chapter 34
Part1:chapter 34
Wayannan tambayoyin su suka Dade suna rikita ma umma kwakwala suna aikin dagula mata yanayin tunanin ta shiyasa ma a kullum cikin yanayin damuwa da fargaba zaka tsince ta ko kaga ta rafka tagumi cikin Nisan tunani mai cike da kunci.
Ayanzu haka gaba daya ta rasa ta yadda zata fara tunkarar matsala guda daya acikin matsalolinta musamman ma Wanda yafi kunnowa mata kai na tsananin fushin da yaa malam ya dauka da ita., hargagin gulma da titsiyar mutane Sam bai dara ta harcan can ba,dan bata taba kai zantukan su har cikin zuciyarta ba,sumtimes in aka fada mata baqar maganan saidai ya mata zafi hartayi hawayen kunci amma daga zarar ta kwantar da Hanklinta sai taji komi ma ya wuce mata,she believe ita kadai tasan gaskiyar lamarin yarta ba mutane ba so why worry?saidai abun na mata wuyar dauka wani bin cin fuska da rainin wayo yakan shiga ciki,dan akan lamarin rufaida sosai tagane fuskokin makiyanta, saida ta kara fahimtar yanayin mutanen anguwar bana wasa ba.
Wato wasu kana zaune da su ne ana dariya ana raha amma dagata cikin zuciyarsu banda tsananin tsana da kiyayya da dumbin hassada babu abunda suke maka, arayuwa jira suke kawai suji faduwarka ransu yay sanyi da dadi,harga Allah jira suke ace musu ka mutu ace baka duniyar gaba daya sai hanklinsu ya kwanta.
Wasu sukan Iya boye tsana da hassada agabanka sununa tamakr basu tsanekan ba amma abayan idonka sune kan gaba wajen gaftare ka,duk wata kofar cigabanka suna yaqi dashi,duk wata kofar musiban daa shafeka suna murna dash, amma wasu tsantsar jahilci ke gindaya musu hakan,a gajeren tunanin su muddin qaddara yasame bawa toh gani suke kamar shiyaga dama hakan ta faru dashi.
Saidai duk da haka in qaddarar ta same su sukanfi kowa nuna son ayi musu uzuri..ko sukama dalilin da zasu lakama alhaki.
Umma duk saida ta fahimce wayannan halayyar acikin kwana biyun nan dama shi halin mutum sai Allah baka isa ka Iya ma Dan Adam ba.
Bisa dogon nazarin datayi kwkwaktan baya bata kakkarfan zugi akan aikata komi face ta gyarota tsakaninta da yaa malam,koma yaya ne su dawo daidai dan tana matukar bukatan samun hadin kansu awannan yanayi na yaqin kubutar da rayuwar rufaida daga mummumn baki da fassarar mutanen anguwa.
Kwana biyun nan haka ta Dora dammaran tunkarar sa akan maganan
Saidai as usual bata ji ta da dadi ba,cewa yake babu ruwansa d maganan rufaida yrda ta bijire masa ta rabasa da mahaifiyar sa,babu kalar baqar maganan da umma bata amsa ba amma hakan dai tayi shiru,saida ya kammala ta nemi alfarman sa akan a sati zata na fita sau daya zuwa gidan yakumbo tana duba lpyar yarta,ahakan ma dakyar ya amince shikansa cike yake da damuwar yanayin jkin rufaida Wanda a duk sanda ya rufe idanun sa cikin nitsuwa toh sai ya hango rama da kwamusher da yarsa tayi.
Babu kalar tsine ma alai bature da bayayi a zuciyarsa amma bai taba Barin hakan ya fito karara a fili ba.
Sosai ya Tara masifa aransa yanata jiran ranan da alhj okene zai fito,already yanada labarin cewa tub ranar da aka kamasa ya gudu ya bar matayensa
,yanzu haka ita kanta suhan wahala kawai take sha dan survival of the fittest akeyo agidansa sakamakon labarin da sukajji nacewa hukuma suna farautar mijinsu akan laifin kisan kai da rufaida ta aikata.
Akan haka aka sako suhan din ita agaba da gore gore,kusan kullum sai matan alhaj okene sun sauke takaicin su akanta na cewa shegen maitar kwadayin ubanta ya jawo musu dukan ukubar da suka tsinci Kansu aciki
Ita kuwa suhan haushin yar uwanta rufaida ta somaji a xuciyarta tun abu na wasa wasa har ya soma rikida yana dawowa tsana da takaici
A duk sanda aka muzanta bata ganin laifin kowa saina rufaida,fisabillah da rufaida ta hakura kamar yadda su suka hakura suka zauna agidajen mazajensu Aida duk wayanann abubuwan basu faru ba gashi ta jawo musu abun magana badama su fito cikin mutane sai an yaba musu baqaqen maganganu.
Day by day suhan tana cikin yanayin nazarin hakan aranta and with each day tayi tunanin sai taji wani muguwar haushi da tsanar rufaida.
Ata bangaren su yakumbo kuwa tunda ta sunkuya amfani da maganin garjajiya bata rusuna ba da kuka da bori haka take tursasa ma rufaida yin wanka da surace har maganin aljanu da mugun baqi saida ta nemo ta Dora ta akai
Wani bin har abun yay ma rufaida yawa sai taji gaba daya jikij nata na daddaureta,itadai badon tausayin yakumbo datake yawan ji aranta ba da tuni ta bijire ma dukan abubuwan da ake ma jikinta
Sassafe zatayi wanka da saiwowin tare ciwon sanyi,
Ganyen goga masu da jar kanwa, jijiyar zogale duk an zibgashi a jikinta ya shigeta ta koina ya ratsata.
Hakama Lime water, qurji, ginger da ppermint leaves
Wanda ake yawan jikasu overnight da sassafe haka zaa bata tashanye shi tas wai zai magance mata duk wani nauin Vagina odour
Bagaruwa powder kuwa har a pap or ko tea ana juye mata,da daddare haka zaa kwaba Helba and salt asata zama aciki as 30min sitbath for kanann vaginal infection da matsewa.
After 1 full week babu Wanda ya kara lekowa face umma da suka balain jin dadin ganinta ranan datazo,sunsha hira musamman da umma ta nitse cikin farincikin ganin improvement a lapyar rufaida,ranar kamar Wanda aka Dade ba a hadu ba haka take tarairayarta tana bata duk wani kulawar datace tana so abata.
Yau Har kusan yamma umma tana tare dasu kafin rufaida ta samu ta dan koma bacci
,hakn yasa suka samu kebewa one in one da ykubmbo inda umma ta shiga gaya mata duk abunda ake ciki
Daga ta bangaren yaa malam da kaf labarin abunda ranar tagansa yanayi na tsafi akan dan uwansa yaa sheikh Wanda haryau bata Iya binnewa a kokon ranta ba, yakumbo ce ta shiga jimami tana famar gargadinta akan tayi takatsantsan dashi,tana dada bata shawarar akan ta cigaba da sakamasa ido duk wani motsinsa tana lura kuma tace mata basaima ta Dora ma kanta wahalar zuwa dubasu duk sati ba tunda jikin rufaidar ma da sauki kardai subawa yaa malam daman samun lokacin da zai cutar da rayuwar wani.
Sosai umma tayi naam da wannan shawarar tabbas yaa malam yana bukatar asaka masa ido,saidai awani bangaren gani take kamar bazata Iya kyale rayuwar yarta rufaida ya karkace ba wanda already tasa damurshi a zuciyarta sosai tana so taga ta tallafawa rufaida ako ta Ina danta dawo daidai.
Saidai kafin ta komo gida tasha mamakin rufaida sosai Da tayi ta mata bayanin kartadamu zata iya kulawa da kanta harta bata labarin yadda sukayi da malam abduljabbr nacewa inta samu cikakken karfin jiki zaina zuwa har gida yanai mata bitar karatu.
Sosai ran umma yay fari da Jin wayannan maganganun albarka tasaka mata tana mai kara ma zuciyarta karfi da tausasan kalamanta masu mugun sanyi da kara karfin gwiwa tana mata nasiha masu ratsa zuciya matuka,ranar haka suka rabu kowa da tarin karfin gwiwa a zuciyarsa Dan sosai suka dau dammaran toshe kunnuwansu daga kan maganganun mutanen anguwa
Yau safiyar jumu'a hjy mama ta sauko daga stairs tana dan dingisawa da kyar dauke da tray din abinci a hannunta,bata dire shi ko ina ba sai tsakiyar falon akan carpet tabi ta zauna a kasa tare da nannade kafafunta da zimman fara cin abincin wanda yay daidai da shigowar maman Abdul da yaronta a hannu..
"Assalamu Alaikum,
Ta rafka sallama da rawan murya mai Dan qarfi wanda yasa hjy dagowa ta setin inda take kokarin bullowar tanai mata wani irin kallon mamakin daya kara rikita ta,jiki na rawa maman abdul ta karaso gabanta ta jibgu a kasa a rusune dake ma bayan yaa sheik babu wacce suke shayinta kamar hajy mama Dan sosai tasan kalar iyeyinsu gidan...maman abdl tace"Barka da safiya Hajiya mama an tashi lpya?hjy mama ta mata kallo daya ta dauke kanta ta mayar gefe,can kasa da murya
Fuskarta kuma babu yabo babu fallasa tace"Lpyata kalau munari sann ta dago tsofaffin idanunta ta kalleta direct lpya kuwa baki leko nan kwana biyu ba ai in bazaki na samun daman fitowa aikin ba xakiyo min aika ko?
Cikin rawan murya maman abdul tace ayi hakuri hjiya wallh na shafa'a ne makwafciya tace..da sauri hjy mama ta dakatar da ita tareda sauke mata wasu harara
Dakata min munari
Kawai kice Dan nabaki daman kina fita waje kinadan hutawa da shirun gidan nan shine zaki mayar dani kamar wata shashasha,bansan menakeyi ba,kasa mamn abdul ta sunkuyar da kanta batace komi ba dantasan bata da gaskiya sam sam,Koda ace su hjy jasmine suna nan garin tasan bata isa ta dau kusan kwanaki dayawa haka batazo aiki ba hjy mama ta jinjina kai tace to anyi nafarko anyi na karshe daga yau Kar in kara ganin kafarki awaje inba lokacin hutu da aka debarmuku ba..
Maman abdul tana kkrin amsawa sukaji dirar sallama akansu kusan atare suka juya suna masu maida kallonsu bakin kofa jin muryan anty fareesa data shigo yanzu tare da yayanta guda biyu sunsha gayun cikin kannan kaya na knti,Yar yarinyar da guduu ta taho ta fado jikin hjy mama tana dariya sosai tana cewa this old woman..?hjy ta shiga tureta cikin wasa tana cewa shikenan wannan mai baqar fuskan tazo zata kashe ni,
Anty fareesa dake sanye da suturarta na alfarma tayi kyau fuskanta tayi haske matuka,kwalliyarta das das ya amsheta kamar asaceta,wani kafurar green dogon riga ne ajikinta itin Dubai abayan nan mai adon golden zare ta gaba to march da takalminta da jakarta na D/G, ta karaso ciki fuskarta dauke da sassanyar murmushi ta zauna akasa daf da hajiya mama cikin yar wasan su ta kaka da jika tace
"Tsohuwa mai ran karfe...,kafun hjy ta amsa ta kalle mman abdul data sake baki galala tsaban gulma tanata kallonta,fuska ba yabo ba fallasa tace "maman abdul ina gajiya?Da sauri maman abdul din ta sauke idanunta kasa tanajin wani irin kunyar abunda tayi cos daman tuntuni banda kallonsun tana admiring kalar shigarsu babu abunda take,da kyar ta iya amsawa dan duk gidan bamai kula su har haka inba anty fareesan ba,take hjy mama ta hade rai tace"..tashi kiyi wajje kibamu waje..inkinga dama kiyi kunnen kashi ki ce bakijini ba nan gaba saidai ita jasmine din ta tuhume ki ko abari inshi zaidun ya dawo saiki masa bayani akan dalikinki nakin zuwa kinai min aiki..
.bakinta harna bari tace Allah ya huce zuciarki hjy mama.
Hjy bata kulata ba sukahau gaisawa da anty fareesa cikin fara'a da barkwanci, mamn abdul ta wuce tayi waje,juyowa hjy tayi tana kallon fuskar anty ressa wacce kusan wata biyu kenan rabonta da kanon suna can garin mijinta sunje hutu tareda yara.
Hjy cikin neman rikici ta hau cewa uhmm fareesatu kenan kinje can kin cinye musu abinci ina zaki kai wannan teba?anty reesa cikin mamaki ta ce habawa hjy nida ake ta cewa na rame nayi baki to ke wai
yanaga kin zabge haka?ya baki tafi abujan ba,shima abbu inna kirashi kwana biyu bama samunyin wani dogon magana mumy kuma tana ta fushi dani wai naki nazo abuja,hjy mama ta tabe baki ta mike sawun kafafunta tace hmmmm tare da sauke wata nannuyan ajiyar zuciya"..ke tashi kinema yaranki abunci sannn ki dawo muyi surutun nasan dai bacin tuwo na zasuyi ba kunriga kun sabar musu da jagwalgwale
Anty reesa tana murmushi ta jawo abincin gabanta tahau sa ma yaranta adan plate tana cewa zasuci mana hjya nifa agidana anacin tuwo baban su ma ai yana ci.
Hjy tace To daya fi muku kam anan gidan kam inaga sai anyi dagaske,shukra dakike ganinta da katon goshinta wai kuka takeyi ma tuwo ita kuma dayar shamammiyar inna Sako musu miyar kuka har amai takeyi dan tsaban iskanci sai kace badashi mukaci muka girma muka haife iyayensu ba
Anty reesa tace hmm batare data juyo ba ta hau zuba musu abincin tare da hjy mama, sanda tagama tas ta kawoshi har gabanta aje tace sann tace toh Bismillah batayi musu ba suka hau cin abincin suna yar hirarsu akan girkee girke kai kace santin tuwon ke debarsu,sanda suka kusa koshi sannan hjy ta sauya fuska zuwana damuwa dan dama tasaba wa fareesatu kawai take iya kawo karar duk abunda yake cinta arain yana damunta, daga nan damin complains da korafe korafe kawai ta rinka zayyanowa game da familynsu musamman akan zuwan su hjya goggo gidan wanda take ganin kamar akwai hatsari sosai a cikin yanayin zamantakewar su tare da ahalin zaidu
Musamman ma yayan sa
Nan ta shiga bawa anty faressa labarin duk wani salon rayuwar karya da tabarbarewar tarbiya da taga alaman ana shirin daura su nazli acan dan sosai take shan cikin hhy jasmine kwana biyun nan dan taji duk abunda yake afkuwa acan abuja.
Cike da bakin ciki aranta Tace fareesatu gwara kija kunnen dan uwanki mufrad,koda ma bazai saurari kowa ba amma ai yakamata ya tattara matarsa da shedaniyar yar uwanta danaji ance ta jajibo ta sunzo daga kanon tare, maza subar gidan zaidu sukoma can gidansa tunda shi yanzu baida wani amfani aikinsan nan ta shamasa kai tarbiyan yan uwansan duk ya watsar yana jiran zaidu ya bar jamaarsa ya kula masa dasu yara duk sun karkace suna rayuwarsu yadda suke so agaban idonsa babu kunya babu tsoron Allah a lamarinsu ana kuma daure musu gindi?..kinganni nan yana daya daga cikin abunda yasa nace kawai zanyi zama ma anan kano suje can su karata tinda bayan dana sukeso sugani,yadda ta karashe maganan yasa jikin anty faressa yay sanyi muryanta a sace tace hjy dan Allah kar kisa wani abu aranki kema fa kinsan ba halayyar su bane kuma nasan mumy bata dacewa ne agaban su hjy goggo, ai nima naji labarin yadda suka maida mana gidan wani sabon rayuwa suka bude nikaina labarin baimin dadi,hjy mama tace hmm farisa wallhy bakisan yadda abun nan yakemin ciwo a zuciyata bane,wai Amma har ace yayan zaidune zasu saka kida da rawa su gayyato mutane ana raye raye ana kiran shedanu wai murnan dawowa sabon gida sai kace wasu kafurai?a ina addini yace aiyi hakan?ko yar waliman saukar da akeyi na komawa sabon gida batada makafa a addini bare ace kida da raye raye,anya kuwa in zaidu yaji wannan abu zai masa dadi?
Jikin Anty reesa a sanyaye tace hajiya ayi haquri..
Wani shiruuu hajiya mama tayi sannan ta soma zubda hawaye,hnklin anty faressa sosai ya tashi...tace habawa hajiya dan Allah kiyi haquri yanzu akan dan wannan matsalar kikeyi wa kuka?kirjin hjy mama dake cike da rudani wajen kokontun kota gayama anty reesa damuwarta akan jikarta rufaida ko tayi shiru shiyake dada tunkudo mata da kukan,dan sosai ta saka damuwar rufaida aranta wani bin yadda taga dare haka take ganin rana ga yaa sheik ya tafi qasar sudan shekaranjiya har yanzu bai dawo ba.
Kukan kawai take tana tunanin yadda zata soma tada damuwarta game da rufaida duba da ko hjy jasmine ba agaya mata komi da komi ba game da abunda ya afku ba,ita kuwa anty fareesa sai rarrashinta take tana assuring dinta akan cewa zata yi ma mufrad magana akan yan uwan su insha Allah zaa gyarota alhali bata san abun ba haka bane a zuciyar hjya mama
Tabbas rayuwan yayan zaidu akan su hyj googo na saka ta jin takaici amma hakan bai kai yadda take jin tsananin damuwa da tashin hankli akan rayuwar jikarta rufaida ba.
Nazari ta rinka yi cikin salon kukan nata can sannan ta yanke hukuncon neman taimakonta tasan faressatu batada da matsala amma still tanajin fargaban kar wani yajiyo sirrin jikarta
Haka dai ta daure ta soma bawa anty reesa labarin halin da rufaida take ciki saidai bata iya fallasa mata komi ba cikin dai mita da hargagi itintasu ta tsoffi ta gaya mata halin da ake ciki
Tace shiyasa take matukar jin nauyi a zuciarta,sanin cewa danta bukar ba na gari bane ya lalata rayuwar yayansa sannan ace kuma yayan zaidun ma anaso a lalata su
Banda shock din da ant faressa ta shiga najin abunda ya afku da rayuwar rufaida shikansa Kukan da hjy maman takeyi sosai ya dagawa anty faressan hankli.
Kusan dolene susan nayi,duk dama tayi ta bada hhy laifin akan kyale ratuwar rufaida datayi a wannan yanayin datafi kowa bukatar taimakon su
Cikin gaggawa ta yanke hukuncin zuwa gidan umma a gobe dan tasan Daga ta inda ya kamata su gyara saidai data furta hakan fafur hjy mama taki tana mai gaya mata cewa zaidu zaiyi fushin inyaji cewa angaya ma wani labarin rufaida dan alkwari sunayi na cewa bazai bari ajijji abunda ya afku da ita a familynsu ba gudun abun da zai iya tasowa nan gaba
Anty fareesa bataji dadin hakan ba amma haka ta hakura ta rinka lallaba hjya mama
Wacce dama al'adantane ita tayi kukan sai ta yi zuciya ta hau cin alwashi.
Tace inde tana raye familynta bazai taba rugurgujewa a duniya ba,bata tsoron bukar bata kuma tsoron su hjya goggo,abu dayane kacal zai iya hanata komawa a Abuja ayanzu danta kafa dokokin tsare tarbiya a gidan zaidu,kuma shine lamarin rayuwar rufaida qanda already taji labarin inda take da kuma irin rayuwar data keyi wanda bai gamsheta ba har yanzu...
Hira suka dingayi da anty reesa,suna famar neman ta inda zasu soma bullowa damuwar datake so ta dabaibaye familynsu sai can da yamma mijinta yaxo itama suka tartara su suka koma gida,itama sosai abubuwan da suka tattauna da hjy mama ya rinka damunta musamman akan rufaidar dik dama bakomai aka fallasa mata ba.
A fannin su rufaida kuwa yau take cika wata daya da sati biyu da dawowarta nigeria,sosai jikinta yayi sauki sakamakon kulawar datake samu daga wajen ummanta da kuma yakumbo dan kwana biyu haka yaa sheik yakn saka amininsa doc mehra ya aika ma umma hadiza kudin abincin wa rufaida duk dama haryau bata san shidin bane,dan kowa yasan shi da mugun kiyaye bakin uwa tunda hjy mama tace mai karya kara shiga shirgensu yaketa takatsantsan saidai haryau yakasa samun sukuni aransa game da rayuwar da sukeyi tsakaninsa da dan uwansa yaa malam,umma kuwa sabida tsananin takurawar azaba da yaa malam yake mata yasa take amsar kudin kawai batare da tayi fogon nazari akai ba duk ta dauka gwamnati ne take bada tallafin aganinta ai sukadai ne kawai sukasan da halinda rufaida ta taba shiga ciki
Iya daurewa rufaida tanayi wajen kawar da ciwo da tsananin tunanin abubuwan da suka afku da ita amma ina wani abun yakan mata nauyin daukawa
Banda satin da yakumbo ta rinka masife magulmatan anguwa daga nan bata sake samun wani sukuni ba
Alwashin da matar mai anguwa ta dauka nacewa sai zaman anguwar ya gagarrsu shiyake shirin faruwa,hasalima badon rufaida ta dukufa da karatun qur'ani da sallar dare ba da babu shakka cutar depression ko cutar ciwon zuciya zai iya kamata
Sosai ta rame ta dishe ta kwanjame damuwa da fargaba kullum shiyake dawainiya da ita kota sa abincin agabanta batama iyaci
Sosai matar mai anguwa da ayarinta suka saka musu daci,hatta zagayawa waje rufaida bata isa tayi ba sai anbibbita da mugayen baki da baqaqen magana ana embrassing dinta duk inda ta shiga duk kawayenta na makarantar gangare tanaji tana gani iyayensu suka rabasu da ita.
She felt alone and rejected,tun tana iya boyewa har ta kasa iya dannewa alamun depression duk yabi ya nuna ayanayinta tanajin ta tsane duniyar ma mai gaba daya.
Musamman ma inta tuna da yanayin matsain rayuwar da mahaifyarta take ciki sanadiyarta a hannun mahaifinta yaa malam,ita kanta ta lura da yanayin walakanci da muzgunawa da ummanta take shaqa sabida ita wanda shiyake bata karfin gwiwar boye wasu damowintan bata iya fadansu a fili amma harga Allah a kullum neman mafita take musamman akan yadda zata sasanta tsakanin yaa malam da familynsa aganinta intayi masa hakan hala zai dena jin tsananin haushinta ita da ummanta da yake zargin sun rabasa da albarkan mahaifyarsa..
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top