaci ya fada yana kallon jasmine din
Toh ta amsa masa

"shi ya fara sauka bayan ya kammala parking
Sannan ya bude booth ya dauko ma salma ledar ta daya na ice crem din daya kuma na gift bag da ita kanta bata san me aciki ba
'" Nagode yaya allah ya saka da alkhairi cewar ta A ladabce
Karamin Murmushi yayi yace Ki gaida su ummah"

Sannan Ya sakai ya nufi masallacin gefe da kofar gidan

Har rige rige suke wajen shiga dan suga me acikin leda sai dariya suke
Nan suka ci karo da ummahn salma
Ena wuni ummah? Duka suka fada yayin da suka tarar da ita a falour sanye da hijabi alamn sallah ta yi
Yau kuma? Ai cewa nayi bazaki dawo ba

Haba umma ta shagwabe tana fadan
Zan dawo mana kinsan fa banje da mota ba

Uhmm chan miki sannan ta kalli jasmine
Ena fatan kowa. Lpya dai ko jasmine
Lpya kalau umma suna gaishe ki

Charaf salma tace
Harda yaya ashween ma" ummahn kinga shiya saiya min wannan salma ta fada tana gwada mata gifts bags din

Murmushi kawai tayi
Tana kallon su gwanin sha'awa
Toh Allah ya masa albarka an gode
Sai a je ciki  kuma ko kin bar min yata a tsugune

Ba tare da bata lokaci ba suka dunguma
Nan suka yo alwala shap shap suka jera sahu suka tada sallar magrub
  Shiru shiru bai kira ta ba ya sa suka shan take da wani hirar
musamman ma da suka ga haddadiyar arabian  dinner  gown din daya ke cikin jakar
Tare da tarkacen sa a gefe
wanda daga gani kasan professional ce ta zaba din komai yayi matching
Hatta turaren dake jikin  tarkacen kalar launin kayan ne

Dan Allah ki dada gode ma yaya jasmine
Am so grateful
Dama ni bawai bana fargaban zUwa dinner nan bane
Din wallhy nasan zamu ga wanka iya wanka ranar

take jasmine tace
Hmm wajen waye kenan tab.?nikam na yarda da kaina
Don nasan muma dole a kalli namu..ko ya?
Dan karamr dariya sukayi suka tafa
Nan har Sukayi isha
Wanda tun kan ta kammala kiran sa ya soma shiga layin ta
Da shike salma ta riga idarwa da kamr zata dauka tace tana sallah sai kuma ta fasa

Sau biyu yana yi yana katsewa charaf ta mike ta kai hannu
" RUHI taga ya nuna kan screen din sai ta tsaya chak tana bi da kallo
Tana waswasin abun aranta

Jasmine Ko addu'a bata sha fa ba ta dauke wayar cikin sauri a hannun salma
Nikam zan tafi salma bani turare na shafa
Salma dake lailaya abubuwa aranta hannu kawai ta mata kan mirror nan ta gwamusa sama sama ta kimtsa tana kallon ta tace
Jasmine waye kuma ruhi?
Shiru tayi kamr bataji ba tace nikam bye ..sai munyi waya

Ohh nice mahaukaciya ko jasmine zamu hadu ai

Sauri sauri tayi ta fuce bakin gate ko sallama bata ma ummah ba

Cikin mota ta same shi
Sai amsa wayar sa yake
Bata ce uffan ba ta zauna shiru tana jin sa
" call u bak babe yace tareda katse wayar
Sosai ranta ya sosu amma saita kauda kai gefe
' shima vaice mata uffan ba
Har na wani lokaci cikin karfin hali tace ummah tace na gaishe ka
Kuma ace maka an gode

Kallo daya ya mata yace
    Um ok..sai bai kara cewa komai ba

  Kamr ta fashe haka take ji a lokacin musamman ma da taga sai zabga masa uban kira ake yi
Wani kira ne ya shigo A wayr sa na musamman ba bata lokaci taga ya parking ya fice abun sa

" ya dai guy how far

Ena ka shiga ne enata kirar ka tun dazu

Yace
  Babu ko ena

Um uhm uhm fadi gaskiya ash
Mutumiyar ka ce tace ance mata an ganka da wasu mata a shoprite dazu

Oh my gudness"
Kaji sabon salon iskanci
Har wani bibiyata take da daddaren ma
Shes insane"

Ofcous she is ash
amma kaida suwaye ne haka

Kai dai
ena tare dai da princess ne  zamuje gida
I just dropped her friend

Uhmm kai dai da princess dinkan nan
Allah dai ya nuna mana ranar abun

Wai me kace ?
Haba mallam ka deba da zafi ai

Yo me zance
Naga ita ka daice hrt controller

Inji ka ba ?
Kaini fa son yaya da kanwa nake ma jasmine nothing more
Stop being silly

Dariya kamal yayi sosai sannan yace
I see..kana chan waje ma kullum cikin cewa ammy ta kula da ita kake" ammy.. karki na barin ta tana fita fa"ya kwaikwaiyi salon muryan sa cikin dariya"
Mswww "eh din, to sai me kuma kamal?, baka da matsala fa"jasmine kam ba sister ta bace?

Uhm uhm ,wallhy ka cika baki sai na fasa kwai kasan ni ba kunyar ta nke ji ba ko

Dan zaro ido waje yayi yace hold on"
Bazaka min haka ba ko kamal?
Kabari dai ta kara girma  yanzun naga kamar rigima ne take ji dashi
Kullum cikin wani yanayin haushi na take musamman en na waje tare da ita

Ohhhhh yanzu ka yarda itace hrt cntroller kenan?

Mswww baka da aikin yi
Nikam sai anjima ,yace yana murmushi a boye

Noo wait yi hakurri
Tsaya mu kammla maganan zahidan nan pls
Nan suka cigaba da kulle kulen su

Daga chan gefe cikin mota kuma jasmine ta share hawaye yafi abun a kirga waima Ko dan  ta samu saukin abunda ke tokare mata kirji amma ena ..kishin sai dada huruwa yake a ranta
Gashi tana dan juyawa ta dubo sa sai taga yana dariya ko murmushi

Kusan minti 15 sai gashi ya dawo
Da sauri ta dauke kanta ta juya masa baya batare da tasan tayi hakan ba

Binta da kallo yyi yace " uhmmm na bata miki lokaci ko
Bata amsa shi ba..
"Im sorry" yace a sanyaye wanda ya sata jin dama dama a ranta
Da Kamar bazata yi magana ba
Ta kuma cewa ba komai

  Ko da suka soma tafiya yayyafi ne mai dan karfi aka soma yi
Ko ena ya kulle cikin motar dan haka a guje   yake jansu har suka isa gida yayi parking'
  " yana fitowa ya zaga ya bude mata kofa baice uffan ba ya kure ta da ido don ya lura kamr fushi take sosai,
Wani fat fat kirjin ta keyi ga sanyin dake ratsata  daga cikin mota ga na rairayin bishiyoyin cikin gidan

C'mon yafada yana tallafo hannun ta cikin nashi
Karar saukan yayyafin ke dada rudata barin ma yadda yake kallon ta baiya ko kifta ido

  Ba musu ta bashi hannun nata
Sai jitayi yayi sama da ita
Da sauri tare sa ma  fuskan ta rumfa da kirjnsa har yakai ta bakin steps ya ajiye ta.
Cikin wani irin Yanayin yake kallon ta yace "shiga ciki ena zuwa,

Tsintar kanta tayi da shagawbe fuska murya ciki ciki tace ok

Nan ya juya ita juma ta rakube gefe tana kallon Sa ya koma jikin motar ya dauko kayan ice cream dinta da wayar ta
Da sauri tayi cikin gida ,

Tana shigewa daki Ruf da ciki tayi kan gado tsammanin ta bazai jima ba zai shigo mata da kayan ta

Ganin kusan minti 20 ba alaman duriyar sa ya sa ta mikewa da niyyar kwabe kayan jikin ta
Auchhh"" innnalihhi,na shiga uku, tafada tana kokarin fincike suman ta daya kanannede zip din rigar ta
sakamakon Sauri saurin da take  yasa ribbon din Ya sabule ya fada kasa

Da kyar ta dan ja rigar kasa ya rufe cinyar ta
Idon ta har ya ciko tsaban azaban zafin da takeji a tsakr kanta
Sai kokuwa take faman yi tana zAresu a hankali kamr zatayi kuka"
'
daga bakin kofa 'minti biyu ya dauka yana kallon ta bata sani ba har ya iso daf
Sai ji tayi lallausan hannun sa kan nata ...
Riko daya ya ma gashin duka Ya tattare su  waje daya a hankali
Sannan ya zAre wayanda suka sarkafe cikin zip din lokaci guda ya sake su
Kunya ne ya rufe ta sosaii do kuwa gadon bayan ta ne tarwal awaje ko bra ita bata cika sawa ba
   Nagode
Tace kanta a sun kuye tana motsu motsu

Shiko baice uffan ba ya ajiye mata kayan ice cream dinta da wani bakar gift bag  wanda ita kanta bata san ta ena ya samo ba
Ga dai wanda ya siya musu da salma
Gefe guda

Here.. yacce yana nuna  mata wayr ta
Yace Gudnite..
Kamar walkiya bat ya bace a dakin

  Ba tare da bata lokaci ba ta bude  wannan haddadiyar gift bag din
Cikin wata matte black kwali madaidaici ta fitar da wata kafirar farar dinner gown fitted

Wani ihu ta zuba da sauri ta toshe bakin ta
Ta hau tsallle tana murna
Oh my god " this is sooo beautifl tafada sannan ta sake maimaitawa
tsaban murna
Da kyar ta ajiye kayan cikin kwalin Ta bude dayan gifts bag 
Itama perfumes ne da
Shoes italian tsaddadu
   Sam bakin ta ya kasa rufuwa don haka
Ko ta kan kayan kwamulashe batabi ba
Ta danna ma salma kira suka cigaba da ga inda suka tsaya
A haka har bacci ya debe ta ...

Fannin ashween ko gadon ma bai kalla ba yana zaune kan soft couchh dinsa yana tunanin abubuwan daya gani a wayar jasmine din

" hankalin sa ne ya tashi sosai zuciyar sa na tsanan ta bugu
Can cikin makoshi
Ya ke furta no. no .. jasmine'wai ke din ma so na kike?

🤔🤦🏻‍♂


*suriiem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top