18

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

And.
    *UMMu FARHANA*
*MEEMAH TA*
   *HALIMA LEEMAh*
    Da kuma
*MOMyn MUFeeda*

*Kulli nafsin za'ikatl maut...Allah ya sa mu cika da imani*


*Page▶18*



Shiru shiru Basu ga dawowar ammy ba bare samun takamammen bayanim enda take..

Daga asibiti kuwa Har kusan karfe goma saura kafin aka cire  ammy cikin life supporting machine
   Sannu ,,sannu hajya hadiza ke jera mata
Da kyar ta daga ido tace
Hadiza karfe nawa Ne yanzu?

Tace Karfe goma saura ne tace tana duba agogon bango.. yunkurin mikewa ta somayi amma saita kasa nan tace
"ki kaini gida hadiza..ki kaini wajen yaya na ..kinga mun dade anan yaran nan nasan hankalin su a tashe yake yanzu

  Shiru hjy hadiza tayi tana bin ta da kllaon tausayi
Chan sai ta kira likita aka daura ammy kan emrgency wheel chair suka nufo gida ba don taso hakan ba

Ganin ba motar ashween ya sa ta danji sanyi a ranta tunanin ta baidawo ba ma daga office
   Nan suka shige daki a gaggauce ba wanda ya san da dawowar su"
    Talatu ce ta shigo tana mutsil mutsil da jiki alamn bata gane meke tafiya ba  nan dai
Ta soma zuba musu gaisuwa don sam kanta ya kulle da rashin lpyar ammyn lokaci guda

  Ena jasmine?cewr ammy tana dubar ta

Tana chan sama dakin ta ,tun dazu take xaga nan bata ganki ba ,
Barin je na kirata enaga bata san kindawo ba

Ah ah,bari kar ki kirata tukunna, ena shi kuma yayan nata ko bai dawo bane?

Nan ma talatu ta shiga bayani 'Uhmmmm,ai  oga baije ko ena yau ba,,shima wai baida lpya dan naga dazu jasmine takai mas magani a dakin sa
   Ammy tace what? Baida lpya kuma?
Kinga ni ko hadiza ,kwana biyun shima hakan yake ta kananan zazzAbin nan..sai yace min gaban sa na yawan faduwa
Toh yanzun ena yake ta maida Kallon ta wajen talatu fuskanta dauke da damuwa

Ai ya fita tun 6 Yace dai zaije nemoki halan ma gidan hajy yaje

Ok shikenan Jeki ...
Ni bari na kira ashraff naji ya abun yake hjiy hadizan ta fada don ko hankalin ammyn zai kwnta
   Bugu daya ya dauka a handsfree ta sa kowa naji
Bayan gaisuwa tace
Nikam ashween ya zo ne?
Ashraf Da kamar bazai amsa ba don yatsani jin sunan ashween din bare kuma shi kansa
Chan kasan makoshi yace
Yanzun nan ya fice enaga gida ya koma
Batace komai ba ta kashe wayar ta

Ta juyo ta kalli ammy dake maida numfashi sama sama tace Alhamdullhi,yanzu zai dawo insha Allah

Ammy tace hmm Dama nasan za'ayi haka
Kwana daya kenan basu ganni ba,enaga ace bana duniyar
Takarashe a sanyaye

Haba hjy shahida,ki dena furta  wayannan kalaman mana dan Allah
Ena tare da ke insha Allahu zaki samu lpya

Gyada kai kawai tayi ta sake murmushi tace
  " nagode hadiza
Banda kamar ki a duniya,
To Ni zan kwnta yanzu
Ko da sun shigo kice musu kawai nayi bacci..gobe su dawo

Toh ,cewar hajiy hadiza  tana lullube ta ita kanta yana so ammyn ta huta ko jikin zai sassauta
Daura da haka cikin minti 30 ashween ne ya soma shiga dakin kai tsaye
bai kula ba ya nufo kanta kamar wanda yayi shekaru dari bai ganta ba
Amm..ammy ..Ammy? Yace yana lalubata  a haukace
  Cikin azama hjya hadiza ta mike lpyarka kuwa
Ashween?
Ammyn ai bacci take ko?

  Nan ne hankalin sa ya dan dawo jikin sa
gefe yayi yana dan sosa keya alamn jin kunya yace toh sai da safe mamy.
Uhm Dama nayi ta neman ta ne bangan ta ba, ince dai lpyar ta lau?

Wani murmushin tausayi  ne ya kufce mata musamman data lura da jasmine a rakube jikin kofa tana jin su
" sannan ta kalle sa tace kalau take,
Itama haka nan take ta tambayar ku kamar wasu kananan yara" sai kuje ku kwanta  gobe ai kwa dawo ku ganta

Murmushi ya mayar mata  baice uffan ba ya mata sai da safe ya fice abunsa

  Buuut.... itama jasmine ta juya cikin sauri ta nufi dakin ta don ma bata bukatar ta sake haduwa da shi
  Duk zuciyan sa yaki kwanciya amma sai yaji dama dama ganin ammyn a kwance ..don haka ya nitsar da kansa yayi baccin sa

    Da sassafe karfe 5 saura ya dawo amma sai yaji gam kofar dakin don haka ya wuce sallahr asubahi abunsa

      Zaune take kan sallayar sai habon jini take amma haka saida takai raka'atanl fajr din ta hade da sallahr asubahi
Amma kuma ta kasa tashi daga kan sallayar donji take kamr lokacin ta ne yayi
   Hankalin hjya hadiza ba karamin tashi yayi ganin yadda jikin ya tsanan ta
  Ganin damuwar kan fiskan hjy hadiza yasa ta  "juyowa  ta riko hannun ta
Nan wasu xafafan hawaye suka soma sauko wa a idanun ta " kiyi hakuri hadiza,..ki karfafa imaninki don yanzu make zan damka amanata " yara na,farin ciki na,rayuwa ta..
Na bar miki su hadiza,ki zama musu uwa duniya da lahira ...ki.....

Hjy hdiza da tuni take Girgiza kai nan ta shigayi  tana kuka amma ta kasa cewa Komai gwanin tausayi

Da kyr ammyn ta daure tace''  Tashi ki taho min da su ,ena son na yi magana da su tace cikin sheshheka itama

Ba tare da bata lokaci ba hajiya hadiza ta nifi waje
Da kyar ta saita kanta tun a hanya sannan ta isa kofar dakin jasmine,
Minti biyu tana jiran ta har ta idar da adduar ta " sannan tace yata fito nan ammyn ki naso ta ganki

Ba jira ta mike ta biyo bayan hajy hadiza
Nan suka ci karo da talatu,
Tace ena ashween din?
   Bai bari ta amsa ba yace gani nan mamy,kin tashi lpya...ya sake duban ta yace mamy
Lpya kuwa,?

Tace Kalau ..ammyn kune ke kiran ku,
Kanshi a daure ya bi bayan ta son shi sosai jikin sa ya soma la'asar

dukan su suka nifo cikin dakin ammyn
    Jingine tayi da bayanta  kafar ta mike akan sallayar har yanzu
    Da mamaki hjya hadizA ke kallon yadda ammy tayi kokarin goge habon dake ,zuba mata tun tuni..kuma take neman hana sauran fita

Gaban ta suka zube duka
Ya riko hannun ta yace "alhmdullh ammy?tare da sauki ajiyan xUciya yana kure ta da idanun sa wanda tuni sun cike da alaman damuwa
Kin tashi  lpya?
Bata amsa shi ba itama tana kallon sa abubuwa ke dawo mata ..yanzu ne take jin ena ma ace zaka iya zaba makan ka rayuwa ko mutuwa da ba zata tafi ta barshi ba.

    Ena ki kaje kika barni ammy, jasmine tafada a marairaice tana shafo fuskan ta itama a hankali,
Murmushin karfin hali ta sakar musu kawai
Tace lpya ta lau" nan sai wani tari ya biyo baya wanda ya ma ashweeen feshin jini a farar jallabiyar sa

  Zaro ido waje jasmine tayi tana kallon yadda hannun ammyn  ke bari
Sai yanzu ta lura da diso dison jinin da ke jikin rigar ammyn... jini? Su kace a tare suna maida kallo kanta  shockingly

Me ya sameki? Ash yace a daburce yana tatttaba ta kamr mai shirin hauka
kallo kawai tabisa da shi'
   Nan hawaye ya soma sauko mata a hankali
Ta  dada riko hannum sa dam tana kuka mai tsuma rai
  Jasmine da tuni ta daskare wajen bata ko motsi sai ido ta tsura tana jiran amsar ammyn?
   ' da kyar ammy ta sassauta kukan nata ta soma basu labarin rashin lpyar nata  run daga rane da yafara har izuwa yanzu
Hade da wa'azantar wa mai shiga zuciya"da sanyaya rai

    Kar karwa yake hawaye ya gama wanke fuskan sa idon sa sun sauya sunyi jajir,yana kallon ta kamr wanda yake shirin kurma ihu ...nan tace ashween
Haka Allah ya qaddara mana.. ena fatan....
Ai bai bari ta karasa ba ya yarfe  hannun sa a nata da karfi
Ya koma baya a zafafe
   Ba zaki tafi kibarni ba ammy
Muje na kaiki asibiti ya yunkuro a daburce zai dagata

Hajy hadiza ce ta riko sa
  Haba ashween,kayi a hankali
Shes weeak now kar ka sake illa ta ta,
Bai san lokaci. Da ya juya a fusace yace toh shikenan sai na barta anan ..baki ganin bata da lpya ne.?

  Wani mummunar tari ta sake wanda ya sa duka suka yo kanta
Jasmine ne ta yi sauri tallafo kanta saboda jinin da ya tsasstafo daga hanci da bakin ta lokaci guda,
Kowa cikin su da irin kalar muryan kukan daya sa yake  kiran sunan ta da shi' nan suka birkice suna hada ta da Allah kar ta mutu barsu,jasmine har  muryan tana kakakkfewa.

        Gefe hajiya hadiza ta koma ta rike  zuciyan ta don sosai yanayin su ya rikita ta,sun matukar bata tausayi

  Kan su ce kobo wuff ashween ya dagota chankak a hannun sa "yana cewa
Zaki tashi ammy ure gonna be fine" muryan sa a dishe gaba daya bayya cikin hankalin sa

  Bayan sa hajiya hadiza ta so tabi amma sai ta lura da jasmine din da Alaman bata senses din ta ,kuka kawai take zubawa tana kwalla kiran ammy alaman bata ma san sun fice ba
Da sauuri tayo kanta zata dago ta sai
Luiiii tayi kasa ta fada summamiya

   Ko da ashween ya hau motar sa gudu yake duk da haka bai dena kukan ba sannan bai dena juya wa yana duba ta jefa jefa ba
Don ma wajen yayi safiya dayawa ba hayaniyar motoci " yana parking ya kinkimo ta ya wuce ciki ba tare da bata lokaci ba akayi emrgency da ita,
   Kallo yabi kofar da shi zuciyan sa na bugun tara tara"
Tunanin sa kar ace ammyn sa tafito ba rai,
   Sai juyi yake shi kadai,tunani kala kala ba wanda bai saka a ransa
  Wani bin ya ba kansa laifin rashin gane ciwon ammyn wani bin ya yi blaming ammy data boye masa tsawon lokaci
  Sai dai duk waNnan ba damuwar sa bane ,shi dai kawai yaga ammy tafito lpya

Daga chan gida kuwa saida aka shafe kusan Awa biyu sannan jasmine ta farfado, ammy,..ta soma cewa  amma idon ta a lumshe
   Hannu hajiya hadiza dake zaune zugum a gafen ta takai tana dan calming din ta
Kamar an tsakureta ta mike firgit ta zauna tana zaro ido..
Mamy Tace sannu jasmine
Ya kikeji yanzu,?
Cewar hajiya cikin yanayin tausayi,

Mamy,  Ena ammy?
Tace kamr zata fashe da kuka ...

Hanni ta kai tana shafo siman kanta ahankali tace Jasmine ki huta tukun ammy tana asiviti yanzu

Ai kamr ba ta ji ba sai ma wani Daka ihu tayi ta sauko kasa a firgice zatayo waje da gudu

Da kyar hjya hdiza ta rirriko ta ,nan ta shiga fizgewa tana fadan
Ni ki sake ni naje wajen ammy,.na san karya kike min
Nan ta sake kwala ihun sunan ammyn kamr kanta zai tsage ...amma sai kuka ne ya biyo baya ,

  Rirriko ta tayi tace Kiyi shiru jasmine ,insha Allah zata warke

Cikin kuka tace toh ki kaini asibitin nima

Ba musu ta ce muje,..don itama ta qaho ta san wani hali suke ciki da ashween duk da ma sunyi waya dazun

Tun daga kofar ward din da shike sashin vvip ne ba kowa ake admitting a WaJen ba
Shi kadai ne tssye yana jeka ka dawo duk yayi fayau fuskan sa dauke da tashin hankali
    Ba su fito ba ko ? Cewr hjy hadza yace
Eh mamy ,,amma enaga sun kusa ya fada cikin dauriya yana satan kallon jasmine din

  Itakam Ba tace uffan ba ta goge guntun tears din ta ta koma gefe itama ta tsaya

    Kusan minti 5 kacal suka yi ahakan wani doc ya fito a ggaguce
   Duka suka dunguma suna tambayr sa ?
Ya jikin nata? Ta tashi,?
   Saida yayi ajiyan zuciya sannan yace kune familyn ta ko?
Eh ashween ya amsa cikin sauri doc yace
Please come in .. alaman da dukkan su yakeyi

  Wani control room aka basu izinin shiga
Ga ammy kwance an sarkafa mata igiyoyin computer E.C.G sai aiki suke
     Wani sanyi suka dan ji aransu duka da suka ganta a nitse idonta a bude tana kallon su"
   " sannu ammy, ya kike ji yanzu?toh kice min ba zaki barnii ba
Ammy kin warke ko? Kowa yafada nashi lokaci guda ..
  Murmushi kawai ta sakar musu tare da mika musu hannu kowanne da na shi,
Ba tantama suka riko hannun suna kallon ta fuskan su cike da damuwa hajiya hadiza kuma na tsaye gefen su,

   Alhamdullhi,ta soma da cewa
Sannan ta dubi ashween,
Kayi hakuri da duniya my prince, nasan kai mai imani da qaddara ne,
Ka dau ka wannan maganan da zan fada maka yau,shine alfarma na farko kuma na karshe da zan so kamin
' dum zuciyansa ya buga
Amma sai ya daure yace
Ki daina fadan haka ammy
Zaki warke,sannan ai kinsan ba wani alfarma a tsakanin mu ko, i can be ur slave if u want,.  Har karshen rayuwar mu.
Dan dada matse hannun sa tayi alaman kar ya sake ce haKN
Sannan ta dubi jasmine ,
Na bar maka amanan ta ka kula da ita,kar ku sake ku rabu da juna duk rintsi duk wahala  kusani wannan ne kawai sakayyar da neke nema A wajen ku,

Jasmine , na san zaki zama mai biyayya gareni
Ko? Ammyn ta ce tana kallon ta
A hankali ta gyada kai  tace eh ammy nayi alkwari...
Toh ki rike yayan ki amana ,kar ki taba rabuwa dashi kinji?
   Hwaye ne ya sauko mata ta sake cewa toh ammy,
   Hajiya hadiza zata sanar da kai duk abunda ya kamata ka gama sani game da abunda na bar muku duk da komai arubuce take,

    " sannan ena son kubata hadin kai nan da sati guda a daura auren ku ..

Wht? Yace yana yunkurin zame hannun sa amma sam taki sake shi,
   Yace Aure kuma Ammy ? Da jasmine ?

Jasmine din ma ta ce ""Amma fa ke kika ce karatu zanyi ammy ..kuma ni ...ni ..bana son na aure shi tafada cikin wani rudadden kuka tana kife kanta kan hannun ammyn?

   Shikam shiru yayi ya rasa abun fadam. ji yake  kamar ranan gaba daya mafarki ne

Shiru ta musu sai chan ta Dago kai  ta kallesa tace kaima baka son ta ko?
Toh Shikenan, ...ta maida kanta gefe alaman rashin jin dadi  ta furta ""kassh naji takaicin buri na na karshe a duniya bazaii cika ba

  Zai cika ammy, yafada yana kallon ta a sanyaye
    " kece rayuwa ta,komai zan iya yi akan ki ...saboda haka
Na amince koda bata sona amma  dai zan  cika miki burin kii,

Jasmine kuwa Jin hakan ya sa ta dakatar da kukan nata
Ta juyo ta kalli ammyn  dake murmushi da kyar tana cewa
Allah ya maka albarka ashween,
Insha Allahu bakomai cikin rayuwar ka sai alheri.....

Nan ta juya ta kalli jasmine din irin kallon da ya razana ta amma murmushi ne daukebsa fuskan ta'"tunanin ta kar fa dagaske last wishh din ammyn na ta kenan.

Nan ammy tace" im sorry princess .....da sauri ta tari numfashin ta tace
Nooo ammy,.kar kice komai
Nima na amince ..zAn aure shin ..ammy kar ki mutu dan Allah
Nan ma ta sake fashewa da kukan tana fadawa jikin ta
Ammy Murmushi kawai tayi tana rarrashin ta

Hjiya hadiza dake gefe tuni itama tabke faman samusu albarka
Anan dukan su 
sukayi amfani da wannan damar suka  musu nasiha sosai akan sabon rayuwar da zasu fiskanta nan gaba a matsayin ma'aurata
Musamman ashween da suke ganin duk nauyin yanzu kansa zai koma...

      Wasa wasa aka kira sallahr azhar nan ya mike ya nufi massallaci da kyar suka rabu da ammyn don haka kawai yake ganin kamar en yadawo bazaii same ta ba. Bayan fitan sa
  Haka itama ammyn ta turje saida suka taimaka mata tayo sallahn azahar din ta
Komawar ta tayi a nitse ta kwnta luff  tana murmushi
sai gawan ta...

😭😭😭😭


*surriem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top