45
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*Page▶45*
Har bakin motar sa ta rakasa sannan ya fice ita kuma ta kama hanyar shiga cikin gida
Tana shiga baifi da minti10 ba aka soma knocking a bakin kofar ta
Har taji gaban ta yafadi a tunanin ta za'a ce mata zahidan ne har ta iso
Nan dai ta bude sai sukayi ido hudu da karime.
Fuska ba yabo ba fallasa tace lpya?
Cikin ladabin kule a buhu ta tsuguna har kasa tace ena kwana madam
Jasmine bata amsa ba tace" enajin ki
Jikin ta ne ya dan yyi sanyi don dukkan alamu jazmine ta riga ta tsagwame ta a ranta,
Nan ta langwame ta dawo kalar tausayi sai da ta ba jasmine labarin yadda ashween ya kawo ta gidan kAf tanayi tana kukan akan ta taimake ta kar a kaita karuwanci
Ce ma jasmine tayi a tasha take kwana gidan masu abunci tun ranan data bar gidan nan ta taimake ta.
Jin hakan ya sa jasmine ta dan sassauto tace ni dama ai magana ya kare awajena,
Sai ki jira shi ya dawo in ya amince sai ki koma bakin aikin ki,
Tace nagode madam,
Amma ena dai zaki dubi Allah ki tayani rokon arziki wajen boss
Jasmine tace naji, toh tashi ki tafi
Nan ta mata godiya ta sauka, sannan jasmine ta koma dakin ta ta zauna
Karfe 4.30 na yamma zahida ta diro yola, nan ma bata tsaya ko ena ba ta nufi gidan straight
Bata ga kowa ba ya sa ta nufi site dinta ta dawo normal kamar ba ita ba ce kalar tausayi last 2 days,
Wanka ta fada ta kimtsa kanta sosai ,sannan ta fito tayi oder abinci,
Duk wannan shagalin jasmine na dakin ta bata leko ba
Sai Karfe biyar saura ashween ya shigo, nan ne ma jasmine din ke shirin lekowa waje dan tarban sa,
Yana sa kafar sa daga cikin mota karime tayi saurin isowa ta rusuna gaban sa
Nan ta shiga jero masa kalaman hakuri tana kuka kamar da gaske.
Ya ma rasa me zaice don shikam ma har ya manta da ita.
Cikin hakan zahida ta fito
Ta na cewa meke faruwa ne baby
Yana shiru, saida ta iso daf
Nan itama ta shiga bada baki,ta ce ka dubi girman Allah ka kyaleta pls,ai laifi namem ya shafe ta
bayin kanta bane.
Aiko ajikin sa dan yayi niyyar duk wanda baison jasmine to sunyi hannun riga da shi kenan har abada.bata san zahidan ma dan dolen sa ba ne kawai,.
Kafin ma yace zaiyi wani magana sai ga jasmine ma ta fito,
Dukan Su sai da suka kalli juna kowa nasa hrt din na bugawa
A asirce ta mayar masa murmushin daya jefa mata,
Tace uhmm yaya,dama tun tuni tazo baka hakuri kuma baka nan, pls kayi hakuri a dawo da ita mana..shes sorry
Ba tan tama yace 'toh ai shikenan bakomai..
Ke kuma Sai ki kula ya gaya ma karime tare da barin su awajen
Kallo kallon suka ma juna jasmine tayi saurin dauke kai tabi bayan sa
Aka bar zahida da karime wajen.
Murmushi zahida tayi tace kinyi kokari aikin ki na kyau,gwara da kika soma samun ta kafin shi
Muje ciki na fada miki sabon dokan aiki na agidan nan
Tace toh madam ..nan suka dunguma cikin dakin zahida
Gefen ashween kuwa yana shiga baiyi komai ba sai ya kwanta da baya kafafun sa na kasa
Alaman ya gaji sosai,
Shigowar sa da minti 5 ta biyo bayan sa ta zo ta zauna daf da shi tace'yaya food is ready.
Bata hankara ba jitayi ya jawo ta gefen sa suna fuskantar juna, yace ko welcome ba ace min ba za'a soma dura min abinci..? To ni bazan ci ba.
Tayi murmushi tace toh im sorry, yace ba na son wannan kin san wanda nake so ai,
Nan suka lume duniyar soyayar su don bisa dukkan alamu jasmine har ta soma sabawa da abun nasa har kukan ma bata cika yi ba kuma.
Shigowar kirar video na mrs hidayat ya sa zahrod tace karime tashi ki tafi anjima ki dawo
Tace to madam sannan ta fice
Nan Ta danna aswer buton tayi rau rau da ido 'Mumy,,,tace a marairaice ganin yadda fuskan mrs hidayat ya dada larnewa kalar damuwa,
Lpya kuwa mum ko ciwon ne na dawo?
Tayi murmushi tace kema kin sani zahida in ciwo bai dame ni ba, mutane zasu dameni.yau da safen nan naji ance minister of foreing affairs ya tsame shares dinsa a construction companyn rodriquez hankali na ya tashi zahida,sai ta fashe da kuka.
Itama zahidan Hankalin yakai kololuwa wajen tashi
Nan Ta soma rarrashin mrs hidayt don tasan duk abunda zai sa mrs rod kuka to bala'i ne dakan sa.
Sai da suka saita juna ,sannan mrs hidayat tace ena ashween son?
Tace yanzu ya dawo na barshi ya huta ne ya chn dakin sa .
Tace good, yanzu dai ki saurare ni da kyau,
Be smart akan maganan yarinyar nan, bana son na sake jin ya kore ki a gidan Sabida ita na fada miki ,u can't leave just yet har sai anyi auren nan,
Tace toh mumy, kar ki damu im on it,don har na dawo da karime ma zata na taimaka min
Tace good girl
Kar dai kuma ki mance duk hanyar dana gindaya miki don jawo shi jikin ki sosai,
Always rmbr shi ne hanya kadai daya rage mana mu dawo kan kafar mu
Tace toh mumy just trust me.. A haka suke magana har suka kammla zancen sukayi sallama
Nan ma ta kira karime ta gindaya mata cewa yanzu salon wasan su ya chnza
Ba zasu na yin komai direct ba.
a munafurce zasu raba jasmine da inuwar ashween cikin gidan
Karime ta washe baki tace wannan shawarar yaje madam, gaskiya kinada tunani
Zahida tayi dariya tace to tashi ki tafi
Kuma kema ki kula duk abunda zakiyi yanzun kar ki bari ki shiga hidiman ta tana ganin ki,ki tabbata sai a bayan idon ta ,
tace toh madam Allah ya taimake ki
Sannan ta fice
Dakin ash kuwa Ba kowa akan gadon yanzu in ba blanket da kayan su dake barbaje akasa ba,
Daga bathrum ne kawai ake jin motsi, ita ta soma fitowa ta kyale sa aciki tana kan tsame kanta da towel,
Knock knoc daya ji ,yasa ya fito da sauri bai karasa ba ya dada sa ma kofar security baiyi magana ba itama jasmine bata kula ba don tasan waye ne.
Sai da suka kammala shirin su tsaf ya dauki wayar sa yaga tex tana jiran shi a kasa,
Sannan suka fice ita kuma jasmine ta shiga dakin ta don ta sake shiryawa
Zahida Kwalliyar ta tayi mai kyauw tana zaune already a dinning
Yana tahowa ta tarbe shi da wani cool smiles tace baby, ai har na damu naga tuntuni baka sauko ba, u tired hun?
Fuska ba yabo ba fallasa yace uhm...so hws ur jouney ?
Bata amsa ba saida ta janyo hannun sa in romntic way ta zaunar da shi tace ka ci abincin mana tukun we cant talk abt it later
Yyi smiles yace ok
Nan ta soma serving dinsa tanayi tana kallon sa tana zuba smiles tana yauki
Tsaban fitina sai da tasa shi dole wai ya bude baki ta soma bashi
Duk da na baiso ba amma haka ta sa ya bude dan dolen sa
ai Yana amsar abincin na farko yayi dai dai da saukowar jasmine wanda ta riga sauya zuwa bakin material da red turban, na suka hada ido
Tuni taji wani abun ya gulleta a kirji amma sai ta daure ta karaso,
zahidan ko ta kula don tasan jasmine yake kallo a hakan,
Tana debo wani zat sake bashi yace mata noo, ya isa haka ke kici
Kamr bata san da isowar mutum ba haka Ta marairaice tace to nima ka bani a baki
Da kyar Yy smiles din yake yana satan kallon mutumiyar sa data riga ta zauna sai watsa masa mugun kallo take
Acikin plates dinsa Ya juya sppon din yakai juyi goma amma ya kasa deban abinci bare
Ya bama zahida
Ita ko zahida duk ta fahimce shi ,sai ta cigaba da murmushin
mai dauke da boyayyen takaici a ranta tace ko mutuwa zakayi sai kayi feeding dina agaban ta yau
In tsoron ta kakeji ni bana shayin ta,
Ganin jasmine ta dauki spoon ta soma cin nata abincin hankali
Ya sa zahida kamo hannun sa da karfi bazata ta deba masa abincim da kanta ta kai tare da hannun da bakin ta
Tana dariya mai kularwa,
Duk Ya rasa me yake ciki, don harga Allah baya son yaga jasmine a wannan yanayin
Ai bai kammla tunanin nasa ba ta ajiye spoon din a hankali ta tashi ta bar musu wajen
Bata fasa ba Haka fir zahida ta hana shi ta shi, gashi ya na so ya kure duk wani zargi
haka ya daure ya zauna sai zuba take tana surutun ta da ba ma jinta yake ba
Jasmine ta na zaune daki takai 30 mints tana dada duba abubuwan da mamy ta bata wanda bata soma amfani da su ba tukun
Nan taji knock tayi saurin kimtsawa ta koma gefe tayi shiru abunta fon tasan shi ne,
A hankali ya turo kofar kamar marar gaskiya, ya shigo direct ya zauna kusa da ita,
Haushin sa take ji a lokacin amma sai ta kasa bayyanawa saboda ta riga ta yi alkwarin bazata na shiga hidiman zahida ba tunda ya mata bayanin meya kawo ta.
Shiru ne ya dan ratsa wajen sannan yace " me zaki ci ?
Kamar bazata amsa ba ta sunkuyar da kai kasa murya chn ciki tace babu komai, na koshi ne.
Bai mata musu ba sai ya bita da kallon rashin jin dadi yace to sai na dawo tare da manna mata kiss a goshi.
Bai ko jira ta amsa ba ya wuce ya fita a sanyaye kalar tausayi
itako tuni sai ta ji wani iri a ranta,..
Dalilin hakan Ya sata ta shiga kitchen ta ma kanta break fast ta samu ta danci .
Tun tuni kwance take tana tunanin yadda zata rage kishin ta akan zahida ko dan ta faranta masa rai amma ena ,
Ta kulla ta kulla amma sam yaki kullowa haka ta bari tayi tagumi tanajin bugun zuciyan ta.
😟😟
*surriem*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top