chapter27


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 27

Agaban wata katotuwar gate din wani kimtsatsen gida mai kyau da yelwa sukayi horn mai gadi ya taho cikin sauri ya bude musu kofar gidan suka shigo har ciki,Kai tsaye mufrad ya karasa dasu parking lot tun kafin ya kammala parking imad ya hau saka wayoyinsa a silent dan zuwa yanzu bazai iya kirga yawan miss calls din daya shigo wayarsan ba, Shiga cikin gidan sukayi kai tsaye Suna baza takunsu a hnkli Mai tafe da tsantsar nitsuwa da kasaita irinna zaratan maza masu ilimi da aji, Inka gansu tare gwanin sha'awa,dake ma yanayin dirin jikin su kusan iri daya ne, banbaci baifi kadan ba,dake shi mufrad yariga yasha Training irin nasu ta sojoji sai yadan fi imad fasalin kyaun dirin jiki harda Dan tsayi,shikuma imad yanada wani irin tsiririn fuska ne mai mugun dauke hankli dirin nashi jikin Bai Kai na mufrad fadada ba dayake gyara nashi dirin yake da gym routine wanda ba a koyaushe yakema iya kulawa ba.

parlour ne mara tarkace amma yana da kyau, wallpaper ne baqi mai zancen sun flower fari da grey zagaye da bangon daga tsakiya kuma akwai fararen kujera masu L shape da throw pillows dinsu wanda suke manya manya saidan karamin round Table da ke gaaban su da Wani sharbeben tvnsu dayakusa cinye rabin bangon...

Wani kamshi ne mai mugun dadi ke fitowa daga falon na turaren halut da sandal wood traditional incense hade da iskan Ac mai dadi da sanya nitsuwa,Suna zama yarinyar data bude musu kofa ta taho da Murmushi a fuskarta a ladabce tace "'Sannunku da zuwa Yaya acikin hausar ta dabai wani gama kama mata baki ba
Imad ne ya dan murmusa ya kalle ta sai ya amsa da cewa sannunki sweethrt,Murmushi tayi tana satan kallon mufrad ganin yadda idon mufrad din yake kan wayarsa stiff yana famar latsawa Baiko kalleta sai dayaba,the girl look exactly like her dad basai antambya kasan yar doc Mehra ce,She is tall and fair,tana da kyaunta na asalin baggara kominta daidai misali a shekaru dai bazata wuce irin sha biyar din nan ba,Karshen ta ita tayi musu jagora suka karasa daga can ciki,Wani bene mai golden rail suka bi suka sauko daidai setin dinning area mai dauke da dogon dinning table shima white colour with little touch of grey Wanda Already an kawata kan dinning table din da manyan kwanuka na alfarma wajen ya karayin haske sabida crystal chandelier dake sama ta tsakiyar su yana fidda wani uban haske...

Haka kawai atmospher gidan yayi ma imad dadi yakuma samasa Wani sassanyar kwarjini a xuciyarsa being around family yana kara masa nitsuwa..

Simple break fast akayi musu plaintain chips french fries na patotoes ruwan shayi mai hade da kayan qamshi da hadadden liver souce,sai tulin deserts an shirya komi a dining din da alaman su kawai ake ta jira

  Cikin nitsuwa yarinyar ta soma jera musu plates da cutleries agaban su da alaman shirin yin serving dinsu..
Ganin yadda take kominta a nitse haka kawai aransa yasoma tuno da yanayin rufaida.

Wani kyakkwan Murmushi ya sakar mata wanda saida tutsiyar Karen fararen hakoransa suka bayyana yace
"Hi sweety I'm imad,and you?
Murmushin sanayya ta maisho masa duk dama bawai saninsan tayi ba da Dan karamin sweet voice dinta tace "Hi,am malak mehra,hannu ya Mika mata suyi musabaha ta maida hannunta baya ta haura sama da gudu tana boye hannun tan,da murmushi imad ya cigaba da karewa wajan kallo,sannn ya dawo da kallonsa Kan mufrad looking at his elegant and alluring look shi Baiko motsa awajen ba,can sai ga yarinyar ta Kara dawowa,nan da nan imad ya maida hanklinsa kanta yanabinta da Wani irin sassanyar  friendly gesture "yace malak right?ta gyada masa kai har yanzun murmushi takeyi cos farat daya taji imad ya zauna mata a xciya,cos imad irin mutanen Nan dat are so cool and jovial,irin masu saurin shiga ran mutunen Nan ne wanda batare da saika shirya ba,awani bangaren kuwa sosai take kallon mufrad,kallo takeyi masa irin wanda bata tabayi wawani da namiji ba dan ya hadu matukar haduwa, ganin kamewar sa da ajinsa takeyi wanda tabbas tasan zai iya saka kowacce irin mace fallen masa Atake batare da yin shawara da zuciyarta ba..

Yana dago idanunsa kuwa caraf suka hade ido tayi saurin sunkuyar da kanta can kasa, muryansa ciki ciki yace wato bakya musabaha da maza Amma kin iya Kare musu kallo ko?
,dada sunkuyar da kanta kasa tayi Jin kamar ta nitse kasa,ga voice dinsa yay mata dadi.

Aje sauran cutleries dintayi tana shirin juya musu baya saiga sallamar iyayen ta daga sama Suna saukowa daga matakala, Doc mehra ne agaba fuskarsa dauke da Wata sassayan Murmushi sai matar sa Anty Ameerah wanda tayi mugun kyau acikin Tsadadden black dubai abayarta dayaji silver stones yana sheki,jakarta silver colour da talkamin sa Duk iri daya...

Da Tafiyarsu mai cike da nitsuwa da Kamala suka karaso wajen imad ya miqe tsaye cikin sakin fuska da murnan ganinsun ayanayin sa cike da zolaya ya shiga cewa Anty meerah kifadi gaskiya anya wannan babe din yarki ce yanaga girman ku daya?
Take take Anty Mehra ta hau dariya tana kallon yarta malak data kasa motsi Doc mehra yy murmushi mai sauti "mekake nufi kanason kace bata tsufa ba kenan ko..
Xugata dai...Anty meerah tace yes now,babu Wani zugi nidai ban tsufa ba,kamar yadda shima baison ya girma nima haka nake, ga mufrad nan ya ajiye mata shi Meyake jira?cewarta Hakan ysa  ya hau Sosa keyar sa baisan meyasa suka dameu sosai da zancen auren San Nan bafa,Daidai lokacin mufrad din ya miqe yana Dan fidda sakayayen murmushi,a ladabce yace"Barka da fitowa Abbu...Doc mehra yace mrning captain katashi lpya?,ya juya Adan kunyace ya amsa da alhamdullhi yace "Ina kwana Anty?dan hararar sa tayi tace sanadiya dai ya jawoka gidana yau ko mufrad?hmm ka kyauta ai,..shiru yy baice komi ba,Har suka karaso dinning din kowa ya zazzauna.
Jim kadan Imad ya juya yana Kallon malak data kasa dago kanta yace c'mon  Sweety zoki zauna anan Kar yunwa ya kashe mana ke..

Da kyar ta zauna a kujeran dake tsakiyarsu mum dinta tashiga serving mahaifinta abinci itama batayi kasa a gwiwa ba ta miqe tsaye ta dau serving spoon ta soma tayata, wa mufrad ta soma zuba dankalin dake shine a right hand side dinta wanda Kallon hannuntan kawai yakeyi da wutsiyar idon sa,irin kallon da baza'ama iya tantance tsawon seconds din dayake batawa akaiba tsaban kankantar sa,mamaki yaketa sha aransa ganin yadda hannun nata ke bari bari a hnkli take xuba mishi abincin kamar tanajin mugun tsoron sa,sake spoon din tayi a bazata sakamakon Jin lallausar fatar hannun sa daya dabo akan nata ya sumar da Ita,wanda batyi aune ba kawai  taga wai har ya kwace spoon a hannunta yana kkrin serving kanshi dakansa,a hnkli sautin muryansa ya fito yace "bari zanyi dakaina..can ya furta can kasar wuyarsa wanda a iska ma kawai ta shaqi sautin maganan Dan har yanzu bata farfado daga sumar wucen gadin datayi ba,uhm uhmm ..gyaran muryan  doc mehra ya dawo da ita cikin hayyacin ta,tana juyowa taci Karo da idanum imad Kar akanta,kunya yasata birkicewa tana shirin zamewa daga wajen ya riko hannunta yana dariya sosai
"..yace Anty Meera it seems like na samu  mata na fa...Kinga tuntuni sai kunyana takeji,dariya Anty meerah tayi tana kallon Doc mehra da ya soma cin abincin sa hnkli kwance, cike da zolaya tace inakaga mata anan kanwa dai,malak is just 16,a tunanin ka sai mu jira harsai ta girma kafin kayi aure?dariya yay sosai tukun yace Hakan nake nufi Anty,Nan da 8years haka ai yayi?Wani hararar baxata doc mehra ya watsa masa,a dake yace 'kamaida hanklinka, da sauri ya toshe bakinsa yana komar da dariyar data kufce masa Jin sautin dariyarsu suma,Malak din ya juyo ya kalla wacce already ta sunkuyar da kanta can kasa tanajin Duk abunda sukeyi,sanda ya Kare mata kallo snn yace"Amarya na Toh zoki samun abincin manaa,matsowa kusa da ita yay a hankli yace mata" Kin saka ma mai mata kinbarni ko?kinga kinjawo ana min gori aida sai a bari Matarsa tazo ta samai'..mamaki ma ya bata Dan bata San harta turo masa bakinta gaba ba,Nan mufrad ya harare sa dake shi yaji maganar tasu da sukayi a tsakanin su su biyun daga nan baice komi ba,babu musu malak ta karaso kusa ta shiga saka masa komi dake kan table din dan daidai sannan ta zauna a tsakiyar su ta xubo nata tana ci tanajin su suna dan jefa hirarsu wanda mostly labarin zaman imad a America ne.

Tagama lura kamar Shi Babu ruwansa da ji da kai haka Nan yake da son sabo da kowa musamman ma ace family ne,Duk yadda malak take Jin nauyin su haka ya ringa tambyarta schl,studies da sauran abubuwa Wani bin har ayita kwashewa da dariya,sosai zuciyar ta ya amshe  yanayin shi dats so elegant nd charming batare da tayi Wani dogon nazari akansa ba..

Tun kan su kammala ciye ciyen nasu kira yabi ya damesu dake ma imad din aketa kira yana dagawa yana kallo Amma baiya iya dagawa agaban su,"..Hakan yasa suka rushing din abinci agurguje  suka kammala Anty meerah ta umarce malak akan dataje kitchen ta dauko cooler pounded yam da vegetable soup data dafa musu tace mata saita samesu dashi a waje,dan da alamn itama binsu can maitaman zatayi shiyasa ma tafito da shirinta.

Waje suka nufa dukan su sunai ma Anty meera godiya tana ta tsokanarsu
Doc mehra bai Wani jima tare dasu ba ya musu sallama dake shikam wajen aikin sa direct zai wuce,dan kwana biyu da bayanan yasan ba karamin bukatar sa akeyi ba..

Motar sa tana ficewa a compound din saiga malak ta fito sanye da dan doguwar riganta irn Turkish jallabiyan Nan masu zanen flower ata gaban sai tayi rolling da red scarf kalar zanen flower tayi kyau kamar ba yar 16yrs ba,imad yaso ace ta biyosu a motar su saboda son surutun dayakeji aransa yau,
Har cikin ran malak tana son tabishi, saidai daga Ganin idanun ta kasan tana mugun jin shakkar mufrad data lura cewa shi kwata kwata bason sake jikinsa yakeyi da su ba,a hnkli ta girgixa mai Kai kawai tabi bayan mahaifiyarta sikinini ta shiga motarsu suka nufi new zayd matazu resident dake cikin anguwar maitama..

Tun akan hanya malak ta shiga damun mamanta da tambayoyi game da su,ita a abuja ta taso takeyin rayuwarta bata waye da fuskokin yayan yaa sheik sosai ba,Nan maman ta shiga bata amsa daddaya dakema ta lura malak tafiye nuna interest dinta akan imad,Anty meera kuwa batason wani kulata bare ta bata Wani deceiving impression game da wasan da imad yake mata dazu na cewa ya samu matan aure,she knows perfectly well how girls can be cunny,bare yadda yarta take fama da fallin balagan Nan ai sai a hakli,ita kanta tasan halayyar yarta,
Idanunta a bude suke sosai,irin kanann yaran Nan ne masu lura da Kuma fahimtar komi,she knew her girl who is already into hausa nd english novels at early stage altho she really trusted her,saidai Duk da haka yaran zamani Suna bata tsoro shiyasa har Yau bata dena saka mata Ido ba,malak bata Wani sha mamakin kasancewar Mufrad sojaba ne,dama can sunan shi take yawanji Amma bata taba ganinsa face to face ba saiyau dayazo,ita dai imad ne yayi mata Dan harga Allah aranta tana son taga energetic and handsome men kamarshi..

Suna isowa gaban babban gate din gidan mai gadi ya bude musu suka shigo,mash mash masha Allahu gida ya balain kayatrwa Dan sosai ya Kere gidan su na kano a girma da yelwa da tsarin kayan more rayuwa.

Basu kai parking lot ba imad yay parking motar dake shiya amshe driving din,mufrad yana gefe yana famar latsa waya,yana tsayawa kuwa baijira fitowar mufrad din ba ya fito cikin sauri ya nufo su Anty meera,a hnkli malak take kallon sa Jin haryanzu gorin aure kawai ake masa shikuwa Babu kunya yana yarfata Anty meerah ta ce malak kiyi sauri kitaho masa harda abincin sa Dan anjima kadan yunwa zaiji baida mai dafa masa.."idanun sa dake waje don mamaki ya tsura mata yace wai Dan Allah dagske abincin kika biyo mu dashi?tace eh man,Babu yadda banyi abarka ka wuni mana yau ba doc yace a'a Nan dinma bazasu hakura subarka ba shine kawai Nace to muma baro muzo Nan din tare akunce jakar tsarabar agabanmu.

Tare sukayi dariya suna kallon mufrad da ya karaso cikin yar sautin muryan sa dabaison budeta da karfi yace
..."me kuke anan? Anty Muje ciki mana karya cikamiki kunne da surutu..
Yana karasa fadar hakan suka dau hanyar ciki dukansu hudu suka jera suna takawarsu a nitse,mufrd na gefen anty meerah,malak na gefe da imad tana takawa sai yadan tayata riko jakarta ita Kuma ta rike cooler abincin a  dayan ahnunta..

Suna daf isa bakin kofar,saigashi har an rigasu budewa ta ciki Wani irin Ihu sukaji sanda suka raxana suka tsaya still ayayin da shukra ta koma cikin gidan da uban gudu in xciting voice tana cewa kufito kufito,oyoyo, woah woah,mumy mumy uncle Imad is here,...
Kamar yar zakara haka take cara tana daga tsalle a tsakiyar babban palon su

Keeyan da already tuntuni ya shirya kansa cikin kananan kaya yana zaune a babban palon yana kallon tv,Nan da nan ya tashi cikin sauri cikin yanayinsa mai saurin bayyana tsantsar farincikin sa, yana fitowa kuwa suka hade ido da imad,da Wani irin shauki Suka harxuko suka rungume juna tsam tsam suka dunkule kansu tamkar wanda zasu balla kafadun juna,a sadade malak taja gefe gudun karsu tureta tanata binsu da kallon mamaki.

Tun kan su wanye hug din saiga Yan cikin gidan bisa layi daya na bin daya Duk anyi rubibi an fito ruututu harda su hjy Adada da hjy saddika, dake hjya saddikan ta kasa hakura tajira shi a kano itama Ajiya jiyan tazo abuja musamman Dan ta tarbeshi dakanta...

Kan kace Wani abu hjy jasmine da su hjya saddika sun kewayeshi da Ihu da hamdala jinsu yasa har ya kasa iya danne ruwan hawayen sa wanda already sun nuna cikowarsu tam a kwayar idanun sa Duk dama basu sauko kasa ba tukuna,..

Daga bakin kofar nazli da shukra ne suka Dan rakube sai rawan dari suke jikin su na rawa rawa kamar masu Jin fitsari,wani ji suke kamar zasu fige kansu sama su tashi sann su sauko akan uncle dinsu tsaban murna saidai gaba daya  ganin mufrad Agefen sa ya hanasu matsowa cikin ribibi,..sai uwar surutayya ake ana kyakyata dariya keeyan ya riko hannunsa dam Dam Suna ta surutu da mutanen gida
..wayar mufrad ne yay kara yaja jikinsa ya koma can gefe yana amsawa,Wani daka tsalle nazli da shukra sukayi atare tamkar anjefosu kamar wani walkiya haka suka diro jikin imad wanda ji yay kamar an watsu masa su ne daga can can nesa,wani  kankame sa sukayi subiyun atare suka manne ajikinsa kamar super glue,sautin kiran sunan sa "uncle mad",uncle mad, kawai kakeji coming in different voices with different sort of emotion.

"I really miss u...nazli ta fada da uban karfi kamar zata fashe tsabar murnan da zuciyarta yake ciki har Wani kasa tsayuwa akan kafarta takeyi..

Gaba daya jikinshi saiya mutu,sai kallonsu yakeyi da ruwan dake cike a idanunsa,gaba daya ya rasa yadda zaiyi da axaban kaunar su dake mamayar ransa,sai bin kowannen su yake da ido bakinsa ya kasa rufuwa,Wani irin strong feeling yakeji aransa irin wanda Bai tabajin irinsa ba,he Neva tot abun zai shigesa haka,missing dinsun dayake yawan dannewa aransa baiyi tsammanin cikin sauki zata iya fitowa filli ba,kasa iya furta magana yy,saidai duk abunda Sukace ko suka tambayesa saidai kaga yana gyada kansa yana dariya Dan ji yake kamar inya budi baki zai sauke musu hawayen tsananin missing dinsu da yayi da kalar dadin dake dawainiya da zuciyar sa ayanzu daya tsinci kansa acikinsu,..alokacin kusa kowa na rike dashi,wasu hannu wasu kafada wasu sun tamke rigar sa,barinma shukra da har yanzu bata freeing dinsa da warm hug dinta ba..

Aikuwa yana janyewa suka hade ido da mahaifiyarsa dake tsaye ita kadai tana kkrin janye hannun sa ajikinsu sai yaji kamar gwiwonsa ake sassarewa Wani muguwar axaban kewarta dayayita dannewa tuni ya shiga rikita masa yanayi

A shagwabe ya Dan susuce fusknsa kalar shagwaba yanata kallon fuskarta dayayi missing tsawon shekaru yana murmushi ya ce mata "mama"..
Mama na dawo nigeria shikenan hanklinki ya kwanta?Hawayen ta data sauke ya sokalo masa nasa,da Dan shaukinta ta taho ta rungume sa tsammm ajikin ta tana shafa kansa cikin tsantsar bayyana tsananin Soyayyar datake masa a zuciyarta da  kwakwalta,shima manne ta yay sosai har sanda suka so su ba mutanen wajen tausayi,cikin haka mufrad ya karaso kallo daya ya bibbisu da shi yaja karamar tsaki  fuskan San Nan a mugun daure Babu ko alaman rahma bare sauki, Ganin mahaifiyar sa agefe tana goge kwalla ya sa ya Kara jan tsaki aransa yana shan mamakin su shi aganin sa baiga abun yamadidin kuka anan ba..

As usual ganin sa yasa aka soma raguwa kowa ya nufi cikin gidan da sauri badai ayadda yaso ba,hjy adada da hjy saddika ne suka shigo tare da imad din,ita kuma hjya jasmine suna baya tare da Anty meera da malak Suna shan dariyar masu oyoyo dake hjy jasmine da Anty meerah dama kawayene, tun a secondary school suka hadu suka San juna,to tunda ma sukazo suka aure majazen su Wanda suka kasance aminan juna sai aka dawo ana zumunci kamar Wani Yan uwan jini.
.

Fannin su ai'nau kuwa ba'acewa komi Dan tun dawowar su abuja Zarah take mugun bata mamaki,
,musamman ma wajen matsata datakeyi akan abubuwa,gaba daya tabi ta maida ta jakar gulma,tamkar wasu magajiyoyin gidan haka suka dawo,Banda aikin shishhigi da neman gindin zama awajen mutanen gidan Babu abunda sukeyi su biyun.

Haka zarah tasa ai'nau agaba saida taki Sam ta tare gidan mijinta dake can anguwar asokoro,suma zaman daram sukayi a mansion din ana damawa dasu Ako Wani harka,daga yau suyi Nan sai gobe suyi can hasalima sune agaba wajen hidiman shirye shiryen bikin dawowa sabon gida da akayi, da duk Wani hidiman murnan dawowar imad Nigeria da ake kanyi..

Halayen Zarah masu ban tsoro da mamaki wanda ko  Ainaun bata San dasu ba su suka firfito mata a fili,  sosai Zara ta Kure mata tunaninta,dan da alamun zarah tayi nisa bata Jin kira a fannin makirci da munafurci da kuma karya wanda ya riga yay ma rayuwarta dabaibayi ya zame mata tamkar rigar ado..

Tun dawowar su gidan zarah take famar fadi tashi wajen shishhigewa manyan matan gidan da salonta na makirtattun mata wanda sukayi course a munafurci yau itace aikin dafe dafe,yau itace kimtsa faloka har Yan goge goge saita tsaya akan masu aiki tana gyara musu,ga Wani dan uban parkaging din karyan ladabi da biyayya data Ara tana musu mai ban mamaki wanda ba lallai bane mai karamin kwakwalwa ya dago salonta cikin sauki,wanda ko gaisuwa zatayi saita langwasa murya ta zube kasa tana Jan aji tana sauke musu makirtaccen fadanci tana riritasu ,in abunma ya cicciyota takan zagene tayi abunda ainaun ma bata taba tunanin aikata musu a matsayinta na surkuwan gidan ba,tun zuwan Zarah gidan komi nasu ya sauya gidan ya zamo so busy and energetic gaba daya sanda ta nemi ta sauya musu tsarin rayuwarsu da biri biri da rawankai da rawan jiki,a
Komi in za'ayi itane Kan gaba yau aje Nan mall din gobe aje Nan chops din,nuna musu take ita gogaggiyace tasan harkan kashe kudi ta Kuma waye Dan harga Allah batason harkan raini,within few days ta shiga juya musu tunani Dan hatta hjy goggo saida ta soma fadawa acikin trap din makircin Zarah saidai daga baya datazo taga tafara xakewa dayawa sai ta dan ja jiki ta dena kulasu..

Hjy adada da hjy saddika kam tuni nasu ya dinke suka hade Kansu kamar dama can sunsan juna Dan kusan halayyar su ma Babu wani bambamci
Cikin Yan kwanakin Nan Babu abunda Zara batayi musu na kyautatawa da biyayya ba,Wani bin har gulman Aina'un suke suna camparing din halayyar ta da zarahn wacce bata da aiki sai zulman da zuciyoyin su musamman ma in ana zaune a dinning haka, aka sako hirar su imad,xarah bata tabayin sanya wajen kkrinta na dasa musu boyayyen manufarta na son kasancewa dashi datakeyi ba altho bata iya fallasa furucin na ta a fili cikin manakisa da makirci take buga musu kai da salon game dinta,har wani sabon salon kunya da respect take bawa hjy saddika fulani abun harna so ya basu mamaki aransu

Dake ma gidan yana da girma sosai sashen sama can Inda Aina'u ta tare itama take kwana.

Daga sun kebe su biyun zasu haura ma juna da zagi gau gau Suna fadace fadace sabida bakasafai ainaun take Jin dadin salon zakewar da Zara takeyi agidan ba,abun haushi yake bata,wani yarfa Kan da Zarah takeyi in d name of neman suna yana balain konata..

Itama zarar haka take zagewa ta dage ta duddura ma ainaun ashar tayi ta mata gorin cewa dabiunta na jan aji da rashin iya bida mutane shiyake kasheta a gidan mijinta,haka zasuyi ta hargagi ma juna da tsiya da bala'i sanda ta rinka cusa ma ainau damuwa aranta, ta kuma sata agaba wuta wuta akan shan maganin mata,within dis short time Aina'u har tashha kusan rabin magungunan mata da zarahn ta sissiyo mata,dake bata saba ba sai takejin Babu dadi ajikinta kullum sai anyi dagske .

Tun jiya da akace imad ya sauka a nigeria Zara ta haukace da kimtse kimtse,suka hau shiri,not just normal shiri,babban shagali suka bude a dakin ainau tamkar wanda zasu tarbi shugaban ksa koma ace mahaifinsu daya riga ya bar duniya,yestades make up da aka biya zunzurtun kudi har dubu sabain haka ya tafi a banza,bata daddara ba tun asuba ta sa aka kara Nemo mata make up artist Cynthia oge wanda ta shahara sosai a fannin iya kwalliya a maitama.
Kusan same amount ta Kara bata ta tsantsara mata make up bamai nauyi ba sabida ita salon nata makircin da brain take yinshi.

Wani bin zakaga kamar tanaso tana Kaiwa kasuwa ne, but still she is nothing like her sister Aina'u who is extremely strict nd Nonsensical bata son yarfa kanta at all cost.

Ko ayanzu ma abunda ya hanata bin zugar oyoyo kenan,cikin ranta Sam babu dadi bazataje araina ta,beside who is imad inba marar imanin guy dib dayake sauri dauke hanklin mijinta akanta ba,ita tun Tuni ana murnan dawowarsan nan Amma harga Allah aranta baqinciki takeji,she secretly hate him sabida kimanta shi da mufrad yakeyi arayuwarsa,many times arabta saitana ganin kamar mufrad yafi daraja bukatun imad akan nata ita datake Matarshi,
infact a duniya bayn aikin sa data tsana imad ne yabiyo baya,she just can't hide d fact,bata son kayan Reni kuma bata son harkan karanta, ko jiya jiya ma sai da ta shaqi maganan banzan da nazli ta yabawa Zarah acikin wasa datace mata"..Omo local gang awon busy body"..she was like..akan imad din ne har za'a ce musu busy body?nazli tana da Wani salon rainin hanklin da kokadan bata so,shiyasa ma atarayyarsu basu cika dinkewa ba.

Ga shukra data lura kamar tana bibiyar su tana kallon Duk abunda sukeyi,she is sure yaran nan sukanyi gulman su abayan idanunsu,by now tariga tasan halayyar shukra na mugun iya saka Ido da dora kahun zuka akan rayuwar wasu,tasan abunda zasuce akan Zarah na batanci Hala kunne ma bazaijuyu ba..

ficewa tayi daga dakin zaran ta wuce nata dakin direct, gaban mirror ta nufa tadau marykay oil control powdern ta wanda yake da haske dayake  colour 1 take shafawa,nan ta Dan Kara gogawa sama sama akan fusktarta,ta dada gyara brow line,ta kikkimtsa Dan ta Kara fito da kyallin kwalliyar datayi ma mijinta Dan da shi kawai takeji azuciyarta take Kuma gani sabida Duk sauran Yan gidan ba damuwar ta bane..

Ita Harga Allah ma ta tsane su kawai dai yanayin rayuwace data zabar makanta wanda yakasance mata dole sai ta zauna dasu tabisu a hankli

Miqewa tsaye tayi agaban Mirrorn tana Dan juyi ciki dada gyara ma wata arniyar fitted gown dinta na atampa lace zama,dark purple colour with touch of gold saiya fidda farin kalar fatarta ya mata mugun kyau,juyowa tayi cikin sauri kamar zata fice tana bude kofar kuwa ta soma jin muryan zarah daga can kitchen Wani wahallalen tsaki ne ya kufce mata feeling d litle litle noise dake tashi a kasa,she despretely want to end all this games da Zarah ta bude agidan nan,ta kosa takoma gidan mijinta,inda tasan ita kadai ne dashi Koda ma zata dan huta da hayaniyar wayannan rubabbun mutanen...VOTE PLEAS

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top