chapter 4:whipped
PLEASE VOTE DAN ALLAH 🙏🙏
BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 4
Whipped
Washe gari da safe
Wuraren shida da rabi rufaida ta farka awahale sabida Wani mugun zazzafar zazzabin daya lullubeta tun jiya cikin dare,da kyar ta iya bude kumburarun idanunta,jikinta yy lagwas dan har wani kyarman sanyi sanyi takeyi babu abunda take sai maida nishi qasa qasa alaman zazzabin ya shigeta sosai kuma yagama nakasa mata gabobin jiki....
Addu'an tashi daga bacci tayi kafin ahankali ta sauko daga kan gadon rike da kanta dake mata Wani irin ciwo,juyawa tayi a hankli ta kalli kofar dakin, ganin ko ina aakulle yasa tay saurin dauke idonta daga nan ta bude kofan bandakin ta shiga,ruwa mai sanyi ta deba atafin hannun ta ta watsoshi akan fuskarta da jikinta,bata Wani dade ba tafito fuskarta da gaban riganta a jike da ruwar da alamar alwala kawai tayi ta fito,agefen gadonta ta same waje ta zauna tana maida kananan Ajiyan zuciya,dan tagumi tayi tukun, can anjima kuma ta sauke Wani nannuyar Ajiyan zuciyar,abubuwan da suka faru jiya ne suka shiga bijiro mata ta fara tunowa,tamkar wacce aka watsa wa garwashin wuta haka ta dinga ji a cikin zuciyarta,atake fuskarta yy jaaa ruwan hawayenta suka shiga zubowa yuuu daya nabin daya,lumshe idanun ta tayi a hankli tanamei diff da numfashinta har nadan Wani lokaci tafi minti talatin ahaka bata motsa ba,can dai ta sauke Ajiyan zuciya wani irin dauriyar da batasan da shi bane ya tason mata, jakar kayanta ta jawo ta hau bincikawa can ta cikaro da Wani black women jallabiyar da ummanta ta fara siyamata arayuwarta,tamkar abaya haka yake saidai babu kwalliyar komi ajikin shi saidai yana da kauri.
Miqewa tsaye tayi ta sauya pants da bra dinta ta saka wasu wankakku sannan ta zura rigar ajikinta ta kuma tattara wajen tsaf,gefe ta dawo ta shimfida sallayarta batare da bata lokaci ba ta gabatar da sallah ra'aka biyu,bayan tayi sallama bata jira komi ba qur'aninta ta dauka ta fara karanta shi tun daga kan suratul baqara har izuwa suratul nisa'i batare da hutu ba..which took her almost 3 hrs awajen,tana idarwa ta ajiye qur'anin tana mai jinjiga bayanta da bango,runtse idanun tayi jin yadda ko inanta yay sanyi gabobin jikinta Duka suka mutu,hannun ta da kafafunta ma rawa sukeyi dakansu,taji sam batajin dadi,her heart was soo heavy,tana matukar bukatar wanda zai saurare ta yaji abinda ke cikin ranta,ji take kmr tana tsananin bukatar taimako,sai dai tasan ayanzu babu wani wanda zai iya taimaka mata sai mahaliccin ta,Wani irin kukan ne yaso ya kufce mata tayi sauri takai hannunta kan labbanta ta rufe bakin nata,yau ko kadan bataso tajefa kanta a cikin yanayin da bazata iya controlling dinshi ba,dan ita kadai tasan azaban wahalar da tasha jiya data kasa iya danne zuciyarta,daga hannun ta sama tayi kanta shima na kallon saman hawayen ta masu tsananin rauni na zirya daga cikin ramin idanunta,muryan ta ne ya shiga rawa cikin sheshekr kukan Tace
"yah Allah na,ya Allah ka saukakamin"Kafirta dani acikin wannan kuncin, ya Allah kacika min burina masu kyau arayuwa...kasa na zamto mai haquri da yi maka biyayya.
Just as she want to utter another word taji motsin alaman bude kofa dagata bayanta
A firgice ta juyo ta kalle wajen jin alaman wayanda suke shirin shigowa nan take ta gane cewa yaa malam ne da hajya mama, kan kace kobo har ya bude musu kofar sun shigo ciki,suna hade ido kuwa ta miqe tsaye babu shiri ta sadda kanta can kasa,dukkan su kallon ta sukeyi batare da wanin su ya furta mata uffan ba,Ganin ta hakan ya bala'in sanyaya musu ransu ba kamar yadda sukayi tsammanin samunta ba,"cikin sauri hjy mama ta bangaje shi ta karaso gabanta..RUFAI..Allah sarki rufai,har kin tashi?Allah sarki magajiya ta,yar amana yar albarka,toh ya jikin na ki?..dada sunkuyar da kanta kasa tayi kawai batace uffan ba,ta shiga shafa kanta a hankli cikin tausayawa da kulawa "sannu rufaida Allah yy miki albarka,insha Allahu zakiyi nasara arayuwarki yan baqin ciki zasu sha kallo...karamin tsaki yaa malam ya sake adaidai lokacin da wayarsa tayi yar kara bai jira ba ya kara a kunne,dan shiru ne ya biyo baya kafin yace
..toh toh gamu nan fitowa..Jin hakan yasa kirjinta ya kara bada sautin rasss.
Cikin sanyin yanayi da dago ta kalle idanun Hajiya Mama dake kanta,atake idanunta ya kara cikewa tafff da ruwa tamkar wacce zata sauke korama
,numfashinta ne ya sauya kala da alaman magana take so tayi amma takasa iya bude bakinta,hannunta taji an riqe cikin tsananin tausayawa hakan ya dada bata kwarin gwiwar furta abunda ke bakinta a hankli Tace hjya...umma fa?ina umma na..jawota hjy tayi zuwa jikinta
Batare data amsa ta ba ta shiga share mata hawayen da suka riga suka kufce mata akan fuskarta,"kiyi shiru hadieza tana nan zata zo..kuyi sallama...itama saita saki hawaye ayayin da rufaidar ta fashe da Wani rusashen kuka..
Adaidai lokacin yaa malam ya katse wayarsa,.."bani son shashanci"..ya harxuko kansu da masifa,"mama muje akaita mutane nata jiranta awaje wai meye haka kukeyi?..cike da hatsala hjy mama ta dakatar dashi cikin muryan kuka Tace "ai saika fita kaje muna zuwa..ko dole ne saika sani agaba ubana?ai sai kaje can wajen wayanda suka fini daraja agunka wayanda sukadai ke iya gayama kaji..
Nidai wannan aure Allah yasani bada yawun bakina ba,sabida Allah Duk anbi rikitawa yarinya hankli,ancutar da ita,Toh Allah ya isa miki rufai...cikin yar kuka takarashe tabi ta rungume yar jikarta ajikinta sosai suna kan kukan tare,"uffan baice musu ba tunda dai yasan babu yadda zasuyi iya dashi ayanzun tunda an riga an daura auren rufaida.
Aransa yace Bana barin nan waje sai naga fitarku dan ba abun mamaki bane hjya ta bude mata window Tace mata ta gudu..kyam ya tsaya awajen agaban su yanata jin kukan su,shukam ko ajikinshi gani yake ma kamar ana batamai lokaci..
Banda tsuka da harara babu abunda yake watso musu..
Can hjya ta kwace rufaida ajikinta ta jin kamar numfashinta na shirin daukewa
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun..rufai?
Ta shiga tattaba ta can ta dube setin kofar ta shiga kwalla kira hadieza,hadieza?
Fuskan Yaa malam kamar zai tarwatse tsaban takaicin su a zafafe yace,toh me zatazo tayi miki anan bayan angama magana,"batako kulashi ba ta cigaba da tsaga kira da karfin balai can anjima saiga umma ta shigo adan birkice..."hajy lpya kuwa?..ganin su tayi a manne da juna sai kuka sukeyi rufaidar ta kasa koda iya bude idanunta sanda taji muryan umman ta ayanzu..
Suna hade ido ta kwace jikinta a jikin hjy mama da gudu ta taho zata taho wajenta,wufff taji an capke ta,yaa malam ne a tsakanin su ya ruko hannun rufaidar tamkar barauniyar datayi satan abinci,"..kada wata mata ta karaso nan...ke wuce mutafi"..
Ta juyo a rikice ta kallesa,"Baba dan Allah kayahakuri ka yafemin in nay maka laifi"..baba dan Allah ka saurareni..babaaa..
Wallahi bana son shi bana son auren
Baba kamun adalci kabari banajin zan iya rayuwata ahaka.
Jawota har waje yay kamar baijin metake furtawa baima kula ta ba,atare hajy mama da umma suka biyo bayan su...babu abunda rufaida takeyi sai kuka tana rokon sa..
Janta yakeyi Bai kuma saurara ba har sanda suka fito kofar gida,dake ma babu yan shaglin hidimar biki motoci biyu ne rak a fake a kofar gidan sun..
Wasu dattijai maza ne aciki sai wata tsohuwar mata,
wacce ana fitowa da rufaida itama ta fito ta rikota..
Tsananta rawa jikin rufaida yay tana famar hargowa da qarfin da Allah ya bata ko inan ta yay sanyi sai miqo hannun ta take tanajin kamar da ranta ake shirin rabata...cikin kuka take cewa
"..baba dan Allah kayi hakuri kayafeni
..ta juya ta kalle mahaifiyartan acan gefe wacce tuni ta jingina da bango ta dafe bayanta tana zubda hawayenta sosai,"umma bazan iya rabuwa dake ba..umma bana son wannan auren..dan Allah ku taimakeni..
Cikin haka Hjy mama ta koma cikin gidan da balain gudu kuma a birkice,babu abunda tsohuwar takeyi sai rusa kuka wayarta ta shiga bincikawa da niyyar kiran danta zaidu yazo ya taimaka ma rufaida saidai kafin ta dawo har anjefa rufaida a motar sun kama hanyar tafiya da ita.
Ta kara wayar a kunnenta,alhj zayd yanata helo helo amma babu abunda ta iya cewa sai kuka
Can da zuciya ya debe ta ta juyo ta kalle yaaa malam
Tace Allah ya isawa rufaida..Allah ya isa..cikin sauri ya nade bujen garden sa ya bar wajen..
Dan baison ta rinka masa mummunan baki,wucewa yay sashen sa ya kulle kofa,yay maza ya jawo jakar kudin da aka bashi akan rufaida ya hau kirgawa dan bakaramin kudi aka basa ayau din ba half of them in naira half in dollars aganin sa wayannan kudi sun ishe sa ya gudanar da rayuwar sa.
Daga waje babu abunda ke tashi sai sheshekr su,can hjya mama ta zago gaban umma da niyyar sassaita ta dan sosai hadiexa take bata tausayi Duk dama tasha ganin laifinta nakin yin yaqi wa kanta,ita kanta tasan hadieza da haquri kawai take zaman gidan danta bawai dan son ranta ba.
Duk da cewa Yaa malam danta ne amma harga Allah sam batajin dadi da Allah ya bashi mace mai tsananin haquri da kamala kamar hadieza ba.,kafadun ta ta dafa,alokacin kukan kawai takeyi,,
"Kiyi haquri hadieza muje ciki kishiga gida kar azo aganki anan ayita gulmacen gulmacen auren yanki..Bukar ya riga ya cuce rufaida da sauran yayan sa Allah ya isawa rufaida...bata fasa ba itama ta kara barkewa da kukan
Nan umma hadiexa ta daure ta dago kanta idanun ta sunyi jajur sun kumbura a tunanin ta ko zata kalle rufaida agaban ta koda tayi mata kallon karshe,Wani jiri ne ya kwashe ta ganin wajen wayam sai a sannan kwakwlnta a ya shiga tsinkayi maganganun da hjy mama taketa furtawa na tsinuwa akan an tafi mata da rufaida,"atake idanunta suka rufe ta soma jin luiiii kamar zata fada kasa,Aikuwa hjy tana kara tabata sai diffff ta yanke jikinta ta fadi kasa sumammiya.
Ihu hjy ta rinka yi da jikin tsufantan nan ta rikito ta koma cikin gidan,anan taci bugun duniya a kofar sashen yaa malam amma bai bude kofar ba bare ya amsa ta,a Duk tunanin sa rashin aikinyi da asara yasa suka daura jarabar masifa maransu akanshi.
Shidai baidamu ba tunda ya cimma burinsa,yau gashi nan a gidan kansa kuma yayi kudin rufan makansa asiri da jarin aurar da yayan sa ga masu hannu da shuni...
A duniya ji yake babu wanda ya isa ya takasa koya nasa gori yace yay masa Wani abu na taimako arayuwarsa.
Jin ba kulata zaiyi ba yasata fitowa ta samu daidaikun matan makwabta har sun firfito ana faman bawa umma taimakon gaggawa,
She went into intense nervous breakdown ko nunfashi batayi bare motsi,anan cikin haka sai ga dirin wata mota,jeep baka kirin kirar landcruiser x20 na tunkarasu,daga ganin motar taso da gudu,tun kan ya tsaya ta fara ihu tana kiran sunan shi
"..Zaidu..zaidu sauko sauko hadiza mutuwa zatayi.na shigga uku ni hasiya wayyo Allah na,..Wani tsayayen mutum aka budewa kofa cikin sauri
dogo yake fari tass da shi mai kakkarfan yanayin jiki,ya saka hadadden yadin shadda grey colour wanda yasha aikin kece raini agaban garen sa, kana ganin sa kaga babban mutum mai martaba kansa dauke yake da nadin malamai wanda aka nannadeshi da hular ciki,tana dirowa kasa Mahaifiyar sa ya soma rikowa ajikin sa ya shiga rarrashinta sannan ya bada driver sa umarni aka dauki umma akayi asibiti da ita cikin gaggawa..
Kallon ta yake ganin yadda ta birkice Duk hanklinta a tashe
...yace.."mama ki kwantar da hanklin ki mana.. ita kuwa babu abunda take sai zubda hawaye
..muryanta a dishe tace zaidu wallh
Bukar ya cuceni
,Allah ya isa tsakani da bukar,..Allah ya wadar naka ya lalace niyau na haifi mugun iri..zata kara furta Wani kalman yayi saurin toshe mata baki, yace "hjy kidena furta Hakan,yaa malam da danki ne,ya zakinayi masa baki irin wannan?ai saiya dada lalacewa ko? muje ki shiga mota akaiki gida.."kanta ta shiga kadawa cikin turjiya Tace A'a.."ina naga ta tafiya bayan ya raba baiwar Allah da yayan ta,zaidu kar ka so kaga rashin imanin da yaron nan Ya tafka mana tun jiya yake dukan yarinyar nan wai dan Tace bata son auren,ta share hawayen ta snn ta cigaba,"in gaya maka yau da safen nan babu tausayi aransa yajawo rufaida yarsa har waje anan yaxo ya miqata hannun wasu mugayen mutane suka tafi da ita,shine fa itama hadizar ta yanki jiki ta fadi,hmmmm,
Allah sarki hadiexa koma mutuwa tayi?naga ko nunfashi bata iya saukewa
Sabon kuka ta fashe da shi..."yoh ba kwanda ma ka mutun ba da a zalunce ka a arabaka da yayanka a irin wannan yanayin?...nidai ka shiga ciki ka same sa ka masa magana tunda shi baijin shawarar kowa to yaje marmaza yayi jinyar matarsa asibiti dan nidashi muka kara hade ido wallhi saina tsine masa albarka dake knsa...mutumin banza wanda baisan ta inda ke masa ciwo ba.
Tunda tafara maganan yaa sheik baice mata uffan ba banda kallon ta dayakei,she look stressed out ta yadda zai fitar da ita anan shine babban damuwar sa dan baison suyita tashin hanklin da zai jawo ayi badaidai ba..
Wayarsa ya fito a aljihu ya dialing wata number,jim kadan saiga driver sa ya dawo,ya juya yace ina kayanki suke a dauko miki gida zaki tafi yanzu sai ki huta inyaso da na gama masa maganan sai in taho nima babu musu Tace A'a bari inje in kwaso su dakaina,in shamata Allahu bana kara taka kafata nan gidan bukar har in mutu bazan kara taka nan ba..
Runtse idanun sa yy alaman baijin dadin furucinta,within some minute ta tattara komi nata ta fito,shida kansa ya bude mata motar ta shiga driver ya kama hanyar cikin gari da ita,suna daf da zasu fita Tace lallai abi da ita taga hadieza so take taji ya akeciki da jikinta.
Da kyar ma driver ya amince dan basu cika saba umarnin yaa sheik ba..
Bayan tafiyarsu yaa sheik bai motsa ba,Wani almajiri ya kira yace masa ya shiga cikin gidan yace ma maigidan Wani babban mutum nason ganinshi,dake yasan Duk almajiran yaa malam sun san shi kudi ya bawa yaron yace karyace shidin ne,Aikuwa ko minti biyar yaron baiyi da dawowa ba saiga yaa malam ya fito da uwar garen sa da alaman hanklinsa akwance yake jin ance hjy mama ta riga ta kama gabanta,Wani miqa wuyar sa yake tana learn gefe da gefe son sanin wanda yake nemansa.
Sai can yaa sheik yy wuf ya bullo abayan sa suna hade idanun su waje guda ya tsime sannan yaja wata arniyar tsaki
Murmushi yaa sheik yy sanin halin dan uwansan sai yay saurin miko masa hannu yace Assalamu alaikum
Yaya malam barkanmu da safiya
Wani banzan kallo ya bi hannun nasa dashi sannan ya dora Hannun san acan sama yyi banga banga ya tokare kofar gidansa dashi,a kasar wuyarsa yace
"Yawwa barkadai"
Yaaa sheik bai damu b ya mayar da hannun sa aljihu
"Yaya bukar nazo wajenka ne..
Yace bagani ba?
Ko sai kamin halinku ne na Arna,zaidu kafa kiyayeni dan ni ba sararka bane kuma kokadan bana son takadaranci meke tafe dakai?yaa sheik bai kulashi ba dake yau baida niyyar suyita dashi ya riga yay rantsuwa tun akan auren yarsa rukayya daya dirka musu tijara, cewa shikam bazai kara shiga tsabgar auren yayan yaa malam ba,yanzun ma badon umarnin hjya ba da babu abunda zaisa shi ya tsaya agaban kungurmin jahilin mutum irinsa,dan shima din ba kyalesa yakeyi ba, yaa malam bai taba kwatanta respecting dinsa ba ko a wasa,daga sun fara tartaunawa sai ya rinka nuna cewa shi babbane ba a isa agaya masa ba..
Gyara tsayuwa Yaa sheik yyi sannan ya isar masa da sakon hjy mama nacewa Matarsa hadiza tana can kwance a asibiti saiya san nayi.
.. shiru yyi abunsa kamar ma badashi akayi maganan ba.
Tuno da cewa haqqi ne akansa daya gaya masa gaskiya a matsayin su na yan uwan jini kuma musulmai yasashi ya dawo ya dubesa cikin girmamawa Yace yaya bukar kaji tsoron Allah,kayi adalci a rayuwan ka da rayuwan yayanka kasan da cewa yaya amana ne awajen iyaye,shikuma amana tamkar Alkwari ne,Wani Nauyi ne mai tsananin girma akan iyayen.
A Duk sanda ka take haqqin yayan ka ko ka zalunce su to ka sani cewa
Allah dakansa zai karba musu haqqin su,a ranar alqiyama,a ranar da baka da abunda zai ceceka sai halinka da aikin ka mai kyau,kaico naga wanda ya mutu ya koma ga Allah mahaifiyar sa tana mai yawan kuka dashi,yaya bukar lokaci bai kurewa ma dan dan adam wajen yin gyaran arayuwarsa face wannan mutumin ya mutu yabar duniya,a matsayina na dan uwanka ina mai baka shwara da kayi adalci kayi kuma amfani da ilimin adiininka ka fahimce tsarin yancin da Allah ya bawa yaya mata sannan kaima ka bawa yayanka wannan yancin koda Allah zai yafe maka.
A Cikin sauri da tsuma yaa malam ya wani hargitso yana mai tsare sa da wata muguwar kallon fushi yace kai zaidu ka dakata min..naga rainin kan
Ya fara yin yawa..
"Harkai ka isa kafadamin magana akan yanci?yaushe kayi ilimi?kaje ka bibiye tarihi zakaji shin ni dan gidan waye ne,waye ubana kuma jinin wayake bin jikina,Ni ba dan gidan Arne bane,Nikaina nan malami ne, dan gidan malami jikan malamai,kuma ilimin ubana shi yake yawo akaina da jinin jikina,ilimi ne da ya tsaga kasashen da suka gaji asalin addinin musulunci ba irin naku ba mai tafe da hudubar kafurai,
nida kagannin nan na wuce abun wasarka ,banda lalacewar duniya Harkai ka isa ina magana kana magana zaidu?waye kai?ko a tarihi ma Allah ya banbanta mu,na fika yin gadon daraja da falala,yaro karyarka kaja dani,Ai kai gadon dukiya da Arnanci kayi,nikuwa na wuce raini,dan ilimi na ajinin jiki na yake,kudin banza kudin wofi kuda kuka butulcewa niiman Allah kukabi tarbiyan Arna kafurai yan uwanku?kai din a ina kayi karatun?kodama aksashen larabawa kayi amma ai bazai kai na da can falala ba,wayannan larabawar naku sun riga sun dulmuya da kafurai suna tafka kafurci waisu yan boko wayayyu,toh Allah tirrrrrr da kafurci Allah wadai naka kuma ya lalace,Kaiwa nan ya gyara tsayuwar sa cikin mugun izgili yana tsantsane muryansa cikin tsantsar nuna girman kan sa yy yar dariya Haha haha haha ha
Yace Yoh zaidu ka saurareni kaji,in wa'azi kake sonji saika tsaya nine zan maka wa'azi bakaine zakamin ba, nina san abunda nake yi,ni inada basirar sanin mene daidai basai an gayamin ba,inde akan yanci ne ai mune nan muka san tsarin yancin ya mace A musulunci
"wato Bayan yancin da addinin musulunci ya lullube diya mace dashi sam bata da buqatar Wani yanci na duniya suba komai suke so ba banda su rabata da Allah da addinin ta nariga na fadawa wa yayana mata a duk wanda yyi kokrin rabasu da Allah to suyi kokri iya iyawarsu su guje shi domin zai rabasu ne da jin dadin rayuwarsu duniya da lahira..
Kuma Duk wanda ya bi Allah babu abunda bazai samar masa ba,bakayi mamaki na ba zaidu?a kaaf anguwar nan ni sukebi sukejin maganata tamkar ubangijin su,inada jama'a inada kuma dalibai.. anan yasa hannuwan ya Wani toshe kunnuwan sa ya doka auzubillahi minashidanirajim da bismilla da sautin muryan sa irinta malaman zaure yanayi yana Murmushi irinta izgilallun malamai
,,wata aya yanko daga cikin ayoyin da suke a izufi biyar Inda Allah yake cewa.."wamai yatawakkalu Alallahi fahuwa hasbuu"...bai ma karashe ta ba ya tsime yace..Zaidu bakinciki shizai hanaka ganin ni'imar da Allah ya lullubeni dashi..
Ina gargadin ka daka sauya wayannan mugayen halayenkan kabini in rabutar da ka,wai Anata riritaka anacewa kana da dukiya kana bi kana fadi wa mutane,toh ai sai ka fito mimbarinka ka fada musu cewa ni bukar dan uwanka Ko biyar dinka bantaba ci ba, a yanzu ka dube ni,da fadi tashi gashi yau nayi Gidan kaina,kuma anaci ana sha agidan ba a rasa suturar sakawa ba, yau kaf yayana mata na aurar dasu ga mazajen su na gari TOH SAI ME?"...Fa bi Ayyi ale'e ..i..rabbi kumatukazzibannn..
Wani shirruuuu yaa sheik yayi yana mai Kada kansa cikin tsantsar rasa abun cewa Can dai ya sauke Ajiyan zuciya kasan wuyarsa yace toh shikenan Allah dai ya kyauta,juyawa yyi kamar wanda zai bar wajen can kuma sai ya dawo ya juyo ta gaban sa ya tsaya cikin nitsuwa yanata kallon sa
"..Yace Yaya Nidai nafada maka gaskiya kuma nasan ka fahimce ta amma bari in gaya maka magana ta ta karshe dakai wala Allah zai maka anfani:
dada kwantar da sautin muryansa yayi cikin aminci yace "...Yaya kai malami ni ban raina hakan ba,amma dai Ka kiyayi duk abunda zai bata maka aikinka,Abunda zai bata maka aikinka ka shine riya,idan kuma ba riya ba to jiji dakai har kaji kafi kowa falala da daraja alhali baka sani ba aikinsa yfi naka koma ya kasance yafika taka tsantsan akan abunda Allah ya haramta,kuma aikinn sa yafi naka karbuwa awajen Allah,idan ko ba jiji dakai ba to son mutanesu yaba maka son yabonsu kuma shine kaso suna girmamaka abisa aikin da kayi suna daukaka ka da baka wani matsayi axuciyarja na girmamawa suna haba haba a wurinyi maka hidima ko aiwatar da abunda kakeso,yya kasani aikinka kana neman rabauta da shi ne aranar tashin qiyama ba a duniya ba,yawaita tina mutuwa ya ishi ya sa mutum yazama mai zuhudu wato mai kwadayin lahira,dogon buri kuma na gudar da karancin tsari da kwarin gwiwa wurin sabo,hasara da nadama kuma yana akan wanda yaje lahira da tarin ilimi amma bai aiki dashi ba.
Wani dariya Yaa malam ya tuntsire dashi yace
"Allahu akbar!!!..toh naji saika tattara Arnayen kafafunka kayi da su can kofar gidan ka,Kuma in aje afadawa tsofuwa kar Wani yaje shi kan matata nibance ina neman taimakon kowa ba.
...yaa sheik baice uffan ba ya kama hanyar barin wajen,bai fasa ba yabiyo shi har bakin motarsa da harara sai magangun yake yana ttsir da yawu suna barin wajen yana binsu da kallon Allah ya raka taki gona.
Surayyahms contact 08060712446 for Business promotion
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top