chapter 5
*™✓SHADE OF RUFAIDAH*
_BY_
_SURAYYAHMS_
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_
BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 5
*Aina'u makarfi*
_*F1 expresso:emirate street, new extension.kano state,Nigeria.*_
Anguwa ne na manyan mutane wanda shaharar sa bai tsaya ga kyafaffun ginan ginan gidajen zamanin dake nan ba harda kasancewar muhallai na muhimman mutane masu tsantsar daraja,kudi,ilimi,mukami,suna,kai harma da masu mulki da sarauta a kasar.
Anguwa ne wanda aka tsara shi ata can gefe da cikin gari ta Inda kokadan ba a samun yawan cunkuso ko hayaniyar jama'a.
Anyi tsarin anguwar ne street by street kuma kowani street yana da lanes dinsa,so gaba daya anguwar yanada mashiga da mafita guda biyar ne kacal,snn akowani mashigar street akwai manya kuma dogayen dirarrun kofunar karfe wanda zai tabbatr maka da cewa ana rufe kowata gabar shiganta musammn in dare yayi..
A kofar Kowani gaban shiga wata yar tenti ne na jamian tsaro wanda aka musu horo na musanman domin lura da masu shige da fice a anguwar.
Emirate street kusan mafarkin kowani dan adam ne, dan acikin masu kudin ma bakowa yake samun daman zama anan ba,Wa duka anguwar ake cewa "emirate street"saidai lane din ne kawai yake banbanta su Inda zakaga dark golden signal board a manne a jikin kofar kowani mashiga
Gate na farko shine f1 expresso, na biyu f2 expresso...har zuwa f5..sannan acikin ko Wanne gate not less dan 1000 buildings zakagani a jere,a takaice za'ayi iya cewa Duka Duka anguwar emirate street na dauke ne da 5,000 exclusive buildings including malls,restaurant,masjids nd churches hospitals and trade fairs..
Saidai kasuwannin su da asibitan su tamkar masu kawai akayi,dan duka mutanen dake zama awajen are born with silver spoons wanda kullum zakana ganin su cikin swags na high standard of living styles,talaka ko mai karamin karfi bazai taba iya jure expenses din zama anan ba.
A first street wato f1 expresso,Anyi Wani kyafaffen gida wanda yake daura da Gidan Wani shahararren 7starred Army general wanda akai ce masa general murtala kosoko
Wannan gida ya shahara ne sabida tsantsar kyaunsa da yadda aka kawata gaban sa da shuke shuken fulawowi masu ratsa hasken idanu,sai kuma uban tashen kima da mutunci damai gidan yakeyi musamman a idon jama'a....
A jikin babban golden gate din shiga ciki aka manna silver bell plate mai bala'in dauke ido anrubuta 4321 Attor.Zaid D matazu residence.
Yadda tawaje yake a kawace da shuke shuke hakama cikin gidan yake,koina an tsarasa ne cikin tsafta da kwarewat so One single lane ne zai kaika har cikin harabar gidan dake dauke da wata madaidaiciyar parking space da dan karamin cool down na zama ko shakatawa.
So the main mansion stays in d middle,dan sosai ake iya zagaye gidan harta bayansa batare da kakai bangon sa ba,sai ya kasance filin daketa bayan gidan yafi na gaban gidan yawa alaman su mutane ne da basason a gifta musu a bazata bare a shiga cikin harkan personal life dinsu
so Swimming pools dinsu,relaxation outdoor palors da main garage da Duk Wani abu na shakatawa Duk anan abaya suke bata gaba ba..
Cikin gidan kuwa bangare hudu kacal yake dashi
bangaren farko na dauke da sashen iyayen ne sai na biyu na kakar su hjya hasiya,na ukun sashen yaran su ne wanda yake da dakuna masu kyau fadi da yelwa guda takwas dukanin su ajere hudu na kallon hudu,anan nazli da keeyan da shukra suke zama kowada personal room dinsa,sai sauran rooms din da suka rage aka barsu kamar quest room musammn ma in baqon na jini ne ko na kusa da su sosai.
Sashe na karshe shine sashin Babban dansu captain Mufrad matazu.
Shi an bashi side dayane sabida familyn sa da kuma dan balain so da girmama sa da iyayen sa sukeyi..
Banda main palour kowani sashe is fully decorated da 2 bedroom and 2 personal palours,sai kitchen da Dan karamin backyard.
Main palon su an kerasa ne da set din kujeru uku guda bakwai bakwai given a total of 21chairs,bangare guda na wasu mahaukatan reddish colour turkish royal chairs ne masu golden crown,dayan bangaren kuma wasu mahaukatan cozy Asian lush sofas ne wanda aka kera design dinsu da silk nd velvet sai Italian sofas masu turquise nd cool orange throw pillows,kujerun sunyi matukar kawata gidan sabida da bold colours da ornate patterns aka tsarasu Sannan aka hada tsadaddun setin gadgets aka kuma daidaita marching colours duka handles din furnitures din gidan anyi shi ne da wasu Tsadaddun brass knobs wanda ya hada da hannun drawers,cabinets da tuff boards ga kuma duckless airmores mai sanyaya ko ina da uban sanyi.
Muddin dare ya rufa to nan ne zakaga ta wajen gidan na haskawa fiye da na uban kowa a anguwar,badan komi ba sai dan sabida wasu shegun brass lantern din da aka kawata bangon ginin gidan da shi
Ata ciki kuwa kowani sashe na dauke ne da copper lanterns wanda in waje ya nitsa suke Kara haske dakan su,sai madaidaitan crystal chandeliers masu fidda Wani irin sanyin haske wanda yake kara haskaka coriders din gidan mai gaba daya.
Kowani sashi is decorated base on favourite colourn mammallakin sa
Altho sashen yara falo daya ne kacal bakamar sauran sashunan da suke da personal sitting rooms ba...
Dayake ma yawancin su bayan zama a kasar bane so the house alwys seems quiet and cool,face sashen hajya mama dake ita mai mugun son jama'a,she is the founder nd owner of shahararren gidan marayun nan na "Asiya children foundation"
Inda take amsar marayu da yaran da aka yarda su wanda ba asan iyayen suba
Tun mijinta alhj dikko matazu na raye take iya bakin kokorinta wajen hidima da wannan wajen,gashi yanzu harta tsufa batama iya zuwa wajen sosai,dalilin haka yasa ta dora amintatun ma'aikatan ta suna gudanar mata da komi ayadda take tsara musu shi cikin aminci kuma fisabillahi
Her foundation became one of the best mortheless homes a arewa gaba daya sabida a harkan ta ita sam bata sako cakwakiyar siyasa ko riya aciki.
So Duk abunda takeyi takance sabida Allah tayi,she spend all her life feeding,educating and clothing wayannan yaran da basu da galihu time to time haka danta alhj zayd yakansaka gasar cin jarabawa kuma Duk wanyanda sukaci saiya dauki nauyinsu zuwa yin karatu a kasar waje..
Ita kuma Hjya jasmine tayi karatun ta sosai hartakai matakain PhD amma tsabar son datakeyi ma aurenta yasa taki bada himma wajen riqe Wani muqamin gwamnati ko zaman office Wani Dan boutique kawai ta bude mai girma sosai a anguwarsun tana saida designer cloths,bags,shoes,jewelries,cosmetics da exclusive spa services wanda tun daga kasar waje ma akanzo mata Ciniki.
Ita sam babu ruwanta da shirgen kowa,she had few friends,Besides her life fully depend on her family,wato daga mamanta hjy saddika da kuma kaninta Imad sai mijinta da yayan ta.
Hjy jasm sam bata da matsalar mugun hali face mutum ya tabota,tana da kyau na gani na fada tsayayya ce mai diri kuma fara ce sosai saidai ba irin farin dau din nan ba kuma tana mugun kama da brodanta imad dan badon taba shi shekaru sosai ba da babu abunda zaihana ace musu tagwaye,saidai Duk yayan ta fuskar ubansu sukabi babban dansu ne kawai za a iya cewa ya Dan hada kamannin su duka which is why son da suke masa yayi yawa fiye da na komai a xukatansu.
******
11:30pm
Dauke da white hair towel ya Fito yana goge black and silky smooth hair dinsa xtrmely gently daga ganin sa kaga shigen mutum mai mugun son jiki
he's 6ft tall,with healthy looking fresh arbs,six packed chest wanda wings dinsa ya fito sosai ya bashi wata mahaukaciyar sexy model look, Wani irin sheqi fatar jikinsan yakei hade da damshi damshn ruwan dake manne da fatar jikin san sai yyi looking sexy,fresh,young and charming.
Captain MUFRAD ZAYD MATAZU is a 29 year old naval captain
wanda acikin gata,tsantsar so da jarumta iyayen sa suka raine shi,tun tasowar sa ake kiran sa da suna captain MUFFY sabida mugun son profession dinsa dayakeyi na navy,shiyasa ma shi baiyi wani civilian school,tun yana dan karami aka kaisa asalin military school yaje yy karatun sa ana masa training da sauran su har ya girma.
Rayuwa Bai taba masa wahala ba saboda he's so vibrant and enthusiastic about his career yana matukar martaba aikin sa a zuciyarsa
A Lokacin da capt muffy yake wani mission dinsa a south korea anan ne suka soma haduwa da Matarsa AINA'U ABUBAKAR MAKARFI wacce a yanzu haka take da 25yrs a duniya,.
Aina'u kyayakkwar mace ce,creme de' la creame,irin yan matan nan ne da ake kira bugun abuja,Ita da iyayen ta suna da zama ne a garin kaduna anguwan nan na badarawa.
Babban yace wajen hajiya Jamila umar matar wani retired permanent sec na offishin gwamnan kaduna,wato Alhj Abubakar MAKARFI
Tana da babban kawarta kuma blood junior sister ta watoh ZAHRA
ABBAKAR MAKARFI wanda tsiran age din su bazaifi shekara biyu ba .
Da shike mahaifinsu Aina'u tunda chan Suna kanana ya rasu sai tarin dukiyar su yay kasa ya kuma tarwatse anan ne kuma hajiya Jamila ta shiga Wani kungiya na yan HISBA tana sadaukar da rayuwanta da lokacinta musamman wajen kare haqqi da mutuncin mata.
Saidai babu irin duniyar da yayan ta ba suci don tarbiya irinna girman carpet da tiles aka basu a dacan,all her girls are so spoilt and addicted to modern westenisation shiyasa a Duk Inda kudi da kyale kyalen duniya yake anan suma zaka gansu kai da fata dan sosai suka tsane rayuwar talauci arayuwarsu
Aina'u itace babba kuma itace mai bala'in girman kan dan tasowar su take nuna son high life dan ita ji take tamkar ita ke da iko da kowa da komi a duniyan nan..
A sanadiyyar wasiyar Wani abokinsa da aka kashe a filin daga capt muffy suka hadu da Matarsa Aina'u makarfi
Dake abokin san was her far cousin wanda dama can shiyake dan taimaka musu da kudin da suke rayuwan karyan nasu dashi wanda Bai sani ba,so ranar da zai mutu he got no option face ya hada Aina'u da abokin sa muffy,all his life ya dauka da kudin nn dayake basu suke ci suke sha sukuma rufa makansu asiri baisan hatta mahaifiyar su bata San suna aikata haka ba,sudai daga sunkirashi zai turo musu kudi suje shopping din kayan duniya da kayan kyale kyale Dan kawai suma suyi kama da yaran masu kudi,jin kamar in ya mutun zasu tozarta yasa saiya roke alfarman amininsa capt muffy daya taimaka ya cigaba da tura musu kudin fisabillahi,daga nan ita kuma Aina'u tagansa sai taji a duniya babu Wani namiji daya mata ta aura sai shi,da tsiya da drama da kukkusawa wajajen malamai haka ta dinga bibiyarshi har saida Allah yazo ya cimma mata burinta akansa,1year kenan da auren su Sai dai bata Wani more auren ba cos a lokacin Auren ne aka nada capt muffy a matsayin sa na youngest nigerian naval comissioned officer in coast guards na united states da kasar france..
Manya daga chan sama suna mugun ji da shi sabida jarumtan sa da kwarewan sa wajen aikin sa, sannan da matsayin mahaifinsa na mai fada aji,shiyasa ma tun tasowar sa yake da daurin gindi in such a way dat bayama cika xuwa aiki sai in Wani abu muhimmi ya taso, a kullum shi baida aiki face bada oders daga offishin sa,rarely yake fita field da kansa cos It's always feel like sun bashi matsayin captain din ne kawai sabida karancin shekarun sa amma a niyyarsu sunso ace ya fito ne a babban Rear admiral of the lower half kafun yaje gaba,So now he is superior to a commander and a junior to a rear admiral of the lower half..
sai dai kuma aduk inda wani abu mai muhimmaci ya taso to tabbas shi din kawai ake nema hakan yasa baya yawan samun zama bare yayi lokacin matar sa,sabida kaff superior dinsa sunfi jin dadin wakilcin sa akan harkokin su fiye da sauran yan uwansa,shiyasa arayuwan sa banda uban meetings da tafiye tafiye babu abunda yafiye saka kansa akai.
Matar sa Aina'u harta gaji da mita akan rashin bata cikakken kulawarsa da lokacin sa daya sabayi,tun watan su na farko dayin auren da ya daure yakaita honeymoon a korea
Sukayi 5 days tare daga nan sai bata kara samun cikakken kulawarsa ba
Infact she can swear dat a shekara dayan nan da sukayi aure baifi sau shida zuwa takwas ya kwanta da ita kwanciyar aure ba,he is alwys busy travelling,or in a closed door meeting with his superiors,Wani lokaci saiyayi 2_3month bai dawo nigeria ba,Wani bin ma koya dawo din in suna tare zai jawota jikinshi yay pamparing dinta nadan lokaci kadan kamar dagaske but daga zarar wayarsa yayi kara an kirasa aiki to ko acikin dare ne he won't spare 1 minute saiya shirya ya tafi ya barta.
Tayi borin tayi fadan Wani bin har kuka take masa tsaban fushi,da baqin ciki,but his career is something he loves more than anything,
In ta fiye damun sa da korafi ma baiya cewa komi saidai taga ya tattara kayansa ya koma can gidan su na abuja kuma bazai taba dawo mata ba harsai ta dawo dakanta ta lallabeshi
Mufrad Wani irin miskilin Mutum ne wanda baidamu da komi ba sai abun daya saka agaba.
Dan haka da wuya kaga fushin Wani ko takurawar Mutum ya dame sa,Mutum ne dake da Wuyan sha'ani,wanda mutum mai karancin hakuri bazai taba jituwa dashi ba
Her first 4 month agidan sa was hell of challenge aganin ta tasha walakancin da harta mutu bazata iya mantawa ba,anayin auren soyayya dan aji dadi amma nata kam was so doom and unromantic,it's feels like shi kwata kwata baiyi dokin auren ba ma,ainau tasha yin yaji taje gidansu Wani binma batare da sannun sa ba har a dawo da ita
Kanwar ta zarah wanda ake yawan cewa mimi
Itace uwar gijiyarta,kanwarta ce amma itake kulla mata komi ta kuma dorata akai musamman na yadda zata tafiyar da rayuwar auren ta akan mijin ta MUFRAD,..
Daga farko ma zarahn itace tayi ummul abaisin samun kan MUFRAD wa sister ta Aina'u,Inda tayi introducing dinta wajn wata kilalliyar yar iskan kawarta mai suna ZEE ZEE,wanda ta shahara wajen bin muguyen Malaman tsubbu da arnayen masafan bokaye .
Duk dama ita Aina'u yar zamani ce asalinta batafiye son harka da sihiri ko bokanci ba kabarta da son life da jiji da kai tana mugun daukaka kanta saidai data lura cewa tabbas zata iya rasa MUFRAD a matsayin miji yasa da wurwuri ta saduda ta bada cikakken hadin kai
Zahra da zee zee suka kai ta aka mata aiki sosai akansa.
An mata aikin ne da zimman zasu rife bakin sa,su toshe tunanin sa harya aureta,Wani dan powder da turare ya bata ta dinga shafawa and she was extremely happy da burinta ya cika akansa suka fara son juna batare da Wani jaaa ba shiyasa ma ta shagala ta dora buri mai girman gaske akan zamntakewar aurensu,she tot he will be hers,zaina binta yana lashe kafarta tsabar so Ita kuma tana juyashi yadda taga dama unfortunately da akayi auren abun sai baimata yadda take so ba.
Gashi nan dai Suna bala'in soyewar amma Daga zarar ya fara prioritizing aikin sa akanta,sai ta soma jin tsananin tashin hankli,a farko ma tayi zaton ko laifin maganin mata ne,daga baya tagane ba hakan bane,...
Sau babu adadi takan kira zarah ta ce mata lallai akoma mata wajen malami a tambaya saidai ko anje saidai ya karacin kudinsu yace musu yyi aiki
Amma basa ganin sauyi akan komi
Da kyar da bala'i tazo ta gane cewa ashe basarwa da nuna baidamu da itan dayakeyi ba habit dinsa ne,kuma babu yadda ta iya dashi musamman akan yadda yake daraja Aikin sa..
After like six month dayin auren sun itama tafara daukan matakai na tsare gida,Ita tana da girman kan da yake sa tajin haushin kanta musamman wajen bibiyar mutumin da bai Wani damu da Ita ba,wai ahaka ma dan mufrad ne, tabbas dawani namijin ne da tuntuni tacikawa rigarta iska Dan ita mace ce mai xuciya sosai, ,but she loves mufrad with her soul nd body,irin son da ba a ma iya fadansa,ba a iya iya kayyade shi..
Ita kadai kawai tasan metakeji akansa,dan tun ranar ta fara ganin sa ta rasa hanklinta da nitsuwarta gaba daya a duniyan nan.
Saidai sabida yanayin halinsa yasa dole tadau mataki,don ta gama sawa aranta cewa mazan zamanin nan ba mazajen da za a cimmusu da soyayya kadai bane yan inbaka yine bani waje,dan haka da wuri ta fara ja makanta layi ta shiga koya makanta yadda zatayi control din kanta agaban sa,musmn wajen rage zafin son shi dake ciccin a zuciyarta wanda yake yawan daga mata hankli
Da kyar ta iya cimma burinta na yin hakan,sai kwata kwata ta shiga dauke masa wuta ta dena ma yawan damunsa da mita da yawan calls da uwa uba son kushe aikinsa data sabayi,kuma sosai hakan ya temaketa wajen kara makanta martaba a idanunsa
A hankli har ya dawo yana kulata sosai,harma inyaji shirun yay yawa saiya kirata ya nemeta daknsa sabanin da can dayake guje mata saboda bayason yawan mitarta da korafi
Aina'u ta takasance mace wayayyiya dan haka tanada wayo sosai,When ever he is acting lovey dubey with her ita kuma anan saita kama ajinta tajashi can sama ta rinka xubamai rigima
,arayuwa tana mugun azaban son shi,irin son nan mai ciccin mutum arai amma a hakan dai take dannewa tayi abinda taga bazai barar mata da martabanta a idanun sa ba.
Tun daga haka ta soma kwace makanta liberty ya zamto kamar ma yana dan jin shakkarta
Rana daya ta sashi dole akan ya nema mata aikin office a ministry of finance
Bai ki mata ba,he use his connection aka bata senior manager,so every morning zakaga ta shirya ta fice aiki bazata kuma dawo ba sai can da Yamma..
Saidai Kamar yadda hausawa sukace daga gyaran gira akan rasa ido, hakan ne yakeso ya faru..
While he was trying to bend his ways ita kuma saita dora girman kai anata sha'anin sabida dama burinta ne ta ga ta mallake sa yana binta kamar wawa,ita kuma ta zamto masa Tamkar abun bauta
Tun dataga yana kulawa sai ta dawo Babu ruwanta da duma kanta akan yi masa girki bare pampering dinsa
So she does that only when she feel like doing it, wai ahakan ji take kamar tana rama walakncin daya mammata ne a farkon auren su..
Ahakan rayuwar su ya cigaba da kasancewa yau dadi gobe babu dadi...
Shikansa capt ayanzu sam ya dena gane salon soyayyar matar sa akanshi Wani bin inta soma wuce gona da iri saidai ya tattara kayansa ya bar mata gidan
****
Thurs 11.58pm
Daga wanka ya fito Yana kan goge kan nasa dayake fidda Wani uban sheqi tsabar bakin dayayi, can yayi karamin scof tare da furzan iska ta cute small lips din sa ya kalli agogon dake manne a bango ya hangi lokaci,dan dafe kansa yy cikin rashin jin dadin jin motsin ta
"I know,tunda dare yaja har haka maybe she won't come"..ya Raya hakan aransa. Aje hair wipes din yay'ya dada kallon kansa ta mirror"..
Wani irin shafo saman kirjinsa ya shigayi yana lullumshe ido cikin dan karamin numfashi can kadan makoshin sa ya furta im so horny cant just sleep like this.
Daga Nan Marmaza ya nufi wardrobe ya dauko wata silky dark coloured sleeping robe ya nadeta tsafff ajikinsa ya kuma daure da yar igiyarta ta cikinsa babu komi face yar boxers dinsa Sai ya cigaba da abunda yake yi,saida ya tattala kansa tsaf ya kimtsa kansa yana zuba wani mahaukatan qamshin turare sannan ya bude kofan sa zai fita nan suka ci karo da Aina'u a bakin kofar dakinsan.
Da hakane zamuyi FREE PARTS DIN?No VOTES FEW COMENTS HMMM AM STILL OBSERVING,DA ALAMA ZA'A FASA BONDING DIN TUNDA BAN IYA GWANINTA BA😭😭😭😭😭
Surayyahms 08060712446
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top