chapter43


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 43

Yau safiyar Asabar gidan yadau wani irinshiru sakamakon yan ziyarce ziyarce na sada zumunci da
hajiya Adada take jagorantar su suje wanda Already tamaida shi tamkar wani sabon al'ada agidan

Kowani ran asabar din karshen wata haka kowa zai shirya,yau ma tun karfe 9:30am na safe duka suka fito kowaccen su tasha kyau acikin dressing na mutunci kalar su makurar daukar hankli,komin su na Alfarma ne kama daga manyan kaya da mayafai na zamani da lafayoyi wuya da hannunsu yaci ubansa da tsadadun gwal na kece raini,kaf cikin gidan hajya goggo ne kawai bata yawan zuwa koina, akan barta ne a daki sabida jikin tsufa da kuma tana yawan rama bacci dake mata yawo akai kisan kullum, ciwo da tsufar jikintan sam baiya barinta tana samun cikakken nitsuwa bare barcin dare.

Ayau Zarah kamar zata mutu haka takeji dan murna dan yaune kawai A'inau ta yadda ta jawota cikin su har aka tafi tare da ita,wani irin hade kansu sukayi da yar uwanta akwana biyun nan bamai jin kansu,yau rawan kai wajen zarah wane wane,tunda Ainau ta sakata ta shirya bakinta yakasa rufuwa,yadda kasan itace ma hajya jasmine din hakata rinka azarbabi tana shishhigewa a duk inda akaje gaisuwa.
,gidan sarki, gidan gwamna,gidan manyan masu kudin garin Abuja duk anje dasu,tamkar wata  zararriya haka zara ta dinga musu murmushi wani binma har bata iya boye zakewarta da kauyancita duk inda akaje saitasan yadda za'ayi a sanda ita.
manyan abokan su na arziki da yan uwa da dangin su na Alfarma kowa yakanji dadin zuwansu dan ba karamin karfafa zumunci hakan yake jawowa ba haka za'a cika su da goma na arziki banda wanda suma suke kaiwa,a lalace dai zarah saida ta damke dubu dari biyar a hannun ta na zallan kyautar da ta samu.
Bayan sun kammala da ziyara suka wuce super market irin window shoping din nan, duk wani abunda suke da bukata na rayuwar su dana gidan dayajajja baya shi suka tsaya tsinta,Ainau ce kawai bata wani tsinci kayan kirki ba dakema yanzu kusan komi da zata saka ajikinta har ya iya birge mufrad ma haushi yake bata.

Zaune yake a babban falon sashen sa dayagaji da haduwa jikin sa sanye da wata alkyabba kirar velor black colour mai  ratsin fararen duwatsu,wani irin qamshin lime basil nd mandarin mai sanyin dadi ke tashi a falon,hannun sa dake rike da tea cup mai kyau ya mika gefe ya hau tuntuda wani hadadden pink harbiscus tea dayaji hadin kayan qamshi citta da danyen qirfa da wani ganye mai dibi da ganyen na'ana mai dan uban qamshi,yana matukar son shan wannan tea din musamman dayagane amfaninta wajen kara lapyar hanta(liver) ,kusan rabi ya zuba tea din a cup sannan yakai bakinsa idanun sa a lumshe ya shaqa qamshin ta ramin hancisa sanna ya bude idon tare da furta bismilla ,a nitse yakai kan labbansa sann yadan kurba harya masa kyakwan kurbi biyu,bayan nan ya mayar da cup din ya ajeshi agefe acikin tray dinsa tare da wasu hadaddun royal tea set da babban flask na zallan ruwan zafi
Tsohon jarida yagani agaban sa zai dauka Sautin takun daya jiyo tun daga bakin kofar ya dakatar dashi,kansa ya dago yanamai gyara zaman sa mai cike da nitsatsen izza,ido ya kafawa kofar yana jiran ganin mai shigowa aranshi ya bari kawai dansa Mufrad ne dan tunda yazo garin Abuja basu wani samu kyakkwan zama dashi ba sometimes he wonder if he eva have a break in his life,he is alwys busy and ocupied da wasu abubuwan.

Haka kawai kuma sai yaji hanklin sa na tashi akan lamarin mufrad,tuno da abubuwan da mahaifyar sa take famar cewa na anya mufrad yanama samun lokacin kulawa da auren sa kuwa?shikansa dayayi duba acikin nazarin wann tambayar nata sai dayaga kamar Akwai nasaba mai girma dayakamata shima nan ya hankara da shi.

Duba da yanayin dansa wani bin har sai an mance dashi agidan ma in aikin sa ya taso,No one in his right senses zaice mufrad yanada lokacin kulawa da family bare kulawa da gidan gaba daya ba.

Koda shike haryau shidai bai taba jin ankawo wata matsala ko korafi dagata bangaren auren sa ba,hala zai iya yuwa hakan alamuce na nuna sun samu kyakkwar fahimta da matar sa
Saidai duk da haka shidai yanada ja akan yawan dauke kansa akan tsabgar rayuwarsu,shine masa namiji babba shin in tun ayanzu bai nitsu ya zamo wani jigo da jagora wa yan uwansa da familynsa ba nan gaba insuka barsu a duniyar da wuyane rayuwa yay musu sauki da armashi.

Shidai Yana mugun alfahari da jakircewa d kuma gwazon dansa mufrad, amma harga Allah cikin zuciyarshi zaiso ace rayuwar mufrad ba hakan take ba,he thinks there is more to life than seeking justice.
Kwafa yay jikin tunani "Shikenan rayuwar mutum ba hutu?dada leka bakin kofar ya dadayi kirjinshi har na bugawa dan har Allah Allah yakeyi ace shidin ne ya shigo saboda akwai tarin maganganun da zai so yaji amsar su daga bakinsa..

"Assalamu Alaikum"
..yace wa'alaikum sallam warahmatullahi wabarkatuh.

Kai tsaye Imad ya bayyana acikin falon jikinshi sanye da wata tsadadiyar black voile ya kafa hula itama baka half shoes dinsa ya riga ya cireta tundaga bakin kofa,daga sama har kasan shi is all black fuskn sa yay makutar kyau da haske wni dan uban gamshin tom ford F fabolous ne yake binshi kamar na maita,straight ya nufo inda yake yana tafiya kansa na kasa,a kasa kusa da kafafun yaa sheik yanemawa kansa wajen zama cukin yanayi nade kafafun shi dayake bayyana ladabinshi da boyayyiyar sanyin halinsa,yaa sheik ya kasa daga idanunsa akansa,Allah ne kadai yasan yay yakeji ransa game da imad haka kawai yakan ji farinciki inya gansa ata wannin fannin kuma yakanji kamar yana takurashi ne yana rage mai freedon din sa nayi rayuwa duba da babu wata kakkarfam alaka ta jini a tsakaninsu face auren yar uwan sa daya hadasu.

But honestly he is more than just that to him,arayuwar sa yakanji kamr yafiye ma imad kallon dan cikinsa daya haifa fiyeda alakar kanin matar sa dayake tsakaninsu,kamr yadda ya lura shima imad din matsayin uba kawai ya ajeshi
ajiyan zuciya ya sauke Imad yay gyaran murya
Yace"..katashi lpya?..Yaa sheik ya amsa da lpya kaifa?
Yace alhamdullhi,
nan ya hau tambayar sa akan abubuwan da suke famar tsarawa game da aikinsa
"..dan imad ne zai rike tsohon office dinsa na kano doc mehra ya riga yay masa bayani akan hakan imad din yace yake so saidai bai bayyana masa cewa akan rufaida bane ya matsu daya tafi,saidai yakan sakaya magana ne da zancen zaifi kyau imad yana zuwa kanon kodan yarinka kusantar mahaifyar sa dake can,shiysa yaa sheik ma baiyi musu musu ba ya kyaleshi,da sharadin anan din zai zauna har yay aure,badan shirye shiryen da zasuyi ba da baifi kwana kadan yau ya rage masa ya fara zuwaba,his working days are just few days a week,dats monday,thurs,friday sauran ranukun he is much expected to be in Abuja.

Hirar aikin suka taba kadan yanayi yana hada masa da nasiha sosai,shi sam baiya iya zama da mutum walau nashi ne walau bana shi ba, face ya tsinci kansa cikin tunatar dashi kalmar Allah da manzon sa.
Yau ma Wa'azin auren kawai ake masa.

Shikuwa imad har acikin ransa baifi ace mai yau yaje kanon ba,duk nasihar da yy sheik ya masa akan yay kkri ya fidda matar aure nan kusa babu abunda hakan yake tuno masa face fuskar rufaida,har wani ji yake kamr yana dago idanunsa sama hala yaa sheik zai karance abin da ke cikin idanunsa tsaf..

Tunda ga shi yanata kokarin karanto rudanin da ke tattare da muryarsa akan furta sunantan dayayi masa dazu, Shi kuma ba zai so kowa yasan da sirrukan zurciyar sa har hakan ba har sai ya ganta ido ido saboda shi kansa bai yarda da kansa ba. Bai yarda da cewa feelings dinsa are far beyond vulnerbiltyn shi ba.

Har iyau Bai yarda zuciyarsa ta kamu da mugun son rufaida ba,don a ganinsa babu wani kwakwarn dalilin hakan.

Abin da ya yarda da shi shine there are some certain characteristics about her da za su iya rikita kowanne lafiyayyan da namiji mai cikakken hankali bawai shi kadai ba.

Her well-shaped body lineage,her plain pointed nose with those thick thick brows nd eye-lashes this pinkish red soft lips da kallo daya kamai saikace bugun xuciya all of her personal outlook are actualy breath taking Kowanne lafiyayyen namiji zai yi mafarkin samunta matsayin matar aurensa na har abada

Shirun imad ya yi yawa,sannan ya ki dago kansa ya kalle yaa sheik.shima shiru yy ya ba shi mintoci masu kyau don ya gama duk tunanin da zai yi, amma ganin ba shi da niyyar magana kuma ya kasa dubansa sannan yana cinye masa lokaci,sai ya kira sunansa cikin nutsuyar murya For all he know imad dinsa bazai taba bashi kunya ba..

Ya dago bakinsa yanai masa mugun nauyi"..Yaa sheik Alfarma daya nake nema awajenka.
Ya kure shi da ido alaman ya fadi kawai,"kirjinshi kamar zai fito a kirjinshi saidai baza'a gane hakan cikin sauki ba ahnkli  yace ,"..yaa sheik pls so nake ka janye maganan ka dani akanta.. sai yy shiru..can sai yace "ru..fa.ida.."Muddin ina kano,nasan zan nemi insan halin da take ciki kuma bana so in sama wa umarnin ka inka bani dama zan kiyaye sosai na maka alkwari bazan saba ma sharudan ka,i swear it.

I just want to help her like my own sister nan gaba bamu san wanda zai rike namu yan uwan ba..yaa sheik ya dauke kansa yay gefe yanakan jinsa"..da alama yaron nan fa baisan meyake yi ba,badar da maganan ma yayi yace "inashi mufrad din?a sanyaye yace yana ciki batare da ya kallesa ba yace.."call him" kaje ka kirasa kawai
Babu musu ya tashi ya fita a falon yaa dheik yanata kallon sa, dakin mufrad din ya wuce direct.

Kwankwasa kofar dakinsa yake yi, tun ana yi a hankali har aka soma yi da dan karfi.shower  ya kashe ya janyo soft white tawul ya hau goge suman kansa da jikinsa a dan gaggauce. A gurguje ya nannade kansa da wata sexy black bathrobe ya dore igiyan a kunguminshi yana jiyo muryar imad a kofar dakin nasa yana ambaton sunansa a tausashe
Baiyi magana a bayin ba har sanda ya fito yana cewa
"Coming"sannan ya bude mai kofar..

Suna hade ido ya dauke kai Wucewa yay ya zauna abakin gado yahau kallon mufrad din dake faman mutsuka la mer rejunavting hand serum yana mutsukwa yatsun hannun sa dan uban qamshin plant extract duk ya cika musu hanshi with all the afalfa,sun flower and barley extract wanda yake taimakwa kwarai da gaske wa fatar hannu againts tear wear and any foam of wahalhalun da akeyi da hannu.
No wonder babu wani tabo ko alamun da zai nuna cewa  yana rike bindiga da miyagun makamai bcos of how he take care of his skin very well,bakaramin pamparing kanshi yakeyi ba sosai yake tattala duk wani abunda ya shafi kyau da lpyar fatar jikinshi kamar wani baby dan wata biyu haka yake bi dashi.

All his body products are strictly from la mer kamar yadda ake cewa no beauty products is ever complet witout la mer,mini facial device dinsa dake kamar remote ya dauka ya danna a fuskar sa duk dama ba wrinkls din zaka gani ba,kawai dai sabo dayi yasa dole yake kunnawa.
Bayan nn wardrobe dinsa ya bude bai tsaya dubawa ba ya jawo iya abunda hannun sa yakai kai ya mayar ya rufe ya shiga closet, Agurguje yay sauri ya kammala saka kayansa sann ya fito wani dark blue jeans ya saka data dan dameshi ta kafa dake booth dinsu na military zai hadata dashi sai bai damu ba,jacket mai kyau fara ya hada ta da wata hadadiyar marks and spencer tshirt ta ciki, yahau daura farin chain rolex watch ya feefesa dfrenr brand na turare designers da suke qamshi ajikinsa sunkai kala hudu,dagowa yy suka hade ido da imad wanda ya sauke yar karaman ajiyar zuciyar datazo mai a bazata.."yace "Thougt ure out..
bai amsa shi saida ya dau wani file din dake aje a kan table ya rike a hannu yana shirin budeta a nitse yace not yet, wasu aiyuka ne suka tsareni tun jiya ban huta ba sai yanzun nan dakaga na fito daga wanka,
Ya karashe maganan hanklin sa nakan file din da already ya budeta,imad Yadan yi shiru,can yace toh muje yaa sheik na kira,hadeda takune fuska alaman baida lokaci isashe na amsa wani kira,can kasar wiyarsa ya firta damnnn,sai ya ya juyo da fuskar sa kadab".. Mad Can you please cover up for me?..imad ya kawar da idanun sa gefe kamar badashi yay ba "pls kace kazo baka ganni ba i really need to catch a meeting with d defence minister righ now .

Imad yace sai ince mishi kace meeting dinka da minister ya fi muhimmanci than kirar mahaifinka.

Wani Hade ransa yay atake yace
"Kaima kasan ba haka bane..u just dont get it,i cant miss dis meeting,in bamu hadu yau ba nasan bazan samu damar yin tafiyar danake so inyi ba ne harsaiya dawo..and dat shud be in 2_3weeks time bana so a batamin lokaci na har haka

Imad ya miqe tsaye
Cikin yanayi shan qamshi aransa ya gama kilewa yanata  kunkini,...malam zaka wuce mujene ko sai naje nafada mishi gaskiya?,tsaki mufrad yaja yana mai niyyar share sa kawai, sai kuma yaji muryan imad din ya fito feettt cikin sauri kuma a mugun tausahe.yace"Muffy kenan ni bansan ya zanyi harka fahimce ni ba..dont you think ur family also need ur attention right now?gaskiya fa akwai matsala agidan nan kuma abunda fa kakeyi baida kyau.

Cikin tsare sa muffy yace hey hey hey wani matsala ne agidan na ? ina dai cewa zakayi banda lokacin kaina but i do have they time okay?Imad ya tabe baki irin hmm
A dunkule yace mashi"toh kaji dashi dan nidai ban gani ba,and There is more to life dan All this stuff da kafiye damuwa akai,yy maganan idanunsa nakan file din yana hararsu..nide bazan masa karya ba inkaga hakan shine daidai awajnka ai saika tafi saika dawo... daga nan bai kara cemasa uffan ba ya kama hanyar sa ya fice,bayansa yabi da kallo cikin dakikar da baifi a kayyade ba ya fahimce komi"..toh shi me?ya rasa mezaina musu a gidan inya zauna,tunanin mai yay oho sai ya dauke kansa, gaban bedside drawr ya nifa ya tattaro wayoyinsa dake table din ya dura su a aljihu ya dau key din car dinsa yay gaba.

Daidai isowar imad kofar palon kenan saiga sallamar doc mehra shima ya shigo ,binshi yy da fara'ar sa suka shiga harciki suka gaisa agaban sa yaa sheik suka hau tattaunawa game da tafiyar malak makaranta dake a tarayyarsu kwata kwata basa banbata abunda ya shafi familyn su yadda yake iko da yayanshi hakan yaa sheik ma yakeda wannan daman dan bakaramin yarda da wani iri shakuwar fitina sukayi da juna ba,inda yaa sheik ya rinka turje musu akan lallai malak day kawai zatayi bazatay boarding ba tunda akwai fareeesa da hjy mama a kano dole ne tazauna agaban daya daga cikinsu..

Karshen ta a haka suka tsaida magana,su biyun suka fita aka bar imad agidan shikadai  tsammanin shi inya koma daki zai ga mufrad ganin wayam babu kowa yasa yaji ransa ya sosu,har wani ziriya yakeyi shikadai yakasa samun nitsuwa He cant just believe it,wato abunda yake son kawai shiyakeyi
Which is soo wrong toh inde tarayyarsu ta gaskiyace yau saiya hankarar dashi akan aikinsa
Ya zaiyi yace masa mahaifinsa na kirarasa ya share kirar akan ganin wani wawan meeting dinsa da minister

Shidai yasan Duk wannan muhimman abubuwan dayake kin basu muhimmaci arayuwa tabbas sune nan gaba zasu zo su rufa masa asiri ba aikin san nan ba,gaba daya yarasa yadda akayi mufrad dinshi ya dawo haka,yea he is obsessd with his work amma bahar haka ba,sabon salon taurin kai da walakancin shi sosai yake nunawa kuma ya gama lura dashi kamar ma kowa yakei..

Mufrad care very less about anyone

Dayan Wayarshi ya dauka ya kira wata private lambar mtn
In few min aka turamai number sectaryn minister
Baiyi wata wata ba ya hada fake urgent appointment da higher ranking officers wanda yasan definately bazai bari mufrad ya samu cikar burin shi ayau din ba

7:30am

Kwance take tsakiyar gado tayi lub ayanayin ruf da ciki idanunwanta duka biyu a lumshe
Wani mayattacen qamshin turaren wuta ne ya tada ta,
Jin sautin sallamar anty fareesa yasata mikewa zaune cikin sauri kunya yasa ta hau mutsike idanunta"..Tun kan tayi gaisuwa Anty fareesa tarigata yin magana cikin sanyin murya tace rufaida kin tashi lpya?har kasa ta zamo daga kan gadon tana dan jajjan wuyar vest din dake jikinta cikin sanyin murya tace "lpya lau anty..'
Zama anty fareesa a bakin gadon daf da ita ta kara da cewa.."yay jikin toh? akwai inda yake miki ciwo ne?shiru tadanyi kafin ta girgixa kai alaman a'a anty tace Alhamdullhi..
Toh Yanzu za'a kawo miki sauran kayanki dana siya miki saikiyi sauri ki shirya ki same ni a kasa,ba musu tace toh sannan anty ta miqe ta fice,ajiyar zuciya ta sauke tana bin rufaffen door din da kallo can ta juya karaf idanunta suka cikaro da madubi. Wani irin kallo tayi makanta ganin yadda ta dawo babu marabarta da gwarngal tamkar ba ita ba Ta kusa minti 10 a tsaye tana kallon kanta kawai,
ji tayi ta burme dan yatsun hannunta acikin kashin wuya dan batama san sanda tahau shafa jejjemewar da wuyarta yayin ba.

Hawaye ne taji suna shirin sauko mata amma data tuno da maganan dr kabeer sai tayi saurin shanye hawayen
,ajiyan xuciya ta sauke har sau uku kamar yadda doctor yake umartan tayi in ta cikaro da wani abunda ya tokare mata kirji,cike da dauriya ta kau da idanunta a sadaf sadaf ta wuce bathrum ta tube kayanta karankaf bata tsaya kula xuciyarta dayake ta son zugata ta damu da yanayin zubewar jikinta ba, ta kunna shower ruwan dumi mai yawa ya soma sauka akanta shaaaaaaa,sosai takejin dadin saukar ruwan sabida hnklinta dayake dada kwnciya.

Sabulan wanka na alveeno ultra da hydrating shower gel ta gogga ajikinta dats so soft and silky tuni yadau qamshi da qyalli
Fuskanta ma sosai ta wanke sa da scrub din neutrogena tayi brush tayi marmaza ta kashe shower ta dora towel ta dawo cikin dakin tahau shafa man Alveeno da wasu rejunevating creams dakema yana farfado da yamishewar skin fata tayi sumul tayi laushi,dadin sa ya saka sanda ko inan ajikknta yaji man sosai ko wani powder bata shafa ba tahau saka dogon rigar abaya baka dataga an ajiye mata awajen

Ita duk batasan  yaushe aka siya mata su ba dukansu jallabiya ne na mata sunkai kala biyar da inners da pad tampoons da panty liners,dan haryau bata taba fitowa ba a kuma basu taba barinta ta tsinana komi agidan ba,toh ko gaisuwa ne saidai taga anzo an mata a daki, face yau da akace mata ta sauko kirjinta nata bugawa ta lillibe kanta da mayafin abayar ta sauko.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top