chapter39


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 39

Acikin kunnenshi ta bude kofar dakin duk da tunani mai nauyi da zuciyarshi takeyi bai hanasa shaqo yanayin shigowartan ba, waje ta nema ta tsaya durus tana kallonsa dan bazata iya cewa dason ranta ta biyo bayansa awannan lokacin datakeji kamar ba a cikin hayyacinta take ba.
Rashin iya bude idanunsa dayayi ya sa wajen ya dauka da wani irin shiru sam Shigowartan bai katse masa tunanin datazo ta iske shi yanayi ba,tun daga ranar auren sa har izuwa yau inyatuna,wasu sukance sukanji kansu kamar a saman gajimare tsabar kwanciyar hankli da farincikin auren su amma shi haryau baisoma jin wannan ba,aure dai yasan yana cikinshi da wacce yake ganin kamar yana so amma bazai iya cewa zuciyarsa a nitse take da aurensan ba shiyasa ma sam ya kasa gane ma kansa bare ma ajega y fahimce matar sa Ai'nau,alot of times in his heart yakanji matukar dana sanin auren ta,saidaii tabbas akwai wani bangare a zuciyarsan datake hanasa tantance komi saiyaji kamar eh dagasken sonta yake yi kuma bazai taba iya rabuwa da ita ba,shidai yasan acikin Rudani yake rayuwar sa Ko ainau ta fahimce shi ko bata fahimshi ba oho,shikadai yasan abunda yake damun sa aransa yanzu.

Ainau dake tsaye kansa bakinta gumm bata iya ko jan numfashi kwararra, kokowa take da fushinta dan kar zuciyarta tayi bindiga ta fashe ta tarwatse bare ajega ta sauke masa tulin ruwan balain datayi dako tsawon kwanaki dominsa na musamman.

Tura yakai bango,in akwai makurar karshe to tabbas haqurinta akanshi yakai yau,yakamata ya fito fili ya gaya mata shin ita mene ne awajen sa dan bata gane meyake nufi da ita ba.

Karkkarfan ajiyar zuciyar daya kufce mata badon tasoba ya tursasa shi adan dole ya bude limsashu kuma gajiyayyun idanunshi wanda suka so suyi luhu luhu tsabar nauyin magananun zuci da zuciyarsan ta dade tanayi ita kadai.

Ainau Tana daf da bude bakinta ya miqe tsaye cikin sauri mai nanike da jarumtar kasaitar sa dake saurin saka yankewar gaba,a nitse ya karaso har gabanta yana kallon figaggiyar nityn data sakan up and down fuskan sa adan daure, cikin wata girmanmen muryansa data fito da yar tashen masifa har yana lullumshe ido yace
"I have had enough of your nonsense A'inau!tunda ke baki da hankali daga yau kar in kara ganin ki awani waje agidan nan da wannan shigar banxan.
,kaiwa nan ya dakata da maganan yay shiru, sannan yaja numfashi game da sassauto da muryan sa kasa kasa yanai mata kallo mai dauke da tsantsar comand da nuna ya isa,araunane ainau ta sadda kanta can kasa,da gefen idonshi ya kara jefo mata wani kallon aransa yana ta mamakin Yanayin ta yace"ohh ok i think is time for u to go park ur things ..zamu koma can gida kawai..
Adan hargitse Tace what?bai kulata ba yana kkrin juyawa yace "u heard me"..

Abbu is already back in nigeria  bazan so yazo nan ya same mu agidan nan ba..ba amfanin zamanki anan.

Yunkurin juya mata baya yake bayan ya kammala furta hakn sai caraf ya tsince ta agabansa a mugun masife, kwayar idanunta ya kalla yaga wai har sun rine sunyi wani rau rau cike da ruwan hawaye tamkar zasu fashe su watso waje.

Wani irin kallon data watso masa saida yasa gaban sa ta dau sautin bugu ya kara maida hanklin sa yana kallon ta dan yaji me zatace ,a zafafe amma bada muryan fada ba tace mishi
"Daga ina kake,Har kadawo ko?yy saurin dauke kansa akanta,ita kuwa kkrinta ta sarkafe kwayar idanunta anashi maybe in ya kalletan zai iya dawowa hayyacin sa yagane metake ciki dashi,dirin hucinta yasa shi lumshe idanunsa kadan snn ya kara budewa ya juyo sai yanzu ma ya tuna cewa ashe bai sanar da ita tafiya mission din dayaje ba,naw he got why she look dis furious aranshi yay wata malalaciyar kwafa shi baiga ma dalili ba,meye ne dan ya tafi bai sanar mata ba,yaga dai bayau aka fara ba,yasan she hates his job so bai wani dara sa da sai ya mata bayani ko yabata hakuri akan dan yaje ba,
aganin sa ainau tafi kowa fahimtar cewa  baya cikin jerin majajen da zasu sanar da kowa abunda ya shafi hurumin aikin su..its a big mission for god sake,dama can metake so yagaya mata mtsww,ackin dakika ya gama ayyana wayannan zantukar aransa shikadai yanai mata kallon batasan meyake mata ciwo ba.

"Ka manta haqqin aure ne a tsakanin mu mufrad?im ur wife, and i dersev to know ur wher abouts no matter what..tafada tana stressing word din no matter what din,"u left me for a month ba kira ba sako u think hakan dakayi min adalci ne?wani dauke kansa dayayi a shashance yasa duk yadda taso tayi dauriyar sanda muryanta ya sarke mata wuya tanajin zafin wani kulluton wuta yana toshe mata hanyar numfashi,wani kuka kuka ta soma ji bazata yana shirin kufce mata,a kassare ta furta a hnkli,.."and all u got to say to me first is banada hankli dan kawai kaganni da nity a dakin yar uwata?Yawo nakeyi dashi agidan na  dazaka cemin banda hankali!?

Hawayen datake dannewa su suka soma saukowa yuuu suna bajewa saman kumatunta suna gangarowa kasa,wani irin rawa hannunta da muryanta yakeyi at same time ta kafe shi da jajayen idanunta tana kan kallonshi wai duk da hakama dauriya kawai takeyi,cikin kunar rai da zafin zuciya ta cigaba da sheqa masa wutar takaicin dake fitowa daga saman zuciyarta tana yagashi da manyan kalamai.

Tsiwa da Masifar data dade batai masa ba ta rinka kwararowa agabn sa tana karanto masa babi babi da shafi shafin laifikan daya tara akanta da haqqin ta dayake dannewa,sosai taji idanunta sun rufe tama kasa control kanta,fushinta ya nuna sosai duk dama bataso ba,saidai batayi tsammanin har ta tara fushin nata yay nisa hakan ba, da manyan baqaqen maganganu da tijara ta karemasa
"Kafada min matsayi na wajen Ka mufrad,im tired of beign a nuisance in ur life,..idan bazaka iya zama dani a matsayin matarka ba ka sawwaka min wallhy bazaka dake ni kahani kuka ba.

Ta dade tana magana dashi anma baice mata uffan ba,sai ya kau da kansa gefe ya tsinke cikin wata salon rigima ta kasaita datake masa azaban kyau tana fidda sirrun jajitacen kwarjiinin sa,take ya turmutsa yanayin sa izuwana wanda maganan nata baiyi ma'anan da zai ma shigesa ba,while deep down within him yasan akwai abun dubawa game da fushin nata,harda da kalaman danne haqqin datake furta masa ayanzu..

Ita kuwa yanayin sa da bai nuna damuwar sa akan abunda take cewar yake dada zafafa mata kai yana hatsala ta.

Itada ta tasha cin alwashin bazatayi masa kuka ba?wani wi wi wi taga kanta tanayin masa kukan yau,She became soo furious with her self also haushin sosai tabawa kanta da kyar ta aro qarfin jarumtar sann tadan yi shiru .

Bai kulata ba kuwa saida tagaji dankanta tayi shiru Juyowa yay ya zuba mata idanunsa da suka jima da sauya launi yanai mata kallon da bazai iya fassarashi ba..

Ayan mintuna da basu wuce Dakika ba ya dauka yana kallonta har cikin kwayar idanunta baice mata uffan ba ya juya ya tattara phones dinsa ya cusa daya a aljihu ya rike daya a hannun sa ya a daddanawa, batare da ya kalleta ba ya jefa wayar a kunnen sa cikin gyaran murya yace"where you at?ta cikin wayar aka ce masa
"Gwarimpa",daga jin haka ya sauke wayar a kunnen sa ya datse kirar,ya juyo da mamakin ganin wai har yanzu ainau tana tsaye,dan karamin smirk yay sannan ya sauke ajiyan zuciya,da yayi niyyar cewa wani abu amma harga Allah yasan bazai taba iyawa ba..he think he is too matured for this mema zai gaya mata,a dokar sa baiya bawa mace hakuri alokacin datake hargagin raini da fushi.Beside shi baiga ma abunda yakeyi wa ainau data zafafa batun ba,inde dan haqqinta ne yaji ai zai gyara,amma ko da wasan wasa bazai dauke raini da cin fuska ba,yana gama ayyana hakn aransa Ya wani hade ransa tamkar bai taba murmushi a rayywar sa,tahowa yy zai wuce ya nifi kofar, ainau ta rufe idanunta cikin sauri tayi tsam ji tayi kafafunta sun kasa daukarta, jiri ne ma yake na neman wainato kasa, dan tamkr ta fasa ihu ta yanke jiki ta suma dan baqin ciki haka ta dinga ji a cikin zuciyarta.

Kiris take jira ya fita baice mata uffan din ba kuwa da wallhy saita nuna masa asalin wacece ita.

Yana rike handle din kofar kamar wanda ya tuno da wani abu ya juyo ya kalleta.
A hnkli Yace,can u put urself together and stop being over reactive?,nifa bangane abunda kike nufi ba,look im tired of u okay?,tafiyar danayi aiki nake tyi ban ma huta ba,im sick of u being childish Aynau,pls maganan nan Ya kare daga nan,daga kinfita ki rufemin kofa nizan wuce wani waje..
"U got me?yatsar dayake reto ta kalla sann ta sunkuyar da kanta can kasa

Muryanta na fitar da amo marar dadinji, sai dai babu wani mummunan kalami dayaso fitowa a bakinta,yanayin kallon datake masa zaka fahimce cewa taji ciwon kalaman sa har kasan zuciyarta ahaka tana ji tanagani yasaka kai yay waje..

Rasa yadda zatayi taji tayi banda dan uban karkrwan da jikinta yakeyi tsaban bacin rai,a haukatacen yanayi ta fito fuuuu cikin sauri ta bude kofar dakinta fado a dakin bata tsaya jiran komi ba tawuce wajen scroll direct ta bude ta hau tattara kayan sakawarta tana jibgasu akan gadon ta,babban akwatin dake sama ta fitar ta bude ta hau dura kayan da sauri cikin tsananin fushi kamar da su take fadar,sanda ta gama shiryawa tsaf snnan ta shiga rabza kuka gaba daya ta rasa yadda akayi ta lalace har haka,saken datayi wa mufrad yayi yawa,harga Allah bazata iya cigaba da jumre halayyr sa ba saidai in son datake masan yayi ajalinta amma dole ne ta kwato kima da mutunci awajen sa wanda take saka ran baisan dashi ba.

Bangaren zarah kuwa tun fitar Ainau bata iya tsinana komi ba ta koma bakin gadonta ta zauna game da sauke wasu gajiyayyun numfashi mai tafe da sautin makurar kasalar dake tattare da gabobin jikinta.

tana zama a bakin gadon ta rafka uban tagumi dagata cikin kwakwalta ta hau yin lissafe lissafen abubuwan da suke gabanta da wanda zata aikata nan gaba,tuno da yau tun farkawar su da asuba bata samu duwawun zama ba suka nausa kauyen barass wajen  malamin zeee zee datayi mata alkwarin zata kaita ajiya in suka kwama tare,a iya wahala kam yau taganshi ta kuma jigatu a hannun kowanne. Su dan banda azabar kwana da jarabar cin da xee tayi ta mata harda yar bulalar da malam yasaka aljanunsa suka rinka shauda mata  wanda tuno da fuskar su kadai datayi yanzu sanda tsigar jikinta ya tashi jikinta yahau rawa,gashi nan dai malami ne har malami,zaka gansa tsaf da yar dattijuwar rawanin sa,ga wani nitsatsen fuskar kamala irinta manyar hafizai daya aro amma kuma hmm har iya yau dai bazata iya cewa ta taba arangama da baqin arne irinsa ba.
Dan Daga isarsu wajen sa yahau labarta mata komi dake nanike a kasar zuciyarta harda yaudarar ainau datake yi arayuwarta musamman indata amshi kudade wanda wani boka ko malami bai taba zamowa soo current kamar wannan malami ba,dan a yadda yake tsilalo bayanin rayuwarta in details game karamin kwakwla zaka iya cewa babu shakka shiya rubuta littafin rayuwarta.
"Yace ma zarah tabbas zatayi nasara kan batun imad kuma qaddarar ta bazai taba zamowa irnna yar uwanta ainau ba,takuwa ji dadin hakan sosai,duk dama ya kukkushe karfin tauraron nasararta, yace mata batada farinjini da sa'a dole ne saita bi sharudan sa da dukan imaninta,nan ma bata damu ba dan bashine ya soma furta mata hakan akaro na farko ba ta sha jin hakan abakin sauran bokaye..

Saidai fa da alamu malamin baras din nan shi nadaban ne koda daga yanayin yadda taga zee tana mugun tsoron sa tana kafafa dashi tana dabbaka sa komi yace bata musawa tasan sun iso gaban makura

Tun akan hanyar isowar su zee take ce mata ta nitsu dan alfarman ta kawai zataci,ta bata labarin yadda takeyin zaman jiran wata biyu kafin layin samun ganin sa yake zuwa kanta yanzu hakama abunda ya kawota abujan kenan.
Zee ta saba da malam amma itakanta bata cikin samun karfin zuwa wajen sa sai intayi babban kamu dan akwaishi da cazar kudi

Sharudan daya gindaya ma zarahn ba wasu masu sauki bane,awajenta ma gani taje yay mata mugun tsauri halama bazai yuwa ba amma ahaka ta amince dan dolenta tace zatayi ya kuma jadadda mata cewa ta guji abunda zai iya zuwa ya dawo.

Kudin yanka da magani da kamun zuciya dayace zai mata a lissafi saida yaci million hudu wanda karshenta zee dinne ta biya mata a matsayin bashi,wanda Ayanzu shikadaine zaisa ta nemi komawa site din ainau amma badon haka ba da sai dai ainau taga anayi dan mamaki tayi niyar shayar da ita bana wasa ba,yau data zo taga alamar samun nasara akan imad, duk wani tsoronta saiya kawar..

Tana cikin wannan tunanin saiga karar bude kofa tana daga ido taga ainau na kkrin shigowa da akwatuna har biyu,
Kirijnta na bugu ta mike tsaye"me hakan yake nufi,ta dafe goshi cikin takaici karde taje tayi masa rainin dayasa ya saketa ohh god Ainau is just a mess.

Ain tana aje akwatin tace zarah ni zan wuce...pls dont tel anyone dat u knw my where abouts kawai kice musu baki ganni ba kibarsa shi yaji dasu

Cike da kullewar kai
Zara tace ban fahimceki ba what happen inazaki
No no pls indan abunda nayi ne kizauna abunki wallhy zan bar maki gidanki

Hawaye akan sauka akan fuskar ainau,tace is not about dat zarah..da
Kizauna da karki zauna duk bata shafeni ba nide kawai xan tafi nabarshi.Mufrd ya rabani da komi nawa,ya rabani da kaina ya maidani wata kaskantacciya,ke ban cika miki burinki ba nima nawa bai cika ba gara ni na hakura kawai,bazan iyaba walakancin sa kullum daduwa yake is asif dukan abunda mukeyi akan sa warware wa yake zarah nasha mamakin yadda kika rufe idanunki baki kallon baqar azabar danake kurba agidan mijina. mufrad now treats me like a trash,he had the guts..da hakane kike son aure irin nawa,auren wanda baisan da abunda kakeji aranka ba?i tried so hard,maiye mace takeyi wa namiji wanda banyi masa ba,and i still mean nothing to him Wannan rayuwa ce?
I can feel it,zarah i can smell from far dat banada wani kyakwan matsayi a zuciyar mufrad.

He dont even care About my feelings kamar ni ba komi bace haka ya daukeni im starting to regret this marriage wallhy na rasa yadda zanyi na ficceki shi araina ne da tuni na qona soyayyarsa da wuta yayi qurmus kodan na huta ma raina.

Kuka sosai ainau ta fashe dashi

Shiru zarah tayi tsaban yadda jikinta ya dau wani mugun sanyi,gaba daya sai taji tayi lagwas tana jin sautin kukan yar uwanta dake kokrin sosa mata zuciyarta matuka,bata iya motsi ba har sanda Ainau ta juya zata fice a dakin cikin sauri ta kamo hannunta tajata suka zauna abakinan gadon ta hau rarrashinta,duk da son zuciyar irina zarah harga Allah saida taji tsananin takaicin yanayin yadda dataga ainau tana kuka cikin axaban damuwa ,da kyar ta lallabeta tayi bacci,tana ta lallbarta cikin bata baki tamkar kamar basu suka gama fada da juna ba,gefe da ainau  tazauna cikin sauke wata nannuyan ajiyan zuciya,arayuwa ita mace ce mai son kashe tsuntsu biyu da dutsi daya,take brain dinta ya hau bata cewa lamarin a'inau baya bukatar wani boka ko maganin mata ayanzu, she must find away to involve imad tasan in harshi ya fahimce ta dole ne sukaga canji ta wajen captain,saidai ita ba sulhunta su take so ayi kai tsaye ba,she just want to blackmail mufrad into seeing things.

Agefe kuma so take taga karfin ikon aikin da akayi mata akan imad Shin izuwa wani xtent zata iya langwasa shi?dan malam yace mata dole sai ta dage akansa sabida yana da yawan sonyin ibada musammn sallah da zhakr,daga nan wanka ta fada zuciyarta cike da tunanin yadda zata tunkare abun

Bangaren mufrad kuwa tun daya fice agidan bai kara dawowa ba Imad yana dakinsa yana bacci yaji an jijjigo shi da sauri ya bude idanun sa Sai ganin zarah yay ta wani sha uban ado tana zuba wani maitan qamshin  turaren ta kuma kuresa da wani irin wagaggen murmushi wanda tabbas da a cikin hayyacin sa yake dasai yay iritating dinsa,mikewa zaune yay cikin ja da baya kadan aransa yana  mamakinta jin qamshin turaren aljanu dayaji dazu yana bacci tukunnama wai yaushe ne har suka soma wasar shigowa har dakin bacci da wannan yarinyar?yasan dai ko da wasan wasa abun nasu baiyi nisa har haka ba,iyaka ayi hira a falo aje yawo kadan asha drinks a pub adawo,sai dai ayanzu baisan meyafaru dashi daya somajin normal da itaba, just today ya soma ji kamar dama tuntuni yasanta,yawan haushinta dayake ji aransa ma sai yaji kamar ankawar.

Zama tayi gefen sa tana murmushi kamar wata mayyar datake shirin cinyesa Tace,hey bby Yaufa Zuwa nayi muyi hira jiya bakaganni bako?
Tokaidin ina kaje baka fadamin ba
Ya rasa ma mezaice mata,ya dan dafe kansa cikin sakaltacen yanayi yy kamar baiji metace ba can yahau magana kamar dakansa kawai yakeyi yace,dnt knw wts wrong with me sai bacci naketa yi
"Mufrad fa..?kafadun ta ta dage tace Uh i don't know
Tsaki ne ya kufce mai ya dau wayarsa batace masa uffan ba harsanda ya kira layinsa ringing daya xuwa biyu raga wai har an dauka
"Kai ya haka kana ina?daga ta dayan bangaren mufrad yace im in urgent meeting zan kiraka pls,bai ce komi ya ya katse wayar tare da maida kansa jikin gadon yana mai lumshe idanunsa ahankli
"He knws we are supposed to go out now,jiranshi fa nake amma wai harya fita,..zarah tace hmmhmmm,sai kuma tayi tsuru tsuru tana bin rufaffen idanunsa da kallo kamar wata kamilar asali, dacan batayi niyyar amsa shi bama amma hakan tamkar wani hanya aka bude mata wajen shigar da wasarta zuciyar sa game da Lamarin ainau,cikin wani makirtaccen salo ta nitsar da muryan ta kamar wata mutuniyar kirki,a nitse sosai cikin yangataccen sautin murya tace masa"..toh kayi  hquri mana,captain will alwys remain captain,kasan hakan fa halinsa yake..dakai da ainau bansan meyasa kuka kasa fahimtar sa ba,im sorry but His work is actually his core priority bai cika daukar zafi akan rayuwar kowa ba...i dont know,but i think is not fair..sai tayi kamar zata futta wani kalma agaba but data kalle shi taga kamar jintan yakeyi dagske sai kuma tayi shiruu shima shirun yy yana lura da ita,cos actually bama jin ta yakeyi har can can din ba,gani yake kamar basu fahimce mufrad dinsa bane shiyasa suke judging dinsa akan haka,but yanayin yadda yaga ta karashe magananta very dramatic yasan akwai sauran bayanai boye abakin ta, as a very good observant sosai ya fahimce wani abu ya auku yau,dan tun daga language din fuskarta ta ya soma dagowa,yanata jira yaji ta hau barbada masa zance kamar yadda ta saba zuba masa saiyaga kuma tayi shiru shikuma  yasan bazai iya tambyarta dan yaji abu a matsayin gulma ba bayama son ya soma wannan wasar da ita,gyara zaman shi yy ahankli yace.."Look don't say it like dat okay,muff is actually a great and a very very veryyyyy caring person.

Harda dafe kirjinta ta gwalo ido waje Tace carring ke?tab di..i knw he is great amma Caring fa kace?U sure ure not getting it twisted?
Anywys..dama sallama kawai nazo nayi maka inaga kamar yau zamu wuce kano gashi ko lambar wayarka baka bani ba so saiyaushe kenan zamuga juna...?

Tunanin abunda tace Bai iya barinshi ya amsata cikin sauri ba,sai ga ta harta matso kusa daf dashi cikin wani irin kisinniyar salo tanai masa kwarkwasa da ido cikin salon yauqi sosai,tamkar zata goge fuskar shi haka ta hankado ta karkarya sautin muryanta akan fuskan shi...
"mad,baby i will like to see you again dan Allah.Zanyi farin cikin in kawance mu ya zarce sanayya,i hope u knw ure speacial to me?

kirjinshi yaji ta amsa da bugu data frta mai hakan dan
Kwata kwata bai gane mata ba,saurin kwace jikinshi kusa da ita yyi ya dire kasa daga kan gadon ya tsaya daga tsaye,tun kan ya gyara tsayuwar sa ta kara darsa masa yan iskan idanunta tanai ma siffar jikinsa wani irin jarabben kallo"..hannun sa ya cusa duka a aljihun wandonsa dan baiya bukatr ta gane halin dayake ciki,he is seriously panting from d inside out of  fear and confusion saiyanaji kamar ba shi bane,ga wani uban bugun zuciya data dameshi matuka..yace
"Ina zakije..i mean keda waye?Saida tadn ja sann ta miqe tsaye tana duban sa da kyau.Tayi mirmushi ayangace
Tace,forget it..in baka ganni ba kawai kasan tafiya mukayi,so Zaka ban numbar taka ce koko bankai wannan matsayin ba,baice mata uffan ba ya amshi wayarta ya rubuta mata 11 digits mtn line, a very special number duka five ne karshen sa zero guda biyu, altho itakam ta dade da haddacewa amma bai hanata nuna masa jin dadinta ba.

Mayar mata wayar yay akan ta saka suna da kanta Batayi kasa a giwa ba ta amsa ta narka masa flashing
Da sauri ya nufi wayarsa dake kan gado ya dauka duk tunaninsa mufrad ne,daf yana shirin dagawa sai ta katse
Ya juyo ya kalleta adaidai lokcin ta kashe mai ido tace.."Dats my number.. dan dage girarsa yy Yace ohhh..To wani suna zan saka maka,hnklin sa nakan wayar yace "imad'..tace no no,suna mai dadi nakeso zan saka maka anawa wayar
Nima ya kamata ka samin special name pleasee,sai anan ya dago ya dan kalleta ahankli sai yace ok sai yay saving number nata da letter "Z" kawai
Kamar ta sani kuwa ta kwace wayar a hannun sa ba zata,tana ganin abun dayayi ta bata ranta tahau bubbuga mai kafa aksa I dont want this name baby dan Allah ka zanca..adan daburce da mamkinta yace what for?idanun nata dayasha kwallin sihiri ta kara darsawa acikin nasa babu shiri yace ohh ohk wateva kisaka dakanki kawai murmushi tayi dan har ranta tanajin shaukin farincinki mai tafiyarwa ko ayanzu tasan tabbas malam yay mata aiki akan imad dan itakanta tasan imad bai san meyakeyi sosai ba.

Da capital letter ta hau rubuta suna agaban lambarta tayi masa saving da "Loml' da emojin heart agaban sunan,data gama saita nuna masa baice uffan ba yadan kyabe baki,"..
Yana amsar wayar tace To ni zan wuce
Yace Keda waye zaku tafi?tace dani da sister..u know i don't want to interfer but my sister just came in dazun nan tana ta kuka tace min kawai na shirya wai gida zamu je,cike da mamaki Imad yace what?kukan me wani abu ya faru a gidan naku shine bazaku sanar da kowa ba..bakinta ta tabe cikin salon shashantar da zancen tace a'a bbu abunda ya faru,but i think all is not well tsakaninta da captain shine kawai..actually tace ma kar na fadawa kowa zamu tafi,sabida in samu lambar wayan da zamuna gaisawa da kai yasa nace dole nazo nayi maka sallama.Maybe in sun shirya ayn zata dawo amma nikam inaga rabuwar mu anan kenan,yar dariya yay sann yace meyayi zafi haka harda wani rabuwa?whats going on u sound really ridiculous pls clear up..

Cikin salon jan aji ta sauke ajiyar zuciya
Tace okay,but hey wannan siirrine tsakani dakai,bai amsa mata ba yace go'on,kamar da wasa ta nemi waje bakin gadonsa ta zauna,"..within some spec of 10 minutes har tagama watso masa kanun labarai.

As usual Duk sauran abubuwanda tace akan muffy bai wani shigesa  har can can ba but He was soo shocked to hear dat wai har Ainau ta tattara kayanta zata bar gidan batare da sannin muffyn ba..

He tried his best danya fahimtar da zarah,but no hnkkinta ma baiya kan bayanan sa,cos dats not her mission dama can zuwa tayi ta baqanta mufrad a idon sa da sauran yan uwansa,she was strongly going againts d fact dat ai yana dannewa yar uwanta haqqinta na aure,sai nanata maganan take tana karawa da cewa yana walakanta ainau sosai wasu kalamn nata ya tsaya ma imad aransa fiye da yadda tayi zato.

"Can u imagine ace mijinta ya dau wata guda wajen aiki bai sanar da ita ba,ya dawo kuma yahau ta da masifa waidan ta fito da nity,no explanations no apologies gaskiya haka ba daidai bane..

..akan wannan batun babu abunda bata gayama imad akan yadda mata sukeji in akayi sex starving dinsu ba,har saida ta cimma burinta wajen convincing dinsa, ya somaji aransa kamar yes tanan fannin kam mufrad dinsa bai kyautawa.

Hade da rokonsa data dingayi akan karya fadawa kowa maganan yasashi karajin tausayin Ainau aransa,tace pls baby dont tell anyone abot this She wil get upset with me"..kasan halin Ainau she alwys wanna keep her things private konima bazanso ace kowa agidan nan Yagane cewa batajin dadin zama da mijinta ba..ahaka ya amince mata but
...he got no choice face ya roketa alfarma shima,yace tadan bashi kwana biyu zai gwada tunkarar matsalar dakansa takuma masa alkwarin zata langwasa Ainau ta janye kudirinta na tafiya ta bashi time taga mai zai faru nan da kwana biyu
..and he asurred her da komi zaizo karshe...xarah taji mugun dadin wannan game din data buga duk dama bata nuna masa komi ba har suka rabu.

Ranar kasa samun nitsuwa yay,duk dama ya lura da zarah,har aka fito cikin family membrs yin gaisuwa bata nuna alamun komi agaban kowa ba,ganin harda ainau wajen da suka sauka yin breakfast
Yasa imad yay tsammanin hala zarah ce tayi convincing dinta

Normal aka kare break kowa ya shirya ya fita aka bar hjya adada da hjy goggo wacce acike famm take da fushi da komi na gidan,gani take kmr duk karya kawai ake mata tin tunin nan zaidu yana kano bawani tafiyar dayay,hala uwarsa hasiyace kawai ta rabasa dasu.

Yau zarah bata damu da ficewar da imad yay ba dan dakyar ma tayi convincing din Ainau suka bar gidn sukaje Har office  tare dan tasa anan ne kawai a zasuyi maganan su a nitse  basai wani yajiyo su ba.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top