chaptr 13

BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 13
Formalities...

Bangaren rufaida kuwa tunda suka jefata cikin akwatin gawan Nan jikinta ya kara sukurkucewa da tsananin zazzabi ko inanta yabi ya nakasa ya mutu bata kara iyayin Wani musulmin motsi ba, tamkar a muce haka take Jin kanta,Sauran numfashin ta dake kara diff difff a can can cikin kasar mgwaronta shine shaida gwara daya da zai nuna cewa ma tana raye

Ta dade ahakan kwarai dagske ga kishin ruwa ga yunwa Dan kuwa zata iyafin 3hrs acikin wannan yanayi sai can tukuna suka fara lekota time to time  haka akan zo a watsa mata ruwa a fuskarta inta samu ta hadiya ohon mata,sukam ma Suna hakanne sabida Kar balain warin naman kan Fatima daya babbaju akasa ya kasheta

Bayan hakan Tunda Alaji BATURE ya barsu da Ita awajen basu Wani kulata ba
Ita kuwa rufaida Duk da kasancewar halin datake ciki bai taba hana xuciyarta ambaton Allah da neman mafita agareshi ba.
Bayan kamar awa daya haka suka zo suka dauketa Duk da akwatin gawar suka kaita Wani da aka feffetsa Wani irin magani mai bugar da kwkwala suka ajeta daganan ma ta dauke bata kara gane Inda take ba.

*Kano state Nigeria*
Same day @9:45am

Da sallama sukayi Shigowar su shashen yay sheik Wajen zama ya samar musu ya miqe da sauri kamar zai fice hjy G ta tsaresa Ina zakaje kuma zaidu kaima tafiya zakayi?juyowa yy ya kalleta Dan baiyi niyyar fada mata ba yace zan kira mama ne Hala tana can sama batasan har Kun iso ba,tabe bakinta tayi batace mai uffan ba
Yy excusing dinsu ya fice sashen mahaifyarsan ya nufa Kai tsaye.

Fitarsa ke da wuya hjy adada ta kalli tsohuwar data tsime da alaman Wani abu aranta na ciccinta Tace mama meyafaru?Dan shiru tayi can ta kalle ta Murya kasa kasa tace nifa bangane komi ba,dube mu sai kace wasu bare ace babu wanda zai taho tarban mu sai zaidu?wato wajen sa muka zo shikadai kenan ko?tun jiya nake dokin zuwa inga yayan zaidu da sauran ahalin gidn nan Amma hmmmm...Wani dogon numfashi hjy adada taja tace hmm nifa bana cire ran hasiya ce ta rirrikesu kinsanta da iya tsara ma mutane rayuwarsu
Da shegen son baza mulki uwa wata yar sarki,ni tuntuni banga ma amfanin zamanta agidan zaidu ba kawai zaman saka Ido da takurawa yara,wani
Kuka Hajiya goggo ta fashe dashi kai kace an kunnata waysan ma ta riga ta rabano da yayan zaidu?koma ce musu tayi niba jinin su bane?to ai NI Nan nayi sanadiyar zuwan ubansu duniya tunda Dana dikko shiya haife uban Dan nata.
Weeeeeee weeee fet fet ta cigaba da kuka tana fyace hanci,hjya Adda ta cigaba da kallonta Dan Inda sabo ta riga ta saba da rikicewar hjya G,
"Mama meye haka so kike azo araina mu?ai tunda munzo gidan nan kowa saiya gane cewa mune da iko da zaidu ba kowa ba
Hatta uwar zaidun saita koma matsayinta

Assalamu alaikum
Wasu yan dattijiwar Sallama ne ya dakatar dasu daga bakin kofa Jin haka yasa hjy G saurin share hawayenta tana kimtsawa

Wa'alaikissalam
Shigo daga ciki hjya Adada ta Furta,Duk dama bata kalle wajen ba amma u can tell dat so take taga suwaye suka zo

Bude kofar akayi a hnkli saiga hjya jasmine wanda ta shigo tare da wata kyakkwar mace a gefenta Tasha Wani hadadden super wax blue da mayafinta babba wanda yayi matukar karamata kima da kwarjini,daga ganin ta kasan a kusan sa'ar hjy adadan take, wanda kamanin su da hjy jasmine din kawai ya isa ya sanar dakai cewa mahaifiyarta ce hjy saddiqa fulani

Murmushi ne akan fuskarta harta karaso cikin falon  banda kallon kurilla Babu abunda suke mata kasa da sama da alama yanayin ta ne yadan burgesu,cikin tsananin girmamawa hjya jasmine ta wuce gaban hjy G da hjy adada ta rusuna ta shiga gaishesu,tana tambayar lpyarsu
Sannan hjya saddiqan ta amshe gaisuwar itama ta rusuna tagaida hajya goggo sannan ta miqe zaune ta gaida Hajiya Adada cikin fara'a dakanta ta sbar dasu cewa itace mahaifiyar hiya jasmine
Jiya ta gaya mata cewa Suna hanya shine tace bari tazo dakanta tayi musu barka da isowa
Sosai hakan yay ma hjya goggo dadi aranta,sai albarka take saka ma hjy saddiqa fulani tana dada gode ma karamcinta tamkar basu suke kushe kowa daxun ba..

Dan hira suka farayi tsakanin su Jin yadda hjy goggo take korafin rashin halartowan sauran mutanen gidan yasa
Hjya jasmine tayi xcusing dinsu ta fice,ficewarta keda wuya saiga Wani sallamar,yaa sheik ne ya shigo tare da yayan sa abayansa anty fareesa Keeyan da nazli da shukra dake ya bar mufrad can tare da hjya mama akan shi zai taho tare da ita

Duka suka rusuna kasa suka zauna akan carpet kusa da Inda mahaifinsu ya zauna suka gaggaishe da kowa a falon cikin girmamawa saidai basu iya sake jikinsu ba tsaban yadda akebin kowannen su da kallo,musamman ma hjy adada dake zaman gidan sarauta ya gama shiga jinin jikinta yasa take son abu mai kyau da kima da daraja,ita tun daga yanayin dressing da kyaun fuskar mutum take mutunta shi,sosai taga kamannin jinin ta ajikinsu duba da yadda suka haske wajen da kyaun su masha Allah abun alfaharine wajenta sosai,already aranta tun bayauba take matukar kaunar yaran zaidu harcikin zuciyarta,sukuwa bayan sallama da gaisuwar da sukayi basu kara cewa kowa uffan ba dukansu kansu na kallon qasa kowa da abunda yake saqawa aransa,cikin nitsuwa ya sheik ya zauna kasa daf sannan ya kalle hjya G yace grand ma gasu Nan sunzo su gaisheki"..ya nuna Anty fareesa yace ga fareesa ga keeyan da shukra da nazli..sanda ta kare musu kallo kallon kurilla sannan ta dauke kanta tayi Kamar batama gansu ba tana gyara zaman gilashi a idanunta da muryanta na tsufa tace suwa kenan?suwaye wayannan haka zaidu,ya nagansu Duk wasu kauyawa, Duk a kwanjame ashe ma duk nafisu kyau,"dariya aka fashe da shi..a hnkli shukra ta dago Kai ta dalla mata kallo.
,keeyan dake Allah yay shi da neman magana Shiya fara yin gyaran murya aransa yace kajimin tsohuwa dawa take?nazli bata ko iya dago kanta ba dake tana mugun shakkar mahaifintan bata cika sakewa agaban sa ba,hjy Adada dake famar Murmushi ta amshe maganan cikin dariyar tace wai da kufa takeyi Wai bata sanku ba Hjya saddiqa ta amsa tace ahhto wannan ai lefinsu ne sunki zuwa matsugunin mahaifinsu ya za'ayi agane su?dariya suka karayi atare da hjy adada daga Gani kasan jininsu ne ya Dan hadu,mamaki hjy goggo tabawa kowa awajen data Wani mugun hade fuskarta ,Anty fareesa ne ta dago ta kalleta daita sauke kanta kasa,dake tana da saurin fahimtar yanayin mutum already tasan tsohuwar is just trying to act emotional with dem maybe tana son tadanyi borin rashin zuwansu wajentan ne da sukayi na shekaru da shekaru har ya kasance bata San girman su ba sai a hoto,Nan sai ta karaso daf gaban ta cikin sanyin yanayi ta dafa gwiwonta cikin salon data san dole zai sanyayata tace
our lovely grand ma din Abbun mu,pls a agafarce mu munyi laifi kuma bamu San ta Inda zamu fara baki hakuri ba.
Da sauri Keeyan ya rikito gabanta fuskar sa a dan shagwabe yace
Amma ai tunda kinzo mana ai shikenan ko?
Harara ta watsa masa shima ya rama,Daga can zaunen shukra ahnkli ta murguda baki tace"Ya kamata kiyafe..
Wani shirune ya Dan gifta kafin nazli ta karaso daf da Ita itama tace Ai kinsan karatu mukeyi bama samun lokaci daga mungama ai har can zamu biki,shukra tace toh yanzu kuma minene  kika zubamana Ido kinata kallan mu?
Tsaki hjy G taja
To aiko a yarinyar taku baku fini kyauba yoke meye ma ajikinki da zan kalla sai dama dama rashin tsayi da kika kwaso daga wajen kakarku gatanan adada nikam dai nafi karfinku ga zaidu Nan tambayesa yay nake da can?...
Miqewa yaa sheik  yyi da sauri ya fice y barsu tare dan shi bai cika son shirme ba

...da sauri shukura ta miqe tsaye kamar dama jiran hakan takeyi, komawa tayi can kusa da Anty adadan ta xauna daf da Ita cos for the first time aranta taga isashiyar kasaitaciyar macen da ta gama burgeta Ga aji ga class ga Wani sasaanyar sigar mulkin dake ratsa yanayinta
wacce har yanzu murmushin farincikin ganin sun kawai takeyi,tunda daga convesartion dinsu hjy dada ta fahimce cewa da alama hjya goggo ne zata amshe mata matsayin ta na kakarsun altho dama ita tasan ba iyawa datayi ba saboda wannan jinin sarautar dayake ratsa jinninta kasancewar tayi kusan dukan rayuwarta ne a matsayin matar dan sarki kuma sarki.

So she rather act like a mother to them rather Dan being a grand ma,tunda ma ga kakan mahaifinsu ai saisu karata tacan
Kan shukra daya jingino da jikinta ta shafo ahnkli cikin tsananin kulawa da so Tace wannan bakin jaraba na karatu Hala shiya lallata ku,"hjya goggo ta dubi anty faressa tace tashi kinji?adada wannan yaa mai yar uban hankli batayi kama da dikko ba kuwa?tashi abunki kekam na yafe miki .Anty fareesa tana dariya ta miqe ta zauna kussa da Ita..
Ta kalli keeyan wanda ya gwalo mata Ido cikin neman tsokanarsa tace Ja'iri wannan rama da baki da kayi nake gani wannan jaraba ta karatu har Ina haka zaidu zai kashe yayansa karfi da yaji yara Duk sun lalace.
Keeyan ya tsareta da harara to ke baxaki bar mutane suyi magana ba saidai aganki agidan mutane kin fado da fushi cewa mukayi bazamu zo ba?saida ta janye tukuna ta juyo da kyau ta dubesa tace Kai dawisu toh ka bari nazo gidan ka babu izini saika koreni Nan kam gidan jikana nazo babu wanda zan jira ya ban izinin zuwa kina jina ko?
Dariya suka fashe da shi nazli tace Duk meyayi zafi haka?aiko namune ma haka zakizo batare da izinin kowa ba,..

Shkura dake ta samu waje gun hjy adada cikin shagwaba tace barta da son yima mutane sharri nide ban lalace nayi baqi ba,Inkika kara cewa hakan to ko kinkoma gidanki ni bazan biyosu inzo ba Fuskan kuka ta saka tana kallon ta baki bude,Hjya saddika dake ta famar Murmushin Jin fadarsun na shirmen tace shukra tashi ki dubamin mamanki kice mata ta zo please
Ba bata lokci Shukra tace ok sai ta tashi,tsohuwa tabita da harara
"Inkin tafi karki Kara dawowa da fuskarki kamar na uwarki
Babu komi sai hanci da Dan gashi da kka kwaso nawa Duk anbi an bata ku da shirme,shukra ta turo baki batace uffan ba ta fice tana kukkuni

Nan hjy saddika Ta juya ta kalle su tace Hajiya goggo nikan inaga zan wuce sai in nakara zuwa..

Babu yadda basuyi ya zauna ba amma haka taki musu firr dama burinta baifi tazo danta kara neman ma yarta jasmine wajen zama a zukatan wayannan matan ba
Koma yayane tasan ayanzu kam sune suke da cikakken iko akan yaa sheik ba mahaifyarsa hjy mama ba,hjy saddika tana mikewa hjy Adada ta tashi tace toh bari indan taka miki
Bakin kofa Allah ya saka da alheri hajy fulani mungode Allah yabar zumunci
Hjy saddika tace aimune da godiya zumunci masha Allahu Allah ya karfafa wannan zuria taku mai albarka tabbas Kun cancani yabo da jinjina hjya goggo Allah ya kara tsawon rai kowa ya amsa da Ameen
Inda Hakan yay daidai da shigowar Hajiya mama.

sanye take da farar hijabi doggo har kasa wanda yasa fuskanta yay haske sosai, mufrad ne agefen ta sai Aina'u dake biyosa abaya baya Ta Wani sha blue shadda riga da zani ta cakka daurinta cakwai tayi dashi duka baya ga atachment cap dinan sun babbazo abayanta babu wani mayafi sai fuskarta da yaci ubansa da kwalliya faudan Nan ta Mary kay ya fito badau yana sheqi uwa wacce zataje gidan biki,

Direct hjya mama
Ta wuce gaban surkuwanta ta rusuna ta shiga gaishe ta cikin girmamawa da dattako,ababu yadda ta iya ta amsa da fara'a da raha sannan ta juyo suka gaisa da kowa

A lokcin ma Duk hanklin su nakan mufrad da Matarsa,shi baida Wani sake fuska Danko sallamar ma baiyi musu ba yana shiru,Aina'u dake Dan Jin shakkar su saita tsaya kikam abayan sa bata gaishe su ba Hakan bakaramin haushi ya bawa hjya goggo ba,Wani kallon kasa da sama hjya Adada ta watsa mata tuni ta sha jinin jikinta ta bar gefenshi da sauri ta wuce sum sum ta Dan rusuna agefe tace "Sannunku da zuwa Hajiya fatan anzo lpya?..Kai kawai ta daga ta dago girarta sama muryanta can ciki,a mugun dakile tace Lpya Alhamdullahi..ta dauke kanta ta kalli hjya mama direct tace hasiya wannan kuma fa?Tayi maganan kamar batama San waye Aina'un ba,atleast ai Duk Suna kallon su a hoto sunsan da zaman kowa,..hjy mama tace matar mufrad ne,Ainau ai itace surkuwan gidan,kallon Tara saura tamawa Aina'un "uhmm kawai tace bata kara tankawa ba ta miqe tabi bayan hjy saddika suka fice daga falon hjy jasmine na tare dasu"sunkuyar da Kai Aina'u tayi kirjinta kamar zai fito waje ganin wayannan mutanen kamar basaran yinta bane...daga can Hjy goggo ta dago Kai ta kalle mufrad daga Inda yake tsaye ganin Inda yayi matikar kyau gaba daya ya kwashe kamannin danta da jikarta Kai harma da kowa yafi kowa kyau a falon,shi dai ba Wani kwalliya yay ba farar kandura yasaka mai Dan sharara da skull cap mai mugun kyau,sai turaren sa na royal oudi dayacika musu numfashin shi,Jin ance Wai Aina'u ce Matarsa yasa taja tsakinta afili gani tayi Kamar basu ma dace da juna ba kwata kwata...

Ganin bai sake fuskar sa ba yasa keeyan da nazli suka zame suka bar wajen,Anty faressa ma ta miqe da cewar zata taya masu aiki shirya wajen cin abinci

Hjya mama ne zanne agefen hjya goggo Suna Dan hirar su ta yaushe rabo,bakace akwai Wani abu na sabanin fahimta a tsakanin su ba
Dan hjya goggo ta dade da sawa aranta cewa hjy mama ita taso ta rabata da danta dikko data jawosa daga katsina suka zauna a kano suka barta acan,tun tale tale take riqe da wannan abun aranta haryau bata fasa ba..

Suna cikin yar hirar tasu ya karaso har wajensu cikin kasaitar sa mai tattare da nitsuwa da burgewa,babu Wani shirme ko yarinta ayanayinsa ya zauna tare da nade qafafunsa aksaitance ya shiga gaishe da tsohowar cikin girmamawa da kulawa,dakansa ya bayyana mata kansa a matsayin sa na babban da namiji agidan yana babbata hqri akan rashin ziyarar da basaayi...Duk mitar hjy goggon Nan haka tayi shiru tabisa a yadda yake
Ko wasan jikan ma basuyi ba...
Tunda tasab shi soja ne sai bata Wani damu da murdadden yanayin sa ba banda ma girmama shi dataji tanayi azuciyarta

Hira suka cigaba dayi yana saka musu baki jefa jefa banda Aina'u data kasance bare a tsakiyarsu can ta xame jikinta tayi waje

Da misalin karfe sha daya daidai keeyan da nazli suka taho suka kirawo su cin abinci ita kuma shukura sosai ta manne wa anty adada,11:30 d table was set kowa ya zauna da plate agaban sa hajya mama dake tafi kowa sanin yanayin yadda diet din hjya goggo yake Dan haka ita dakanta ta tashi tayi serving dinta,hjya jasmine saita karbeta ta cigaba da zubawa kowa,still sai kallon kallon suke jefa ma juna,musamman ma akan wannan matar mufrad din datake basu mamaki,hjjya goggo da harta ce bazata ma kulata ba,Amma Allah Allah take su kebe ta tambaye mufras Inda ya samo wannan bakauyiyar mace wacce bata San ciwon kanta ba
Ace kina surkuwan gida kya bar uwar mijinki da serving din abinci,aranta ta tabe baki tace "waiko makauniya ce da bata ga yadda hasiya ta girmama ni ba?yaran zamani hmmm,har aka fara cin abincin ana yar hira Amma bashi ya hana su saka Ido akan Aina'u ba,da alama in mutum ba jinin su bane to tabbas saisun ga damanshi,tsaban yadda suke babbasar da ainau kota sako baki acikin hirar da sukeyi da yaran gidan basa cika amsa ta,harta gaji ta sha jinin jikinta tayi shiru daga bisani ta zame ta bar musu wajen tace musu Wai zataje amsa waya,Aikuwa tana tafiya hjya goggo ta soma barbade tana masifa Tace waye zai tattara Nan wajen da zata tashi ta tafi anakan cin abinci Ta Inda take shiga bata Nan take fita ba da kyar yaa sheik da keeyan suka shawo kanta "keeyan ya Dan kakkare Ainaun yace Hala daga wajen aikinta aka matsa mata shikam mufrad cin abincin sa kawai yakeyi bai ce musu kala ba,har dai aka dai kammala aka tashi
Karankaf din su suka nufi sashen ya sheik including mufrad Dan baison ya hadu da Aina'u yasan definatly she will complain Abt yadda sukayu treating dinta and he just don't have time for that aganin sa ai maganinta dayake ta riga ta gwada masa bason zaman gidan take ba aikin office dinta ya zarce haduwarta da familynsa tsaki yaketa ja aransa ya bata shiru ajikinsu time to time haka yana Jin shirmen su har mamaki yake yadda su kannen sa suka Wani sake da su onetime kamar da can sunzauna da juna,Wani irin surutun balai sukeyi anata dariya ana nishadi,dama
Dama ma anty faresaa yasan wannan halinta ne
But he is actually suprise of the quick bonding,tsaraba kala kala aka bude ga kyautuuka kowa saida aka kawo masa abunda inyagani zaiji dadi.

U can tell thy feel so happy,musamman shukra dataga harkan girma da arxiki ba irin nasu ba,she is sooo proud to be their own spec,badan zaman mufrad anan ba da babu kalar barbaden labarin da bazata basu ba.

Anty fareesa ta shiga shirya musu dakin dakma sunce anan sashen YAA sheik din zasu zauna kafin atafi can abuja sabon gida,so spare room dinsa aka dada kimtsawa nazli dake da danbanzan kyuwa ahaka dai ta daure ta tayata jera kayansu suka shirya musu ko ina tsaf..

Kafin su fito falo suka samu yaa sheik ya fice shida keeyan,mufrad ne zaune kusa da hjy goggon da Dan sister sa jawad a hannunshi yana masa wasa...sai kallon sa take dan
Sosai take so ta masa gulman Matarsa Ainau saidai har yanzu bataga fuska ba hakan yasa tayi shiru tana jira ko gobe in yashigo gaisheta da safe tabbas itakam zata gaya masa Sam basu dace ba...

Bangaren Aina'u kuwa tunda ta shiga dakin tayi zamne durus agaban mirror,tsaki take ta saukewa uwa dattijiwar tsaka itakai tana kumbura fuska uwa kububuwa tana famar kadakai  kamar kadangaren gobara,Wani huci takeyi itakadanta kamar xakanya data fito farauta da alamar ta razana ganin sun hjya goggo Kai musamman hjy adada datake mugun daukar kanta kamar wata sarauniya

Ji tayi komi na gidan ya fita mata akai duba da yadda suka Wani basar da Ita tamkar wata shara,altho ba laifin su bane aranta tasan ko itace take da irin kudi kyau da ikon su wallahy da zaitayi abunda yfi haka ma mutane

Gaba daya ma haushi suke bata
Da girman kantan Allah yasani bazata iya jumre halayen su ba,Dan arayuwa bata taba yarda Wani Dan adam ya taka taba sai muffy shidin ma dan son shi ya mata yawa ne,sauke idanunta kasa tayi cikin damuwar yadda zata fara dasu,gashi tana tsananin son zama cikin familyn su,she knew she have to do sumtin to earn her respect batare datayi dogon tunani ba kawai ta dau jakarta da mayafinta ta sulale agidan taja motarta ta wuce office yin abunda ya dameta..

Isar ta office keda wuya saiga kanwarta Zara ta iso,bude kofar tayi babu ko sallama taci uban material da zararan kitson chiko akanta ta kafa daurin ture kaga tsiya her lips was illuminating evrywhere da zumbuton Sa tsaban Jan janbakin da aka lafta mai tana shigowa ta ja tayi kak ta tsaya tana bin Aina'un da Wani irin kallon raini
Kallo daya Aina'u ta mata ta kau dakanta dake she is not in d mood also,gaba daya hanklinta bai jikinta Dan tun zuwarta kwakwalta yakasa samun nitsuwa da yadda zatayi zama dasu hajya adada
Da can yaya taKare da jarabar hjya mama gashi an Karo mata wasu?Allah Allah take muffy yazo kawai tayanke hukunci zatace mai su koma gidansa kawai cos she just can't live with too much family members around gaskiya

raya Hakan datayi yasa ta Dan sake fuskarta wa zarah cos tasan she will be needing zara's help akan mufrad batun komawar gidan nan.
Bata son yace mata no so she won't mind ta kara bada kudi dan akawo mata Wani maganin buzuwa da zai mata amfani.

Kai ta dago ta daga girarta sama tana kallon Zarahn
Yanzu kuma meye kika shigo min office kamar wata mahaukaciya

Zarah ta watsa mata harara mai zafi idanunta Nan kamar zasu fado
"Sis kina ban mamaki"..
Banzata ayadda nake buga kaina akanki haka zaki watsar da lamarina ba,meye bana miki akan damuwarki?
Wani taimako ne bana miki akan mijinki mufrad...
Wato kin maida nu sakarai,asha mangwaro a yarda kwallon ko?Da sauri ayn ta mike tsaye cikin tsananin mamkin Jin kalaman nata muryanta harna karyewa tace
Hey hey hey stop here,its enough,zarah
Wannan Wani irin magana kikeyi haka?What is it?
Meyakawo wayannan baqaqen maganan?

Cike da tsiwa da harara Zara tace aikin sani
Pls don't even pretend,tayi rau da idanunta ta dauke kanta gefe
Kasa kasa ta  furta...mtsw na tsani munafurci wallhy.

Ran Ayn take saiya soma baci danta tsani raini matuka tace nasan me?
Me nasani ?or are here to disrespect me Dan kawai Kinga Ina wasa dake?
Cikin yanayin rainin Zarah tace
"To karkiyi mana ni baqin cikinki ne yake damuna
Aina'u u knew dat IMAD kanin surkuwan kin nan zai dawo nigeria in 2 days time and you Neva care to tell me sai awani wajen nakeji!Ayn dakeji kamar kanta zai kuNce ta nade hannayenta cikin dakewa tace
And So what in IMAD zai dawo?
Ina ruwana da Hakan,"cikin tsawa xara ta dakatar da ita Ohhh haka zakice?kituna alkwari kikamin zaki jona ni da shi inhar ya dawo nigeria  don't just tell me U've forgeten about that..Kamar zatayi kika ta Furta haKan alaman bacin ran ya shigeta sosai

Ganin Hakan yasa ainau ta Dan saussauto ta dauke kanta slowly dan itakam ma ta manta da cewa sunyi hakan..a hankli "tace NO now,I haven't. Amma ai kyamin magana a nitse yadda zan fahimta u were just shouting and insulting me

Zarah Tace ai dole tunda dai baki damu da damuwata kamar yadda ni nake damuwa akanki ba

Kinsan fa auren Nan nima nake so,and I choose to be in ur husband family kodai baqin ciki zakiyi min bakiso in mannu daku nima rayuwata tayi kyau irintaki

Lumshe Ido Ain tayi tanajin yadda zuciyanta yake mata zafi,bata ma iya amsa ta saida ta samu waje ta zauna
Ta dafe kanta
"Inyi miki baqin ciki kamar ya?U're my sister for godsake
..Nifa bansan da zancen dawowar IMAD ba mufrad bai fadamin ba,cos tunda nafara amfani da maganin Nan all he cares about is to have me day and nite all the time and I just can't breath wallhy harna soma gajiya da jarabar mufrad,saita danyi shiru .."yanzu ke A ina kikajin Hakan?
kujera zara ta jawo ta zauna ta harde kafafunta cikin sauke Ajiyan zuciya tace Wani friend dina ne a states danasa yana dan bibiyarsa,he told everything Wai jibi by now maybe ma yana Nigeria.
But am suprise da kikace mufrad bai fada maki ba I tot thy are best of friends,Ayn ta tabe baki kema kinsan muffy he won't talk about dat unless I insist,"so how can I help u now?wallhy Zara matsala yayimin yawa.
Can u imagine baban muffy ya kara tarkato danginsa na katsina Duk sunzo sun kara cika mana gida And u need to see how thy treated me like.."TRASH"..ta karashe maganan da kunan rai Da sauri Zarah ta tabe bakinta tace tabb Aikuwa wayanan zaki shafa dasu Dan kaf labarinsu nasani sunada arziki da wayewa sosai musamman ma
Kanwar mahaifinsa ita Hajiya bintun shehuri,ai ita matar Dan sarki ne Kuma Kinga mijintan kan ya mutu ya zama sarki sunyi Mulki sun baza sarauta so haryau Jin kanta take kamar wata hamshakiyar sarauniya"..Nide babu ta yadda zanyi in temaka miki akansu wayannan sunfi karfina...
Dama ace kin samo min mafita ne akan imad dasai nayi tunani
Da gudu ainau ta taso cikin magiya
"Ah Ahh no now haba Zarah kawai kice baxaki taimakamin ba,meye kuma na cewa saikinyi tunani?Ba zancen imad bane?we will know what to do daga ya dawo nigeria kawai kizo min hutu Koda na sati gudane,kinga yau tun asuba dawowan su muffy
Daga abuja kuma yace min kwanan zamu koma can da zama,including imad din Kenan ai,Kinga inkinzo hutu frim der sai a San nayi u got me?
Sauke Ajiyan Zarah tayi with quick relieve tace ok naji
Amma kema zakina Dan shishhigar Dani wajen mijinki ai naji ance Suna matukar shiri da imad tace done deal karki damu So gayamin ya za'ayi batun mutanen nan

Zarah ta mata Wani irin Kallon rainin wayo,can cikin Jan aji tace "kawai ki tashi muje wajen mama..

Ayn tace mama kuma?me ya kawo wannan maganan.
Kawai kice inje a zazzage ni,mama fa gani take komima laifi nane tariga tasa aranta cewa ninake cusa kaina wa mufrad

Zarah Tace kyaleta abar wannan maganan u don't just listen, kawai ki biyonin mana muje kiga yadda zan nema maki wajen zama daram awajen wayannan tsoffi ta hanyar manipulating dinsu.
Ke barikiji Daga zarar anzo anyi musu fadanci annuna ana mugun daraja su karrama su toh shikenan.

Da zarar munje gaban mama sai ki gaggaya mata karya da gaskiya akan abunda sukayi maki kice kina son taje ta gaishe su,Kinga ai yakamata ace akwai dan abun tsaraba da zamukai ko?to anan nikadai nasan mezan bata takai musu ai akwai sauran barbaden maganin farinjini da zee zeee ta karba mana kawai sai asaka musu suyita shaka cikin turare,atleast Koda basa tare dake 100% Amma in basu saka miki ido ba ai kya huta,Ayn tace hakane kam,jakarta ta dauka tace
To muje gidan Nan da nan suka fice suka dau hanyar gida,samun mahaifyr su sukayi tana nafila kafin sallahn azahar dake ita mai riko da addini ne sosai,haka suka zauna suka gaggaya mata karya da gaskiya duk dama bawai ta basu hadin kanta Kai tsaye bane Amma ta basu tabbacin cewa washe gari sassafe inta karya zata taho din.

Part 1 IS FREE,TUKUICI NE GAREKU MASOYA NA U CAN READ IT HAR ZUWA INDA ZAMU TSAYA,SAIDAI CIGABAN SHI NA KUDI NE,PLS SHOW SOME LOVE AND SUBCRIBE

the ACCESS FEE IS 300 NAIRA ONLY
VIA 0152983148
MOH'D SULE SURAYYA GTB.
OR katin MTN vtu tran via 08060712446

Screenshot ur evidence to SURAYYAHMS 08060712446

OR MAMAN MUBENA
08036651119.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top