41
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*Page▶41*
Jabir ne ya taso ya doso su Da shike bai cikin hankalin sa sosai ,yana ganin rubibin jamian fbi din tare da mumym sa ya wani iso cikin bunkasa da takama,irin Gashi celebrant,nan ya iso daf da su yace whts happening here?
Jabir A rod ,gani nan nine jabir yace yana duban ogan su ido da ido
Taro anyi tsit kowa na kus kus,ana kai kaiwo da maganan ana gulmace gulmace ,a gefe ga yan media sun yi ready har sun soma dauka a camera,
Nan agent ya fito da arrest warrant ya wangale masa a idon Sa ya karanta da kyawu yace
'Ure under arrest'
Mrs hidayat tayi saurin juyawa ta fauce paper tace what for?
For what,? Tace a tsawce ,ohh no no no.enermies of progress are working againts my son
bazan taba amincewa da rashin mutuncin nan ba takarashe a hatsale
Ko su kula ta suka soma yunkurin gudanar da aikin su,
Shima nan ya tsaya zai musu gar gar, ogan yace sir" with all due respect in bazaka tafi ba fa doka ya bamu dama mu sa maka handcoufs mu kawo ka ko da karfi me,
So to avoid further disgrace muje kawai ya nuna ma jabir hanya,
jabir da tuni zufa ya som tssafo masa aka bar sa da kiran sunan mrs hidayt yana mummy kar ki bari a tafi dani, ko a kula su
Nan hidima ta kwabe tuni zahida da mrs rod suka haukace a wajen sai riirriko su ake yi suna zage ..zage,
Kamal tsaban munafurci yana bi yana tare media
Daga daukar al'amarin yana calming din su amma ena kamr ana dada azzama su
Don ko ena hura wutan zancen ake yi ,
ana cikim hakan acikin rubibin aka soma sharing sex video da jabir yayi da jummai da kuma hotunan wayanda ya kwana da su a daren jiya,mutane suna kallo gashi nan bororo
Maganganu ya zafafa,gurun tsumi ya munana,sai aika musu tsinuwa ake waje ya kaure da cece kuce"
don da zafi zafin sa anan din mrs hidayat tana ji tana gani wasu manya manyan abokanan harkokin ta data gayyato sukayi Allah wadar da rayuwar danta ,
yawanci anan suka soma tsame kansu tun yanzu a cikin harkan ta, cewar su familyn ta ba abunda suka iya illah public stunts da zubar da mutunci ,kuma business is busniess ba wanda zai sa kansa da dukiyar sa a hanyar halaka.
Abun ya mugun mata zafi..karshen ta ma da wani babban aminin gudanar da harkan ga ya gaya mata wani abun ma gani kawai akayi mrs rod ta fada kasa sumammiya
Nan aka bar zahida da kukan fitan rai, tana wailing tana rolling akasa sam bata cikin hankalin ta.
Duk hidiman nan ba wanda ya lura da cewa ashween baya wajen,
don tunda aka soma yaja hannun matar sa cikin motar sa
shima nan yayi zaman sa tare da ita daga wajen suna kallon Fitinan da ke tashi a wajen
Jikin jasmine yayi sanyi duk da bata san meye asali ya faru ba,
Tuni idon ta suka sauya don abun ya kazanta
jikin ta kawai ya bata lallai to mummunan al'amari ne..
Ganin mrs rod a kasa ga zahidan ma a kasa na birgima,
kamal na kan fama da jama' ah, ya sa shi juyowa ya kalli jasmine,
Kallon irin Naje?
Tayi shiru ta sunkuyar da kai, chan ta dago tana kallon sa
Yayi murmushi yayi kissing lips dinta sosai ,sannan yace ki zauna anan kar ki motsa ena zuwa kinji.
Ta gyada kai ta mayar mai da murmushi,
Yana tafiya ya dialing number security nan aka zo aka kora media da sauran yan yada gari, kan kace 10 mints waje yayi shiru daga su sai su,
Ambulance kamal ya sa mrs hidayat
Zahida na rafka uban kuka akasa har yanzu kamar ranta zai fice,
Daga mota jasmine ke kallon ashween ya kamo ta,don taki amincewa kowa ya raba ta sai hauka take kamr mahaukaciyan gaske,
Amma da shike ashween ne
Tuni ta lafar da kai ta fada jikin sa tana kuka tana surutai, ya taimake ta ya taimake ta,
Maman ta, brodan ta ,familyn ta komai ma tana fada tana dada kankame sa tana sharban kuka
A hankali yake rarrashin ta,
Wanda ya sa jasmine sunkuyar da kai da sauri cikin kishi.nan hawaye suka soma sauko mata itama don haka kawai taji tashin hankalin ya taba mata zuciya,
Kamo hannun ta yayi, suka shiga ciki nan ma taki ta sake sa ,amma dai yayi iya kokarin sa sai da yaga tayi shiru tare da mata alkwarin yanzu zai je kan case din jabir din.
Alluran bacci aka mata kafin aka samu akaji kunne.
Nan ya fita ya nufi enda jasmine take tayi kukan nata har ta share hawayen tayi shiru
Kallo daya ya mata ya karanto malamar san,
Baice komai ba ya ja motar suka bar wajen,
Jikin ta yayi sanyi, fushi ne, tausayi ne duk ta rasa wanne take ji aranta, sai kakkamewa take tana basar da shi, har yai parking
A dakin su ma haka ne ba wanda ya tanka shima anan ma
Bai kulata ba sai ya fice, sai da ya kammala sallahr azahar dinsa ya dawo
Itama har ta cire kayan ta daura towl alaman wanka za tayi
Bata hankara ba taji shi daf a bayanta shi bai taba ta kuma bai matsa gefe ba
Ta san dai inta juya daf da daf suke sai taki ta juyo din
Nan yace nifa yunwa nakeji abar wankan nan tukun ,sai da taji sanyi aranta da ya soma mata magana
Murya ciki ciki ,cikin yanayin rigima tace ni
Ba ci zanyi ba sai nayi wanka kawai kaci katafi abun ka,
Nan Ya juyo da ita tana fuskan sa a take yace hmmm sabida zakiyi wanka bazaki ci abinci da kazami ba ko?
Tuni ta gwalo ido kamr marar gaskiya tace ni?,yaushe nafada? Ai naga u have sumting to attend to ne
shine ni..ku.ma...sai yyi saurin sa yatsa a bakin ya dago haban nata a hankali ya cusa harshen sa ciki nanbya shiga aikin romancing dinta
A haka har yayi nasaran
Taya ta wankan, taji dadi kam amma sai tura baki take ,
Ba bata lokaci Yayi sauri ya sauya kayan sa ya shirya tsaf don ya samu ya
shirya musu abincin da aka kawo musun,
Nan ma sai da ya sata agaba suka ci tare a hakan ma ta dinga bori sai da ya amince zai kai ta gidan mamy kafin ya dawo daga wajen su zahidan
Haka akayi kuwa do. Saida ta sa ya dauki kusan awa biyi chur tare da ita a gidan mamy kafin ya rabu da su
Nan Ya kama hanyar detention office inda aka ajiye jabir.
Amma sai kayai rashin sa'a Komai kamar dada hura sa ake yi evidence sunyi karfi akan sa,
a hakan har aka kai kwana biyu ana case, ga shi media ena ka saka,ko ena ba matsuguni an baza labarin har angaji
familyn mrs hidayat cikin kankanin lokaci ya fada kasa war was,
Wasu ma har suna mocking din zahida akan cewa saura nata salon zubar da mutucin suna zuba ido su gani.
Tun ranar da baun ya faru Ashween da kamal sune akan abun
sosai suka tsaya ma mrs hidayat musamman ma shi ashween da yake bata emotional suppot,
Brain din ta ya riga ya bata downfall dinta ne yake harin tasowa ,ta dubi Ash cikin jimami
Tace masa yara biyu kenan na rasa ashween,
Im a failure, i failed..ya karashe cikin kuka
Shi dai aikin kwantar mata da hankali yake amma cikin ransa ba hakan bane
Don kowani hawayen ta dake zuba sai yaji sanyi a ransa ,yace ashe ba dadi tsawon lokaci kike durgushe rayuwae mutane kike gina naki?
Zahida da mrs rod Gaba daya sun dawo abun tausayi
don zahida dake gidan ma akwance take ana sa mata drip tasha yakai leda 4,duk ta bi ta dawo shiru shirun dole
Kullum zuciyar ta nace mata" kin rasa ashween kin rasa farin cikin familyn ki to meye amfanin rayuwar ki,ki kashe kanki kawai ki huta,in ashween ya ki amincewa ku dawo xakiyi rayuwar talauci kenan..nan hawayem dole suka bi kuncin ta
Da shike jahila ce, da tunanin abun ya ishe ta ,drip din dake hannun ta ta fincike ta cire tabar jini ya soma bin hannun ta zirr yana zuba kasa
Gashi Ba kowa awajen har saida ya tsiyaya ta suma.
Dai dai Kamal da ashween sun dawo kenan da mrs hidayat
don tuni aka yanke ma jabir shima hukunci child abuse and rape,
Sassaucin da su ashween suka sama masa shine an masa ragwanya sosai a shekarun da zaiyi atsare,gwamnati ne tayi seizing faundation din aka sata under till furhter notice,
Suna zama a falo ,Mai aiki ne ta shigo ta gaishe su
ashween na tsugune gaban mrs hidayat yana kan calming dinta
Nan ta dagi ta kalli mai aiki Tace ya jikin zahida je ki dubo min ita,
Cikin mint 10 suna zaune gani sukayi ta dawo a haukace tana cewa madam, pls come naga bata numfashi
wani razannanen yunkuri mrs hidayat ta yi da sauri dukan su uku na biye da ita suka haura sama ,
Ga Zahida tayi galala da hannu kamar mutacciya
Kamal ne ya soma ganim jinin yace ohh my god meyasa ta cire drip din
A kaita asibiti
Tuni ashween ya tallafa ta aka yi asobiti da ita ,kamal kuma ya zauna da mrs rod da hawan jinin ta ya dada tashi bata ko motsi sai numfashi
Doctrs ne akanta suna famar aiki Wajen karfe 9 saura na dare kafin ta bude ido,
Shine zaune agefen ta
Ta juyo ta kalle shi, sanda taji wani sanyi a ranta,
Nan ta soma jin ashe yana son ta tunda har ya tausaya mata bai guje ta a wannan bakin tashin hankalin da ta shiga ciki
Gefen su kamal kuwa tuni mrs hidayat ta san yadda zatayi ta sa ya tafi gida da assurance din ta samu sauki
she just want to be alone, baiyi musu ba don dama shima ya gaji yana so ya samu ya kula familyn sa.
Bayam ya tafi,Mrs rod Zama tayi cikin nisan tunani tana yi tana shan heavy wine mai karfi amma kamar baiya ratsa ta tsaban bakin cikin data keji
'wani furzan iska tayi tace saura min chance daya tal,don haka bazan yi wasa ba.
Ta sake sipping, tayi ajiyam zuciya tace "Ashween dole ne su dawo sosai da zahida i want the marriage,
Tayi noding kai cikin gamsuwa ta dada cewa "yes,don Abun kenan da zai dawo min da martaba da arziki na agarin nan auren zahida da Ashween R.
*nace tab, tufka da warwara kenan😂😂😂duniya ena kika fito duniya ena zaki...su mrs hidayat iyayen son duniya*
*surriem*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top