chapter48
BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 48
Fitowarsu waje suka samu har drivern yaa sheik ya tada motar harma sun bar bakin gate suna neman shan kwanan anguwar
,da sauri imad ya ciro key din dayar suv din dake parke a tsakar gidan atake batare da bata lokci ba ya budeta suka shiga ciki su biyu,key yy ma stater motar ya wina stiring da karfi suka fice suma suka hau binsu abaya.
Wani irin shiru ne ya gifta tsakaninsu kowa da kalar abunda yake sakawa aransa Imad was looking soo calm tuki yake da jinin jikinsa tamkar ma babu abunda yake gudana acikin ransa bacin ya lura sarai da cewa hanklin mufrad a mugun tashe yake musammn yadda yaga ya kasa samun cikakken nitsuwa,bai taba ganin sa yana yawan motsi awajen zamansa kamar na yau ba,gaba daya hanklinsa baiya cikin motar a hnklce yake ta satan kallon bayan motar yaa sheik dayake gaban su ana tukashi.
Murmushi imad ya sake aransa yace hmm zakaji ta yau awajensa kuwa,saida na ce maka kayi hqri da ita ka fahimce ta amma ka kasa hmm...i rest my case Ahaka har suka isa inda zasuje din basu iya cewa juna uffan ba,20min drive yakaisu babban confernce hall inda yaa sheik yake yawan gabatar da islamic gatherings dinsa da wasu harkokin fadakrwa daya shafi addini
Yawancin wajen acike take da jama'a malamai da dalibai hardaga kasashen waje amma yau sai basuga wulgawar kowa ba,a karkashin parking space suka aje motarsu,imad was looking much better da kalar suturar dayasa shi bai wani damu dame zasu tarar aciki ba anan ma kirjin mufrad bakaramin bugawa yakeyi shikadai ba dan yau shikadai yasan meke gudana a cikin zuciyarsa dan sosai yasan kalar rigimar mutanen abbun sa,yawancin su yan kokkfi da qa'ida ne yanzu haka saisun nemi su yi magana akan kananan kaya daya ke yawan sakawa
Wani babban kofa aka bude musu suka shigo banda masu aiki babu wanda ya gaishe su,direct suka bi bayan sheik din harcikin hall din
Da mamakin su ganin babu kowa aciki sai daliban da suke shirin zuwa gasar qur'ani ta qasa da qasa.
"Assalamu alaikum, daga cikin dalibar wajen kowa yazo ya hau musu sallama suka amsa da sakin fuska suna kallo daliban sukayi wajje
Bayan wajen ya zame empty Gani sukayi ya sheik acan gaba har ya nemi waje ya zauna ata layin seat din gaba idanun sa na kallon electric lecture board wanda babu komi akai sai hasken wuta
Kamar wasu munafukai suka karaso wajen sa suka dan tsaya
Kanma susan me zasuce saiga daya daga cikin daliban ya dawo da tulin littafai a hannu da farar takarda plain guda daya ya diresu agaban sa..
Yaa sheik yana sallamar sa ya juya yana kallon su saiya kira sunan imad yace mai ya taho gaba,ba musu ya taho kirjinsa anan ta yanke ta fara bugu
Yaa sheik bai kula su ba tukun ya bude takardun dake gaban sa yadan dudduba su sama sama zamar eye glass dinsa ya gyara sann yaja wata krmr numfashi..yace yes pls"Go to the board"
Ka karanta mana wannan kamana bayani,imad ya amshi littafin ba shiri ya wuce gaban board ya fara delivering lectures
Kitabul tauyid mafi akasari zallan tafkin tauhidi ne aciki,Alhamdullhi his lectures was impresive..shikan sa saida yaji wani abu daban aransa daya tunatar da kansa wasu abubuwan yau
After 40 mint yaa sheik ya umarce sa da ya zauna,baice ma mufrad komi ba sanda yaja lokci yana kan karantar yanayin firgitan da yake ciki.
Bakinsa ya tabe sannan ya kira sunan sa ya amsa umartan sa yayi da yaje gaban board amma shi bai bashi wani littafi ba
Tsayuwarsa a wajen keda wuya yaa sheik ya fara kokarin zautar dashi da kala kalan questions Cikin ikon Allah bai bata a amsar ko wanne ba kuwa.Sai tambaya daya dayaso ya rikitar masa da tunani,kuma bawai dan bai san amsar sa bane, amsar ce tamasa mugun nauyi a bakinsa musamman da ayanzu da zuciyarsa take cike tam dan dana sanin yadda yay treating din a'inau agaban su dazu,..
Yaa sheik ya gyara zaman sa,idanun sa kurr akan dansa dayay tsuru tsuru cikin rasa yadda zai fara bayani akan matsayin aure,yafi minti biyar yana inda inda yaa sheik yace ina tambayarka wani irin vows ake dauka a ranar aure?Wani irin shiru wajen ya dauka dashi,Da kyar mufrad yay kuru ya bude bakin sa ya soma jero dukka haqqin matar sa dake kansa wanda aka karanta agaban kowa cewa zai dauka daga ranar auren su..
Sanin cewa da biyu aka kawosu nan Yasa shi barin gaban board din da sauri ya taho gaban mahaifinsa danyay bayanin abunda sukaji yana gaya ma matarsa dazu.
Isowar sa yay daidai da mikewar yaa sheik,cikin masa masifa yace..im highly disapointed in u..."Both of u..ya juya ya kalli imad daya sunkuyar da kansa sosai agefe.
In ita ta zabe tayi ma kowa karya ai idanunmu bazai mana karya ba
How dare u treat a woman like that?
Yarka ce?ko mai aikin ka?inde matar daka auro ne bani na koya maka hakan ba.
Juyowa yy kan imad shima ya haura masa da fada sosai
Kai imad kaiba kawunsa bane ashe bazaka nitsar dashi ka fada mai gaskiya ba?dake shi baida juriya take ya juyi zaiyi magana yaa sheik ya daga mai hannu cikin fushi
"Ilimin ku na banza ce tunda bai amfaneku da komi ba.
I cant belive Yau Ina kallo yadda mufrad yake dakawa mace tsawa kamar wata sa'arshi,baka da kunya ka ture hannun matarka ajikin ka har saida ta kife da bango what is more worst can u do?yaaa subhanallah..mufrad ka haukace ne?nace ka haukace ne..?
A hnkli yace Abbu dan Allah kayi haquri akan abunda ka gani its totally a minderstanding.
Saukar wata karamar mari yaji a kumatunsa,..
I neva raise u like dis..Ka tambaye kawunka nayita tunanin yadda kake tafiyar da rayuwar aurenka,na dauja kaime hikima ne,na kiraku nan ne sabida mu rabauci juna,tsakanina da ku mun dade bamu zauna tsakanin mu mun tunatar da juna ba,Then i saw u acting like a beast to ur wife,treating her harshly like an animal..Dat compel me to taste ur brains here dan wallh dazun dana ganka agaban mace kana walaknta ta sainaga kamar ba dan dana haifa bane aciki na kamar ba mufrad din dana sani na tarbiyantar na kuma ilimantar da hannuna ba...Ashe da sanninka zaka iya take sani?im higly dispointed in you
Mufrad Kamar zaiyi kuka yace abbui pls listen to me, i have my xplanations wallhy ba laifi bane
"I don't wanna hear it,.Yaaa sheik ya dakamai tsawa a hatsale..Wani irin masifa ya haura masa dashi Tun imad yanajin su daga zaune harya tsorata ya miqe tsaye shima,kan mufrad na kallon can kasa yay shiru kamar wani qunki dan ko motsi baiya iyayi Sun balain dadewa basu bata har haka da mahaifinsa ba.
Yadda yay critizising din sa ya dora laifin komi aknsa yake sashi jin kmar ya fashe musu da kuka koya fito sarari ya bayyana musu asalin abunda ke cikin ransa game da auren sa.
He wish dat zai iya furta musu afili cewa aransa kwata kwata baiya kaunar zaman Aure da Ai'anau baisan ma ya akayi ya aureta ba.. evrything abt his marriage is frustrating him.
Baban sa yay masa diri sosai,da kyarma imad ya sassauta shi yay shiru,anan
Ma dan ya fice waje ne ya kyalesu su biyun awajen
Jiki babu kwari mufrad ya nemi waje ya zauna tareda dafe kansa dake can akasa
Kusan minti ashirin basuce ma juna komi ba,sai can da imad ya dago cikin sigar lallami ya dan dafo kafadunshi sann ya hkra da tunanin ya juyo suka hade idanun su
Irin kallon tausayi da fahimta da imad yay masa yasaka shi jin wani irin karayn zuciya yama rasa me zai fara gayamasa.
Kansa kawai ya dauke ya mayar da kallon sa gefe bai iya cewa komi ba,wani irin lumshe idanunsa yayi sosai,a hnkli cikin sauke nanauyan numfashi yace
"Imad Dan Allah kaje ka bashi hakuri im wrong Wallhy bazan kara ba..I dont knw what has gone over me Yarinyar ta balain raina ni ne but
I know i shudnt have treated her like dis
Kaima kasan ba son raina bane ko?
Gyada kai imad yay yana ta kallon yanayin yadda yake maganan he is so distubed and quilty.
"Baba bazai taba fahimtata ba sabida yazo a dai dai lokacin da Ainau ta gama harzukani,she was holding my god damn shirt kamar wani barawo what kind of a wife does dat?...gosh, im just messed up..ynzu duk abunda nayi abbu laifina kawai zaina gani..nd im honestly tired I wish i can have a break from dis marriage ni wallhy nagaji da aure.
Da sauri imad ya miqe tsaya yana mai rufe masa baki
"Baka da hankli ne? Wato bazakayi shiru ba bakasan ko yanajinka har yanzu bafa?Will he love to hear dat aurenkan ne ma kakeson ka karar?
Da kyar ya mufrad ya danne zuciysa datake amon wuta ya juyo,cikin sanyin murya yace "Imad ba haka bane
Ni bance zan saketa ba,altho she asked me to..but i dint do it okay,rabuwa da auren nan fa shine abunda nake matukr so azcyta amma wllh nakasa yin shi sabida nasan hakan bashine solution ba
Kai kanka kasan ainau is freaking annoying,she is frustrating me,zata iya kashe ni lokaci na baiyi ba...i hate evrything she does with my life she is depressing me.
Imad ya mike zaune har jikinsa na tsuma ransa a mugun harde yace "Mufrad stop it kadena cwa hakan so easily please,dama ai kowacce mace tana da tata matsalar..kafadun sa yay hitting sann ya sunkuyar dakansa suka hade ido a hnkli yace"..Be a man mehn..ai dama sai da na fada maka ranar ka tsaya ka fahimce damuwar matarka amma kakiji.
Da sauri muffy ya taresa da idanun sa yana cewa"Ni banki jinka ba,i swear i went back to her dat very day tunani na we talk it down in d morning amma safiya na yi kawai naga wai har tay wucewarta office batare da sanni na bama
Imad i tried hard to control myself kwana biyun nan musmmn akan abunda kace yar uwnta ta fada maka game dani,to be frank with u am not cool with dat,a duk sanda na tuna sainaji raina ya matukar baci bansan iyakar abunda Ainau take bazawa akaina ba
To whom to who?
Im no longer conformtable with my life.
Wallhy daba dan naji zancenka ba da akan wann maganan ainau bazata taba kwana min a gida ranar ba i hate somene who cant even respect my secrets.
Haba da Allah dis is too much
Wani doguwar Ajiyan zuciya imad ya sauke dukansu sukayi shiruu na dan wani lokaci
..sai can imad ya kallesa da gefen ido yace 'so what are u going to do now?
Dan Lumshe ido muff yay yana kallon kasa.after like a min ya mugun hade ransa yace
I dont know.
Kawai nide ka bawa baba hakuri,inta kama ni Zanje na nemi gafarar a'inau kodan baba.
And from today I wll try soo hard to understand her,I wanna fiqure out if am really wrong .
"Imad yanata kallon bakinsa dayake furta maganan a gajiye,a hankli cikin yanayin sassaita shi ya dafo kafadunsa a hnkli yace "okay good idea"Yana fadar hakan ya mike tsaye yace Barinje in duba shi toh banfa san ina yayi ba..gyada mai kai kawai mufrad yay baice uffan ba saiya fice ya barsa anan.
Yana fita mufrad ya sunkuyar da kansa can kasa cikin jan wata ajiyar zuciya mai cike da tashin hankli,he felt dat no one will ever get him,bawanda zai iyajin kalar ciwon da yakeji aransa, kansa ya rungume da hannenya sa yay wani irin tsamm da ransa bai hankara ba saiyaji idanunsa na neman tara ruwa sosai komar da kansa jikin seat yy ya lumshe idanun sa yay tsam da shi shikan sa yasha mamakin hawayen data zubo masa masu balain zafi da ciwo wanda shikadai kawai yasan ma'anarsu acikin ransa.
Share hawayen yay cikin hanzari ya mike zaune aransa yanata maimaita fadar da mahaifinsa ya mammasa musmmn game da sauke haqqin aure.
Ya dade cikin wannan tunanin atake acikkn ransa sai ya soma fahimtar cewa hala laifin rashin haqurin shi ne da rashin nitsuwar da kwata kwata baya dashi acikin zuciyarsa bawai tsaban laifin matar sa ainau ita kadai ba
Imad yana fitowa yahau neman layin yaa sheik kodama zai gansa a farfajiyan wajen,
,Samun sa yay a can cikin harabar waje yana tsaye zagaye da wasu manyan shaharrrrunn malamai sunata hira cikin nishadi da annushuwa kamar ma bashi ya gama wanke su tasss aciki ba,..
Da mamakin sa ayanayin imad ya iso wajen,suna hade ido ya masa hannu akan ya karaso.
Ba musu ya taho cikinsun yana mai musu sallama a ladabce,yau har kasa ya rusuna ya gaida kowannen su su kusan su bakwai Duk idanunsu nakansa Kusan kowa awajen ya dauka ma dansa ne,saida ya fayyace musu cewa kanin matar sa ce snn suka lura..suma anan suke sanin ya dawo nan Kasar da Aikin sa dan akalla imad yay suna ya shahara ba laifi sabida kwarewar sa akan Aikinsa sosai
Shidai bai iya hira da manya ba,haka ya tsaya agefen yaa sheik yana jin hirar su har ya fahimce ashe ma taro zasuyi anan Mata da maza from 10-12 da yamma za'ayi gathering na zallan maza arnd 4-7pm, atakaice dai yau sai bayan ishai zasu bar wajen da mutanen sa.
Bayan baqin sun bar wajen yaa sheik yake sanar masa shima baisan da program din ba amma tunda ya iske su anan kawai insha Allahu shi zai halarta Adan dolen su suka yanke hakan kawai aransu suka jira.
Ranar Gaba daya hnklin mufrad baiyajikin sa sabida yadda yaga kamar kowa na rayuwarsa cikin walwala duk ya banbanta dana shi.
Gani yake kamar shikadai ne acikin maza baida wnn nitsuwar ko ince sa'ar,irin feeling din nan na weather im wrong or right sosai ya saka zuciyarshi acikin wani irin wahaltaccen yanayi
Banda azaban fargaban da Fadar da mahaifinshi ya kara ma zuciyarshi
Kowa awajen yana cikin walwala da sauki amma shi bai sanda wannan ba ma tukuna.
Bangaren a'inau ma kusan hakane ba kalar tambayar da hjy jasmine bata mata akan zamansu da mufrad ba amma fargaban rasa shi arayuwanta ma kadai ya isa ya hanata cewa komi
Koda ta fita office aikinma kwata kwata bata iyayin shi ba,gashi ta kira zarah layukanta bamai tafiya.
Tunanin yadda zata kara fuskantar muff shiyafi daga mata hanklinta a yanzu.
Sosai tayi dandana sanin gayama zarah wasu sirrikan aurenta,duk dama tana mugun jin haushin muffy amma ata wani bangaren tasan bata kyauta masa data barbaza zancen auren su a inda har zai dawo kunnen sa ba
Tun tana jin tsoro sosai aranta hartaxo ta haqra ta sallamar da komi
Ata fannin su kuwa haka suka jajirce akayi program dasu aka gama dasu
Har karshe.
Wajajen 11 na dare suka dawo gidan lkcin kusan kowa na sashen sa,washe gari sassafe mufrad yana idar da sallahn fajr ya nufi sashen mahaifin sa ya same sa yanata karatun qur'ani jona sa yy suka karasa karatun tare.
Hakan bakaramin tasiri tayi wajen saurin kau da sauran fushin da mahaifinsa yake ji akansa ba, bayan sun kammala karatun baiyi kasa a gwiwa ba yahau bawa mahaifin sa haquri,yanayi yana baiwa kansa laifin komi,har ya gama yaa sheik baice masa uffan ba banda nauyi dayaji kirjinsa tanayi.
Kallo daya zakay ma mufrad kasan give up kawai yay don ya faranta musu rai amma bawai don ya amince da cewa hakan shine zallan adalcima ma lamarin auren sa ba.
Ko ma mene yake tafiya tsakaninsu sam sam bai dace ace dansa yana treatin mace as harsh as hakan ba.
Annabi muhammad s.a.w.ya nuna mana siffofi dayawa masu sauki da saukakawa musnman wajen bi da matayen mu in sunai mana ba daidai ba.
Allah yasaka hakan shine mafi alheri arayuwarsu,,koma da laifin matarsa,yau hankli zaifi kwanciya idan yaga dansa yana kwantanta haquri da shaanin rayuwa da juriya akan shaanin zamntakewar auren.
Sabida yana son hakan yayi karfi a raywar dansa yasa ya fasa tambayar sa asalin gaskiya kodan yaji asalin kan matsalarsu da matrsan
Wani sabin babin waazi ya masa mai mugun shiga jiki yanai mai tunasar dashi cewa lallai fa Aure bautar Allah ne.
Inkayi mai kyau zaka ga sakamako mai kyau,hakama in kayi son ranka zakaga ba daidai ba.
Yace mai baida cikakken hurimin tsawwala matarsa yana mai basa misalin yanayin karancin qarfin tunanin su da wautar su musmn akan abunda suke matikar so arayuwar su.
Abun yakan dame sa musmmn Inyana magana yaga mufrad ya bata shiru baiya kuma musawa akan dukan wani abu,da akwai bambanci da in mutum yana jinka, da kuma in kawai nauyi mai cutarwa yake shirin dorama xuciyarshi danya tsira da mutuncin sa da kuma kimarsa agaban mahalilccin sa.
Karfe bakwai da rabi saura imad ya shigo wajen ya same su sanadiyar tsayawar maganan kenan.
Wani maganan ta daban ya bijiro musu dashi,akan zai tura imad saudi arabia gobe akan zai wakilce shi a wani taron sharia mai mugun muhimmci tare da mutanen sa,cewar sa daga ya dawo daga saudin ko basu hadu ba zai iya wucewa kanon abunsa.
Kusan dolen sa ne yaje sabida kusan da duk wayanda zaiyi aiki dasu a kano din suma zasu halarci taron.
****
Bayan kwana biyu
Mufrad ne kawai a gidan,tunda abun nan ya faru for two days baiyi yunkurin nemar matarsa ba
A kullum yana cikin dakinsa,saidai wannan karon ba tunanin aikinsa yakeyi ba,wa'azin da abbunsa ya masa kawai yakeda muradin yaga shigar cikin kwakwalwnsa da zuciyarsa,ko ba dan komi bama shiknsa yana son ya samu nitsuwar da zai iya farfado da farinciki acikin rayuwar sa mai gaba daya.
Cikin kwana biyun nan sosai ya maida hanklinsa kan sallar dare yana nemar Allah ya dafa masa wajen yaqin kwato hanklin Ainau da maidata kalar macen da zuciyarsa zata iya samun nitsuwa da ita na har abada.
Ata bangaren Ainau kuwa bakaramin gabaituwa da tsoro
Tayi ba,kawai zama take agidan amma hanklinta gaba daya baiya jikinta musamman kan karyan data shiryawa hj jasmine cewa komi na tfiya lami lpya a tsakaninta da mijinta muffy
Despite the fact dat tanaji dakanta amma inta tuna da fushi,taurin kai da bacin ransa sai taga kamar maganan iyayen ma bazai wani tasiri akansa ba,kwana biyun nan Da bata gansa ba kamar zuciyarta zai fashe haka ta dingaji tsabar ta rasa inda zata aje tunaninta akan abunda zai biyo tsakaninsu nan gaba.
Abu daya Kawai tasani aranta shine bazata taba bashi wani haquri ba,aganinta babu dalilin da zata taba bashi,he step on her ego,ya saka ma zuciyarta da rayuwarta mummn fargaban rasa shi,itace zata bashi haquri ko shi zai bata?ita kam tasan har abada bazata bayarba saidai duk abunda zai faru ya faru.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top