24

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*SURAYYAHMs fans page and groups👏🏻👏🏻*

             💋


*Page▶24*



Karar budewar kofa ne bazata ya razanar da shi yayi saurin tsugunawa kasa kar agansa ....bai bar wajen ba don yayi niya duk rintsi yau sai ya nuna musu jasmine nashi ne ...don haka yakai minti 10 bayan window yana jin tana magana alaman mai aiki cevta shigo aika
daga bisani kuma da yaji shiru..ya leka sai yaga bakowa awajen.
Da kyr ya lallaba ya koma daki ya cigaba da hade haden sa..

Gefen ashween kuwa Tare da kamal suke tafe  bayan yagama amsa wayar zahida data zage tana neman daga masa hankali cewar ankira ta daga chan porland an gaya mata an daura auren ashween da wata daban...

'  da shike tinkiya ce bai dauki dogon lokacin wajen shawo kanta da cewa "ai shine aka daura auren sa ba ashween ba,don ma ya tabbatar mata sai ya tura mata hoton auren sa da salma
   Anan ne ta sauko tace..hmm ai ko da yanzu yanzu zan diro kasan nan... karya ne wata ta aure min miji ashween is mine..only.

Kamal yayi dariya sannan yace becarefl kawai ,,kinga gashi an soma baki wrong ..

Ehh haka ne kamal Tace ...ena yake yanzu?

Ashween na nan na jiran ki a yola ,sai kinzo
  Da hakan ta gamsu  amma tana Allah Allah lokaci yayi jirgin ta itama ya dawo nigeria ta ga ashween ido da ido cewar ta
Kwana biyu da ya shareta  basu cummunicating har kuka takanyi don tsaban missing dinsa dake addabar zuciyan ta
 
   Ko kula surutan su da kamal din baiyi ba yana fama  da tunani kala kala ,gashi har yanzu da yake jin ya mallaki princess dinsan amma sam bai daina jin haushin ashraf a ransa ba,

Walkiyar camera ya gani wanda ya sashi yin wani kayataccen post bazata

Kamal yace "Wow, kaga ango,yau ko zahida zata kashe kanta sai nayi posting wannan pics din
Gaskiya ka hadu na jasmine ruwa sai antace,

Dan karamin tsaki ashween ya ja baice uffan ba ya koma ya dada jingina bayansa kan sit
Kamal kuma na tuka su a hankali har suka isa gida..
Duka fararen kaya ne ajikin su fadin kyun da sukayi bata lokaci ne

Kai tsaye ya shiga site dinsa ya tattare sauran abubuwan da bai kammala ba don umarnin ammy ne akan ya tafi da jasmine cahn yola asalin gidan sa mallakin kansa bayan aure duk da ma tasan bai cika zuwa chan ba.
  Ta fannin Jasmine Dama chan ita kam ba abunda ya dauka mata daga dakin nata ,dan haka yaja ya kulle kofar ya sauko

Shikam kamal zama yayi tunda suka shigo yake waya da salma don har kuka tayi don rashin halartan bikin kawarta
amma ba yadda ta iya uzuri ne babba ya dakatar da ita.

Can suka kammala da kamal, ashween ya ba ma wayar suka gaisa suna hira da salma sama sama har suka shiga mota
shi kuma yana tuka su har suka fice suka nufin gidan iyayen kamal din

Ranar salma cire kunya tayi ta mika Amanar kawarta sosai ma yaya ashween' murmushi kawai yake yana amsa ta
Don Bai ji mamaki ba  dama shi da chan tasu ya zo daya da ita..don tana da mugun kama kai da nitsuwa.

Anan gidan su kamal din suke Kamar da wasa har sukayi sallahr la'asar

Nan ma kamal ya shiga masa barkwanci yana nuna masa likes din da hoton ya samu cikin awa daya tal
Bai kula sa ba..shikuwa
Yana cikin scrolling
Ya gano hoton amarya jasmine a shigar da aka mata na daurin aure  wato pitch material din nan  
Wanda Jide of stola Make up artist din da suka  mata kwalliyar walima dana daurin aure duka sukayi posting sai rububin sa ake yi a media

Lokaci guda ya gauraye ko ena amma an kasa ganin futher updates saboda auren ba wani hidima..

Kamal Yasan inyayi wani xclaiming akan kywun datayi mutumin sa zaiji haushi don haka ya danne abun aran sa saida ya kammala hada hoton  kamr pics mix sannan yace

" hey look,kaga family photo, su jasmine ansha kuka kuwa gashi kyuw batayi ba'' hmm

Ba shiri ya juyo ya kwace wayar don yaga meke faruwa don ya tsani ace masa tana kukan nan ..

Idonsa na sauka akan hoton Wani kayataccen murmushi ne ya kufce masa
yakai Minti 10 yana gushing din kyunta a duka pics din a ransa

Kallo kawai kamal yake binsa dashi suna hada ido ya tuntsire da dariya
Yace, ango"
Toh tashi muje mana muga amryan namu face to face  kaga sai ka kalli original achan

Dan karamin dariya ashween yayi baice komai ba sai da ya mika masa wayarsa yace ai dama dole ne ma mutafi yanzun
Jirgi na karfe 5.30 zai tashi kuma kasan zamu tsaya a adamawa na duba gona kafin mu shiga yola ko?

Ba musu kamal ya ce toh ai sai muje
Kaga nima sai na isa  ga baby na naga ya ake  ciki da maganan ummah a asibiti...nan suka sallama da gidan suka kama hanya ba bata lokaci

Gefen su mamy tun kafin Wajajen hudu saura aka kammala shirya mata komai tsaf da duk wani abunda hajy hadizan ta tanada mata na gyran mace budurwa,turarruka na jiki na kaya na gida,da kayan tarkace masu amfani ga ma'aurata..
Wasu tuni tasata a gaba tayi amfani dasu wasu ta mata bayani har rubuta mata sai da tayi ...
Sannan daga karshe ta dada jan hankalin ta sosai ta sa mata albarka...

Nan ta bada ba masu shirya ta waje  tare da mika musa sabbin kaya wanda ta hado daga bangaren ta

Material mai kama da lace ne farare sol, riga da skirt da mayafin sa
nan aka kwama mata shi aka mata simple make up mai dauke numfashi
Qamshin dake tashi jikin ta har wani jiri takanji jifa jifa....

Dama da alwalar ta don haka bayan an watse
Kowa na kasa ana jiran zuwan ashween

Nan ta dauko qur'ani ta dan soma karatu kusan minti 20 don zuciyan ta yaki dena bugawa tun safe...amma tanayi
A hankali ta soma jin normal komai ya soma sasaauta mata a zuciya lokaci daya,,
"tana kaiwa aya 
ta sauke ajiyan zuciya tace Alhamdullh,,
nan ta  Dago kai  charaf suka yi ido hudu da ashraf tsaye yana kallon ta...

Mamaki ne a fuskan ta tana kallon sa don maimakon taga bacin rai tattare da shi wani munafukin murmushi ya sakar mata
Yana tahowa gaban ta..

Bata motsa ba har ya dakata ,
Murya a sanyaye tace Yaya ashraf

Tuni ya daga mata hannu alaman dakata bana son jin komai ,,nan ne ya daure fuskan sa ya soma huci wanda ya dan razanar da ita ta mike tsaye

Bata fasa ba tace kayi hakuri yaya ashraf wallhy ba hakan nayi niyya ba aurena da yaya ash qaddara ne...i ...i ....i am

Sai tas taji a fuskan ta, ya sauke mata mari, aranta tace kan bala'i???!!ai itama bata bata lokaci ba tayi saurin ramawa sai tas yaji a fuskan sa kamar an zugata sannan ta koma baya 
da shike abune wanda bata taba yin sa ba tuni jikin ta ya hau kyarma tana bari don tsoro,

Idonsa yayi ja ya daka mata tsaqa yace""  Jasmine Kika mare ni? Ehhh lallai kam na sake miki kinga makwanci na.
Toh yau sai na ga uban da zai hanani yin abunda naga dama dake anan,,daga yau aka ce ki mari yayan ki ba za ki kara ba..nafi karfin ki yarinya sai da ki mari shi wawan mijin naki ya barki amma ni uhm uhm..

Nan ta soma kuka ..don ita kanta tasan zuciya ne yasa ta rama marin

Ya cigaba a tsawace ""kimin shiru 'Ai dama munafurci ne abun
kika ki aure na don kinaso ki kaiwa wani wawa banza sanwar jikin ki....marar gaskiya kawai yau sai na koya miki hankali

  Kamr ba shi ba haka take ganin sa Karkarwa jikin ta yake kamar an tsomata a frezeer nan ma hawaye suka zubo  ta soma matsawa da baya tana bashi hakuri ..

Ko ajikin sa,don ya kurmance burin sa yaga ya biya bukatun sa da ita.
Sai da yaga ya kai ta har jikin window ba hanyar motsawa
Sannan ya sa ta a tsakiyan sa ya ture murfin window ya budu da kyu don ta san inta sake motsi kasa zAtayi mutacciya

Ta juya ta kalli bayan ta ta dube sa ta sake Kuka mai cin rai numfashin su na gogar na juna da kyar take fitar da yaya ashraf...yayah ...ashr.... dan Allah ,ka dubi darajar wanda ya hallicce ka ka kyaleni

Harshen sa ya sa yana lashe hawayen nata koya kula ta bare ya amsa
Wani ihu ta tsala bazata jin hannun sa na neman yaye mayafin ta da karfi

Yaya ,yayaya ...take fada a rude shikam kukan ma kamar dada azama shi yake
Yana kawo bakin sa tayi nasaran gantsara masa cizo da karfi  a wuyan sa ta yi saurin kufcewa ta nifi bakin kofa da gudu tana kuka a rude ...

Kabas ta ci karo da mutum a gaban ta.

🤷🏼‍♀🤔


*surriem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top