chapter14
BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 14
Lord's perfect plan.
Kano state
Anguwan gangare.
Ana kiraye kirayen salla ta shigo gidansu da sallama babu kowa a tsakar gidan, hijabin ta tacire ta daura kan igiya tadau butan datagani agaban wata tsohuwar rijiya tai hanyar bayi sanin tsohuwar nata Hala tana salla yasa bata kira sunanta ba ta shiga bayin tayi tsarki bata jimaba tafito ta tsugunna tai alwala tadau hijabin da Dan ledarta tayii sallama a kofa ta shiga dakinsun da babu abunda yake tashi aciki sai warin tsufa da tsamin tsamin talauci..
Agefen tsohuwar dake salla taje ta tsaya ta tada nata sallan bayan ta Sallame zama tayi tadaura kanta kan kafadar tsohuwar da ake cewa yakumbo data idar da sallanta tuntuni tana zaune,a mugun gajiye tace "wayyo Allah na yakumbo nagaji wlh, yunwa nakeji akwai abinci agidanga kuwa? dagota yakumbon tayi tace "sannu hadiza sannu kinji,fatan kin samo cikakken labari akan yayan naki?shin yaya suke ciki kinji labarin rufaidar kuwa?..atake yanayin umma hadiza ya sauya idanunta suka cikko ruwa da alaman bata ma San me zata fara cewa ba,ganin alamar data bayar yasa yakumbo tayi saurin kawar da maganan tace ke da kikejin yunwa, toh kiy maza ki tashi mana, nasaka ruwan zafi akan murhu ki dau kofi ki dama kunu ki dumama cikinki, wanka zakifarayi kokuma abincin zaki ciki?,riko hannunta umma hadiza tayi tace A'a yakumbo zandai sha kunun Amma bazan iya kara bata Wani lokaci a gidan nan ba kema kinsan halinsa ai,kuma tunda nayi masa karyan baki da lpya zanzo dubaki hklina yakasa kwanciya yanzu haka Hala yasan Inda naje karma inje gidan ne ya harxuka ya fatattako ni,...
Cikin tabe baki Yakumbo tace hadiza ba gwamma ya korokin da irin wannan zalunci ba,ace miji ya rabaka da yayanka sannan yahanaka yin magana akansu?yo Allah na tuba inbadan bashin maganin shi danaci ba har shi ya isa inbashi aurenki ne? Ai har abada malam bukar bazaici darajar samun mace kamar ki ba hadiza saidai a qaddara jahilin banza jahilin wofi
Ke Jeki ki debo kunun inkinsha saiki bani labarin yadda ake ciki da batun yara shi zaifi min,Mikewa umma hadiza tayi babu musu ta wuce waje cikin Dan karamin kitchen din falange dake tsakiyar gidan ta kutsa kai garin kunun geron su ta kamfata ta dama shi da dan kauri tasa musu zuma ta taho musu dashi daki Adan koko
Samu tayi har yakumbo ta gama kimtsa Inda sukayi sallan tana zaune abakin gadonta na Tum Tum tana kan jiranta Zama tayi ta zuzzuba musu a kofuna bayan ta kammala ta miqa ma yakumbo nata sannan itama ta xauna ta fara shan nata a hnkli wani kuuuuuru ru cikin yake bada sauti alaman abu mai dumi yana ratsa hanjin cikinta yau tun safe rabonta da abinci banda yawon neman cikakken labari akan yayanta Babu abunda takeyi
Saidai Alhamdullahi hankalinta yadan kwanta yanzu data ta jijjiyo wasu labaran saidai kokadan yanayin labarin data juyo game da zaman kangin da sukeyi din bai mata dadi ba...
Musammn ma na yarta suhan da akace sau biyu mijinta yana lakada mata shegen dukka irin na kawo wuka,murja da rukkya km ma bbu magana dan labarin auren sun Sam babu Wani dadi aciki, aika ta musu a boye Dan karma akai gulman ta wajen mahaifinsu ya dawo musu bala'i dukkansu awajen sa ko ya tsine musu.
Suhan da murja dake mijinsu baiya musu kulle sukam sun samu damar mayar mata da sakon ta hanyar yar aikan da aka aiko wacce itace take kawowa hadiza rohoto akan dukkan abunda datagani da suke ciki
Rukayya kam kwata kwata mijin nata bai sake mata ba saboda shi mai arxikin dabbobi ne, daga baqon fuska ya shigo saiyahau bori yana cewa anatara masa barayi agidansan akan haka ya raba matayen sa da kowa nasu,yana da arxiki kam amma ya shaharawa wajen yin kyem kyem da abun hannun sa hakama Babu mai ci ko sha agidan sai inyaga dama,
shikam da almajirin gidan sa ma hadxa tasa aka hada baki sannan takejin halin da ruqayya take ciki
Duka Yaran Sukanji matukar dadi da sanyi aransu idan akace musu ga umman su acan waje ta zo dominsu tana bibiyar lamuran rayuwar su Dan kuwa bakaramin kaicon rayuwa da tsantsar takaici suke kwasa a gidajen mazajen sun ba.
Acikin su wayanda suka maido mata da gaisuwar babu wanda baiyi mata maganan rufaida ba,Hakan ya dada saka umma hadiza acikin damuwa sosai,waima ya zaayi ace har Yau babu wanda zai gaya mata Yaya rufaida take?Ina aka kaita ko Wani irin hali take ciki..
Wasu irin maqudan hawayene suka sauko daga cikin idanunta yuuuuu ayayin da ta sauke kofn kunnun a bakin ta a hankli Duk jikinta yay salak daganinta kasan tana cikin tsananin kunci da azaban damuwa.
Baki a wangale yakumbo take kallonta tana tsananin mamakin yadda mutum zaiyi shiru ya bace cikin tunani shikadansa yayita jimami
Tace oh ni A'i
"Yanzu hadiza Hakan d kikeyi adalci ne mkanki?
Dan kunun ma da zakisa acikin ki kiji sauki shine Kya sa shi agaba ki zauna kina masa kuka?...wannan irin rayuwa ne hka hadixa? ohni A'ishatu jikar shehu
Itama kukan ta barke da shi irin na tsofaffi tana matse idanunta suka hadu dukansu suna famar kukan,Nan aka rasa wanda zai rarrashi Wani Dan sosai umma hadiza take kukan da iya qarfin xuciyarta Wai Koda wani abu zai kau daga zafin da takeji a kirjinta game da rayuwan yayanta da tunanin yarta rufaida dayake cike mata kwakwalawa..
Can yakumbo ta sauko ta karaso har gabanta cikin yanayin tausaya
Mata jawota ta jikinta tayi cikin lallami tana bata baki tadau kofin a hannunta tana tura mata a baki wai koda ma zata cigaba da shan kunun taji sauki sauki,kwanciya kawai tayi a jikin yakumbon tana sauke Ajiyan zuciya idanunta a lumshe sosai Babu abunda ke sauka acikin su sai hawaye.
Cikin shesaheka a hnkli ta furta
"Yakumbo nikuma haka Allah ya tsara min qaddarar rayuwata.
Na girma bansan iyaye na ba
Ga Yaya na mata kaf anjefasu acikin ukubar rayuwar aure.
Babu abunda yafi daganmin hankli kamar inna tuna da cewa Babu ta Inda zan shiga inji labarin yar auta ta rufaida.
Yakumbo rufaidai har nawa take?ko 16 batagama cikawa ba meta sani da har za'a rabata da mu,shikansa malam a dame yake Amma yaki yacemin komi
Nikam ko mutuwa rufaida tayi ne? naga babu randa zan runtse idanuna banga fuskarta acikin Wani irin mummunan yanayi ba,yakumbo nikadai nasan menake ji araina game da rashinjin labarin rufaida, bana tsammanin rufaidata tana cikin koshin lpya..tabbas akwai matsala game da shirun rufaida,jikina yana bani wani abu yakumbo.. Kaico na da bansan inada zanga yata ba..Wani matsanancin kukan ne ya kara kufce mata wanda yake fitar da hucin sa mai tsananin quna da ciwon datakeji acan cikin xiciyarta yana mata zugi da zafi
Ita kanta yakumbon kuka kawai takeyi ga kanta na mata Wani irin ciwo sabida tsufa da ciwon daji dayake fito mata a makwagoro,Duk Saita ji kamar laifinta ne data aurar da hadixa wa yaa malam da Duk Hakan bai faru ba.
Ahaka dai ta rinka rarrashinta tana lallabata tsaban batajin dadi ahaka ta miqe ta shirya ta wuce gidanta batare da Tasha kunun ba
...daga isarta gidan ta samu har ya shiga sallan ishai Dan haka tayi marmarza ta shige bayi ta doro alwala dakinta ta shiga ta kulle kofa,kamar yadda ta saba ko bacci bata samun sukuni face ta shimfida sallayarta tayita roqon sauki ma rayuwan yayanta,Saidai tunda ta idar da sallanta ayau akan rufaidarta kawai takeyi wa Allah kuka tare da miqa kokon bararta Koda zaisa wata rana taji labarinta.
Ivy cottage USA 2:00pm same day
Ko minti goma rufaida batayi a sumen ba ta farka cikin fara wani mafalki mai cike da ban tsoro Gani tayi wasu halittu masu cike da ban tsoro suna biyo ta da wata karamar yarinya da bata wuce sa'arta ba
Gudu sukeyi a cikin wani mahaukacin jeji dayakenan baqi qirin wanda ko tafin hannunka baka isa ka gani ba, sai famar gudu take tana ihu sai da tayi nisa sosai wanda ba lallai bane a iya hangota sannan tadan tsaya tare da juyowa ta bayan ta ta gani ko har yanzu wadannan mugayen mutanen na biye da ita amma sai taga babu komai,cikin nishin wahala tare da shashshekar gajiya ta sake juyowa ta gabanta da niyyar ta dan karasa gaba ko zata samu gurin buya sai kicibus tayi Karo da wadannan mugayen mutanen sunyi carko-carko a gabanta ko wanne rike yake da zundumemen wuka a hannunsa da alaman kasheta kawai zasuyi a hanzarce ta sake yunkurawa da niyyar sake gudun sai ganin tayi ta koina gaba daya sun gewayeta Nan take taga wani wargajejen mutum kansa baki jikinsa fari wanda gabadai wajen ba wanda yayi girmanshi da kuma girman katon cikinsa xuciyarta ya riga yabata cewa alhaj baturen ne,har gabanta ya bayyana cikin takunsa mai cike da kasaita daga bisani kuma taga ya shiga gewaye wajen da take da Wani magani yana barbadawa..
Daganan ta juya sai taga wannan yarinyar da suka gudo tare ta kafe jini nata yoyoywa zuwa kasa daga cikin bakinta
waje guda ta tsaya cak Cikin mugun rudewa da ajujuwar dake dibarta ta tattake ta buga wani mahaukacin ihu sai da ko'ina ya girgiza daga bisani kuma ta zame jiki ta fadi kasa tana ta ihun,Dan Allah kuyi haquri Dan Allah ku barni karku kasheni
saukar bokintin ruwan da aka kwaroro kanta ya zuba gaba daya ajikinta shaaaa shyasa ta miqe a gigice ta zauna a wahale tana zazzare idanunta Babu shiri ganin Wani mugun mutum a tsaye akanta yana huci.
"Meye kikeyi wa mutane ihu ? mutumin ya daka mata Wani hatsalallen tsawa
Wanda tsabar rudewar datayi bata San sanda
Kuka mai cika kunne ya kufce mata ba
"wayyo Allah na zan mutu..cikki na yanamin ciwo
Dan Allah kuban Wani abu insha inji sauki..wayyo mutuwa xanyi
Cikin wahalallen yanayi take kukan Amma ko ajikinsa baice mata uffan ba,can sai ga Wani mutum shima ya shigo Adan gaggauce,Jan Dan uwansan yayi suka nufi gefe suna magana sai zufa sukeyi da alaman Wani abu baiyi daidai ba,..Suna kammala maganan ya juyo cikin sauri ya nuna rufaida da bindiga,fuskar San nan a yamutse cikin tsawa yace "ke tashi Muje,dayan ya dafa kafadun sa yace a'a,kabarta anan kawai oga yace karmu kara Koda mintidaya anan zata iya bata mana lokaci..
A gaggauce Wanda yake pointing bindigar akanta ya fara komawa da baya kamar dai baison ya tafi subarta anan din,danshi irin qurds din nan masu tsananin loyalty ma ogoginsu aganinsa in suka barnan hala rufaida zata iya kufcewa.
Ahakan dai dayan yajashi suka kulleta a dakin suka bar wajen tare da dukan sauran masu aikin agaggauce suka bar gidan sukaje wajen boyewarsu kamar yadda aka umarce su already labari ya riga yazo musu cewa anyi ma Alaji Bature cune FBI sun kama shi,so in ya fito lpya zasu dawo a cigaba da gashi inbai fito ba dama sunsan me zasuyi dan ba yau aka fara irin Hakan ba
Rufaida kawai aka bari a gidan tana yashe akasa ciki tsananin Jin ajijiya da zazzabi ita daya Babu motsin kowa
Har gari ya rufa yafarayin duhu duhu alaman magrib ya gabato amma bata ji motsin kowa ba Wani azaban baqar yunwa da tsananin kishirwa ke ciccin hanjin cikinta yana Murda mata ciki
Ga tsinannen duhun da yake shirin mamayarta ji take kamar ta zauce tayi ta kurma ihu Koda zataji sauki sauki..
_HERMOSA D'LA PUB, las Vegas. 7:40pm_
Parking hadadden motar sa bodyguard dinshi yayi a parking lot din babban pub din yana zaune a owners coner baima san sun isoba sabida wayarshi dayake ta famar daddannawa
Casual dressing yay Inda yafito a cikin wata shegiyar unbuttoned shirt na givency white and black color dayamai kyau banawasaba ya hadeta ne da dawani Black carmourflage trouser kafafunshi sanye da wani black boot na balenciaga, ya Taho da jacket duster coat ne sabida muran dayake yi sai wani hadadden kamshin turaren quilty absolute yakeyi kaman ka lashe shi tsabagen haduwar sa,budemai kofan da akayi yasa ya dagokai ya kalli bodyguard din dake tsaye agaban sa jiran ya sauko
Karamin Ajiyan zuciya ya sauke baice komi ba ya sauko ahankali tare sa zuba hanayenshi a aljihu, gaba yayi yana taku daidai kamar Dan sarki
Rufe motar bodyguard din yayi cikin sauri sukabiyo bayanshi suka nufa cikin pub din juyowa yayi fuskarshi adan daure jin karan takalman su daf daf da shi,wani irin haushin su yakeji yanda suke binshin nan kaman wani karamin yaro daga yay korafi ace ai aikin su sukeyi na kareshi,but he already knew dat Babu mai Kare shi a duniyan nan sai Allah,but wani bin dole ne yakansa
Kabada hadinkai domin akare rayuwarkan gudun Duk abunda ake tsoro din ya faru
Beign a top notch barrister who was well knwn to be in double shits with major corupt criminals da dangerous terrorist is not easy
,musamman yin cases akan wayanda suke ganin doka bazata taba hawa kansu ba
saidai fa Sosai Allah yakan bawa IMAD sa'a akan irin wayannan mutanen,hakan tamkar baiwar sa,he is too observant and a dangerous deep thinker,Allah ya riga ya bashi hikima da fasaha akan harkan aikinsa wuce tunanin mai tunani,
Shiyasa a Duk sanda case ya shigo hannun sa to tamkar anyi angama ne Duk dama shi bai dade da fara aikinsan ba but atleast a iya shekaru bakwai din nan dayayi ya taka muhimmiyar rawa a cikin manya manyan cases da suke addabar kasan such as drug dealers,cyber crimes,terrorism da human trafficking.
Bayan International law daya soma karantawa he had his second certificate in international criminal law kuma har iyanzu bai dena karatu yana kara iliminsa ba
Saidai shi arayuwan sa Babu ruwan sa da cases din daya shafi mata,most espicially in akan women abuse ne,ko rape ko Wani domestic violence toh baya taba karban irin wannan cases,cos he know how vulnerable he is
Yanada matukar tausayin nakasa dashi,in namiji xaiyi convicting baya damun sa,amma Daga zarar yaga ya mace acikin Wani hali tou qaddara ko bacci mai kyau baya daukar sa,yakan iya shiga damuwa inyaga ana oppressing din mace ko Dan karamin yaro musamman ma ace masa dan maraya ne,so he Neva wanna ruin his career bcos of his vulnerability shiyasa kwata kwata ya gwammaci yay risking life dinsa a gaggan laifukan da mafi akasari mazane suka fiye aikawata
Ahankali cikin soft voice dinshi ya juyo ya kalle grds dinsa dan baison yamusu ihu ya janyo attention din mutane yace
you guys should please wait for me outside pls give me a break,Kaiwa nan yawuce yay ciki cikin daure fuskan sa sosai sukuma babu yanda suka iya suka koma gaban mota suka zauna
Budemai kofar shiga VIP reservation securityn wurin sukayi ya shiga cikin har cikin pub falour din da wakar su Rihanna da bryson tiller ft dj khalid.."wild thoughts" yake tashi mutane na rawa a dance floor kamar zasu karye kwankwason su,wasu na buga bar games wasu suna caca dauke kansa yayi yana dan cije lips dinshi ya hau kan stairs din yay sama ya doshi wani waje da aka rubuta men Only.
security dake wajen suna ganin shi suka matsamai ya shige yana shiga wasu mazaje su hudu ne a zaune dukansu kamar black Americans sai sauran fararen turawa ga cigarete ga shisha pots kala kala agaban su da manya manyan bottle din hernesy da wine glasses a hannun su, suna ganin shi sukai ihun nuna Jin dadin ganin isowr sa daya daga cikin fararen turawa yace we are glad ure here
But you are late zama yayi kusada guy din dayayi maganan Wanda shikadai ne yay kama da yana cikin hayyacin sa sosai a hankli yace wash, my back" dayan black din ake cemai Nando ya juyo cikin neman magana yace hey MAD where are your guards? Dan haka suka saba kiranshi tun Suna college sabida tsaban rikici da gagaransa suka maida sunan sa ya dawo "MAD"dakema daga jikin sunan sa suka yanke I din suka bar MAD gashi hartana kkrin binshi, daga yanayin yanda yay maganan zaka gane tsokanar shi yake nema hakan yasa sauran suka fashe da dariya sosai,"danger zone ba...hararan su yayi ya hade ransa sosai yace "no fucking qurds,i came alone" "wowwwwww Kai, lemme just call this a beautiful lie right guys?nando ya tambayi sauran mazan atare sukace "yeah,suka cigaba da dariya ganin iskanci kawai sukemai yasa ya kalli bar attendant din wurin mace ce Latino babe kyakkwa yace
"non alcoholic pls" Da sauri ta yajuya dan zuwa dauko mai, juyowa yayi ya kallesu ganin duk sun tsareshi da idanun sa dayayi ja suna shan shishan su yace so wats up guys? Nazo ne sabida muyi bankwana am leaving tmrw,
Wani iri sukayi da fuskan su Inda bakace abun bai daga musu hankli ba,but thy are men already,so thy just have to man up daga Hakan kowa yay masa fatan alheri akan rayuwarsa na Nan gaba suka cigaba da sharholiyarsu
wanda yake facing dinsa mai Suna yanar ortugru u can tell dat shi Dan kasar turkey ne, cikin harshen turanci dan duk da turancin suke magana yace "yawwa mad dama hira mukeyi akan irin matan da
mukeso mu aura,not now but in the future,da sauri dayan black din dayake faman shan sigari wanda kwata kwata ma baimayi magana ba yace I, officially.. Edwardo jackson Perez, I want to marry a spoilt brat..Atare dukan su suka juyo Suna kallon sa yace yesss Yarinya yar gayu mai kyau wacce aka taso ta acikin tsananin gata yar gidan Wani shegen powerful business man or a multi billionaire wanda zamu lalace tare,Wani dariya suka fashe masa dashi,cos he is sooi high, yanar yace ma Nando da imad to ku wasu irin mata kukeso?daidai lokacin bar attendant din ta taho cikin takunta mai dauke hankli ta ajiye ma imad non alcohlic drink din dayay requesting karban drink din yayi ya zuba a white glasses ya tuttila ice blocks akai,Nando dake kusada shi ya kalli wanda yamasu tambayar yace "Yanar,meyasa kake tambayar mu irin matar dazamu aura, kaima kasan MAD tough girl zai aura am sure yarinyar Wani mayor zai Auro ko yar wani wrestler this guy is too serious menhn.
Dariya mai hade da ihu suka fashe dashi"..ure fucking right or maybe he will go for a detective
Tabe baki imad yayi jin maganan da yanar yayi yakai drink dinshi bakinsa yana kara shigewa cikin kujera da kyau
ganin kamar baida niyyan yin maganan yasa sukayi shiru sun saba dama da iskancin shi na son sharesu alhalin in shine yake neman tsokanan mutum baka isa ka sharesa ba,hakan yasa daya daga cikin turawan mai suna emilliano, Suna cemai mills yacigaba da hirar yace "niko? inaso in auro hamshakiyar matan data girmeni sosai wanda zan zamo mata tamkar asset at least tabani 17 yrs hakanan" atare dukansu suka juyo suka kallashi ciki harda imad dake famar sipping drink dinshi .daga musu kafadarsa yay yace trust me guys,I hate baby sitting I wanna be pamperd by some hot mama de la hot,bazaiyu nayi bursting ass dina a wajen aiki na dawo gida Babu mai lallabani kamar kwai ba,my mum is already late hunn..ahh need a sweet mammy ptsss..Yana karashe maganan ya wani daure fuskar san kamar da gaske
dariya dukansu su kayi banda imad da yadanyi murmushi alaman choice din Mills din yadan bada citta, kana ganinsu kasan duka suna enjoying hiran da sukeyi ganin yayo murmushi yasa Nando yce "come on mad tell us yours mana kodan nayi azarbabi?
So how isshe gonna look like?yanar ya zubamai Ido daga can shima yana saurara, dan bude idanun sa yayi ya kallesu saikuma yay murmushi mai sauti ya daga glass cup din hanunshi yana kallon sauran kankaran dake ciki Dan shiru yy kaman yana tunanin wani abu,dan furzar da iska yay tabakinsa ya gyara zaman dayay akan kujeran yyi xama mai kama da kwanciya daura glasscup din akan kirjinshi yy snn yace "forget it guys,I dont think i will ever get married, but if Eva I do matar danake so na Aura....???sai yay shiru yasa hanunshi ya cire glasscup din daga kan kirjinshi ya aje akan table
Tare da nade hannyen sa akan chest dinshi yy jimmmmm kadan.
yace "I want a criminal dat look like a suspect..
Dukan su suka kureshi da alaman basu gane meyake nufi ba
Yace okay inason na auri mace dat is so innocent on d inside,but kinda bitch on d outside,cool and uncool,cos I seee rich girls are too stupid I hate the prouds,I hate them ya yatsine fuskan sa cikin rigimamiyar muryanshi ganin sun kasa cewa komi banda girgiza kai da
Wasunsu sukai
Yanar yace "I want a smart girl mara son jiki a girl dats sooo vibrant and more formal smarrt as hell.
Nando yace i need a peaceful obedient and softgirl that love me for who I am,..simply
Imad ya kallesa yace cheers bro if her heart is beautiful I think am also okay....yayi dan shiru kafin ahankali yace "a girl that my heart will naturally fall for cos it's sumting that’s really hard to fake"..
yanayin shiru edwado ya kallesa yace "so u mean u don't want girl that is too expose? yarinya mai hankali da son taimako ko?"
Dariya sosai suka karayi atare,imad yadanyi shiru kafin ya yatsine fuska ahankali yace "I just want a girl that will fill my imaginations
,innocent nd fierce kind of dan murmushi yayi ya kara daukar drink dinsa ya kurba yace "enough guys anyway, nasani such girls doesn't exist on this earth so I ain't gonna stress myself with marriage talks nifa ba aure nace muku zanyi ba nowadays girls are too bitchy yasake yatsine fuska agajiye duk dariya suka hau yi masa
Yanar yadan buga kirjinshi yace "u are just talking imad maybe ma duk saika rigamu yin aure ai muna nan dakai"
Harara ya watsa mai yana hamma at same time yana duba oyster watch din dake hanunshi ganin kusan 2:30pm na dare ya miqe tsaye Babu bata lokaci yace "gudnight guys am gonna catch my flight tomorrow" atare duk sukace See you tmorw Yajuya ahankali yana daga musu hannu yay waje
Wani bacci yakeji bana wasaba da kyar yakai gaban mota aka budemai motar ya shiga ya kwantar da kanshi jikin kujera ya lumshe idanun sa daganan kuma sai bacci
Murmushi guard dinshi yayi daya juyo bayan yarufe kofan car din kaiwa gida sukayi yay parking suka fito ya zagayo yabude kofan yadan bubbuga kujeran yace "sir.we are home can I help u?dan bude idonsa yayi ahankali ya kallesu ahankali yatashi yaziro kafafunshi kasa guard din zai rikeshi ya harareshi cikin bacci yace excuse me sai yay gaba
su dai suna biye dashi har sukahaura upstairs yabude dakinshi ya shige yafada kan babban gadonsa batare daya cire koda takalmin sa ba, ciremai takalmin guard din sukayi suka lullube shi da duvet sannan suka rage mai karfin AC sabida muran dayakeyi.
Dayan kuma ya kashe wutan dakin suka juya suka fita dan already tun dazu da sassafe suka hadamai kayan dazaiyi tafiya dasu gobe.
Bangaren rufaida kuwa cikin Wani irin yanayin firgita ta farka jin kamar motsin mutum akanta,da kyar take iya motsi tsaban yadda yunwa da kshr ruwa yay mata lahani
Fincikota taji anyi an watso ta waje,
Babu Wani haske awajen Amma Duk da Hakan tagane cewa Alaji Bature ne yazo mata saidai batagansa da mutanen sa ba shidaya ne dagashi sai yar rigar bacci daya sakaya
Har gaban Wani famfo yakaita ya gurfanan da Ita akan gwiwarta tare da fincikar pipe din tamfor yana wataa mata ruwan sanyi daga kanta har izuwa kasarta,Wani numfashi mai Nauyi take saukewa,can ya umrceta data wanke jikinta rufaida ta rasa yadda zata farayin hakan agaban sa
Ganin taurin kai kawai zatayi yasa ya fincikota tsaye bata hankara ba kawai ji tayi jikinta babu kaya daga ota sai brexiya da pant dinta wanda yy dukun dukun Dan datti Dan tun zuwarta rabonta da samun wani kaya
Batama San kalar kukan datakeyi ba kawai dai tana tsaye ne Jin yadda namiji yake sassaka hannun sa a sasassan jikinta Wai yana mata wanka.
Sauki daya da bai ce zai mata tsarki ba amma still shiyake zuba mata ruwan tana wanke private part dinta
Sanda ya tabbata ta wanku ya kashe ruwan,bai jira ta dau kayanta ba ya dauketa cak ya shiga cikin Wani daki da Ita...
Part 1 IS FREE,TUKUICI NE GAREKU MASOYA NA U CAN READ IT HAR ZUWA INDA ZAMU TSAYA,SAIDAI CIGABAN SHI NA KUDI NE,PLS SHOW SOME LOVE AND SUBCRIBE
the ACCESS FEE IS 300 NAIRA ONLY
VIA 0152983148
MOH'D SULE SURAYYA GTB.
OR katin MTN vtu tran via 08060712446
Screenshot ur evidence to SURAYYAHMS 08060712446
OR MAMAN MUBENA
08036651119.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top