chaptr 42


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 42

Da kyar yakumbo ta amshe kudin ta rike a hannunta tanajin kamar itama ta shirya ta bisu asibitiin sai dai tasan bazata iyaba itama jikintan sam babu wani dadi.

Har bakin kofar gidan ta rakosu, mayafinta data dauko dazu akan zata saka shita warware ta yafawa rufaida ta lullubeta dashi, suna isa ta bakin hanyar fita suka iske wata hadaddiyar mota kirar CLS baka kirin tasha tsadadiyar tinted an parke ta ta bakin hanyar yana jiran su,gani tai babu kowa aciki da alamar ita ta tuko kanta ta zo batare da sanin kowa ba..

Bude musu gaban motar tayi yakumbo ta zaunar da rufaida aciki tanai mata sannu sann ta maida murfin motar ta kulle ta koma tayi sakakau abar tausayi aranta tanajin kamar rabata da rufaidar za'ayi na har abada,cikin sanyin yanayi tace"toh me za'a dafa muku in kun dawo kinga yanzu sai inje kasuwa inyo cefane.

janyo hannunta anty fareesa tayi suka danja gefe cikin langwamr da wuya kamar wata mei neman wani babban alfarma
"Tace Kaka dan Allah kiyi hakuri kibari na dan kula da rufaida na kwana biyu ba ciwo bane ajikin rufaida,batajin dadin rayuwarta ne tana da bukatar zanjin muhalli danta samu cikakken nitsuwa,kema kanki kinga abunda ya faru yau,inta iya daure bakin mutane ba lallai ta iya daure na yan uwanta ba,in bamuyi hakan ba wata rana tunani zai iya sata ta kashe kanta da haka nake rokon kibani ita inta samu nitsuwa dakaina zan dawo miki da ita,hawaye cike falll da idanu yakmbo ta juyo.
.."au yanzu ba asibitin zakuje ba tafiya da rufaidar kikazo yi?kai amma wannan yar kin shammace ni,toh wallhy nikam babu ruwana,banci ba ban sha ba Kar hadieza ta zo ta lakamin laifi tace nayi kyauta da yarta databarmin amana.

Anty fareesa tace insha Allahu Bazama akaiga haka ba,nan dai cigaba da lallashin ta da kyar dai ta sauko har suka fahimce juna,wasu nakasashun hawaye ykmbo ta rinka saukewa dagata cikin idanunta na tsantsar tausayi da kewar rufaidar saida ta makurar bawa anty fareesa tausayi,murfin motar da rufaidar ta kwanta ta ciki tayi lamo tahau shafawa ta waje kamar wata tababbiya...tace" dan Allah ki kula da ita kinji?insha Allah nikam bazan gayawa kowa ba,ni?sai kuma infada musu rifaida ta tafi gidanki?hmm ai munafikan anguwar nan har gidankin kuwa zasuje suna tsangwamar ta dan haka in kunje kema karki na barinta tana fitowa tsakar gida..inba haka ba wallhy sai kingan su algungumai.
Anty fareesa dake murmushin karfin hali tausayin su sosai ya cikke kwayar idanunta,
tace karki damu kaka inama zasu san gidana,bare ma akwai karnuka da masu gadi bamai iya isowa ciki bare su tabata kedai kawai kicigaba da yi mana addu'a kece uwar tamu ayanzu Adduar ki ce kan gaba muna barar adduarki..da wuri ykumbo ta hau share fuskan ta tana cewa karki damu at same time tana saka mata Albarka nan ta juya ta kalle cikin motar taga kan rufaida a kwance akan seat tayi shiru idanunta a lumshe sosai kamar wanda tayi nisa a cikin barci wani maqudan ajiyan zuciya ta sauke..
Tace ma anty Reesa Toh Allah ya tsare ai saiku wuce ko kafin azo a ganku akaimu gaba,Anty fareesa tace toh snn ta mata godiya ta zaga ta shiga motar itama cikin sauri,seat belt ta kwance ta sakaya wa jikin rufaidar sannan ta tada motar tayi winning duka glasses din ta rufesu kirif har sama,nn ta kunna musu Ac a slow sanyi mai dadi ya gauraye cikin motar, babu abunda yake ratsa su fiyeda sassanyar qamshin turaren jikinta na victor and rolf,"flowerbomb"  hade dana motar ta shima mai qamshin tonka da vanilla dayake gauraye da niimar sanyi mai mugun kwantar da hankli.

'Har suka bar wajen yakumbo bata dena daga musu hannu ba donji take kamar har abada bazasu sake haduwa da rifaidarta ba da kuka ta koma cikin gidan ta tana dan goge hawayenta da bakin zaninta,bata iya shiga cikin daki ba,zama tayi akan tabarman da suka bari a tsakar gida ta rafka wani uban tagumi dake tafe da damuwar kewar rufaida dazatayi.

Cikin wannan yanayi taji an diro mata cikin gidan babu sallama
Weee wee take kuka hannunta makale akan fuskarta ta rufe idanunta da bakin mayafinta tana jan sheshheka
,Wni wawan tsaki ykbmbo taja tana famar kare mata kallo da kamar ma bazata kulata ba ganin ta dabu a kasa kamar mahaukaciya yasata cewa waimeye aka miki da zakizo kina tsaga min kunne da ihu,Suhan ta dago jajayen idanunta da muryanta na kuka kamar zata fashe "
"Yaa malam ne ya koro ni yace wai kar na kara taka masa kofar gida..tun kan ta karasa yakumbo ta miqe tsaye cikin masifa tace "Toh madallanki,ai anan kika gama zagin yar uwanki da mummunan qaddara ya afka mata,akan namiji kikace bazaki taba yafe mata ba,itama da ta shiga mummunan hali na rai da mutuwa ubanku bai amsheta ba saike yar kanzagin asara?

Suhan tace wallhy laifin rufaidace badon itaba da baba bazai taba korata ba..ykmbo bakiga tsangamata da akeyi bane shiyasa kike kare rufaida..akanta rayuwa na ya lalace koni yanzu wazai aure ni aikowa ma cewa yake dangin shekakku masu kashe miji..kuma duk laifinta ne ai dataki biyewa umarnin baba
Yakumbo dakejin kamar ta hankadeta da qarfi cikin hatsala tace
"Ke Da Allah ki rufa min baki wawiya kawai mai tosheshiyar kwakwla,kowa yasan halin ubanku kasurmin malamin jahilai ne wanda baisan haqqin dake rataye a wuyar sa ba,da laifin rifaida da babu laifinta kema kinsan ba amsarki a gidanshi zaiyi ba,toh uban waye ma ya kawowa rifaida mijin dayaje zai kasheta y cinye namar ta inba mijin na ki ba?Kema aida laifinki suhane tunda kinsan yar uwanki batason auren amma haka  kikayi burus ki kasa gayawa mijinki.Toh wayasan ma sana'ar mijikin kenan dayake ta boyewa jama'a,sana'ar saida mutane da kai mata waje yin karuwanci yo inba haka ba ina mai hankali zaiyi abota da mugun mutum irin mijin daya auri rifaida?

Cewa fa akayi har naman mutane yanaci kema saiki binciki kanki suhane halama ana hada muku dashi acikin kayan jefane kuna dafawa kuna ci,ke ba abun murna bane  ma da Allah ya rabaki da shi?
Galala Suhan tayi da baki tana kallon yakumbo cikin tsananin mamaki da fiskar razana
"tace..naman mutum fa kikace yakumbo?yakmbo ya za'ay kihada mijina da sana'ar karuwanci,yakumbo tace iyii mana..ba haka muka ji ba? ai jamaiar tsaro bazasu mana karya ba..suhan ta fashe da wani sabon kuka
"Nikam na shiga uku na lalace,amma ai mu ba haka akace mana cewa fa akayi rufaida ta dabawa mijinta wuka aciki don kawai bata son sa.
Da gatse Yakumbo tace ehh sannan kuma mijinki ya arci na kare ya sakeku a walaknce baikara dawowa ba tsaban gaskiyar sa ba?,shin kin taba tambayar kanki meyasa mijinki yake wasan boye boye da hukuma,toh da walakin goro a miya..gwara ma ki nitsu kisan inda dare yay miki nikinga tafiyata cikin daka,da kallo suhan tabi yakumbo kirjinta na balain bugawa can anjima ta tashi itama tabi bayanta.

Bangaren rufaida kuwa bacci ta rinka shara musamman ma dataji ta acikin sanyi da qamshi.

Karfe 9:30 na safe Dot anty fareesa tayi horn agaban wani hadadden gida
Ginin zamani ne mai kyau modern scandanavian design komi na gidan Ash da light brown colour ga yelwataccen furanni masu dauke ofo da bishiyoyin umberalla da palm trees yn dagwal dagwal gwanin ban sha'awa..

Mai gadin su da ake cewa yaa liman da gudu yazo ya bude musu gate ta shigo ciki tayi parking motar ta a inuwa bata sauko ba harsanda ya kulle gate din gidan kirif,..barka da dawowa hajy, Anty fareesa tace yawwa malam liman please bayan likita na dazai shigo yanzu kada ka bari wani yashigo,duk wanda yaxo kace mai bana nan, strict oder.

Malam liman yace toh angama hjya..
Yana barin wajen ta bude kofar motar  ganin har yanzu rufaida bacci take kanyi yasata sauke ajiyan zuciyaa a daddafe ta tallabota jikinta tana dan shafa fuskarta ahnkli harta dan farka saidai kallo daya zaka mata kasan ba a cikin hayyacinta take sosai ba,cikin wannan yanayin ta sauko kasa anty fareesa ta tarbota ajikinta suka wuce can cikin gidan tare.

Bata ajeta a koina ba sai dakinta dake can saman bene banda kalle kalle babu abunda rufaida takeyi a cikin nitsuwa ta shimfideta akan wani makeken italian bed wanda yagaji da haduwa an kawata shi da kwalliyar jan zanin gado,zama tayi abakin gadon tana kallon fuskarta da yay fayau,,a hnkli ta furta mata kalman sannu..sai sannan hawayen ta suka kara gangarowa ta gyada ma antyn kai

Tausayi sosai take bata shiyasa batajin aranta yadace ta takurata tun aynzu tayi wani magana dan gani take kamar itama zata iya barkewa da kukan tausayi agaban yarinyar alhalin alkwari sukayi da mijinta nacewa bazasu bari rufaida taji aranta ita abar tausayi bace awajen su

Jiya cikin dare suka yanke wannan hukuncin tsakanin su su uku itada mijinta da hajya mama,acewar hjy mama tunda ance musu yaa malam baya gari kawai fareesatu taje ta dauko mata rufaida ta riketa wajen ta nadan wani lokaci kafin suje abuja da yaa sheik su dawo,Alkwari sukayi dacewar babu wanda zaiji hakan atsakanin su harsai an sasanta komi.

Mijin anty fareesa ne ya kara karfafa ma hjy mama gwiwa akan haka,aganin sa Anata jan lokacine wajen neman sulhu kar kuma azo ayi dan dana sanin hukuncin da aka yanke akan ita yarinyar dan har yau babu wanda zaice ya san asalin metake ji a zuciyarta na damuwa.

Anty fareesa Tana zaune awajen tana ta tunanin yadda zasu taimakawa rufaida har likitan ta yazo,sunan shi doctor kabeer mathur Speacial  physchologist ne dayayi karatunsa a kasar india ya balain kwarewa a fannin harkan psychology da social human neuro therapy,he can deal with trauma and stress at all levels akanyi aiki dashi har a asibitan dabbobi dana mahaukata infact he do work for security agency for intelligence jamian tsaro sukan daukesa in ana neman wani taimko akan gane yanayin mutum musammn inshi murdadde ne ko physcopth ko narcisst,nan da nan ya hau duba yanayin rufaida ya mata wasu allurai masu zafi wanda atake atake suka kashe mata jiki tahau wani sabon bacci nan ma ya ja jininta a syringe ya musu sallama dacewa sai can dare zai kara dawowa ya dubata.

Around 2pm rufaida ta farka,Zama tai ta dukunkume kanta cikin cinyoyinta kafafunta na rawa rawa ga wani irin zufa dake keto mata ta koina sabida azaban ciwon cikin dake murdata, tun tana zaune har saida takai kwance awajen tana juye juye,tsahon lokacin data dauka ahaka yasa ta jin kamar anyashe mata hanjin cikinta ne,tuni ta soma harsahen hala ba ciwon bane kadai harda yunwa dan rabonta da abincin kirki tun jiya da daddare,tashi tayi zaune a hankli tana waige waige ganin babu motsin kowa,gashi bata son shhiru yayi yawa ba waje yakan tuna mata wasu mugayen abubuwan data riga ta binne akasar zuciyarta

A hnkli ta koma ta kwanta ta rufe idanunta gam gam zuciyarta ta na kkrin karanto Addua, cikin ikon Allah kuwa saiga wani baccin mai mugun dadi ya kwasheta da alaman hakan nada nasaba ne da wahalar datake sha na rashin samun cikakken nitsuwa ta zuciya..

Fannin Ainau kuwa basa ko ga maciji da mufrad dan har wani tsanar sa matakeji aranta iyanzu,ganin tun ranar baibi takanta ba yake kara hatsala ta

Sosai idanunta suka rufe wajen son ta aje duk wani digon son sa dayake mata dabaibay aranta danta hukunta shi.

Duk dramar da akeyi agidan baiya kulawa,yauma daya kammala aikin dayakeyi ya sauko yaci abinci,bai wani ci dayawa ba ya tashi ya shiga toilet don dayake kasa yay alwala ya wuce masallacin farfajiyan gida,anan yakai har 4:30pm yana tashi awajen ya dawo gidan ya haura sama yacigaba da ayyukan shi bai neme kuwa sai kuma sallah dayake tadashi,haka yake rayuwar shi har dare after 12pm normally yake shutting eyes dinsa ya kwanta bacci,washe gari 6 zaka nemesa ka rasa agidan sai kuma inya dawo..

Ba Ainau ba hatta imad bai wani gane kansa kwana biyu nan ba,ga fitinar zarah data mugun makalake masa a wuya aynzu sam sam bata barinshi ya shaki iska a kullum tana nanike dashi kamar wata jela.

Fannin malak kuwa tunda mahaifyarta ta nuna rashin gamsuwarta da zuwa kano sai jikinta yay sanyi ta soma cire abun aranta kawai..
Yawan waya da sukeyi da imad ma tuni ta dan tsagaita duk dama haryau ta kasa iya furta masa asalin dalilinta.

Hjya mama dake shirin biyo yaa sheik Abuja wanna karon wani zazzafar zazzabi ne ya hanata,karshen ta shikadai din ya taho yazo ya tarar da gidan babu dadi dan sosai sukayi fushi dashi kusan kwana yay yana lallamin su
Yana musu bayani
Ahakan ba sonda suke masa ne kawai yasaka suka dan sassauto sukayi hakuri amma bawai har ransu suka yafe mashi ba...

Tun zuwarsa suke kayyado masa nasu dokokin daya saba na hjy mamah
,wanda akalla yasan bazai taba yuiwa ya dauki nasu ba sabida uwarsa ta wuce abun wasa.

Kawai amsa musu yakeyi,amma agefe tuni ya umarce matar sa akan ta soma nazarce nazarce da shirye shiryen dawowa da yaransu gaban sun kawai....

Haka suke ta abubuwan su a boye batare da sannin kowa a gidan ba,imad gaba daya ya daukewa yaa sheik hnkli kusan duk fitarsu tare sukeyi akan maganan kawa kan aikin sa.

Bayan kwana biyu.

Kamar kiftawar ido da bismilla Rayuwa ya fara sauyawa rufaida,kulawa na musamman ake bata ta kowani bangare,doc shima yana balain taimakwa wajen engaging dinta da deep converstion session irinasu na depressant professionals ahankli yanayi yana jin ra'ayoyinta tana kuma fitar da abubuwa da yawa wanda suke toshe mata tunani da jin dadi,ga wasu allurai da ake mata ajijiya suna da mugun zafi kam amma cikin kankanin lokaci ta somaji kamar kwacota kwaklta akeyi daga halin data shiga na tsananin damuwa,  sosai ta soma fahimtar kanta ta soma jin sauki sosai a zuciyarta sabida samin nitsaten bacci da kwanciyar hankli,no one to scold or hurt her babu kadaici ko lokacin tunani yaran anty reesa ma kadai basa barinta da kalar suruntun su thy are alwys in her company,safe rana dare suna sakata dariya da magana dan dole,kuma sama docton cewa yay abashi sati guda da ita zai iya bakin kkrinsa wajen rage mata tunnani da damuwa sauran kuma su dasu dora daga nan...

Dan haka Anty reesa da mijinta suka hau shirya abubuwan da zasu na dorata akai
kamar kara rike addini ,karatu,girki Kallo da wasa da yara da duk wni abunda zai sauya mata yanayin ta zuwa normal mutum kamar kowa.

Burin su baifi suga rufaida ta dawo cikin hayyacin ta akan lokaci ba.
They all belive she have a better future ahead of her dan sosai hjy mama take so tacika mata burinta nayin zurfin karatu,haryau kokadan bata karaya da rayuwar rufaida ba

Ataikace dai zaman rufaida agidan anty fareesa kusan wani babban cigaba ne a rayuwarta,anan ne ta samu sukuni har take iya kawo tunanin wayanda suka soma taka muhimmiyar rawa a rayuwarta musamman lokacin datake matukar bukatr taimako
Hakan ya jefata cikin tuno da fuskar imad,koma ina yake oho?but wani abu can kasar xuciyrta yana gaya mata cewa a duk inda yke he wll remain special to her and she owe him alot,tabbas nan gaba zataso ta kara ganin shi da idanunta koba dan komi ba gayen yana daya daga cikin mutanen da har abada bazata taba iya mancewa dasu a duniyarta ba.

Thursday morning.
Karfe 10:30 aka danna door bell mai aiki ta taho ta bude kofar,imad ne ya shigo sanye  da wata half jumfa yadin yoloyolo white colour data mugun amshar dirin jikinshi hannunshi dake kyallei yasha agongon dave martins dayan hannun sa sakaye da awarwaron maza germ d'ela parisà masu mugun kyau bakake kirin,turaren shi na guilty absolute sai binshi take da sanyin qamshi cikin salon takunshi mai tafe da aji da nitsuwa ya nemi waje ya zauna acikin kayattacen falon inda baiyi wani minti biyar bama saiga shi ya sauko Mikewa tsaye yay baima barsa ya karaso ba yace good mrgning pa doctor,..
doc mehra dayake kan kallonshi tundaga can nesa ya saki wata mischievious smile
Batare da ya sake fuskan sa sosai ba,Har gaban imad din ya karaso ya aje wani file akan table fuskn sa adan daure gyara tsayuwar sa yy tukun kafin yace
"Imad What is d meaning of this,wai na fara wasa dakai ne?Wani Shiru imad yy dan baisan me zai soma cewa He neva wanted it like this,duk shirun malak ce ya tunxirasa.

Doc yce Dakai nake magana are u daft?
Numfashin sa yaja har can sama snn ya dago idanunsa da sukayi mici mici
Kasar wuyar sa yace.."Doc please im sorry..nasan nayi maka shishhigi but just wanted to be der for malak as my litle sis fa shikenan,

Doc yace karka karayimin haka cos i dint ask u  to take any additonal responsibility,infact inkayi wasa dani harkaima bazaka je kanon ba,da har yy shiru sai kuma ya dago kansa da alamun Zaiyi wata magana,cikin dakatrwa doc yace
"A'a Ban yarda da tsarin kan nan ba
Kuma aydda ka fara komi kai kadai haka zaka warware shi.

Masifa yahau masa "Ni nataba ce maka kayi wa malak registration?infact who d hell admited her in dat university batare da taje tayi screening ba?u havent even thoug of it..itama ai zata gamo da ni..im sure she is aware, u two are acomplices.

Ahnkli Imad yace
"No she is not..
Doc please..ya fada a marairace sosai.
Doc mehra ya kureshi da idanu, iska ya furxar ta bakinshi yadan shafe gashin kansa yace.."Okay i w tell u d actual truth,well is true nina fara kawowa malak tayin zuwa kano yin karatu but aganina hakan zaifi mata sauki tinda canma gida ne,and All of a sudden sai naga ta sauya ra'ayin ta wai tafasa zuwa karatun wai zatayi anan din kawai and i know malak,she neva wanted to give up on her dreams, saidafa na takurata sosai sannan nagane cewa ashe ma kune dai baku bata support ba...nd i wonder why wll you do that to her?soo unfair..
Shine Kawai dana samu oppurtunity jiya saina nema mata makarntar kawai..and

..da sauri doc yace and da permission din waye?

Nan ma shafa kansa yay ahnkli yace,babu, am sorry sir..kallonsa doc mehra yy har cikin kwayar ido,..taje ya susutar da fuska yahau bayani
"Doc malak is like my blood sister,i just wanted to fulfil her dreams inna mutu wata rana ai bazatace banmata kkari akan abunda take so ba ko,toni meyasa zaace banda iko akanta uve been more than evrything to me,a father a friend a mentor,my evrything ,i also wanna know how intense it feels to love and care for sumone dat ure not bloodly related to,dan Allah kabani damar kulawa da rayuwar malak kamar na yar kanwata da bani dashi,.Hararshi doc mehra yay cikin jan shaukin da yay maganan dashi wanda babu alamar wasa aciki sai tulin shagwaba,a hnkli yace toh ban amince ba,..imad yy shiru.Shima shirun yay sai can yace ka nemi waje kazauna toh sai nayi tunani na yanke shawara
Bai masa musu ba ya nemi waje ya zauna yana binsa da ido harya haura sama yakoma dagata ciki,jim kadan saigashi ya dawo da Anty meera da malak din dukan su atare.

Ita batama sanda cewa malak ta yanke hukuncin hakura da karatun ta a kano sabida ita ba,koda doc mehra yay mata bayani sosai taji dadi aranta kuma tasha mamkin da ya gaya mata cewa imad ya dauke musu nauyin komi da komi na karatun malak daga nan har karewarta unirvsaty duk na rubuce acikin file din.

Haka suka sauko suka kara sakosu gaba suna titsiye su da tambayoyi,anan ma malak ta kara tabbatar musu da cewa itamai hanklice,jin tace ra'ayi da farincikin iyayen ta na gaba mata da komii

Murmushi doc ya yi,
Wato yar tana son Babanta irin sosai-sosai ko?Murmushi tayi Kafin tace.Yes, Daddy sosai-sosai take matukar son dadynta yace toh shikenan tell me 10 good reasons why u want to study dat course "information tech,Yadda suke maganar tactically with nodding head sai da suka baiwa su imad dariya sosai karshe haka suka kyaleta Doc ya barsu a nan ya wuce upstairs yana dariya shima yana cewa kansa "i just cnt belive this dan shikansa baitaba tsammanin yarsa tana da nitsuwa har hakaba..

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top