chapter41


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 41

Juyowa yay ya zuba mata idanunsa da suka jima da sauya launi yanai mata kallon dabazai iya fassarashi ba dan har cikin kokon zuciyarshi yakejin ciwon kukan datakeyin,tambaya yay ma kansa a rude kode wani abu ya farune bayan tafiyarsa?yanzun suka gama wasa da dariya within next minute ace tsohuwa ta birkice haka?saidai abun bai wani fito masa a dunkule ba dan Sosai ya soma fahimtar inda ta dosa da maganganun tan duk akansu hajiya Adada ne, ya kuma yadda ya amince sunyi sakaci ata fannin tarbiyan cikin gida,saida bai wani yadda cewa laifin daga matarsa bane danko shi ya shaida iya bakin kkri tanayi akan tarbiyan yayan su saidai dan abunda baza'ara sa ba.

Tuni ya sauke muryanshi kasa kasa yahau rarrashin ta da dukkan imanin sa
Yana kalallame ta ta kowani hanya amma duk abanza, Borin data barke masa dashi yajanyo hjya jasmine dake can sama saukowa cikin sauri tazo ta samesu,zama tayi tana tambayar su meyafaru bata samu wanda ya amsa mata ba, ganin yadda hjyr ta birkice tana ta rikirkito da manyan maganganun da basusan farawar sa da gamawarsa ba yasa tuni itama jikinta yay sanyi.

"Ni za'a mayardani mutumiyar banza?

"Ace Kaf dinku dana haifa bamai jin magana na,baku dauke ni komi sabida kunga bana da gata a duniya bani da kowa saiku sai Allah,bukar anan ya kada rigarsa yayi tafiyarsa yace min ya fita a harkata kaima Zaidu danake alfahari dakai kana neman watsamin kasa a ido,sam ban isa dakaiba saboda kana ikirarin kanada wasu iyayen atawani waje Toh insha Allah nima zakuga gata na, kuma rana na zuwa da zaku nemi ku rasa kaida dan uwanka bukar tunda banzame muku komi a duniya ba sai gwandon shara,tana ta surutai..yaa sheik yay wani irin shiru tuno mishi da xancen illegitimate doghter sa lailaa zayd matazu datayi yasajin asalin jin karayar zuciya ,hajiy jasmine ta fashe da kuka dan sosai take ganin harzuka a yanayin hajy mama "mama dan Allah kiyi hakuri in wani laifin mukayi miki kifada mana wallhy zamu gyara,mama dan Allah kiyi hakri,ko ajikin hjy mama dan so take yau din nan ta fitar da dukann abunda yake cikin ranta inyaso kowa yaji ita bazai dameta ba, danta gama lura saken da sukeyi suna kau da ido akan abubuwan dake faruwa dasu bazai taba ficcesu ba...
Cikin kukan tace
"Bukar yafi karfina ya lalata rayuwar sa harda na yayan sa,kaima kadau hanyar hakan zaidu..wayyo Allah na,ni menayi muku ne?ina zan saka kaina da wannan tijara ba gwamma na mutu da in zauna ina kallon tabarar nan ba ! Yaa sheik ya kasa iya dago idanunshi da suka sauya kala ya koma zallan ja,tunani masu nauyi ne suka cikke birnin fadar zuciyarshi,Kallo daya zakai masa kasan shi irin  mutanen nan ne da suka tsane ganin fushin iyayen su musamman ma hawayen mahaifyar shi daya mugun tsana dayake gani ayanzu.

Sai ayanzu ya yadda ya amince da cewa tabbas akwai sabanin fahimta mai nauyi tsakanin iyayen nasa harda kakn kan sa hjya goggo

Tuno da yadda kowannen su yake behaving kwana biyu daya wuce inya kirasu a waya don yaji lpyar su,wani binma hjy goggo shareshi takeyi sam bata amsa masa gaisuwar sa saidai tayi ta jefa masa maganganu marasa dadi,suma acan cewa suke bayaji dasu sabida yabiye wa uwarsa,toh gashi anan ma uwartasa cewa take yabi hudubar wayancan ya kyaleta.

Gaba daya sai yaji ya rasa meyake masa dadi,aransa ya rasa menene mafarin matsalar su da basa cika samun fahimtar juna,ko da can ma yasan mahaifyrsa itace mai yawan kauda kai da ido waidon kawai azauna lpya,amma birkicewan ta ayau ya balain tsorata shi.Does dat mean dat she cannot tolerate anyone anymore?,ta yaya mahaifyarshi zata furta masa kalman cire hannunta akansa da familyn sa gatsau babu wani shakku ko tantama,tsoron hakan sosai ya nuna anayin sa har rawa rawa hannun sa da jikin sa yakeyi shikadai,tayaya shi zai iya jure irin wannan rayuwar, itakadaice hasken rayuwan sa,itace mabudin aljannar sa,Abun yanai masa ciwo aransa matuka.dama can bai taba yin tsammanin zata kyale yaa bukar ba,duba da yadda take matukar kaunarsa take kuma masa uzuri arayuwa,amma kuma saiyaga ta aikata komi kamar yadda ta furta musu,da alama soyayyarta agare su bazai taba yin tasiri wajen aikata abunda take so ko daukar wani tsatsauran hukunci akansa shima ba,shikuma harga Allah baijin akwai abunda zai rabasa da ita har abada,yaa bukar din ma dolene yau yaje duk inda yake ya samesa su sasanta kansu koda hakan bazai samu cikin sauki ,dan tun bayau ba yake cikin damuwar rabuwarsu baiyarda da zaman da sukeyi ahakan ba yasan nan gaba wannan zaman nasu bazai taba amfanar su ba .

Cikin zurfin tunanin sa yaje jiyo yadda hjy jasmine take faman aikin lallami da rarrashinta da magiya da komi harda jan shesheka wai koda hjy mama zata sauko amma ina abun sai gaba gaba yake,duk wani complain dinta game dasu saida ta amayar dashi.

Kama daga sake kan tarbiyan yayansu,Izuwa rashin girmama zumuncin da sukeyi a tsakanin su dayake so yay qarfi.

Hjya bata dena kafa musu sharuda da dokoki da wayo ba har saida suka jiyo sallamar Anty fareesa da yayan ta sa suka shigo musu bazata,nan ma dai kamar an kunnata ta cigaba da azarbaba zance tana kwakwalo magana akan lallai tana son akwaco mata rufaida ta zauna agaban ta.

Anan nema yaa sheik ya samu daman shiga zuciyarta,tuni ya kalallemeta da cewan yau din nan shi zaije har anguwar gangare dakansa ya samu yaa malam su tattauna kodan acika mata burinta na dauko rufaida

Haka ta rinka basar dashi,ta nuna bata damu da a sulhunta ta da bukar ba itawa rufaida kawai take kkri,while azahiri kowa ya fahimce ta abunda take matikar bukata kenan taga cikakken hadin kan atsakanin yayanta da jikokinta.

Bayan fitar yaa sheik awajen aka barsu su uku agidan suna shirye shiryen tafiya Abuja nan duka suka hau hirararrakin yadda abubuwan gidan zata kasance.
Sosai hjy mama ta rinka ingixa zuciyar hjy jasmine akan ta dage ta tsaya akan tarbiyansu na nazli tanata kafa mata misalai masu mugun kashe jiki.

Tace in aka koro yarki agidan miji akan bata iya girki ko kulawa da gida ba abun kunyar akanki zai kare ke kadai,su wayanda suka lalata miki su suka sangarta su suna can daga gefe saidaima su zageki suce kece baki iya tarbiya ba ,dan haka tun wuri ki raba gidanki da masu aiki, ki bar yaranki sunayi suna sabawa dashi,ki zamto kece mai saka doka akan tarbiyan yaranki ba wasu nadaban ba.
Gata kam ai mun nuna musu oya gata amma kukan kurciya fa jawabi ce

Hjy jasmine tasan hakan duk gaskiyane amma amsawa kawai take don tasan akwai babban cwakiyar agaba,tayaya ma za'ace ma nazli datake daukar kanta so high ta dawo da karatunta na medicine nigeria?toh gwamma ma keeyan baifi wasu tsirarrun watanni ya rage masa ya kammala komi nashi acan ba.
Shukra kuwa tasan zaa debe yan kallo da ita wjen koyan aikin gida musamman ma girki...
Aranta sosai take harsasho yuwar babban ruguntsimi dan tabbas a rubuce yake,bazai taba yuwa a kwashe lpya dasu hajya Adada acan abuja da wayannan sabbin tsarrukkan da hjya mama take so din ba.
Haka dai tayi shiru bata furta harsashen ta wa kowa ba,hakama anty fareesa bata nuna musu tasan wani abu game da abunda ya afku da rufaida ba.

Dagata dayan bangaren kuwa Zarah da kyar tayi convincing din a'inau akan ta zauna agidan,ahakn ma bayan ta amshi kudade masu yawa na kusan kimanin milliyan daya harda rabi a kyauta dan su sasanta,wannan karon Bakaramin zulmar da zuciyar Ainau tayi ba,ko irin kushenta nan data saba yau batayi ba,zallan zugi da gammon ingaza mai kantu ta rinka nada mata akanta tana kuma dora ta akan hanyar mugunta mafi tsauri.

Ita kuwa A'inau dake zuciyarta a matukar harzuke yake dashi sai bai dauketa wani lokaci ba ta yanke hukunci karban hakan,tuni tayi na'am ta kuma amince da dukkan shawarwarin da zarah ta tsiro mata dashi na daukar tsatsauran matakin rama walakanci da mijin ta mufrad yake mata

Zara kuwa Duk wata hanyar dazata bi ta nuna wa ainau cewa ta gama da zuciyar imad saida tabi
Haka ta bar Ainau da jin tausayin kanta da cizon yatsa,hakan yasa ta kuma mugun saka ranta akan tabbas hala zarahn ce data raina zata iya saita matashi,bata damu ba tunda ance blackmailing dinshi kawai zasuyi basai ankaiga zuwa wajen bokan zee ba.

Cikin kwana biyu kacal zarah ta maidata wata shasha dan akwai wani turaren datake bata akan tanayin hayaki dashi zai cire mata tsoro,alhali bata sani ba shine tasirin plan dinsun lakani ne da boka ya basu na asirin mallaka,dan ita kanta zarahn tasan ba lallai bane imad ya aikata zak zak iya abunda suke so din ba boka ya riga ya gaya musu cewa muddin imad yana sallah kuma yana kiyaye addua ba dole bane Aljanun su suna cin galaba akanshi akowani lokaci.

Bangaren yaa sheik kuwa sosai hanklin sa yaso ya kasu kashi biyu akan lamarin shi da dan uwan sa,dan ko da ya isa kofar gidan ranan almajirai kawai aka hadasa dashi wai acemasa yaa malam baya nan,sawun sa uku yana zuwa daga bisani sukace mai wai tafiya yaa malam din yayi,ahaka harya gaji yabar anguwar bai samu daman ganawa ko da da umma hadiza ba.

Ata fannin Hjya goggo ma abun babu sauki dan sosai suka daga hanklin su suka birkice fushi da sukaga har anci kwana biyu da dawowarsa zaidu amma baizo musu Abuja ba,tsaban fushi hajya goggo harda yin barazanan tattara kayanta zata bar masa gidan sa, hakan yasa dan dole hajya jasmine tabiyo jirgin dare tun awashe garin ranan ta dawo Abuja.

Mufrad kam babu abunda ya dame sa da borin su agidan hasalima batasu yake ba,haka zasu nemesa yazo suyita surutun su harsu gama tass yana jinsu saidai ya kada kansa ya fice amma bai taba ce musu uffan ba,Ainau dayake matukar bukatarta ajikinsa na daya lura wai tana fushi dashi share kashin ta yayi yay banza da ita bai kara neman ta ba bare su.

Imad ma babu abunda yakeyi kwana biyun nan face yan nazarce nazarce akan tuggun da zarah ta dora sa akai na batun yar uwanta A'inau,Abune wanda yake gannin zai fi masa komi sauki n wrwarewa amma saiyaga wai haryau bai iya furtawa ma mufrad ba,gaba daya ya rasa ta inda zaiyi ya soma tunkarar shi da wannan maganan Har yau tunanin rufaida bai kyaleshi ba,ata dayan fannin zuciyarshi kuma malak ce datake matukar bukatar taimakon sa akan komawarta kano,kusan kowani lokaci sukanyi waya dashi mai tsaho, inba su hadu a wayar ba to a gidansu ranar zai wuni suna hirar rufaida itama sosai hanklinta ya kwanta ta samu nitsuwar fahimtarsa musamman data soma gane cewa rufaidar nan ta musamman ce a cikin zuciyarshi.

After 3 days

10am malak ta sauko cikin black abayar al-layl yasha kwalliyar stones ya mata matukar kyau fuskanta ba komai daga powder sai kwalli ta tarar da kowa na falo,doc mehra me ya som dago kansa yanata kallonta a fakaice batare da ta lura da hakn ba, tana isowa gabansu ta rusuna har kasa cikin sanyi murya tace" _ndwattu baba?_
Da faffadan murmushin sa ya amsa ta da cewa "lpya Alhamdullhi" cikin jin dadin yaren data mishi duk dama yasan bason yi takeyi ba, haka ta juyo ta gaida mahaifyarta cikin ladabi sannan ta nemi waje ta zauna kusa daf da shi dake ita dama can yar lelenshi ce
Doc mehra ya kalleta yace
"Mama na yau zakuje ayi changing course din ko?adan shagwabe tace aaa baba,..nifa ..na  Anty meera tayi saurin tsareta da wani muguwar ido,cike da hantara tace "kefa me bayan har an gama shirya komi naki? shiru malak tayi batace uffan ba banda hade ranta datayi
Doc mehra ya ce
"..kan naki ya dena ciwon?da sauri tace eh baaa danayi bacci aiya warware.

Straight Antu merah tace toh tashi kije kitchen ki dauko abincinki,"toh tace sannan ta nufi sama tana takawa ahankli harta isa sama ta bude kitchen dinsun ta shiga,warmers din dake kan kitchen tables ta hau bubbudewa,wani white colour plate ta dauka ta hau saka almond berry pancakes da hadadden syrup na oranges ta dawo falon ta zauna a babban dining ita daya tana ci a hnkli har ta gama ci ta dawo cikin main palon basu gama tattaunawa ba

Tana zama doc mehra ya juyo ya kalleta yace.."malak mai nakeji wajen mahaifiyar ki wai bazakiy school din anan ba?..tace baa,
Thats wat am just about to say mama ta tsareni"..baaba nace tunda bansamu anan ba why not amun change of institution kawai ni zan koma wani wajje,a hnkli tace ga kano na abbui, nafa duba buk su ai basu kare screening dinsu bama..da mugun mamaki a yanayinsa yace kano kuma? but why kano?anty meera dake hararar su duka tace shirme mana, ai nafada maka she just want to be there sabida imad ma yace zaije kano..toh wallhy ki maida hanklinki inagaya maki karatu ke zakiyi ba saurayi ba ke mema kikasani? hade rai sosai malak tayi dan ta tsani a rinka gwada mata hakan akan imad hakan yana lalata mata zuciya,ta lura kowa dai so yake yace tana ma imad biri biri ne dan kawai angansa kyakkwa mai aji hala zatace tana sonshi and all dar stuff while its pains her really.
Aranta tasan imad yana matukar burgeta amma bata taba sako zancen soyayya dashi a zuciyarta ba,ita koda zatayi soyayya ma saidai ace ta fallen ma wancan Yayansun captain din dan harga Allah tafison military stuff cos yawancin novels din datake bibiyar na stars sojoji yana balain burgeta
..doc mehra yay shiru yanajinsu suka hau musu akan imad tare da mahaifyarta,dan sam taki amincewa da akan imad take son zuwa kano kararu maman ta kuma tace saammm ba haka ba,da hawaye sharbe sharbe a idanunta ta tashi ta nufi dakinta cikin fushi,tare da sauke ajiyan numfashi doc mehra ya juyo kadan yace ma anty meera meke faruwa ne kike takurawa yarinyar nan?bayani ta hau mishi akan hirarrkin data ji sunatayi da imad din kwana biyun nan, sai ya lura kamar hanklinta ne bai kwanta akan alakarsu da malak ba, duk tsoronta kar yarta datake karama ta fada tarkon son da bazai amfaneta da komi ba sai radadin zuciya,kwafa yy aransa yace"hmm women can be silly..,saiya saki guntun smirk mai tafe da murmushi fahimtar kowaccen su,yana dan murmushi ya mike tsaye yacewa matrsa ,hmmm stop over_thinking it Ameerah,abata lokaci zatay tunani nidai adena batawa mama na rai atoh..
Anty meera tanajin sa ta kadakanta kawai,yace
anyways zandan fita,i wll get back to you okay?..anty ameera batace mai urfan ba dan tasan halinshi na mugun son abunda yarsa take so..bayan tafiyar sa ta haura sama taje hardakin ta sameta da waya a hannunta sai sintiri take tana neman layin imad dayaki shiga.
Anan ma wani sabuwar masifar tasha awajen maminta,za'acewa basu taba samun sabanin fahimta akan namiji ba sai wannan karon,sosai malak tayi fushi tayi kuka sai dai daga bisani data nitsu sosai sai taji ta soma tsintar zallan nasiha da soyayya acikin fadan mahaifyr tan sosai,
But she have to find a way to make her understand dat zata iya rike mutuncin kanta sann bazata taba yaudararsu akan kowa ba.

Karfe 8 na safe yau rufaida ta farka da zafin jiki da zazzabi sabida period dinta dayazo,a dukunkune take tana bari akan katifar yakumbo wacce itama ba wani dadin jikintan takeji ba amma haka take daurewa tayi mata komi.

Ruwan magani da kunun daka mai dan uban qamshin citta da masoro ta dama ta kawo mata har cikin dakin da kyar rufaida ta iya daddafawa ta mike  daga kwance ta zauna da duwawunta tana kallon waje daya kamar wata zararreiya, duk damuwa da tunanin duniya ya janye mata dan haibarta sai wani uban kashin wuya daya bulloko.

Cikin lallami yakumbo ta tursasa ta ta shanye maganin sannan ta mika mata kunun tace mata maza ta shanye dan intana period bata cika iya saka wani abu acikinta,Batace uffan ba Tayi kkrin amsar kofin kunun daga hannun ykmbo saidai bata iya kaiwa ko kusa da bakinta ba sabida mummunn tashin  zuciya dayake maklkleta,take ta soma jin amai amai hanjin cikinta yana hautsinawa da zafi zafi,aman dakan sa ya soma tunkuduwa daga makoronta xuwa kasa a dakin,sai da tadanyi kafin nan ta samu karfin mikewa tsaye ta fita tsakar gidan da uban gudu ta zube akasa ta soma gwaza amai mai kara da gigitarwa kamar hanjin cikinta ne zai yu waje,rike da hargagin murdewan ciki ta fashe  da kuka sosai,inda sabo yakumbo ta kusa sabawa da laulayi irinna rufaida abu kadan ya sameta yanzun saikaga ta birkice sosai tanata amai ko kuka,tun da aka raba rufaida da jin dadin rayuwanta ta sauya,ummanta da kawayenta duk bamai lekowa,ya zamto babu mai taya yakumbo lallashin ta daga rikicin tsangwama da fitanar gulma na yan anguwar datake fusknta matuka face malamin su Abdul jabbar,shima din basu kyaleshi ba suka saka rayuwar sa agaba har aka lakamai sharrin cewa jikin rufaidar kawai yake nema yy lalata da ita,hakan ya jawo dan dolenta ta hakura da zuwa wajen sa daukar wani karatu saidai tayi kominta acikin gida..

A dunkule ta durkushe kafafunta awajen cikin wani irin jigataccen yanayi

Ga murdawan ciki ga azaban ciwon kirji da kai amma babu abunda yake yawo a kwakwalnta takejin ciwon sa fiye da tsananin damuwa da tashin hanklin dayake bibiyar rayuwata na kunci.

Sau tarin yawa takanji kamar ta kashe kanta da kanta,sai dai inta tuna yin hakan babban asarace saita hakura ta kuma lazamci tuba.

Atakaice gani take kamar babu wanda zai taba iya fahimtar Abunda take ji aranta sosai ta cire rai akan rayuwa,tayi dan dana sanin zuwanta duniya bana wasa ba..

Tuno da shafin iyayen ta dayay kama da sun mance da ita a doron duniya yasata kara ragwabewa cikin kuka ta zube ragwaf har kasa,tari mai karfin data somayi babu kakwatawa ya saka yakumbo yin ihu ta hankado waje a rikice ta tsaya a
Kanta tana dube duben bakinta koda zata ga aman jini danta gama sawa aranta cewa rufaida ta riga ta kamu da ciwon zuciya"..
Ganin aman ne kawai yake fita saita ji zuciyarta yay sanyi,sannu rifaida bari inje in dauko hijabi muyi asibiti
Hala zasuyi miki Alluran cin abinci da yunwa sosai acikinki bari inzo kinji auta na, cikin wahalalleyar yanayi ta gyada mata kai
Yakumbo tana qusa kanta cikin dakin aka wani bankado kofar gidan da uban karfi aka shigo har ciki babu sallamu

aman bai barta tajiyo sautin kowa ba kawai ganin mutum turus akanta a tsaye tayi
Koda bata dago kanta ba tasan wani walkancten kallo ake aika mata daga sama
"Ke!!! Ke kuma aman me kikeyi haka?Cikin wata gigitaciyar tsawa suhan ta daka mata tsawa amma bata damu ba jikinta na rawa rawa ta dago kanta da sauri cikin mugun jin farincikin jin muryan yar uwan ta.da murynta na kuka hawaye na saukowa yuuu a cikkn kwayar idanunta at same time tana kkrin yin murmushi tace "Adda..Adda suhan,wani kuka kuka mai tsuma ne ya kufce mata tundaga kirjinta tana kkrin toshhe wata mummunan tari,tace yakumbo ki fito ga Adda na ta zo..Adda suhan sannu da zuwa suhan dakeji kamar ta zuba wuta ta qona rufaida atake ta hankade da kafa ta fado taci da bakin ta cikin aman
"Zan mangahe miki baki Inai miki magana kina share ni..nace aman me kikeyi?wani abun kunyar kika sake jajibo mana ciki kika je kika kwaso ko?
Allah ya isa tsakani na dake rufaida taurin kan ki ya jawomin duk ukubar danake fiskanta arayuwata,miji na sabidake ya gudu ya sake ni,duk kinsaka an tsangwame ni.
Dan gidan san danake zama ma matarsa ta siyar Har niyau za'a ci ma mutunci a watso ni waje.?Allah ya isa tsakanina dake rufaida wallhy bazan taba yafe miki ba muguwa kawai mai arnen taurin kai ai saiki gayamin abunda kika tsinta da kikyiwa baba taurin kai akan auren naki duk gari kinsa an tsangame mu halama wanann laifin da kka aikaa har yayanmu da basuzo duniya ba sai yashafa..
Kin cuce kanki kin cuce mu,anan saitay shiru ganin yadda rufaidar ta sunkyar dakanta can kasa a mugun daskare tana zubda magudan hawaye acikin kokawa da numfashin ta dake shirin daukewa,tausayin yar uwanta sosai ya balbale mata xuciya sai kuma ta fashe da wani zazzafan kuka

Yakumbo tuni ta fito waje bayan ta gama jiyo abunda suhan take fada tuni zuciyan ta ya hau bugawa tashiga kallon yanayin su duka

Saurin rage tafiyarta tayi tana cewa hasbinallahu wa neemal wakeel
Juyowa tayi ta dibe rufaida taga kamar bata motsi..
Hannun ta ta daga sama cikin yin mata fada tace Toh Alhamdullhi tunda kin kasheta saiki san nayi da gawarta

Suhan Zatai magana yakumbo ta watsa mata wata makahuwar mari.
Wanda yayi daidai da tsinkayor wata bakuwar sallamar  da aka doka dagata bayan su,atake dukan su suka juyo banda rufaida data kulle idanunta gamm gamm cikin juyayin jiri jiri da duniyarta yake mata tanajin  tsananin zafin abunda yar uwanta tagama furtawa akanta har cikin zuciyarta wanda dafinsa yafi na kowa yin mata zugi,sake baki yakumbo tayi tanai ma Anty fareesa kallon bakunta suhan kam sarai ta gane ta amma duk da haka bai hanata durkushewa kasa da gunjin kukanta ba,bude baki ykumb tayi da niyar yima Anty reesa sannu da zuwa,Caraf idanun Anty fareesa ya fada kan rufaida datake kwance cikin ruwan amai lifelessly tamkar wacce bata taba numfashi arayuwan ta ba,"da sauri ta isa wajen ta durkushe gaban ta cikin yanayin nuna makurar damuwa da tashin hankli,a sukwane ta tallabo jikinta tana cewa subhanallh rufaida meya sameki haka?
Jin shiru yasata ta dago kai ta kalle yakumbo tace"Kaka meya sameta ko batada da lpya ne?.
Cikin matse murya ykmbo ta juya ta kalle suhan tace gata nan ai saiki budi baki kiyi mata bayani,Nide wallhy babu ruwana daga shiga daki in dauko mayafi naji wannan babban bazan tana hankada mata munanan zagi
Har cewa take bazata taba yafe mata,yanzu fisabillahi in wani zaiyi wa rufaida  wannan abun sai kema kiyi mata?yar uwanki dakika sha nono kika bar mata
Ubanwa ya jefata cikin wannan ukubar inba Mugun mijinki ba,ai daba dan shi ba da ba haka rayuwar rifaida yake ba,..Allah ya isanki ya koma kanki katuwar banza marar wayo,..
Kuka yakumbo ta fashe dashi wiwiwi ta juya a rikice ta shiga daki ta dauko ruwa da tabarma ta shimfada akasa wa anty fareesa, anty fareesan datake kan kallon suhan cikin kankanin lokci gama fahimtar komi shiru tayi batace musu uffan ba tahau tattaro rufaida dake kasa suka dawo kan tabarman ta shimfideta akan kirjinta,sai data zauna ta rungume ta ajikinta tsammm sannan ta san da cewa ma tana jan numfashi..

Tattara nitsuwarta tayi ta hau gaishe da yakumbo at same time tana lallashin rufaida,har iyanzu suhan kuka kawai takeyi batace ma kowa uffan ba suma basu kulata ba.

Anty fareesa dakan ta ta shiga gabatar da kanta wa yakumbo har sanda ta ganeta sosai

Wani sabuwar gaisuwan ta sake mata tun daga farko tana tanbayarta mutanen gidan su bayan sun kammala gaisuwa,nan ta fara labarta ma Anty fareesa duk wani halin da Ake ciki wanda dukansu awajen baimusu dadin ji ba,a daddafe suhan ta miqe ta bar gidan ta nufi can gidansu da niyyar koma yayane saita kai kukanta wa umman su,dan haryau gani take rufaidace kawai ta cuce rayuwarta ba wani ba.

Duk surutun nan Da akeyi rufaida na manne da kirjin anty fareesa,sanda yakumbo ta gama surutan ta sannan Anty reesa ta janye ta daga jikinta ta kamo hannayenta tana kallonta har suka mike tsaye,juyawa tay tace kaka zan kaita asibiti a dubata ta, yakumbo cikin tabe baki tace asibiti kuma?wani abune ya same rifaidar?kinga,al'adarta ne fa yaxo sai wannan shashar dadanta datazo ta qumsa mata bakinciki banda haka rifida kalau take babu wani ciwo ajikinta
Anty fareesa tace karki damu kaka shima al'adar ai za'a iya dubawa,zip din jakarta ta bude ta debi kudi mai uban yawa ta damkawa yakumbon a hannu tace mata takula da gidan yanzu zasuje su dawo.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top