16

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Page▶16*

Hakan akayi kuwa Ba wanda ya san madam hidayat ta haifi yan biyun ta
Bayan kamar awa daya an kimtsa ta fes da baby girl dinta wanda tuni ta laka mata suna lailah,
Sunyi kywu cikin shigar su na sky blue and pink jacket da rigar sanyi mai hula tsadade
  Wani zuciyar tana mata juyi akan  condition din mijin koya yake ciki oho" ta wani bangaren kuma tunanin ta na nan akan dayan jaririn ta da aka je dubowa

   "sallama personal assistant din ta tayi me suna mrs jamila
Yes shigo ..tace tana  dan rufe fuskar laila

Mrs jamila ganin baby a hannun ta yasa tace" Wow masha Allah
Mrs rod congratulations madam.kin sauka lpy?

Ba yabo ba fallasa tace
Uhm ..toh meya kawo ki nan bayan nace kar abari kowa ya shigo?

  Dan shiru jamila tayi kafin nan tace ' akwai matsala fa mrs rod

Wht? Matsalan me
Meya faru kuma?
Ena yay'a na ? Cewar ta a birkice

Noo,, calm down sua lpya sukam, dama na nemi na zo nan ne saboda matsalan tana dan girma 
mrs amma in bazaki damu ba muje ki gane wa idon ki please
  A hargitse ta mike ba jira kamar ba mai jego ba  ta bi bayan jamila fuuuh suka fice sai wani section din asibitin da ba kowa aciki sai uban sanyi dake ratsa wajen

Ena ne nan kuma jamila whats all dis? tafada hankali a tashe

   Bata ce uffan ba ta bude wani kofa mai taken room 13 enda nan take madam hidayat tayi ido hudu da gawar alhj abdul fatah rodeiquez

    Innalihhh..mr rod? Cewar ta tana cukuikuye sa  da tsananin
Rawar jiki
nan ta birkice akansa wanda  ya sa doctr da mrs jamila suka koma gefe suma suna jimamin abun
"na shiga uku ka bude idon ka kaga abunda na haifa alhji?
Don't leave me alone pleass wake up'ta cigaba da girgiza sa
Ta ke fada a rude

Can mrs jamila ta soma bata baki tana sassaita ta da kalman hakuri
Har ta dan samu kanta
"doc me ya kashe shi?
I mean how comes miji na zai mutu.

Doc yace" Calm down madame a sanyaye yana mika mata wasu files
   Tare da bayani "Wannan ya nuna alamn buguwar zuciya
Wanda muke da tabbacin cewa akwai wani abu da yayi makasudin sashi a cikin yanayin da ya shiga ciki ba normal bace
  Sannan bincike ta nuna anyi ragwancin kawo sa dawuri hakan yasa jini ya haura jijiyan kwawlawar sa
Munyi iya kokarin mu amma qaddara ya riga fata ..im sorrry

Guntun hawayen ta ta share ta sa ido tana dada bin result din da kallo
   Ko da mrs jamila ta lura da ita nan ta karaso gefen kunnen ta tace
Maamm akwai matsala ne?
  Come with me, kawai tace mata sannan ta fice fuuuh ta bi bayan ta
a dan gefe suka tsaya tace
    "yawwa jamila kina jina ?
Kinga yanzu akace ma media ga abunda ya faru da alhj duk mani za'a laka ma laifin mutuwar sa 
Wanda hakan zai iya jawo min bakin jini wajen yayan sa musamman zahida dake ganin bani na haife ta ba

    Hakane mrs rod kinyi gaskiya
To whats d plan ranki shi dade..

  Sauke ajiyan zuciya tayi ta dube ta ""Doctor"cewar ta tare da bada jamila baya
Shi zaki fara kalmashe bakin sa a canza result din  nan dana wani daban.

Sannan ni zan gudanar da sauran harkokin gadon yayana da will din Sa akan su yanzu

    An gama hajiya ..tace a ladabce da niyyar komawa wajen doc

Tsaya jamila..madam hidyat ta dakatr da ita
Ena so ki yi duk yadda zakiyi komai ya tafi  mana dai dai
Sanin kanki ne 70.% na will din alhj bana ciki ko?

ta gyada kai

Toh Bana bukatar abunda zai rabani da yaran nan kuma bana bukatar su san komai har abadaa

Cikin ladabi da gamsuwa mrs jamila tace bakida matsala ..u can count on me mrs

Kada kai tayi alamn gamsuwa itama ta je jeki toh
Sannan ta koma dakin ta na haihuwa

Sannu a hankali akayi sati hudu
Duk an gama taro da rububin mutuwar alhj abdl fatah
Sai media da ke kan juya labarai kala kala san ransu
   Sosai su jamal da jabir suka jimanta lamarin
Musamman zahida da abun duniya ta dame ta tunda ta kyallara taga an haifi lailah
Sosai kishi ke damun ta a ranta .tunanin ta an haifi wacce zata karbe matsayin ta na mai kywu a gidan

   Don haka ko taba ta batayi bare ya dame ta.tafi kula dayan baby boy marar lpya wanda ka laka masa suna lateef
Wanda har yanzu an kasa sanin me ke damun sa"
  Su lailah da lateef sun kai shekara 2  lokacin ne
A ka tabbatar ma hajiya hidayat lateef yana da abnormal neonatalophalmic issure wanda yafi tsanini a ido daya (wato baya gani sosai kusan dai makaho)
ne sannan gefen kafar sa abnormal ce a juye take kuma ankasa samo dalilin faruwan hakan

   Mrs jamila ce tsaye kan ta bayan sun dawo daga wani meeting
'mrs rod yakamata muyi resolving issures din gidan nan fa tun kafin yafi karfin mu

   Tace ,Ke jamila ..yanzu ba ta wannan nake ba  kinga
Tunda lateef bawan da yasan na haifeshi sai ku agidan nan
Just keep ur mouth shuts ....
Na riga na bada oder face marks wanda zaina rufe fuskan sa da shi  yanzu don kar ya shafa ma sauran yara na nakasa da munin hallitatr sa
God forbid na haife wannan abun ..hes not my blood

Shiru mrs jamila tayi tana jin jina ma tunani irin na mrs rod da ba alaman jin Wani remorse ko tan tama a yanayin fuskan ta

Shikenan ..tace tare da sauke ajiyar numfashi
Tana kallon mrs rod din
  T<oya kenan zamuyi da shi ? Kashe shi kenan za'ayi ko zai cigaba da zama ne a gidan nan a boye?

Ajiye biro tayi tadan dafa kai  tace
Zauna jamila.....

  Look nima bansan ya zanyi ba amma dai bana son ya mutu ,kinsan fa
Akan maganan kisan nan ne zuciyar alhj ya buga
   Lets just find another way.

  But mrs boye shi agidan nan is equally imporsible saboda watarana fa dole zamu fuskanci barazana.

Ok ..ok.. just stop it haka jamila ...ni kaina yayi zafi mubar maganan nan haka
Kiyi abunda nace miki kawai
Ki rabasa da yayana musamman lailah
Akaisa chan side din dana shirya ana kula dashi shi kadai..kin fahimta ?

Yes maaam

Ok u can leave ...batace uffan ba ta juya ta fice

Fitar jamila keda wuya "Wani zazzAfan sauke numfashi  tace ohh Allah
Me na maka da zaka bani wannan mummunan halitta? makaho mai juyayyen kafa a matsayin da na ?(wa'eyazubillahi)
Ka manta ya ya na sune jari na? I invested so much akan su
Wannan kyawun nasu shi zanyi amfani dashi a future na daga rayuwar su da darajar gidan nan

God Im sorry
Gaskiya bazan iya lissaafa lateef a jerin jini na ba..its so embrassing ..i can't
Ta mike ta wuce dakin ta ..
  
Luff luff suman kansa yayi a nitse kamar yadda ya saba yanaji aka rufe masa gefe daya da mask din sannan akA tallafa  Sa zuwa wani daki aka jiye sa haka aka cigaba da rainon sa awajen sai tayi wata  daya wata biyu bata leko ta gansa ba don tuni ta nema masa mai shayrwa da kula da duk wani dawainiyan sa

   Ko da  zahida da su jamal da jabir suka tambaya ena lattef din ce musu tayi likita ya tabbatar musu da cewa yanada matsalar kwawalwa wanda zai iya cutar da su ciwon kisa ne ke damunsa mrs jamila ta dada musu kashedi ,shiyasa aka kebe sa kar ya dame su

   Zahida dama ba har cikin ranta take taba sa ba Basu damu ba,
kowa ya cigaba da harkan sa don kuwa zahida sam bata jin zata iya hada jini da nakasasshe ko mummuna yanzu matsalar ta daya ce 'lailah

Haka rayuwa ta cigaba  mrs rod harkan vusiness din ta take yi
Tana dada zurma zahida jamal da jabir akan turban mummunan rayuwar ta na kaskantar da mutane

Sunyi suna sosai a duke enda suke karatu ko programes
tun suna cika shekara 14 zahida ta fara operating fashion na teenagers a film industry na italy chan kasar waje
Haka jabir shima tuni ya soma shiga harkan mobilization programe akan mata da abunda ya shafi rights din su
Shi kuma jamal law yake so ya karanta don haka karatun sa kawai ya sa kai da wasu special training da mrs rod ta sa ake musu

   Sosai wayon su da ilimin su ya wuce shekarun su
Don kuwa duk abunda take yi akan su bisa tsarin jarin arzikin su take yi a nan gaba..
   Duk da yanzu ba kamar da ba zahida da lailah basu zama inuwa daya tsaban yadda zahida take dada jin kishin kyawun fuskar lailah..ita shiru shiru ne, tunda taji labarin lateef ta karyata abun aranta ,sai shaukin son ganin sa ma daya addabe virgin pure hrt din ta
Mugun ta kala kala zahida ta mata amma sam bata cewa komai
Har suka kai shekara 8 gashi bata taba ganin lateeef din ta ba

Shima yana chan tsaban baiwa da basira, hankali da nutsiwar sa, a sace nannny mai kula da shi take koya masa abubuwa kala kala boko da arabi don a gidan mrs rod sai kanada certain qualifications na karatu kayi mata aiki ko da gadi ne kuwa..

Lateef ma Dai dai da yan uwan sa take koyar masa batare da kowa ya sani ba har yakai shekara 8 din
Sun shaku da nanny zarah Kullum idan ya soma tambayar mahaifin sa sai ya sata kuka

Don tuni mrs rod ta gama bayyana masa matsayin sa a wajen ta duk lokacin data leko duba sa
Sosai abun ya masa zafi amma sai ya nuna bai ma san me ake nufi ba

Haka yake rayuwar sa zuciyar sa fal da tsanar kan sa
Kullum sai ya roki Allah ya Yaye masa ya saukake masa da halitta mafi alkhairi da rayuwar sa batare da kowa yasani ba

Bayan wasu lokuta ,Ranar kowa ya taho hutu ana zaune ana raha ana ta dariya komai na tafiya dai dai a familyn rodriquez rana ne dayayi dai dai da ranar zagowar haihuwar su lailah da lateef

Kowa na nishadi  In banda lailah datake zaune shiru bata ma jinsu
Don wajen kaf ya kaure da surutu kowa na gwada kansa suna nuna ma juna achievement din su
Daga gefe Sai washe baki mrs rod take don kuwa hankaln ta kwance yake  tunda tasan yanzu kam
Ta daura yaran ta akan career saura su zama jajayen wuya a kasa kamar yadda take hange..

     Sun lume cikn sha'anin su  basu lura da lokacin da lailah ta haura sama ba
Ko da ta haura zuciyan ta ne ke dada bugawa tanajin wani irin shaukin son ganin dan uwan ta sosai...

Zaman durus tayi kan step wanda ya hada link din wani side da side din su amma basu taba bin nan ba..akan step ta zauna
Hawaye ne suka soma zuba mata a tiny cheeks dinta
Cikin ranta ta raya " ena ma naga dan uwana muyi wasa ? Koda bangan sa ba I missed  him so much
nasan bazai cutar dani ba'
Har tayi niyyar tashi zata tafi taji wani abu ya fadi gum a qasa saida ta razana ta mike tana waige waige

Kan..kan..kan take ji alaman ana buga wani abu da sauri ta haura sama kusan hawa step uku kafin ta kai layin karar abun

Hankali take takawa tabi layin karar abun zuciyar ta na bugawa
   Kofofi guda uku ta gani
Ga wajen shiru kamar ba a gidan nan yake ba tace
Helo?
Helo..hello ta fada da baby voice din ta mai rawa don tsoro

  Kamar daga sama yaji muryan ta amma sai dai bai gane  ba" bai taba ji ba amman kuma sai ya tsinci kansa da jin daban aran sa game da mai muryan
Hakan ya sashi mikewa ya na tangal tangal har ya buga kafar sa mai ciwon take ya buga ihu dan radadin dayaji
Wayyo Allah nah, ya rike yana jimantawa

Hakan yasa ta karasowa da gudu ta tura kofa na tsakiya
A gurfane ta gansa fuskan sa ba mask din sa sai kakarin kuka da yake don zafi

Chak ta tsaya kallon sa cikin mamaki da nazari chan daga bisani
  Cikin shaukin tausayi ta tallabo sa tace latte...efff
Are you d one?

Shima Tsit yayi nadan lokaci kafin shima yace' yes, wa cece ke? Lailah ce?..a sanyaye ya karashe yana mika hannu zai lalube nata hannun
Hawaye mai zafi ne ya kufce mata tuni ta rungume sa  tana rarrashin sa ..cikinnkuka tace
  " lateef are you ok ?
Meyasa baka fitowa muyi wasa?
Ko dan mamy tace baka da lpya ne? Ni Ai bazan kuje ka ba im your sister rememmber?

Shi dai muryan kukan kawai ke fita baice uffan ba tukun ya riko ta dam dam ,kamr an bashi abun da ya dade yana nema
Da kyar ya dube ta da ido dayan sa yace 'im fine
Lpyata kalau..dama ni ba abunda ya same ni
Mumy bata so na saboda ni mummuna ne kuma bana kallo ido na daya a rufe yake u see? Ya soma kokarin nuna mata dayan idon sa daya manne

A take tace"Nooo ...ba haka bane
Shhhhh'' ta karashe tana girgiza mas kai alaman yayi shiru ba hakan bane

   Bai sake cewa komai ba kuwa sai shishikar kuka da ya ke fitarwa a zuciye gwanin tausayi

Zo muje waje ..zan kaika daki na
Tace tana kokarin jan sa waje

Dan fincike hannun sa yayi ya ja baya kadan
"ah a ke ki tafi
ni nan ne daki nah anan zan rayu'
Alhmdullhi tunda yau mun hadu da ke ..ko da bansan ki ba sosai na san ke ba kamr mummy bane ko?
Bata kula sa ba sai ma kokarin bada baki data keyi don ya biyota su tafi, Duk juyi tayi don ya samu ya bita amma sam haka yaki fir

Karshe itama zama tayi gefen sa nan suka cigaba da hirar su gwanin sha'awa
Gwanin tausayi

  Suna nan a haka Har wajen kimanin awa biyu...
Lailah karama ce amma yawancin maganan ta cike suke da hikima da basirah don haka ya nutsu shiru yana jin ta

"   Meyasa kika yarda lpyata lau kuma bakiji tsoron muni na ba kamar mumy da sauran da kika fada ?
 
Dan Shiru tayi kafin ta ce"i dnt know
Ni dai daga lokacin dana fara ganin ka nasan lpyar ka lau
"Kuma jini duk enda yake yafi ruwa kauri"kai jini na ne lateef

Yace "Uhmmm haka ne..amma...? toh shikenan dai
I wish ido na nada kywu da na ga kamannin ki sosai,
is alot blurry bana ganin komai da komai"  nasan ki nada kyau sosai lailah

Dan karamin murmushi tayi ta kalle sa sannan tace'kaima kana da matukar kywu dan uwana don har kafini ma

   Dan daure fuska yayi ya sun kuyar da kansa,yayi shiru
    Hey..tace a sanyaye tana dafa sa
Im seriious bro ka fini kywu'domin kuwa
" kyakkwan zuciya itace kyakkawan fuska"

Nan ya dago yace Kyakkwar zuciya Kika ce,
Amma meyasa mumy bata gani ba?

Riko hannun sa tayi a hankali tace
Saboda taka zuciyar daban ne lateef'kullum ena so ka tuna da wani abu....
Sai kuma tayi shiru bata karashe ba ta zuba masa ido

Ehen me kike so na tuna? Yace bayan jin shirun ta yayi yawa

Kafin su ankara ji sukayi an banko kofa...
" laaaahhhh
gata nan anan mummy"
Ur every stupid lailah
Wayace kizo nan?
Zahida tafada a tsawace tare da finciko ta tayi jifa da ita sai da ta fada kasar dakin

Sosai suka razana har shi lateef din yana neman lalume lalaume don ceto lailah a hannun zahida data gauraye wajen da tsawa da zage zAge
   Kuka kawai lailah ta fashe da shi
Inda shi ma ya shiga kai hari ma zahida ta ko enan duk da bai ya kallon ta da kyw

'    ta rike rigar sa yana fizga rai a bace yana hargowa tace ""Just stop there u ugly monster
tare da hankade lateef kasa da karfin ta
Tana masa mugun kallo

  Ke kuma yau sai na daka ki kafin na kaiki wajen mumy
A gidan nan ba mu taurin kai kaece mai kunnen kashi ko?to baki isa ba
Zungurin ta tayi ta tura keyar ta waje sai kuka lailah take

  A daburce ya rarrafa yana kukan mai xAfi ""lailah.....Yar uwa ta kar ki tafi ki barni .ya fada ranshi a matukar bace yana huci kamar mai shirin zaucewa
  Ko da yaga abun bazai masa ba zumbut ya mike ya soma bin sound din kofar yana kiran
sunan ta da karfi ..har yawu na bin bakin sa
 
Ko da zahida ta gansa yadda yake limping yana kuka yana kiran lailah dake tafiya tana kukan zuci hawaye sharbe sharbe a fuskan ta

  Wani dariya ta danyi na jin nishadi sannan ta ja ta bashi hanya ya wuce... dai dai kusan kan step ya iske lailahn ya mika hannu zai riko ta
  Itako  Ganin ya iske tan yasa ta juya da sauri ta rungumesa cikin kuka mai tsanani tace masa
Go back"lateef
Im fine karka damu dani,kullum ka tuna buri na wata rana kullum mu kasance tare .....
Cikin sheshheka tace zanzo maka wata rana brother

Kankame da ita yana kyarma don zafin da zuciyan sa ke masa
Dan Shiru yayi kafin yace mata you promised? Ta gyada kai tace
I promised.

Zahida da ke kallon su bawai abun baidan ratsa ta bane amma sai ta dake tace"" Ok. ok, enough ta karashe cikin wani shu'umin dariya
Tare da ture shi gefe guda

Nan ta sa hannu ta hankade lailah gaba
Sannan ta juya ta kamo kunnen latteef kamar zata balle"
   Kanaji na? Daga yau kasake fita daga caging ka sai na sa an kai ka bara ko gidan mahaukata koma nasa a kashe ka a gidan nan
Mummana,kazami.ure a curse to our family ..mai ciwon kwakwalwa kawai...dodo
Nasan ko baba na bazai yarda da wannan abun ba.mtswww

Fin cike kansa yayi da karfi saida zahida ta buga yatsun ta a madafan stairs din da suka tsaya...nan take
Ta yarfa hannun tace Kai ..kai. kai ... Bura uba?ni..sa ar ka ce ?ta kai hannu zata wanka mas mari na biyu lailah ta damke ta""
Aunty ki dena dukan sa baida lpya baki gani ne?

A hatsalw ta amsa ""Ehhhh bana gani..in fact ni ne ma shi
Kin bace anan ko sai na wanka miki mari kema,stupid girl

  Shiru tayi tana kokarin kawo hannun ta don ta janye lattef daya kafe don taurin zuciya yana huci daga gefen zahida

A garin ture hannun lailan da zAhida tayi
Sai  akayi rashin sa'a
Kafin ace wani abu lailah tayi tangal tangal tafada kan matakalan daya raba wajen ginin ta ciki
Mai sauka 3 har kas Rigijib da kai...

Wani irin kara lailah ta sake kafin ta isa kasa
Daga bisani sai jini ya soma kwalala ta kan nata,take numfashin ta ya dauke,

Ko da zahida taga hakan sosai hanjin cikin ta ya kada da sauri ta sauko tayi kasa itama tana famar kiran sunan lailah  a razane

  Ko da lateef yaji haka
Shima a dabarance ya soma rarrafawa ya buga nan ya buga nan haka ya dinga saukowa duka steps guda ukun nan duk ya gurje a jikin sa don sauri da fargaba

  Surutun su ya masa jagoran inda suke a falon yace
  "lailah? Ena kike
Lailah meya faru
Yar uwa ta?
Cewar sa yana lalume yayin da kowa ya tsura mas ido cikin zahida da mrs rod data fito daga sashin home office din ta data ji ihu,

  Gashi nan ,duk laifin ka ne mugu kawai azzalumi
Zahida tace rai a bace tana nuna shi ma mrs rod

Meya faru dake ne,ena kike .....
?lailah......
Lailah?.....
Kawai yake fada cikin zafin nama bai kula su ba

Dayake idon sa daya na dan gani Dishi dishi ya hango ta a kasa suna tsaye akanta sun rasa me zasuyi zahida sai bari take

Nan ya karaso wajen su Gurfana yayai agaban ta ya tallafo ta da kyar
Ya fashe da kuka mai cin rai" lateeff?
   Kamar da wasa yaji tace ciki ciki amma idon ta alumshe
Cikin kuka yace
   Lailah, lail,
Ki tashi Zan rama miki
I promise zan rama miki..ya karashe  a zuciye yana huci
    Dan kadan ta bude ido kamr mai shirin bacci
Ta dan murmusa ta kamo hannun sa
' kai kyayyawa ne'ena kaunar ka
Pls Ka kula da kan.. ka.. And
Alw..ys.kno..w i be..ived .in you..sai bata kara cewa komai ba ta kwanta luff a dan karamin hannun sa

Shiru yayai na dan lokaci ya kure ta da kallo duk da bai ganin ta da Kyawu har yanzu

Nan mrs rod da zahida suka karaso kansa daf da daf tace
Ohh my god she's dead
mumy! Tangal tangal zahida ta soma yi cikin zaucewa tana neman fasa ihu
Don harga Allah bata so kashe lailahr ba

  Mrz rod Hannu ta dauraa kai fiskan ta alaman damuwa ta amma sai ta kamo zahidan tace shhhhhhhhh
Zo nan zahida keep quite
Ki nitsu ..

Girgiza  kai ta soma yi tana cewa ,No, no mumy na shiga uku..yanzu za'a kama ni kenan?A rude zahida take fada

Shhhhhhh ke, shut up bana ce kiyi shiru ba zahida
Ko So kike ki jawo min asara biyu ?bakisan idan wannan maganar ta fita shikenan kin kwaba komai ba ko?
Idan naji kince wani abu anan zan mare ki ..shuu
tafada mata da alaman  tsawatarwa

Da kyar tayi composing kanta ta tsaya tsuru tsuru a bayan mimyn kamar marar gaskiya

Suka zubaa lateef ido dayayi turus kan gawar lailah

Nan mrs rod ta danna security alarm kafin wani cikakken mint uku
Sai gashi an shigo da security

  Shi dai lateef ya kafe idon sa kan gawar lailah ya na faman danne goguwar makaman daukan fansa dake kururuwan fitowa a zuciyar sa

  Sam hankalin sa baya kansu
Sai da yaji ance
ga shinan
Ku kama sa
Ya kashe min yata ..dama sai da nace ku dena zuwa kusa da shi
Baida lpyar kwawalwar
Amma taki ji
Wayoo Allah lailah na
Ya kashe min Yata

Dum dum ya ji a ran sa ,kansabya wani irin bugawa a razane ya juyo
Ya ce " na kashe ta?

Eh mana jamal da suka shigo daga baya ya fada yana kai mas naushi a baki
Sauri akayi aka
tare sa
inda jabir yayi jagora wa cid police da likitan su na musamman xuwa cikin wajen

Lateef  Bari ya ke yana kumfan baki yakasa cewa komai
Haka ma kunnen sa ya toshe ya  dena jin abubwn da ke faruwa awajen
Sai huci yake kamr kububuwa
Bayan an tattara bayanai gaba daya na zaHida  da mrs rod da sauran yan gidan
Handcouf aka daura ma karamin hannun sa
Sannan liktar cid tace
Mrs rod
Zamu rike sa mu duba ciwon kwawalwrsa
Kafin nan idan yakai munzali
Za mu aika sa gidan yari kamar yadda doka ta tsara .

Idon ta cike da hawayen karya tayi luiii zata kai kasa tana cewa oh ni hidayat
Na shiga uku"
Da sauri mrs jamila ta riko ta
" mrs rod
Cmon
Ai hakan yafi ..ko so kike ya kashe miki sauran yaran naki
Wannan hukunci itace dai dai da shi

Fatan mu Allah ya bashi lpya
Nan aka wuce dA lateef da ya kage ba alaman dariya ko kuka ko magana a tattare dashi

Kamar dutse haka yake tafiya ko juyawa baiyi ya kalle su ba har a
Suka bar gidan ..

Shiru wajen ya dauka bayan kowa ya wuce dakin sa

nan taje gaban hotun mahaifin su ta kure da ido tana jimami cikin ranta tace
" ka yafe ni abdul fatah"
Nasan duk enda kake yau ka tsine min rayuwa ta"
Ena son danka lateef' don shima jini na ne amma kasan so yakan zama makamin cuta ko?shyasa ma na fifita son yan uwan sa akan sa don sun fisa amfani'

"ta  dada shafa hoton tace "he's just a burden to me ,nasan hakan ma zai fi masa sauki kuma
nasan kaima ka fahimce ni mr rod
Ba laifi na bane miji na

lateef baizo min ta yadda zan amfana da shi bane"
Forgive me,

😪😪😪



*"surriem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top