Chapter:8

BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 8
At d core of my pain.

Old maguzawa site:Anguwar bayan gari, kano state.

Kwance take akan tabarma bayanta jingine da Wani motsatssen matashin kai tana maida numfashinta a hankli,daidaikun matar makwabta ne a zagaye da ita ana famar jajantawa ana bata baki,Matar mai anguwar ne ta kara maimaita maganarta tana cewa"Lallai Sannu hadieza,Allah ya kara sauki, Allah yasa ciwon nakin nan kaffara ne.

Da kyar Umman take dago kanta inta dan Kare musu kallo sai tace Ameen sai ta kara maida kallon ta gefe batare da ta kara furta musu uffan ba

Daga ganinta kaga yanayin wacce kwata kwata batajin dadi aranta
,musammn ma yanayin taruwar matan nan  agabanta,ita kanta tasan ba Wani abu bane yake kawo matan makwabta gidanta face gulma da son jin kwakwaf kowa dai nason yaji asalin labari game da Auren bazata da akayi ma yarta rufaida..

Duk Dama tasan tunanin rufaidar shine silar ragwabewar jikin ta amma tana matukar tsoron wanda zata sake ta tattauna damuwarta da shi
Ayanzu Bata da kowa na kusa da ita Dan haka ta qwammaci ta cigaba da danne abubuwan dake damunta masu Nauyi da kuntatawa acikin xuciya.

mijinta Yaa malam ya riga yahana yayansa Koda yin waya da ita inba Wani abu muhimmi bane ya taso musu,ko da ya tason ma yafison su kirashi direct amma ba ita ba,Dalilin sa na cewa ai ana zugasu ne Dan su bar gidan mazajensu suki zaman aure.

Tun da ya rabata da su rufaida take cikin tsananin bakin ciki da damuwa and She have no one to talk to Bare ma ta amayar da kuncin ta waje Kodama zataji dan sauki sauki a zuciyartan dake mata nauyi.

Ta gama lura cewa wayannan mutanen anguwar nasu kusan Duk jirgi daya ya debosu acikin su babu mai isashen karatun arabi bare na boko,su basu San komi ba sai azaban saka Ido da bibiyar rayuwar mutum in tayi tsami suyi ta tsegumi ana dariya intayi kyau sununa tsantsar bakin ciki da hassadarsu a fili.

Hasalima badon an shede rufaidar da tsananin kamun kaiba da tuni an karade gari da cewa cikin SHEGE tayi ko ko ace an kamata tana zina shiyasa akayi mata aure irin wannan babu hidima babu shela kawai agaggauce batare da sanin uban kowa ba.

As usual Tunda suka shigo gidan babu abunda sukeyi sai raha a tsakanin su da kwakwale kwakwalen magana
Kowa dai burin sa baifi ya fadi wata kalman da zaisa hadieza ta harxuka ta shiga bude musu duka sirrikanta ba,burinsu ne su baje kunnuwan su kwasa sirrinta cikin satin nan sai asamu abun bazawa,Ita kuwa hdiza Sam taki kulasu,Koda ma an tambaye ta silar ciwontan saidai tace ciwon zuciyarta ne ya motsa kuma ma yanzu tanajin saukin shi,su Sam ba Hakan suke gani atttre da ita ba,Dan shi magulmacin mutum kusan yafi
Kowani mahalukin Dan adam iya lura da yanayin mutum

aganin su tabbas akwai abunda yake tafiya game da Auren rufaida wanda su basu gane ba,kuma koma menene sun san tabbas babu dadinji Dan sun dade basuga hadiza acikin yanayin tashin hanklin irin wanda take ciki yanzu ba

Ana cikin wannan yanayi saiga sallama a kofar gidan sun,bayan kamar minti uku da ansa sallamar can saiga almajiri ya shigo Niki Niki da kayan makulashe ya shigo da su ayar babban leda,wata kyakkwar mata ce ke biye dashi fuskarta babu yabo babu fallasa,tun daga kasar zaninta har tsakar ka suke kallon ta babu kiftawa,"..sallama alaikum..umma hadieza tana ciki kuwa?,Duk yawansun Nan ba a samu wacce ta iya amsawa ba sanda umman ta mike da kyar ta amsa maganan fuskarta dauke da murmushin jin muryan Barister fareesa matazu a tsakar gidan

Lale marhaba fareesatu ce? Ahh sannu da zuwa...
Shigo mana,Umma ta fadi hakan ayayin data Dan mike zaune fuskarta dauke da murmushi

"Ina wunin ku?
Barister fareesa ta Dan rusuna kai ta gaishe su duka,sai ayanzu suka farga daga azaban kallon tan da sukeyi,.atare duka suka ce uhmmmm Lapya barkanki da shigowa,tace yawwa,Daf tana shirin zama kusa da umman knan sautin wani magana ya dakatar da ita, wata magulmaciyar ce data kasa hakura azauna,tace hadiza
Wannan kuma fa?

Take umma tayi Murmushi tace
Maman abdul kenan,ai Kya bari ta zauna ko?...wannan fa antyn su rufaida ce,Fareesatu ce babban yar gidan Yaa sheik..Atare Suka washe baki "Awooo Allah sarki,sannunki da zuwa fa? lale marhaban
..Nan da nan suka kara gaisheta kowa na tambada nasa kalar iyayin,daga bisani da sukaga batayi kalar wacce zata kula haukarsu ba da daddaya suka zame suka basu waje.

Sai a sannan umma ta juyo a nitse ta kalle Anty fareesan
Tace "yata kin baro gidan lpya?Yaya Hajiya jasmine da yaa zaidu?Hajiya mama fa?ina fatan yaranki ma Suna Nan kalau Murmushi mai sanyi anty faressan ta saki tana mai riko hannayen umman cikin tsananin tausaya ma yanayinta aranta tace"Kowa lpya umma..toh Yaya jikin naki?..kina samun sauki kuwa?Ni kaina na kasa samun sukuni tunda hjya ta gayamin halinda kike ciki,yau da naji ance yaa malam bayanan shine Nace to bari inzo inganki,Umma fatan kina samun sauki daiko?ko Hjya mama ma ta mugun daga hankalinta da tunanin ku Dan Allah ki kwantar da hanklin ki umma,ki gayamin damuwarki Inda Wani taimakon da zanyi miki sai inyi mikishi yanzu

A hankli umma ta zame hannun ta anata,ta kuma kau da kanta gefe gudun
Kar hawayen da suka ciko idanunta su gangaro.

Koda ta saurare fareesa sai taji kamar garin barkwano aka kara zuzzubawa akan ciwon dake ciccin zuciyarta,sai taji zuciyar nata na mata Wani irin quna da zafi,Tafi minti uku cikin Wani irin yanayin bakinciki da tunanin kuncinta mai azabtarwa kuma marar misaltuwa wannan murmushin dauriyar shikadai yaki kufcewa akan fuskarta

Dagowa tayi cikin tsananin dauriya ta kalle kwayar idanun fareesan bakinta na shirin buduwa tamkar wacce zata furta Wani abu sai dai wani maqudan hawayene suka sauko mata a bazata"muryanta na rawa rawa tace.."lapiya na kalau faressa..tafin hannun tasa ta goge hawayen nata,still basu dena gangarowa,it feels asif she want to control her self nd her emotions Amma Ina sai tagama takasa iyawa,hawayene masu rauni da daci ke gangarowa daga cikin kwarmin idanunta,ta daure iya dauriya anma daga ta budi baki bata iya furta komi sai tace.."lpyarta kalau...Dan riko hannun ta da Anty fareesan tayi ne yasata ta barke da Wani marayar kuka mai tsuma da shiga jiki,tanayi ahankli gwanin ban tausayi,Murya na rawa Anty faressa tace"..umma dan Allah kiyi hakuri kifadamin abunda yake damunki Koda bazan miki maganin  yaa malam ba na tabbata zakiji sauki a zuciyarki..karki bari tunanin su rufaida ya cutar dake,in kika bar duniyar Nan wazai tsaya musu umma?anan itama sai ta sauke hawayen ta tanamai tsananin jin tausayin umman..Rungumar ta tayi tana kukan tace"..Umma dan Allah Kiyi haquri ki samu lpya dukkan tsanani yana tare da sauki,da kyar umma gyada kai cikin danne ciwon datakeji aranta ta dauke kukan chak snn da ta dago,Dan kallon ta shiga yi
Tace fareesatu bani da kowa fa a duniyan nan sai Y'aya na,gashi ya rabani da su dukan su,.shin Taya hanklin uwa zai kwanta bayan bata San halin da yayanta suke ciki da rayuwarsu ba? rufaida tana can wajen wanda bamu San shi bamu kuma San yanayin rayuwar sa ba.
Yau In Wani abu mummuna ma ya faru da Ita ina zan sani?ya hana su kira ya hanani neman su..ni Sam bansan me nakeyi da rayuwata ba..
Ashe haka maraya yake shan kuncin arayuwarsa?tunda na aure kawunku nake cikin halin kewar iyayena na tabbas na gwammaci na zauna da iyayen da suka yarda ni a bola da in zauna da mutum irin yaa malam,wanda Duk Wani farincikan ka sai ya tsinka shi ya yasar,...Nide Allah na Gani Duk Wani nau'in wahala da mugun halin da yayana zasu shiga bazan taba yafewa ba kuma Alhakinsu na wuyarsa..Wani zazzafar numfashi taja alaman takaicin furta maganan ya shigeta sosai..
Wani kalman zata furta kawai saiga hawaye rututu Suna saukowa daga idanun ta kamar an kunna su Atake Anty faressa ta share hawayen ta ta matso kusa daf da Ita cikin yanayin rarrashinta tana mai dan shafa mata bayanta a hankli,tace "umma babu abunda yafi karfin addua,kiyi fatan rayuwa mai kyau wa yayanki a Duk Inda suke,Addua yana sauya qaddara daga mummuna ya dawo kyakkyawa ina miki fatan samun sauki umma,sannan kisa aranki ni ina tare dake,insha Allahu Allah bazai barsu rufaida a hannun wani mugu ba
..Nakasahiyar Murmushin ta mai tafe da hawaye ta sauke tana kallon fareesan"..tace toh shikenan fareesa na ji shawararki..Allah ya miki albarka Allah ya saka muku da alheri dake da iyayenki nasan kunyi iya bakin kokarin ku akaina da Yaya na.Yanzu dai ki zauna kihuta,jikina da Dan sauki bari inshiga ciki in samo miki ruwa..da sauri antumy reesan ta rikota tace A'a umma kibarshi kawai,saita mata karya tace inama azumin litinin da alhamis,kedai zauna kici abincin Dana kawo miki

Murmushi kawai tayi Dan rabonta dataji sha'awar cin Wani abinci tun satin daya wuce Amma sabida damuwar datagani a idanun faresatun yasa tace zata ci "..
Miqewa Anty fareesa tayi ta shiga ciki Jim kadan ta dawo da plates har guda biyu da serving spoon Dana cin abinci,ajewa tayi sannan ta koma ta debo kofuna ta kawosu, ledojin data shigo dasu ta bubbude ta fidda Dan madaidaicin cooler abinci da sauran abubuwan ciye ciye data kawo

Gyara zama umma tayi tanata kallon yadda ta ke saka mata abincin,komin ta a nitse yake tamkar yarta rufaida,fried chicken stew ne da spagehti,adan roba haka kuma tayi couslou mai kyau ta hada mata dashi da fruit salad da ruwan gora mai sanyi
Tana kammalawa Mika mata tayi tana Dan murmushi umma ta amshi abincin badon ranta yaso ba,a hanklli ta shiga ci sai dai Duk hanklinta naga kan yayanta ne musamman ma rufaida..koma Suna samun abincin suci ko Yaya ma take ciki?shin lpyarta kalau? Duk dai bata sani ba,kuma ta maidashi abun damuwarta.

Tana kan ci anty fareesa ta shiga yayyanka mata fruits daga cikin wayanda ta kawo abarba ne da apple da kuma lemo sai kankana da ayaba.

Umma zan aje miki wannan a fridge in anjima saiki sha.
Yanzu kam nafiso inga kinci abincin nan sosai sabida jikinki babu kwari,karamin Ajiyar zuciya umma ta sauke tace Toh faresatu Allah dai yy miki albarka. .tace Ameen,"can umma tace "uhm dama zan samu wanda zai tayani ci ne Dan bana jin dadin cin abinci ni kadai, babu tantama
Anty fareesa ta bar Duk abunda takeyi tawanke hannunta ta taho suka hau ci tare,mamaki sosai ta bawa umman saidai batace mata uffan ba dake ta fahimce meyasa da can din tace mata tana azumin
'babu laifi sosai Anty reesa ta ja umma ta cika cikinta da abincin tam,sosai take nuna mata kulawa da tausayi Duk dama ata Wani fannin Hakan kusan umarnin mahaifiyarta ne da kuma kakarta hjya mama Dan ako yaushe basada abokiyar tada  damuwarsu sai ita

She is not planning tama gaya musu cewa tazo din,Dan tasan inhar ta fada to tabbas Hajiya mama zata iya barbada maganan awaje har yaje kunnen yaa malam da ko kadan bata son yaji cewa tana zuwa bare a kara saka umma acikin Wani matsalar..

Sosai umma ta samu relieve da kasancewar anty fareesa atare da Ita yau,wacce bata bar gidan ba saida ta gama mata aikin komi ta tsaftace mata gida.

Bayan kwana biyu haka ta kara dawowa each time taxo saita nemi taji damuwarta badon komi ba danta tayata rage abubuwan datake dannewa a zuciyarta tana fama da azaban nauyinsu itakadai..

Barister fareesa tayi iya kokarinta a satin har saida umma ta soma dawowa hayyacin ta..Wani bin inta mata hira harka ga tana dariya sosai

To aranar da yaa malam zai dawo ne sukayi ban kwana kuma aranan ne faressan take hadasu awaya da su hjya jasmine wacce ta gaya mata cewa sun yi tafiya da mijinta Yaa sheik suna can Abuja..

Fatan alheri tayi musu sannan tayi godiya,she was bit ok yanzu kam data samu wayanda suka Dan kwantar mata hankli wajen gaggaya mata maganganu masu sauki wanda suka kara mata jib karfin gwiwar fuskantar rayuwa..

Abu daya kawai tasaka aranta yanzu kuma shine Allah
..dukkan lamarinta da na yayan ta gaba daya ta mikka masa
Ta kuma saka aranta cewa zai Kare mata yayanta a Duk Inda suke a Duk halin da suke ciki..

*Bayan kwana biyu*

Agogon _Mariano de veio_ din dake manne jikin bango ne yayi ticking dot 6:30am dai dai na safiya tare da yin sautin alarm mai karar morning scent wanda tuni ya gauraye wajen da kara mai cikka kunne.

Tashi yayi tare da mikewa daga kan lallausan katafaren gadon da yake kwance akai,yana mai karanto adduar tashi daga bacci i.e Alhamdulillahillazi ahyana ba'a dama amatana wa illaihin nnushur sannan ya kara dayiwa Annabi (SAW) salati

Dagowa yayi sann ya juya ya kalli agogon da ya farkar dashi daga bacci yaga har 6:35am tayi,da sauri ya diro kasa daga nan baijira ba ya fada toilet din dake cikin dakinshi

cikin hanzari ya saka toothpaste acikin brush dinsa wanda yake fari kal brand din bojaler senteler,da sauri sauri yayi brushing teeth dinsa ya kunna shower yay wanka sannan ya fito daga toilet din daure da hadadden white body towel da kuma wani dan karamin towel din a hannunshi yana famar goge fuskarshi da ita har ya karaso gaban wani babban mirror da mutum kan iya kallon kanshi gaba daya tun daga kai har kafa yana kare makansa kallo,..

yana cikin karasa goge kanshin kenan zai shafa mai yaji karar wayarshi na ringing,Dan daga girarsa sama yy da har yayi kaman bazai dauka ba sai kuma ya juya ya karasa inda wayar take yana ganin mai kiran da sauri yayi maza ya dauka tare da neman wajen zama cikin risina kai mai nuna alamar tsantsar girmamawa tamkar mai Kiran na gabanshi zama yayi kamin ya kara wayar a kunnanshi tare da cewa Hello mummy kin tashi lpya?Daga daya bangaren aka amsa da cewa lpya  Alhamdulillah  sannan aka sake ce mishi harka shirya ka fita ne yace à ah mumy Amma saura kadan yanzu zan shirya in fita

tace ok,uhm yawwa Dama munyi magana da Aina'u ne tace ta kikkiraka baka dagawa ko lafiya?

Take walwalar fuskan sa ta dauke tuno da abunda ya afku jiya, Dan shiru yayi sannan yace lpya kalau mumy bacci nayi dawuri or..or maybe I wasn't aware..

Tace toh saika nemeta pls..it's asif she is tensed ni bangane mata ba,ko Hala bata San zaka dawo nigeria Ajiyan bane oho?I dint know that she is not back yet Ni tun ranar da tace min zasuje kadunar ma bamu kara magana awaya ba,but yestade she told me dat you ain't picking up..nikuma bana gidan ma bare ince a kiraka ka amsa.

Adan gaggauce Yace "No..Karki damu mama,I will call her..bye.

Yana fadan Hakan ya katse wayar sa batare daya jira Wani furucinta ba,da alamar ranshi ya lalace.

Closet din kayanshi ya bude sannan ya dauko wani sky blue din getzner mai laushi da tsada ya saka ajikinshi,ya bude wata madaidaicyr transparent visconte safe ya dauko cuff links dinshi masu azaban kyau na kamfanin Mandarina duck sannan ya sanya su a hannayen rigartasa tare da dauko hularsa ta Zanna bukar shima sky blue mai ratsin brownish_black da dot din red ya seta Dede a kanshi kamar da kan akayi hular ta zauna d'as das,agogon shi na rolex oyster ya makala a hannunshi na dama sannan ya dauki Turaren paco rabane da Calvin Klein dake gaban mirror dinshin yafesasu a jikinshi
Duk Inda ya juya kansa qamshin ne ke binshi
... kamin ya koma gaban wata small coffee table,hannu ya Mika ya dauki car key din motarsa dake ajiye akai da kuma wayarsa daya jefata acikin aljihu sannan ya jawo takalminshi baqi half cover ya fito  daga dakin yana saukowa yana dan kallon agogon hannun shi yaga wai har bakwai da rabi tayi

Saukowa yake daga kan benen cikin kwanciyar hankali da natsuwa har ya karasa sauka ya isa katafaren parlourn su, karasowa yayi cikin parlourn ya isa wajen wani dattijon mutum mai dan haske yana sanye da manyan kaya na alfarma , sanye yake da farin glasshi à  idonshi  hannunshi kuma riqe yake da Wani katoton littafin sharia at same time ya saka tashar Iqra yana jin yadda yaran musulmai ke nuna farin ciki ga ubangijinsu wajen saukar da karatun qur'anin sa mai girma da sukayi.

gabanshi kuma glass table ne dauke da hadadden royal flask din tea an zuba Kadan a dan karamin transparent kofi na shayi,Nan ya karasa gaban sa tare da zama dab da kafan dattijon tare da Ce mishi "fatan ka tashi lpya Abbu?Barka da dawowa,
Sauke lttafin dattijon yay daga idanun sa yadan kallesa kadan yace barka dai mufrad ka tashi lafiya? yace Alhamdulillah abbu sannan yace mishi Jiya na tura Adamu da aika wajen ka an sanar maka?yace min ka rufe kofa kuma wayoyinka ma duk a kashe

A hankli yace ehh Abbu na gajine jiyan shiyasa na shiga da wuri na kwanta,Amma kauyukan da kace aje kai zakka an gayamin wai hanyoyinsu babu kyau amma keeyan ya kirani ya fadamin
Komi ya tafi daidai

Atakaice dattijon Yace ehh tun jiya ya kirani,daga Nan shima yace okay bari in shiga  inga Hajiya mama dan tun safe ta aika a kirani ban San meye matsalarta ba

murmushinsu na manya kawai alhj zayd yy yace ai Hajiya tun karfe biyar ta tashi bata koma ba sai da tashi kowa har masu aikin gidan nan,kaga tun sassafe aketa hidiman dafe dafe.hmmmn

Dan murmushi yay yace ai Hajiya akwai kokari,ya karashe maganan sa Tare da miqewa tsaye,"na barka lpya Abbu..
gyada kai kawai yay ya Dan kallon sa harya sauka daga kan matakala da basu fi taku sha biyar ba yabi wata hanya har ya isa bangaren kakarsu tare da yar sallama a bakin kofar Wani Text ne ya shigo wayarsa adaidai lokacin da yay knocking kofar palorn sai ya tsaya karantawa,daga ciki kuwa nazli ce a zaune akan dinning table tana shan corflakes wanda ta tula masa rabin kwalin madarar dano da dan water flask haka agabanta dake bata ma iya shan shi da ruwan sanyi ba.

Daga cikin palon kuma Wani hadadden matashin saurayi ne wanda kwata kwata bazai wuce 25 years ba ya nitsu sosai ya maida hankalin sa agaban wani babban tv screen wanda already ya jona da wayarsa ta iphone yana kan buga video game dinsa mai suna Assassin's creed da alaman dukka hanklin sa nakai

Daga ta dayan bangaren kuma shukra ce akan cinyar yar tsofuwar sun babu abunda take sai rabza mata shagwaba,tayi nasha nasha akan cinyarta da system akan cikinta Suna jin wata waqa tare..
Jin an kara yin sallamar yasa ta harare su duka tace
"To wa zaije ya bude muku kofar..

Cikin su kowa ya turo baki,da alaman keeyan kam ko jinsu bayayi,"da gefen ido shukra ta bibbisu da kallon kasan Ido sannan ta dada gyara kwanciyarta tana tabe baki..Nide bazanje ba wallahy
Ai nagaya maki tun jiya na fadi ciwo ma fa kafa na yakeyi
Hjy tace I min shiru waye baisan halinki ba shukra?dagowa ta karayi tana dubanta ..to ke kitashi kije mana ai Nan falon ki ne,baki bude hjy mama tace
In tashi inje ko?toh saukar min da wannan gingrimin kan naki a jikina ki tafi can dashi,ai ba kurguwa uwata ta haifeni ba kune dai
Kuka lakawa kanku sakalci,narkewa ajikinta shukra ta karayi,hjy Dan Allah Kar ki je ni gaskiya bana son in mike zaune,"..a hankli take kallon yayun nata tace baga su Nan zaune ba?su din me sukeyi,hjy taja kunnen ta,cikin biye mata itama kasa kasa ta furta maganan ta tace eh lallai kam to bari dai sujiyoki keeyan kadai ya ishe ki anan, sannan ta juyo ta kalle nazli dake shan cornflake dinta hankli kwance
"Bokan turai ai Kya tashi ki bude mana kofar ko?ko kema kin karya kafan ne inje dakaina,nazli batace uffan ba ta miqe ta nufi kofar ta bude,gaban ta ne yy mummunan faduwa ganin yaa muffy ne a tsaye da uban sauri ta bashi hanya ya wuce tana binshi da gaisuwa,"..good morning yaa muffy".
Muryan ta na Dan rawa ta ce hakan kallon 2 scnds ya mata sannan yace
Morning,me kikeyi a gida?tace hutu aka bamu..shi ne hjya tace wai nadawo Nigeria,shekaran jiya na dawo..
Wani irin kallon ya wtsa mata ya tabe bakin sa sannan ya furta".Good for you
Now..excuse me.
Matsawa tayi can gefe da shi har ya karaso ciki dawuri ta koma kan dinning din ta zauna ta cigaba da shan cornflakes dinta

Shima wajen zaman ya samar makan sa kusa daf da su hjiya ganin yadda dukan su suka sha jinin jikinsu yasa shi hade rai yy tamkar bai ma gansu ba

"Keeyan ne ya juyo ya fara gaishe sa ya amsa masa normally ,baima jira ba ya katse kallon game din San kawai yay waje,a hankli shukra ta janye jikinta zata miqe saura kiris ta fadi
"Get out of here ya daka mata tsawa sanda ta kara tsorata,hjy ta riko ta"a'a ya haka yarinya ta tashi xata gaishe ka zaka Wani hantare ta?.
Kuma fa kafarta ya karye...baima kula mgn da kyau ba ya furta"to meya hanata zuwa asibiti?ita yarinyace da sai angaya mata..ya furta hakan a hankli yana mai relaxing kansa akan cushion din,cike da barin Murya shkra tace..ai Hjya ce..yay saurin dakatar da ita da idanun sa
."Shut ur mouth..ba dake nake magana ba..meit ta nade bakin taja tayi shiru tayi tsuru tsuru ta rasa meyasa yaa muff baya saurara mata arayuwa,
Hjya ma batace musu uffan ba nazli ta gama ta tattara cups din takai kitchen daga Nan bata kara saukowa ba,shukra ta zame tabi bayanta a sudade..

"Ke bazaki saka Ido akansu ba.
Islamiyar da kika ce za' ana koya musu fa..one is busy eating rubbish kinbi kin sakalta wann wawaiyar ta girma bata San ta girma ba,gwara ma maska(keeyan) atleast hutawa yakeyi..

Ai dole zaka ce haka kabi bayan Dan uwanka namiji dake buga game din banza a wofi sabida sukam zunubi kaga suke aikatawa ko?

Dan tsaki ya sake kasar wuyar sa
Why did u call me
Meye?ya dage qirar sa sama yana dubanta a tsime.

Ajiyan zuciya ta sauke ta danyi shiruuu kai kace ba ita ta gama masifa ba"..can ta juyo ta kalle shi ganin ya dauko bootle water yana shirin bude murfin da alaman zaisha,yasa ta kyale sa harya saida ya gama sha yy hamdala..gyara zamanta tayi
Uhmm magaji?ganin ya shareta yasa ta saka fuskar kuliya tace dama wata magana ne ke tafe dani,Idanunshi ya wara akanta da alaman yanaji..Dan shiru tayi sannan ta sauke Wani sasanyar Ajiyan zuciya"...Akan kawun ka ne?
Nace ko zaka iyayin anfani da mutanen ka ka binciko min
Shi Ina son insan halinda jikoki na suke ciki dan Allah magaji kataimaka min bana bacci inna tuno su..Nan da nan muryan ta ya sauya kalar kuka yace hmm,"tou meyasame su su kuma,ta fashe da kuka ai dama baka damu ma dasu ba ta ina zaka San damuwarsu?yan uwanka ne fa mufrad?hr ace baka san halinda yayan kawunka suke ciki ba,kukan ta karawa sauti kamar wanda aka bugeta,yy shiru yana kallon ta sannan ya dauke kansa akanta

Har saida ta sasaauta kukan sannan ya juyo,
"Ki fadamin meyene? ni bazama nake ba bare in sani..Sanin kanki ne abhu yace Kar muje gidan kawu Wani hidima Arne fa yake ce masa

Tace eh Amma ai yan uwan juna ne kuma ni na haifesu duka...hannunka bazai rube kayanke kayar ba tunda shi yace babu ruwanaa ai kai saika na kulawa da rayuwarsu ko?

Hmm kawai yace bayan wasu mintina yace toh ni me kike so nayi musu naga dai dukkan su matan aure ne kowa tana gidan mijinta

Eh nasan da Hakan Amma ai auren bada son ransu bane,yafa hana kowa yaje musu kuma ya hanasu kawo ziyara gida...

Dan Tsaki ya sake yace"..Kuma suka yarda masa ahakan?it's thy choice den..
Dan daure fuskarta tayi ta shiga mita kasar wuyarta tana ta fade fade kusan anan yaji Duk abunda ya afko daya baya Nan

Ganin abuntan bana karewa bane yasa shi ya amsa ta amma badon yaso ba,miqewa tsaye yayi da alamn ficewa zaiyi yace insha Allah Zan sa a duba miki halin da ake ciki,Amma saina nemi izini daga wajen abbu
Dan share fuskarta tayi da bakin mayafinta tana mai washe baki tace toh shikenan,Dan Allah dai ataimaka musu magaji,Duk Inda naka yake au naka ne,ya gyada kansa,dan
Murmushi tasakar masa hade da saka masa albarka
Daga Nan ya sakai ya fice a sashin.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top