chaptr32
BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 32
Hasken ranan daya hudo ta labulen dakin yasan Mufrad farkawa daga barci,a hankli ya bude idanunsa da Sukayi Wani irin ciki ciki tamkar ba baccin yay ba ya budesu yanajin wata muguwar azaban kasala da gajiya a dukkan gabobin jikinsa ga Wani azazzaben nauyi da ciwo da kansa yashigayi,agogon dake gefe ya kalla ganin 6.30 am yasashi mikewa a firgit ya zauna a tsakiyar gadon can sann ya juya ya kalle Aina'u dake famar sharar baccinta rungume da pillow ta Kuma sake jikinta ayanayin da baisaba ganinta ahaka ba...
Kansan dake masa Wani irin ciwo da juyayi ya rike cikin kasa iya gane abunda yakeji aransa Shidai yasan ya Tara da Matarsa jiya Amma ahalin yanzu bazai iya tuna komi daya faru ba..
Wani wahallalen tsaki ce ta kufce masa ya shiga takune fuskan sa dats so fresh and fair,cikin rasa nayi ya sakalo kafafun sa kasa yana mai mikewa tsaye tsar namiji dashi Dan daga shi Babu komi ajikinsan sai zaratan jijiyoyin sa da suka hargitso suka mimmike tuni ya hau miqa yana langwasa qas qas cikin yanayin son ya warware kasuwan jikinsan dayake masa tsami tsami Dana kwankwason sa dayakeji Kamar duka akayi masa awajen yana daddana su da palms dinsa Koda ma zaiji dama dama,bayan Nan
Bai yi wata wata ba ya fada bathrum ya saki cool shower akansa to help him relax his nerves and muscles shiyasa ma Bai yi amfani da ruwan dumi kwata kwata ba,agurguje ya fito bayan ya kammala wanka Duk hanklin sa naga kan lokaci, ko mai Bai iya shafawa ya janyo wata dark blue jallabiya ya zura ajikinsa ya hau biyan sallan asubahi dabai samu damar yinta akan lokaci Yau ba
Har ya idar da sallansa Aina'u bata farka ba sai faman juye juyen ta takeyi tana Wani irin harhade kafafunta tana matsewa cikin bacci mai azaban Nauyi,Wani Allah Allah yake ya kammala axkar dinsa ya miqe
Ya sameta one of the things dayake hadasu fada kenan
Ita bazata tashi akan lokaci ba bare ta tashe shi yy sallah inya makara shi mutum ne da ya tsani yin salla a kurarren lokaci,...
Yana kammala idarwa ya nannade sallayarsa ya tura cikin drawersa ya rufe yayo Kan gadon ya sameta fuskan sa Adan dore Babu yadda baiyi da Ita ta farka ba anma haka taki amsa shi firrr har Sanda ya harzuka cikin masifa..Yace "babe meye haka da Allah ki tashi ki tafi aiki it's 7:am already"..
Jin Yace 7:am ta hantsala ta miqe zaune firgit tana dube dube u mean har 7 yayi Ina cikin gidan Nan..?
C'mon muffy meyasa baka tashe ni ba,tsaki taja mai tana mai yatsina fuska,Yau fa zan soma zuwa new office nd u just ignore it,Wani wawan kallo ya mata wanda sai da wata jakr tsaki ya kufce masa,bai ko kula ba ya miqe yay waje batare da ya kulata ba ya wuce ya nufi can kasa aransa yana Furta "I can't believe this."..
Kafada ta daga alaman Bata ko damu da ficewrsan ba ta sauko kasa tana laluben kayan baccinta datazo masa dashi Ganinsu tayi akasa barbaje ta shiga tsincewa tana gama kwashe su ta kama hanyarta tayi waje
Dakin Zarah ta shiga ganin Wai har batanan yasata kada kai ta nufi bathroom ta doro wanka da alwala Duka duka Within 30 mints harta kammala komi ta fito,anan dakin Zarahn ta cancada makeup dinta,sosai ta fito tayi kyau hodar take shafawa masu haske ne saitayi lining lips dinta da pink jambki
Room dinta ta wuce feeling Abit relieve a sassan jikinta Duk dama Zuciyarta na mata bala'in nauyi da zafin abubuwan datayi na zubda aji jiya da daddare, she just can't believe herself, ji take kamar Zara ta Gama cutar da rayuwarta data jefata halin sakewa namiji kanta kamar wata jakka,isn't it any oda way apart from sex da zata iya using danta mallake soyayyar muffy?She honestly believe dat a man is suppose to be the one worshiping a woman desires bawai mace ba,tana son sex Kuma muffy yana mata bala'in dadi Amma kwata kwata ba haka ta tsara abun aranta ba,she want a life with him Wanda zatana Jin komi nasu dashi ma tafiya daidai har cikin zuciyarta da kwakwalta,but she knew she can't continue like this da sex din Nan,shikansa shan maganin matan ma is actually bothering and stressing her,gaba daya atakure yake dakema nasu salon yadan banbanta da yadda ta sabaji mata nayi,a yanzu haka Babu abunda yafi gajiyar da Ita face irin abubuwan tsibbace tsibbace da Zarah tasata tanayi inshata hadiye wasu magangunan,Wani bin haka zata sakata ta tube tsirarar da bottle din maganin a hannu,sai tace ta dubi gabar ta kira sunan sa ta dube arewa ta kira sunan sa har karshe sannan Tasha ita wayannan abubuwan duk sun Daure mata kai,Nan gaba ma jitake kmr
harga Allah bazata iya jure neman namiji ba saidai in Ace sha'awa ne zai kasheta..
A hankli ta turo kofar dakinta kallo daya tayi ma koina Ganin yadda ta barsa a kimtse haka ta dawo ta samesa,bathrobe din dake jikinta ta kwance batayi wata wata ba ta bude hadadden scrolls dinta na kaya ta soma fidda kasaitattun dresses dinta na zuwa office Dan tuni tasa muffy yasaka baki aka dawo da ita Aikin a abuja Wani hadadden milano gown green colour ta dauka ta saka as usual ta hadashi da maching colour na make up dinta,pink heels da bags dinshi na kamfanin torch berry Dan karamin multi colour veil tayi rolling kanta sannan ta feffeshe jikinta da turarruka masu Dan uban qamshi da tsada ta dauki key din babban motarta ta fito.
Cikin yar sauri take takunta tanayi tana duba writswach dinta dayaci wata katuwar gold watch tsaki ta sake ganin she is soo late aranta ba haka taso ba,taso ne ace yau ta isa da wuri danta same daman yanka rashin mutunci ma new juniors dinta ita mace ce dabatta son raini ko kadan.
Isarta kofar Zara keda wuya taga Wai haryanzu Babu kowa aciki juyowa tayi fuskanta Adan daure, zuciyarta har Wani bugu yake da tunanin Inda zaran zata kasance da sassafen Nan Wanda ko ahalin gidan ma bawai sun tashi bane
Tsaki taja Jin ydda
Kwakwalnta yaketa famar sakonyo mata abubuwa,atake taji ranta ya hargitsa ya soma baci da tunanin abunda Zarah zata iya aikatawa na zubda aji agidan da sassafen Nan..
Where d hell cud she be?cikin zuciyarta take ta Furta Hakan ayayin da ta soma bita kasan stairs tana saukowa cikin tsananin damuwa da takaicin zuci
A daya bangaren kuwa tuni Zarah ta fice Dan ita ko salla bata yi dake kawarta xee zee ta riga ta kwabe ta dayin sallah da wankan tsarki cewarta malam yace in tanayinsu maganin da ake bata bazaiyi mata aiki ba..
Da zee zee da malam sun riga sun cusawa zuciyar Zarah sanin cewa tanada sanyin jini gaba daya sun rudata da karyan cewa aljanu sun duba sunga cewa asali itace bata da sa'a a arayuwarta,
Inhar Kuma zasu magance mata matsalar haka to dolene ta dena salla da wankan tsarki sannan tayi Duk abunda suka umarceta da tayi
Shiyasa arayuwa Babu abunda ya dameta duniyan kawai ta sako agaba,Daga ta farka abarci sai ta fada ban daki ta ci uban wankanta na yan karya tanabi da kanta a slow kamar wata sarauniya komi cikin tattali takewa kanta sannan bata sanya wajen neman cikar burinta
Shiyasa ma tun barinsu falo jiya ita batayi Wani bacci ba,around 4am ta farka ta hau hada maganin wanka tafi minti ar'abin tana cikin ruwan tana tsuma kanta tana wasu tsibbace tsibbace,kafun ace an fito Daga sallahr fahjr harta kammala ta fito da zimman tare shi awajen motsa jiki,cikin shirinta tsaf ta fito cikin wata arniyar sport wear white colour ta kamfanin puma Wanda ta kwama ajikinta shima bata kyalesa hakanan ba sanda ta feffetsa masa turaren sihiri, rigar sanyinsa irin mai hular Nan ne Dan haka bata daura Wani Abu akanta ba ta tufke attachment din ta kamasu sama da ribbon, saidan wandon ta wanda yadan kama dirin jikinta ya mata cas cas ta saka white and black canvas booth ma kafafunta Wanda ya mata masiffar kyau,wani balain son kalar datasa din takeyi har cikin zuciyarta dan komi datakeyi saboda imad takeyinsa by now Babu abunda bata sani akan yanayin rayuwarsa ba,his favorite colours his fav food Duk Wani abunda yake so da abunda baiya so hatta abubuwan da yakeyi da Inda yake zuwa tsaf sanda tanemi masaniya akansu
As part of her plan na samun shakuwa dashi yasa yau din dole ta yi sammakon fitowa wajen motsa jiki ta sameshi dantasan motsa jikin kusan al'adansa ne,saidai Duk da haka harta fito waje bata dena Jin fargaba ba sakamakon yadda Wani bangaren zuciyarta nata yake zargin cin karo da mufrad awajen saidai da abun mamaki yau bata gansan ba..
Da yar karamar sallama ta shigo ganinsa zaune akan waist mill machine kanshi akasa daga Ganin irin zamn dayayi kasan hanklinsa ya riga yayi nisa ta Wani wajen Dan harta karaso daf dashi bai wani lura da sautin takunta ba,tsayuwa tayi na kusan mintina uku tana famar aikain kallon sa,as expected kayanjikinshin all white ne Babu surkin Wani kala ajiki wanda hakan ya balain Kara mai kyau da gwajiini a cikin idanunta tanajin Wani irin sonshi da shaawarsa na mamayarta har cikin kokon zuciyarta da ruhin ta,dafa kafadunsa dayaji anyi ya sashi katse tunaninsa ya juyo suka hade ido da Zarah wacce already ta tarbe sa da wasu irin sihirtattatun Murmushi mai kumshe da tarin manufofi,turaren jikinta Dana shi ya gamutsu ya sauya ma yanayinta nitsuwa mai rikitar da gangan jiki murya mai sanyi da taushi ta kakalo ganin yadda ya kafe kwayar Idonta da kallon da shikansa Bai San yanayi ba, tana murmushin tace mai hi?..ba yabo babu fallasa ya Kau da idonsan yace mrn batare daya motsa ba koya nuna rudewarsa a fili ba sabida shi mutum ne mai sanyin nitsuwa da kamun Kai...
Harta zauna gefe da shi bai kara kallon ta ba Nan da nan ta shiga drawing conversation tanayi tana jan aji cikin nuna masa ita sam batayi tsammanin ganinsa anan bama.
She was just acting normal tana Kuma balain watching salon kalaman ta Inda tasan dai bazai taba cewa bibiyarshi takeyi ba
A hankli harta soma drwing attention dinsa kanta da irin hirar game din da ta dinga yimasa while shikam Bai fiye son tankawa ba all his tot nd worries naga kan tunanin datazo ta samesa yanayi na rufaida.
"He dream about her yestade,daya farka saiyaji hanklin sa ya bala'in tashi aransa yanajin mugun sha'awar ganinta da sanin halin datake ciki.
He just can't get over the girl,Duk halin da ake ciki yana makale da Ita azuciyarsa,shiyasa Duk gargadin da yaa sheik ya masa akan ya mance da ita aransa sai yanajin kamar bazai taba iya ba,bayajin samun nitsuwa a zuciyarsa daga ya kwanta shikadai rufaida ce zata shiga fadowa aransa da zuciyarsa saiya rinka Jin kamar baida Wani babban burin daya wuce sanin halin datake ciki ayanzu.
Har Zarah ta Gama barbadenta tayi waje Bai Wani bata fuska sosai ba altho she is convince maganinta yana samun kusanci dashi yadda take bukata she just one is a matter of time kafun shidakansa ya soma bibiyarta
Da soyayyarsa so Duk Wani abunda zai mata ayanzu bawai damunta yakeyi ba tasan dai dolene ya shigo hannu,he was on call with yaa sheik hakan yasa yyi xcusiing dinta ya nufi hanyar dakin sa da wayar a kunnen sa,Babu yadda baiyi yaa sheik ya barsa ya taho kanon ba Amma haka yaki masa fir yace masa yabari kawai shi zaizo abujan jibi inyaso zasuyi magana cos he is kind of busy now da wasu abubuwan haka imad ya tsinke wayar badon yaso ba dan Wani irin mugun Nauyi yakeji aransa nason tambayarsa halin da rufaida ke ciki
Wanda ya kasa iya furta masa a fili.
Daga Nan Bai kara fitowa ba yafada wanka yama Gama mancewa da wata Zara daya bari a waje,ita kuwa Zara cikin salon makircinta sanda ta jawo hanlin shukra kanta Duk dama bawani sake musu fuska takeyi yau saita tsinci kanta da bata labari tanata cewa tuntuni tare da imad take wajen motsa jiki,aranta tasan muddin shukra ta san da haka toh tamkar da kowa ya sani ne..
She just want ppl to start picturing her real intention akan imad tana so asan da cewa lallai akwai Wani kulalliyar Ajiyar romance dake shirin tashi da zafin zafinsa a tsakanin su wanda takeso ta zafafasa banawasa ba.
Nazli is busy da i don't care attitude dinta ta Dade tana sharban baccinta batama San me akeyi agidan da sassafen Nan ba
Shukra ce dai ranar da kyar ta samu ta nitsu tunda ta tabbata da cewa ba dawowa yaa sheik zaiyi yau ba take bushasha Duk da bata kwanta da wuri ba Bai hanata farkawa da wuri ba kaf tabi ta tashe su da gulman Zara da imad data debo mutanen gidan sunata mamaki wasu kuwa basu dau maganan da Wani muhimmancin ba wani sabuwar gagarumin shirin aka shigayi kamar na jiya kowa na kille da dokin ganin sa..
Haka kawai xuciyar zara yake bata cewa akwai wani sabuwar abu muhimmi Wanda ya shafe rayuwata game da haduwarta da IMAD,Wanda by far bazata iya tantance shi ba,wato haka kawai jikinta da zuciyarta yake bata shidin nata ne wani sabon al'amari ne mai karfi a zuciyarta dake yawan alakanta su Wanda a wannan lokacin bazata iya cewa menene shi ba akalla hanklinta dai ya kwanta da kalamn mutanen gidan koba komi sun tabbatar mata da ta karbu awajen su saura shi Dan tabbas yadda taga ake kaunarsan Nan baza a taba kin masa auren Wanda ya yace yaso ba,..
Haka Aina'u ta fice agidan batare da sun hadu ba sai ta waya datake gaya mata komi,zarahn ce still ta dada karfafa mata gwiwa akan magani zaiyi aaiki akan muffy tunda har ya soma kusantarta is just a matter of time shizai soma bibiyarta harsai ta gaji dashi.
Duk yadda ai'nau taki cusa Hakan aranta haka Zara ta ladabtar da Ita harsanda tayi Imani da zancenta ta Kuma yarda da Hakan kwarai da gaske.
Yauma normally akayi breakfast mufrad ne kawai bayanan acikinsu sabida Wani early morning meeting din daya fita a presidential villa
Bai dawo ba sai wajen 11am Nan ma shiryawa kawai yayi suja fice da imad basu kara dawowa ba sai can dare...
Daga ta bangaren rufaida kuwa tunda su maman Iman suka bar gidan ta kasa samun nitsuwa a xuciyarta Duk dama yakumbo tayita rarrashinta da kalamai Masu taushi masu Kara karfin gwiwa da karafafa zuciya saidai Hakan baiyi Wani tasiri akanta ba, can bayan ishai datayi sallah tadanyi karatun qur'ani sannan taji nitsuwa ya Dan sauko mata kwanciyarta kawai tayi batare da ta kula yakumbo ba ta takure kanta waje guda akan gadon tare tarin tambayoyi da bukata masu dumbin yawa a zuciyarta wanda har iyanzu takejin nauyin furtasu waje
Haka daren ya Kare yakumbo bata fahimce yanayin rufaida ba,Dan ko cikin dare taji motsinta sai taji kamar ba baccin takeyi ba inta leka ta gani saikuma taga idanunta a rife
Washe gari da asubahin fari lokacin iskan asuba ya cilla yakumbo Wani duniyar rufaida ta zame daga Kan gadon cikin sanda ta sabi doguwar hijabin ta tayi waje.
Duk da yanayin jikinta na yadda take fama da rashin cikakken nitsuwa da lpya Bai hanata nausawa cikin anguwa ba danjin kanta take kamar wata zautacciya Wanda xuciyarta yake shirin tsinkewa da damuwa da kunci,a wannan yanayin datakeji bata bukatar Wani abunda zai karya mata gwiwa,atleast not a shaming party,Duk dama Hakan kusan dolene Amma bazata iya bowewa aranta jiya ta matikar tsorota da yanayin fassarrar dataji anmammta ita da iyayenta a abakinsu maman Iman wanda bata da aufi tasan aduk sanda aka Furta mata Hakan zataji zafi da ciwo axuciyarta bana wasa ba,jiya har kasa iya runtsawa tayi, cikin zurfin tunanin data yi tayi taga ya dace taje ta same malamin islamiyar su Wanda ake kira da malam sheik Abdul jabbar mohd sule,which she is sure zai saurareta batare datayi judging dinta ba,snn da alaman shine kawai zai iya gaya mata abunda zai iya tallafawa rayuwanta a halin yanzu datake matukar bukatar kwakwaran mafita..
Agaban masallacin da mallm Abdul jabbar yake jan salla ta nemi lungu ta rakube rike da kanta dayake mata Wani irin tsananin ciwo kamar ba sanyin safiyar Allah ba
Hanklinta kwance ta cigaba da kallo har aka watse dake tasan malam yakan tsaya ne harsai ya kammala karatun qur'anin sa sannin ya wuce gida
Sanda wajen yayi shiru bakajin sautin komai sainashi sannan ta tattara sauran karfin gwiwarta ta shiga takowa a hankli harta iso bakin masallaci.
Sanda ta iso daf sannan taji ta kasa iya daga kafafunta awajen tsayuwa tayi tsam tanamai lumshe idanunta batare da shirya ma Hakan ba Jin yadda karatunsa yake mugun ratsa mata cikin kunne yana mai shigan jikinta kamar iska mai tsananin sanyi.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top