49
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
'''
Godiya ta musamman ma besty na da swty na
Nagode sosai da adduar ku sakallahu..good friends are wht make us''' lit
*Jinjina marubutan brilliant kun iya samu a shocking,ena yinku yan uwa 😂😂*
*Page▶49*
Jasmine da isar ta ta shige dakin ta taja kofar ta da wani irin wani bugun da saida ya shiga security lock dakan shi
Yana kaiwa ya tura yaji dam dam a kulle, Kofar dakin ya shiga bugawa a zafafe yana magana amma taki sam ta bude
Sai kwala ihu take tana birgima akasa tana kuka.
Sunan ta yake faman kira ta bude masa amma kamar bata jin sa haka ta cigaba
Duk Yana tsaye wajen Yayi lallabin,yayo fadan har ranshi yayi mummumam baci , amma sam taki ta yi shiru ma bare ta saurare shi
Hankalin sa ya riga ya tashi sosai bai ma yi tunanin yaje ya kawo wani key ya bude ba ,
Sunkai minti 20 ahaka da kyr Sai da ya yi hakuri ya danne zuciyan sa yayi sauri sauri ya je ya dauko ya dawo ya bude
Gani yayi Har yanzun tana kasa tana birgima tana kukan fitar rai.
Hannu ya sa ya dago ta tayi sauri fizgewa cikin bacin rai "ya daka mata tsawa yace me ye haka ne wai kam
Wht is wrong with you haka daba zaki saurare ni ba?
Itama cikin tsawa ta mayar tace everything"ni kar ka sake min magana kawai kafice min daki na..
Takaici da haushi duk suka gulle shi lokaci guda
Ji yake kamar ya mare ta ta dawo dai dai amma sai yayi tunani to meya mata da zata birkice masa hakan.?
Itakam Kukan ta kawai take tanayi tana hararar sa tana maganganun da shikan sa baiya fahimtar su
Ya sake kawo hannu zai taba ta ta kai masa duka kamr mai aljanu
Riko hannun yayi Yace jasmine,cikin kukan tace na tsaneka, i hate u..
I hate u ...i hate u.... i hate u...i hate u.
Duk cikin Kuka da bori
Nan ya damko ta da karfi ya manne ta a jikin sa ko motsi bata yi,idon ta yake kallo ko zata sarara in sun hada ido dashi amma ena
Ganin abun yayi tsanani ya sa shi tsorata don kallo daya zaka mata kaga bacin rai da fushi sosai cikin idon ta
Muryan sa na karkarwa yace me namiki jasmine talk to me pls?
Tace i hate you, kawai ka sake ni ai jikin ba naka ba ne.
Yace bazan sake ki sai kin fada min me aka mikki?waya taba ki,pls na rokeki ki fada min mana
Nan ma bata amsa shi ba ta shiga fincike kanta da karfin bala i daga jikin sa
Jikin sa yayi sanyi Duk yabi ya damu ya rasa me musabbabin wannan fitinan
Daga karshe yace in na sake ki zaki fada min ?
A zafafe Tace ,ni me zan fada maka aika fini sanin komai, dama abunda kakeyi kenan shine kake so kayi dani?.
Toh Wallhy ni ba yar iska bace kuma kar ka sake taba jiki na mugu kawai,
Baice komai ba yana binta da ido nan ranshi yayi mummunar baci
Bata damu ba tana faman fizga a jikin sa ta cigaba da maganan ta
"Kuma wai in dan auren ka ne akaina ai dama kace ni ba matar ka bace kaga hanyar ka daban nawa daban,
Kowa yaje yayai abunda ya dame sa mana
Waya damu ?en ba tsoro ba kadaina taba ni mana kaga ko bazan sama ma kaina kwanciyar hankali batare da kai ba.
Nan Ya daka mata tsawa a hatsale sai data razana
Yace " jasmine zan wanka miki mari kika sake wani magana anan wajen are you insane?
Nan Ya sake ta a zuciye don har idon sa sun cicciko da kwalla jikin sa sai kyarma yake yi.
Yace ok fine, dama don haka ne kike wannan haukar ?to na dena taba ki jasmine. Ena damuwar kenan.
Tana shiru Ba kunya ta gyada kai tace
Ah'a ba shi kadai bane
Ya dada danne zuciyan sa Yace sai kuma mene
Tace ka fita min a daki na,get out now
I hate you, ta karashe cikin wani sabon kukan
Kallo kawai ya mata na dan lokaci baice uffan ba kuma Bai jira ta sake cewa komai ba ya juya yayi waje a zuciye yayi banging mata kofar ta shima
Sulalewa tayi nan kasa tayi ta sake bude shafin kukan ta rasa meke mata dadi,
Wani bangaren na gaya mata she's wrong da bata fito fili ta gaya masa meye asalin abun ba.
amma wani bangaran ba abunda yake tuna mata sai abubuwan da taji zahida nayi da sunan shi dazun.
Ashween da isar sa daki Wanka kawai ya shiga.
ya kai minti 30 aciki kawai sai ya sunkuyar da kai ya bada ruwan shower baya na dokan sa.
Wasu zafafan Silent tears ne taf a idon sa suna sauka
Don Shi dai ya kasa fassara magana biyu zuwa uku"
Meye jasmine take nufi da ita ba matar sa bace,ita ba yar iska bace,?
Sannan babban abun daya tokare masa kirji data ce en ba tsoro ba ya daina taba ta mana yaga ko bazata sami hanyar kwantar ma kanta hankli ba.
Wannan maganganu Su yake ta lailaya wa aran sa zuciyan sa na tafasa
Da kyar ya kammala ya fito jiki ba kwari
Nan Ya samu ya kimtsa kansa ya nufi office
Chan office din ma ya kasa tabuka komai yana zaune
Ganin abun na neman hana sa sakewa sai ya ajiye komai ya fita
Ya dan zaga gari chan ya dawo sannan ya wuce gida
Gashi Gaba daya zahida taki lekowa bare ya fahimci wani abun
Ganin ba kowa ya sa kawai ya shige dakin sa ya kwanta yana jimami.
Itama jasmine nan haka ta wuni bata sa komai cikin ta ba har zaazbi sai da ya rufe ta.
Ba wanda ya motsa a gidan har dare daga ita har shi
Yana kwance yana juyi bai samu bacci ba har safiya yayi bai sani ba
Bai fasa ba da sassafen ya sake nufar dakin ta
ya samu
Dai dai ta fito daga wanka kenan
Iya kokarin sa yayi don yaga ya lallbata ko dan yaji meye matsalan amma sai ma abunda ya karu
Masifa ta masa Tas tas ta sake masa kamar na jiyan ma .
Duk da yayi niyyar bazai kyaleta ba sai sunyii magana amma tsaban rikici Don dolen sa saida ya hakura ya fice,
Kwana biyun gaba daya gidan bai masa dadi ba
Zahida na gefe na lura da su duka
Kwata kwata idon ta ya rufe bata ganin abunda ashween yake yi don shawo kan matar sa ,don dama burinta taga ance basu shiri ,jasmine na bakin ciki to nan ne kawai take so sai taji dadi
A Haka haka har sukayi kusan sati biyu ba abunda ya canza duk da ma haka kawai takan zauna taci kukan rashin sa a kusa da ita
Amma kishi ya ki sam yayi freeing dinta bare ta sauko suyi maganan fahimta.
Shiko ganin in ya cika biye mata raini zai na shiga tsakani
Sai ya ajiye abunda yake ji agefe ya cigaba da hidimar sa
Abun yadawo Sai ma ya wuce ta sau dari bai kalle ta ba bare ya mata magana..
Bata damu ba don tasan yakan sa cook nana ta duba lpyar ta kowani rana
Zahida ko da shike tasan ta gama aikin ta sai ta yi kamar bata san me ake ciki ba suka cigaba da hidiman aikin su
Jasmine Tun tana dauke kai har abun ya soma damun ta don gani take kamar an ware ta agidan komai sai dai a mata a dakin ta ,sai dai intayi ra'ayi ta fito hakan ma ba mai tayata hira
Gashi Wani lokacin in zahida ta mata wani abun a gidan sai taga kamar da makarkashiya akasa.
Amma ena sai tana kokarin kaucarwa tana dada tursasa zuciyan ta ya amince shi mai laifi ne
Amma yanzun daya dauke mata wuta kwata kwata ya dena biye matan
Sai ta soma jin zafin abun aran ta sosai
Ta zauna Tayi tunani tayi tunani amma sam ta kasa fassara wasu abubuwan
ganin ba mafita ya sata yanke hukunci makanta
Yanzu dai burin ta taga itama ta kwace sa ne a hannun kowa ko ta halin yaya ne.
Sai dai kuma inta tuna ta tsula masa rashin m sai taji bata san taya zata fara ba.
Gashi bawai zuciyan ta ya sauko bane bare tace zata bashi hakuri
A hakan ma jira take ya sake kawo kanshi
Don ta riga ta kullata a ranta da ta barshi ma zahidan gwara ayita gwabzawa kowa ya ji abunda take ji.
*mata a rage ba wa shaidan waje a zuciya yana hura mana wuta mu tuna fushi sauti ne daga gangan shaidan*💯
*my people i hrt ur sprits and coments wallhy kun burge sosai.naso ace zan iya yadda wasun ku ke so amma is not possible zaisa labarin yayi drifting daga ma'anar sa,*
*don tun kafin na soma littafin a media na riga na gama rubuta scripts din littafin from A-Z . I gues am just following d scripts odas.😉😜*
*just Keep believing keep trusting me we wil get there insha Allahu.i love u all.*
❤💋
*surriem*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top