38
*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*
💔
*SO MAKAMIN CUTA*
_'the sword of evil love'_
_Story and written by_
*SURAYYAHMS*🔥
*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.
*😹😹😹 my people zahida aka beauty tace baku kyauta mata ba gaskiya ba amana*
*Page▶38*
Zahida dake jin kanta kamar zai bude sai abun ya zamo mata kamar hauka komai yazo gabanta jifa takeyi da shi, ta watsar da nan da fasa nan haka tayi kaca kaca da dakin ta tana kuka.
' ranta ne balbal yana ci da wuta bata iya ma tattara komai ba ta dauki jakar ta da wayan ta tayi saurin dialing call airpot ,maza ta fice a gidan rai a bace bata kula kowa ba.
Cikin daren ta bar garin ba ita da samun dawowa abuja ba sai 1.30 na dare
Karime kuwa da shike ta san bata da wani mafita sai ta lafe a dakin ta tana tunani yadda zata nemi afuwan jasmine a taimaka a dawo da ita don tasan inta fita a gidan cikin daren bata san ena zata je ba
Dama ita kadai tasan cikin bala'in da ashween ya ciro ta aciki tunda chan , gashi yau yace ta tafi 'tunanin ta inta koma chan gidan su ba abunda zai hana uwarta ta turata karuwanci
Gefen jasmine kuwa haka taki kwana fir a dakin ta wai tana tsoro
Shi ko dama abun nema ne ya samo ,duk da waina ta da ya dinga yi daga karshe da kansa yayi dakon ta zuwa dakin nasa
a nan ma sai da jikin ta yagaya mata sannan ya kyale ta har su kayi bacci,
Washe gari Kafin 5.30 na safe ya kammala shirya musu komai sai ji tayi yana tashin ta tayi sallah su tafi
' da kyar ta tashi don bacci ne sosai a idanun ta,
Bata maji meya ke fada sosai ba ta nufi bathrum din nasa ta kimtsa ta fito
Ganin ya gama shiri komai set ya sa kanta dada daurewa
' yaya,ta kira sunan sa
Bai amsa ba ya dago kai
Fuska ba yabo ba fallasa
Tace Yau ma da sassafen zaka tafi ka barni ko?
Yace eh.
Kinga bana son fitina kiyi sallah tukun sai mu karasa maganan
Ba musu ta zo zata tada sallahn
nan ma taga kayanta komai a gefe
Ita kawai ake jira..
Tana cikin sallah yace na baki 15mints ki shirya
Kafin nazo if not wata zata zauna ita kadai anan sannan ya fice.
Ai kuwa tana sallamewa ta shiga lalumo su nan tayi sauri ta sa kayan ta taje tayi light make up a dakin ta ta shirya tsaf, tana zuwa ta tarar har ya dawo dakin.
troly pink dan dai dai sai na shi baki, ya sa aka kai musu mota
Tana so ta tambaye shi ena zasu je da sassafe amma kuma amsa kira yake yi tuntuni yana sauke wani wani ya shigo har ta soma takuna fuskam ta a gefe...
Sunyi nisa kusan daf su isa aiport kafin ya kammala amshe amshen kira '
Lokacim ta kulu Ko kallon sa batayi ba gashi tayi kyau sosai
Lace ne cool ash colour(ruwan toka) da bakin mayafi mai stones shara shara.
Shima Ganin ta dauke wuta ya sashi maida googlez dinsa ya kau da kai
Kukkuni take a ranta wai ita a dole yaki sauraronta yana ta waya
Har suka shiga jirgi bawan da ya sake magana,anan ne ta soma fahimtar abuja zasu tafi.
Haka kawai taji nishadi ya mamaye ta,gani take kamar in sukaje abuja za a ce mata ammyn ta zata gani.
Suna sauka kuwa mota ya zo ya dauke su sai dai sabanin taga sunyo hanyar gida sai taga ankaisu wani sharbeben quest house an dire su.
Tuni ta soma turo baki tana surutu ciki ciki ko ya kula ta,don kafin nan abubuwa sun masa yawa ga kira ko ta ena kansa yayi zafi
Wajen ya hadu kam sosai gashi shiru nan ma ba mutane sosai a enviroment din,
Wannan daya ne daga cikin gadon da ammy ta bar musu amma jasmine bata taba shiga ba sai yau.
Sai da aka kammala ajiye musu kaya komai da komai suna zaune a dakin sannan ya juyo ya kalle ta,
Suna hada ido ta murguda masa baki ,murmushi yyi yace zo nan.
Ba musu ta mike ta zo sai ya jawo ta kan cinyar sa yace ,sarauniyar fushi ne ko na kuka, ?baki son nan din ne na mayar dake yola?
kasa amsawa tayi don inyana mata irin wannan salon nasa sai ta soma jin kunyan sa sosai.
Chan ta daure tace ai kaine bakace min zamu zo abuja ba sai wayar ka kakeyi ka barni.
Yace sorry, na manta ne,kuma duk laifin ki ne
Ta zaro ido tace ni? Me na maka
Yace bana fada ai,sai da na gwada miki in kina so
Nan tayi saurin Tashi jikin sa ta goma gefe tana murmushi cike da jin kunya
Yay dariya yace c'mon tashi muje muci abinci to
Ni yunwa nakeji
Haka suka fita a dakin.
Gefen zahida kuwa dama haduwar su da ashween ya sata dena daga kwalba
amma ranar daga isarta gidan tasha kwalba yakai hudu sai kuka ta ke zabgawa gaban mrz hidayat tana maganganu
Itako mrs rod bataji ba bata gani ba amma sai ta haura mata da masifa da bala'i kamr ita ta haifi jasmine din ,tace ai laifin ki ne ,
Haka yace ki fita a hanyar tania kika ki sai da kika kashe masa ita ,yanzun sai ya kyale ki ki kashe masa yar 'uwa hauka yake?
Ai Kin bani mamaki zahida kamar ba mace ba .me ye ne bazaki kwantar da hankalin ki ki ja ta ajiki ku zauna lpya ba,fadan da yafi karfin ka ai sai ka maida shi wasa
Jin hakan ma ya sata galla ma mummyn nata harara tace in jata ajiki fa kikace mummy ? Tabb di jam
Yarinyar da take acting kamar ni kishiyar ta ce a gidan?
No,wallhy nikam na tsane ta,i wish her dead,, duk tabi ta dauke hankalin sa akaina
Mrs rod ta zungure ta tace just shut up ki nutsu kiji ni wawiya.
Nan mrs hidayat ta shiga rarrashn ta kafin ta zana mata hanyoyi kala kala da zata bi don ta zauna da jasmine din har ta rama duk abun da takeji aranta yanzu,
Zahida kuwa ta gamsu sarai, Duk da ma abune mai wuya awajen ta saukar da kai
amma shawaran mumyn ne kadai hanyar da zai sama mata licenced in dawo wa wajen ashween lpya.
A haka ta amince mummy tace taje ta shirya gobe ne asalin event din jabir zai fara
Kuma ta tabbatar mata cewa ashween yace zaizo wajen.
Da haka zahida ta samu sauki a ranta ta shiga daki ta cigaba murda maganan madame hidayat tana dada dan kulle kullen ta itama yadda zata dawo wajen su ta dauki fansan ta akan jasmine.
Gefen su jasmine kuwa A wani hot suka ci abinci, tana ta kallon sa tana so tace ya kaita wajen mamy amma bata ga fuska ba sam
Kuma shidin ma yana sane da hakan amma yaki yacewa komai ya kyaleta.
Bayan sun kammala lokacin ana neman 11 saura,
Da kanshi ya tuka su sukayi wani office na international relations,
Anan taga an dau ke ta pasports,thumprints ya cike foams tayi signing da sauran su
Bayan kamar minti sha biyar tana jiran sa kafin ya zo da papers a hannun sa still bai mata baya ni ba suka wuce,
Har wajen yamma ana neman 4.30 tana daki ita kadai don shikan tuni ya fice ya shiga hidima,
Kwata kwata ita bata jin dadin komai sabida yaki bari ta motsa sannan bata samun lokacin sa
Tana cikin wannan jimamin taji anyi knock knoc, da sauri ta gyara don wanka ta sake yi tasa dogon riga dake cikin troly din,tayi roling mayafin akanta
Murda kofar yayi daga waje suna hada ido ya sakar mata murmushi yace come,.
Nan ba tare da bata lokaci ba ta biyo bayan sa
Suka nufi palo enda kamal yake
Da Wasa da dariya suka gaisa duk da ma kunyar shi take ji sosai.
Amma haka dan dolen ta ta dan sake don tana son ta tambaye sa labarin kawar ta salma.
Suna cikin maganan su wayar ashween yayi kara har sau biyu bai daga ba
Gaba daya hankalinta ya koma wajen don gani kawai take zahida ne ke kiran sa
tuni taji wani bakin kishi ya soma rufe ta bazata.
Shikuwa bai amsa wayar ma a gaban su ba sai ya fice yaje gefe
Ashe ma mrs hidayat ne da kanta ta kira shi,..
Kamal na lura da ita sai yayi murmushi yace amarya jasmine kenan,
Nan ta juyo ta kalle sa da kyar ta kwawlo murmushi tace yaya kamal, dan Allah kasan enda salma take?
I missed her so much,.kuma kaga yaki ya bari na fita da naje gidan su ummah naji labarin ta.
Yyi murmushi don ya dama tuni ya gano abunda take so ta tambaya
Sai dai ya riga ya qudira a ranshi suprise zasu mata da salma har yola zasu zo kwanan nan.
Nan yace kiyi hakuri amarya
Ai ko nima bana Samun ta kam yanzu , nayi har na hakura, amma insha Allahu zan nemo miki ita i promised
Tayi murmushi tace ok,dan Allah kayi kokari yaya ,nagode
Ya amsa yace insha Allah amryan mu,
yanayi yana dariyar ashween dake galla masa harara a gefe
Ashween Minti uku bai bari ta kara a wajen ba yayi mata alaman ta koma ciki .
Tana shigewa kuwa suka fice suma don cigaba da tataunawa akan hidimar goben.
*surriem*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top