14

*⚜BRILLIANT WRITERS ASSO🖊*

💔
    
   *SO MAKAMIN CUTA*
       _'the sword of evil love'_

_Story and  written by_
  *SURAYYAHMS*🔥
    

*DEDICATED TO-*@UMMERHERNY NERSALLAH.

*Allah ka kare mana yan uwa musulmai a duk enda suke,ka kuma bi kadin wayanda aka zalunta a hanyar jos,ya ubangiji ka saka mana😪😪😪*


*Page▶14*


Ashween ne Zaune a asibiti kamar da gaske
   Kamal ya tinkaro sa
Yana dariya ciki ciki kamar munafiki ya sai yazo ya tsuguna daf

  ' daure fuska ashween yayi ya kau da kansa
Wanda ya dada sa kamal fashewa da dariya,

  Da Allah ni ka kyale ni,banson iskanci fa
Ya fada a fusace

  Ok calm down ..mr zahida rod
Wallhy dramar ce take bani dariya
Lallai yarinyar nan yar iska ce ji enda tayi lumui ta kwantaa asibiti ta hanaka motsi? Hmm

   Mswwww kayi na kudin ka fa kamal,
Itama Ba barin ta nayi ba ta san hali na sarai,so nake ta sa hannu akan wancan abun dana fada maka shiyasa kaga ena bata lokaci na  anan din im so tired..yafada sounding serious

  Ka kara hakuri kamal ya dafa shi ..fuska ba yabo ba fallasa
Ya labarin ita madam hidayat din? Yaushe xata dawo daga china?

Ashween yace, In four weeks time,amma kafin nan insha Allahu na kammala komai sai dai next plan
Gyada kai kamal yayi yace " insha Allahu roh
Barinje na duba babyn namu ....ya mike ya shige cikin room din yana dariyar tsokana

Zahida dake kallon karasowar su ta glass din kofar Kifi kifi ta so mayi da ido ,tana nishin karya "shiko kamal sauya fiska yayi ya dube ya yace
Sannu zahida luv ,.hw r u feeling now?
  Tace, Fine ,sai yanzu kake zuwa ko ai ka kywta

Dan tabe fuska yyi yanayin tsokana yace " so kike ki hada mu biyu ki nakasa..abokina fa har ya rame pls get well mana kar shima fa ya kwantaa
   Dariya tayi cike da jin dadin maganan
Amma sai ta marairace fuska tana duban sa
" bayan sai nayita ihu anan kafin yazo kusa dani,.ash is so lazy kamal.. ta karashe a shagwabe...

Ashween Murmushi kawai yayi baice komai ba,
Don shi ya san me take nufi,. Amma ya riga yayi alkwari har ya mutu ba abunda zaisa wani abu mai kama da romance ya shiga tsakanin sa da ita...ko da kiss ne

Hmm karki damu kamal yace
Ki warke kawai..kinji?
Kamar baby haka ta gyada kai
Jefa jefa suna hira,har suka watse

Gefe guda bangeren asibitin
Ammy ne zaune a counseling room tare da doc
" zugum tayi
Bayan ta kammala karanta sakamakon gwajin ta
   Kallon nitsuwa doc ta mata sannan ta ce
Kinada sauran lokaci hajiya shahida
Kar ki manta farincikin ki is important a wannan stage din
Kiyi kokari kibi kai'dojin maganin dana kara miki yanzu  in akayo haka ba matsala insha Allahu

  Murmushin karfin hali ammy tayi tace
Hakane doc,kullum kina fadan haka karki damu insha Allah zAn yi kokari

Dan shiru doc tayi...daga baya tace tun da nake bantaba ganin mace mai karfin zuciya kamr ki ba hajiya,
Sau dayawa mutane masu dauke da brain tumour ke qarar da rayuwar su ta hanyar damuwa da kunci  tun kafin ciwon ya yi halinsa
Amma ke kam sabanin haka ne ,,na miki murna

Murmushi kawai tayi ta ce" nagode kwarai ..kema ai kina iya bakin kokarin ki Allah dai ya saka miki da alkahiri..

Bakomai hjy en akwai matsala a kirani anytime

Insha  Allahu ..Sai anjima  sukayyi sallam ta wuce gida

Tun daga ranar ammy ke kokarin danne zuciyar ta
Amma ena waNi bin damuwa da tunani na cin karfin ta tasan mutuwar ta yazo ba shakka
Kullum tunanin ta rayuwar  ashween da jasmine
Musamman Da yanzu ta lura ko maganan ma ba sosai sukeyi ba.

Kwana na tafiya kullum tana dada kirga ranakun ta ne ,..don likita ya tabbatar mata tana mataki na karshe

Amma Haka take daurewa ta danne duk wani alama ,.tana cin abinci ta tana shan maganin ta amma duk a boye ba wanda ya lura da halin da take  ciki

Bangaren su zahida kuma Yau kusan sati guda kenan media tana news akan familyn  madam hidayat wanda mafi aka sari sun samu tallafawar kara bude ido ne ta wajen ashween, yanzu haka jabir ne zaiyi wani gagarumin concert na tallafawa yan mata wanda basu da galihu  karkashin wani companyn kamal...

  Daga gidan hajiya hadiza kuwa ashraf tsungune yayi kansa kasa yana kukkuni
  "Mamy amma wannan ba adalci bane
  Ni banga wani abun jira anan ba ,kawai dai ana neman a hanani yarinya

  Yi min shiru da Allah'
Toh ai sai kayi tayi, sau nawa zan kira jasmine din baki da baki tace min ita bata muradin auren ka,ta nuna sa da dan yatsa tace ashraf
Kaine kake tilasta ta,

  Wani cunkusashhen bacin rai ne ya durmuye sa amma sai ya danne zuciyan sa don hargowa take kamar zata fashe nana ya sake cewa" Mamy ai dama basai tana so ba ,ke fa yar uwan ammyn ta ne. kawai ni in za'a bani kawai  a bani....

Wani mugun kallo ta bisa da shi ta ce
Lahhhhh ta dafe kirji
" zaka mata na dole ne ,? Toh bisimillhi

Amma dai Kar ka manta idan jasmine ba amince ba na tabbata hajiya shahida babu abunda zatayi akai..gwara ma ka saukaka rashin kunyar dake damun ka kaje chan in kun shirya da ita to sai kazo min da magana ni ba ruwana da iskanci
Bude baki yayi zaice wani abun ta dakatar da shi dacewa tashi,oya. .oya ..fice min naga  wuri
Bai ce komai ba "Sum sum ya wuce waje rai a bace  ai kuwa
Bai tsaya ko ena ba sai gidan su jazmine din

Sosai ta sha Mamakin ganin sa don kuwa ta san rabon sa da zuwa yakai 3 months kenan yau

  Lpya kuwa ?
Ta fada tana dan tura sa waje kar wani ya hango su
  Bankade hannun ta yayi yace"   Ai dole zAki min wannan tambayar?jasmine Ashe ke munafuka ce

  Cikin mamaki tace ni kuma yaya ashraf me namaka na munafur ci?

     Ohh..tab...baki ma sani ba ko, ai dama bazaki sani ba tunda kin mayar dani shasha sha..wawa uhm

Ranta ne ya soma baci amma sai ta dago calmly tace
Ban fahimce ka ba fa har yanzu?

  Tswa ya daka mata " Meyasa a gabana kike gwada min kokarin ki akan maganar auren mu alhalin ke kike cewa su ammy baki son auren? Answer me ya karashe a tsawace

   Shiru tayi tana kallon sa , don tuni taga alaman bacin rai sosai tattare da shi ,ko tsayuwa mai kyw bayayi

Gashi Tarasa me zatace don batayi tsammanin maganan zaije kunnen sa da wuri ba

Kayi hakuri yay ashraf, ni ba wai cewa nayi bana so ba,
U just misunderstood me

  Cikin kunan rai yace"da Allah malama kimin shiru ..ko tausayi na bakiyi jasmine ko dan kinga sonki tayi min illah ne ? Aure fa nace ba wasa ba...
Nan idon sa ya ciko da kwalla ya soma binta da wani irin kallo ....nasan baki dauki komai da muhimmanci game dani ba shiyasa kike min haka
Amma ba komai ,
Zan baki dama kije kiyi tunani na miki alkwari duk abunda kika yanke a zuciyar ki ,zan karba ..kaiwa nan ya juya ya tafi ya barta anan tsaye

  Durus ta tsaya kallon sa har ya lume ,mamaki da tausayin sa ya kamata lokaci guda,
  Dan tabe baki tayi cikin ajiyan numfashi tace" ohh ni jasmine wallhy
Ba laifi na bane, zuciyata ce ta ksa aminta da soyyayr ka yaya ashraf..don ban taba tunanin da gaske har haka kakeyi ba .gani na jiki na kawai yake so"

Juyawa tayi tana tafiya cikin nazari tace "But I think i will give him a real chance..tsakani da Allah ko dan naga in dagasken yake.
Inshi ne miji na Allah ya bayyana alkahirin dake ciki
Ta karasa magananta tare da shiga cikin main hause

Bayan kwana biyu bata kira shi ba haka shima bai neme ta ,
Don ita kam tsaf take shirin inta juya kan yaya ashraf ba abunda zai karkata ta kuma sai aure kawai,.. ..sai dai kullum inta soma wannan tunanin sai ta kasa kaiwa stoping point..shiru shiru mafita taki fitowa

Gefen ammy kuwa kwana biyu da shike ashween bai cika zama ba, sosai shakuwa mai karfi ta sake ninkuwa tsakanin ta da jasmine

  A Kullum acikin mata nasiha take,wani lokacin tayi kuka wani bin suyita dariya don kuwa ammy cikin fasaha da hikima irin na manya take koyamata har da tattalin zaman aure da rayuwar zama da mutane

Duk da haka sam taki bari jasmine ta fahimci ciwon dake damun ta duk da ma ta sha kama ta tana shan magani a boye.

  Yau ma kamar kullum
Tana kwance ta rasa abunda ke mata dadi
Zafi jikin ta yayi sosai gashi yaki sauka duk da maganin data sha da daddare

Hannu ta daura akanta tana ambaton ubangijin ta a hankali
Tana maimaita addu'o i kala kala,
Tanayi Amma Kamar ana bulbula ciwon kai haka takeji
Jim kadan jini ya soma fita daga ramin hancin ta

   Hawaye ne mai zafi ya sauko mata zuciyan ta na neman ya zama weak
Sabida yanayin data  shiga ciki tunanin rayuwar da zata bar ma ashween da jasmine a lokacin

    Muryan ta na karkarwa ta daga kai ta kalli sama  tace"
Ya mujeeb,
Yah zul jalal wal- ekram
Ubangiji na mafi tausayi da rahma kan bayin sa
Kai ka rike ni ka rike yaya na ,kai kaba ni ikon tafiyar da su bisa amanar iyayen su
Nayi imani da rayuwa da mutuwa, nayi Emani zaka   rike min su kan amanarka tabbatacciya bayan rai na,
Yah kareem
Ena rokon ka ka basu rayuwa bisa kan tsarin ka,ka kyautata imanin su,ka basu juriya da hakuri ko da bana nan tare da su,
Sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya
Bakin ta na bari ta najin wani zafi a zuciyar ta,

  Shigowar  hajiya hadiza ya sa ta jin komai yatsaya mata chak tunanin ta ko jasmine ne ta shigo gaishe ta,

Don lokacin da ashween ya zo sam taki juyawa don kar ya fahimci wani abun, sai tayi luf  kamar tana bacci har ya gaji yayi tafiyar sa
    Sauke ajiyan zuciya tayi jin muryan hajiy hadiza,
Hajiya shahidah? Subhannalhi
Me nake gani ?
Abun naki ya yi tsanani hakan ne tace a rude tana neman zama daf da ita
  Hmm bari kawai  ,yanzu Ba wannan ba hjy hadiza
Ai har na tsorata da naji shigowar ki

Ah ' karki damu nice, Ai ena ganin shigowar sakon ki na ce ko lpya?

Ammy tace "Uhm lpyar kenan,kinsan doc tayi tafiya,ciwo kuma ba kai kake da shi ba shi yake dakai
Daga ni na kimtsa kafin yaran nan su zago

Ba musu mamy ta taimaka mata
Sai yanzu ta ke ganin yadda ta rame fuskan ta yayi fau kamr ba jini,

Nan ta shige bathrum da kyar ta samu ta kimtsa kanta sannan ta fito

Nan ta samu Tsaf hajiya hdiza ta gyara wajen
Sannan ta taimaka mata ta gyara kanta ssma sama jikin ta ya dan samu karfi
    ' ko minti biyar ba suyi da zama ba saiga jasmine ta shigo

Ena kwana mammy,
Ta gaida hajya hadiza a ladabce
" da murmushin ta ta amsa
Jasmine sai girma takeyi ,kwanan nan zamu  yi shagali ashe

Kunya ne ya rufe ta cikin sauri ta mike tafada jikiin ammyn nata tana murmushi

Ke kinga irin abun ko?
Ai sai ki fada jikin wacce tayi maganan ba ni ba
   ' dan dariya kawai tayi chan kuma kamr an tsakureta  tace
Ammy ya naji jikin ki zafi
Fever ce? 

Uhm uhm,cewar ammy tana forcing smile a fuskan ta

Ahhhh ni dai kifada min ko na miki allura tafada a shagwabe

Ammy tace To wa ke jin tsoron allura in ba ke ba
Ni tashi min toh . ammyn ta daga ta da kyr

   Murmushi hjy hdza tayj tace yawwa autar ammy
Jeki ki shirya mana,ogu sausage na kifi da white rice yanzu ki kawo auta na,,
Da murnan ta ta amsa
Cewa toh
Dan tana mugun son tagan ta a kitchen tana girki kamar amarya,abun na burge ta tunda ammy ta soma mata training irin haka

  Duk murmushi suka bita da shi har ta fice
Nan hjy hadiza ta maida kallo wajen ammy
' nikam yaushe zaki fahimtar da yaran nan naki halin da kike ciki ne?

   Dan shiru ammyn tayi
Daga baya tace
Baza su sani ba hadiza
Ba yanzu ba,nan annurin fuskan ta ya dauke

  Ah ' a hajiya shahida toh sai yaushe ?
ni dai anawa ganin
Wannan babban kuskure ne
Qaddara yau ace wani abu ya sameki a gidan nan ya zakiyi inba ni ba doc?
Ai ko adduan su ma babban makami ne awajen ki,sai Allah ya ji tausayin su fiye da mu ma ya sawwaka miki lalurar ki

Tace  Haka ne ,amma hadiza
Me riba ta in na fada musu ciwon da nasan mutuwa ce kawai saukin ta?
" ena tausayin su fiye da yadda nake tausayin kai na hadiza
Hawaye ne mai zafi ya soma saukowa mata
  " shiru ne ya ratsa wajen sannan ta ce
Nasan kinsan jasmine jini na ce
Yar twin sister na ce da mijin ta yayi sanadiyar mutuwar ta  a plane crash don kawai son ransa da  na karuwar sa"

Dama itace dangi na kwalli daya a duniya
Ta tafi ta bar min yarta ,
Yau Jasmine bata san ma wacece mahaifiyar ta ba bare mahaifin ta
ni kawai ta sani iya rayuwar ta ,
Kina ganin en nazo mata da wanann labari taya zance mata mahaifin ta ne ya hallaka mahaifiyar ta akan wata ya mace?sannan ko sau daya bai taba neman ta ba ai yasan tana raye,
Toh Da na mata karya gwara ban fada mata komai ba hadiza

  Ita ma hjya hadiza shiru tayi jikin ta ya dan yi sanyi
Tana famar nazarin maganan

  Chan kuma sai tace shi kuma ashween fa
Kinki gaya ma kowa alakar ki da shi
Tun kafin yaya abbas ya rasu ya sha fushi dake akan yaron nan amma sam kinkii bude baki kice komai
Shikam ai ba jinin ki bane ko?

  Wani dogon numfashi ammy ta sauke
Ta sa hannu ta share hawayen ta
Sannan ta dubi hajiya hadiza
    Labari ne abun al'ajabi kuma  mai tsawo
Amma zanso kimin alfarma daya  hadiza

'fade ta ko wani iri ne

  Uhm, ena so Ki min alkwari wannan maganan da zan fada miki anan zaki binne ta
Ena nufin bazaki fada ma kowa ba,
Kin amince?

  Dan shiruuu tayi sannan tace duk da ban san dalilin ki ba amma na amince shahida"
Waye ashween? Menene asalin sa?ena iyayen sa?

Ba bata lokaci ammy tace  'kin tuna wani hoton yaro da kika gani a drawer ta ranar tun muna turkiya har kika tambaye ni waye ne ?

dan shiruu tayi cahn tace Ehhh na tuna

Yawwa ,toh da farko dai zan ce ke kadai kika taba sanin asalin kamannin ashween amma na boye miki nace miki ba shi bane!
Ba don komai ba saboda  na tsare sa daga mugun hannun daya fito shiyasa nake boye sa ma kowa,har ma ku yan uwana

Ta cigaaba, Ba anan ya tsaya ba
Bayan dan binciken danayi akansa da zaman fahimta da na ma yaron anan na gane asalin waye shi
Shine kawai na qudiri masa jinya a boye,

Hadiza Da hankali na Na yi saurin amincewa da jinyar plastic surgrey da doc yace zai masa  don itace hanya daya na tseratar da shi daga  jami'an tsaro dake neman sa zasu kamasa

    Dafe kirji hajiy hadiza tayi tana salati, kanta har  ya kasa zama waje daya tace
  Ban fahimce ki ba hjya shahida
Kina nufin wannan nakasasshen yaron dana gani shine ashween?

Gyada kai ammy tayi tace tabbas shine

Wani salatin ta sake bugawa cikin mamaki
tace to waye iyayen sa? Meya hada sa da jamia'n tsaro a dan wannan shekarun nasa

Murmushin takaici ammy tayi
Ta sake goge  kwallar dake gefen idon ta tace
  ' a hanya ta ta dawowa daga asibiti lokacin jasmine na karama bata karban ruwan nono sai madara
Sam Ban lura da haddarin dake gari ba nasa musa driver Allah ya jikan sa"
Ya dawo da mu gida

A hanya wannan ruwan ta same mu,gashi ba wajen fakewa driver mu ba yadda ya iya  haka muka kusa kai cikin ruwa muna tafiya sannu a hankali
  "sanadiyar tafiyar mu a hankalin ne na hango wani abu a kasa a shimfide gefen wani mutaccen itace na ni dauka irin kayan nan ne na datti na mahaukata a dunkule..amma damu ka iso kusa
Sai kuma naga ashe  fa mutum ne
Munzo daf da shi charaf muka hada ido
Ashe yaro ne a nakashe ya dunkule sai kyarma yake ruwan nan na dukan sa amma bai motsa ba
  Lokaci guda zuciyata ta kamo da tsananin tausayi sai na kawo ace dan da na haifa ne cikin wannan yanayin ' ba yadda musa baiyi ba kan cewa mutafi kawai mubarsa

Dalilin sa kuwa cewa mutanen duniya abun tsoro ne ba kowa zakaga ni a titi ka tausaya masa ba
Amma haka naki fir,
Sai da na dawo na dauko shi,
Share hawayen ta tayi ta cigaba da cewa

En takaice miki sai da yakai kwana uku yana zazzabi sannan na ma gane kansa
  Kullum yana mugayen mafarki' mai ban tsoro
Ciki yana kukan mutuwar wata wacce yake kira lailah"
Dana ga abun ya yi tsanani ga shi yaro ne
Sai Na kaisa asibiti na mika sa ma therapist,

Anan suka tabbatar min da emotional trauma ce ke damun sa, ban bata lokaci na soma jan sa ajiki har na samu nayi nasara muka fahimci juna sosai

Da bakin sa ya bani labarin yadda uwar sa da yan' uwan sa suka juya masa baya sannan suka laka masa mutuwar twin sis din sa wacce yake kira da lailah a mafarkin sa.
Ashe ma daga prison detention na yara ya gudo
Kwanan sa uku yana tafiya shine ya rakube wajen nan da na tsince sa,

  Kuka hajiya hadiza ta fashe da shi tana salati tana sallamewa
Chan da zuciyan ta yayi sanyi tace 
Toh me kikayi akan  hakan,nasan dai ba ZAllan wannan ba ne tarihin ashween
Kinko san suwaye iyayen san?
Kuma a wani gari suke?

Ammy tace Tabbas na sani mana,
Nadai yi kokari na sauya sa ta hanyar jinya
Saboda na samu daman bashi kariya
Kafin na bincika al' amarin sa da kyuw

Ganin yadda mood din hjya hadizan ya sauya ya sa tace
Yanzu dai muci abiinci anjima zaki ji komai"
nasan duk yadda akayi jasmine ta kammala kar ta shigo ta fahimci wani abu

    Ha ka ne  cewar hjiya hadiza da tuni jikin ta yayi lukwi yayi sanyi ...

Falour suka fita suka ci abincin cikin raha da dariya kamar ba abunda ke damun su
   Kiran ashween din ne ma ya dan katse su
Nan ya sanar mata bazaii samu dawowa da wuri yau ba ,
A Haka sukayi sallama da kyar don yana mugun jin ammyn san nan aransa

Jasmine da ke murnan dawowar salma tuni ta nufi gidan su hankali kwance "

Nan suka tattara suka suka ka daki don cigaban lAbarin ashween.


🙌🏾👀


*surriem*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top