chapter 33


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 33

Kara matsowa kusa malam abduljabbar yay cikin Mamkin ganinta yace koba rufaida bace?kanta dake a can kasa ta dago ahnkli ta dan kallesa ayayin da take kkrin tare tulin ruwan hawayen dake bulbula daga cikin kwayar idanunta wanda ita kanta tasan bata isa ta tsare sa ba,cigaba da kallonta yay har saida sautin muryan ta Mai tsananin sanyi da rauni ya kufce ya fito daga can kasan tantanin makwallonta tare da sakin wata yar karaman dirin numfashin ta Mai tafe da rawa rawa,cikin yar sheshekar kukan datake kkrin danne rurinsa ta daure tace Assalamu alaikum malam katashi lpya?"Lpya" kawai.. yace ynata kallonta duk jikinsa a mugun sanyaye da yanayinta dayake lura daga Nan Wani karamin shirune ya gifta a tsakanin su,baice uffan ba itama bata kara iya ce masa komi ba,kallon yanayinta kawai ya dingayi already jikin sa ya riga ya basa rufaida ba lpya ba,ita kuwa alokcin abubuwa dayawa ne suka shiga damunta suna ruda mata tunaninta game da zuwanta datayi Nan saitanajin kamar bai Dace ma ta fito a wannn yanayin ba

Wani irin rudani ne ya gauraye fuskarta da zuciarta wanda yake kokrin kulleta mata Kai ta hanyar cunkushe mata zuciyarta da karfaffan waswasi

Tunani take aranta tana sakawa tana warwarewa"..shin A Inda mummunan labarin ta ya baza koina a anguwar su tasan dai da kyar ne in shima baiji labarin cewa tayi kisan Kai ba so What if he also choose to misunderstood her now?wajen wakenan zataje ya tallafa mata wajen taso da qarfin imaninta dayake neman gushewa?
tasan dai bazata taba iya komawa ga kawu zaidu aynzi ba,Sam bata son ta Kara jawo masa Wani matsalar da mahaifinta yaa malam,Wani irin karayar zuci ta dingaji ayayin datake wannan tunanin Wanda ya haddasa mata Jin mumuman rauni a zuciyarta Wanda bazatama iya fasalta kalar ciwon dayake tafe dashi ba,Wani irin cunkuso da ciwo ta dingaji a Kan kirjinta da zuciyarta,sai tay wani jimm Babu wani shiri sai taji hawaye zirrrrr nabin kuncinta suna saukowa har kasa bisa kumatunta hartana Jan shessheka sautin kukan nata ne yake fitowa a fili..

Cikin yanayin damuwa malam Abdul jabbar ya hau rarrashinta da kalamn sa masu sanyi yana mai bata haquri yace:

"Kiyi haquri ki shigo daga ciki malama rufaida, ai Koma menene matsalar taki bai dace ki tsaya anan kina kuka ba ko?..Dan Allah kiyi haquri ki shigo ki zauna ki nitsu inbawai har kin yanke ma Allah hukunci ba ne
Jin tayi masa shiru yasa yace malama rufaida kinaji kuwa?
A Babu shiri ta gyada mai kai batare da cewa uffan ba tabi umarnin san ta shigo daga cikin masallacin tana Dan goge hawayen dake manne akan fuskarta, can nesa da shi akan tabarma ta nema waje ta zauna,tana zama ta kife kanta akan kafafunta tana famar sauke nannauyan Ajiyan zuciya..

Malam dake kkrin sauraran damuwrta Bai wani jira Jin ta bakinta bama yahau mata nasiha da wa'azi masu bala'in shiga jiki da ratsa Imanin mai Imani Wanda acikin furucin san ne kadai yasa ta fahimce cewa ashe shi baima sanda labarin abunda ya afku da Ita da aketa bazawa acikin anguwar jiya ba.

Hakn ya Kara bata damar Jin zata iya fayyace masa damuwarta ta fuskar neman kofar mafita da sauki,tana hawayen ta shiga rero masa kadan daga cikin abunda ya afku da Ita bata iya boye masa komi ba sabida raunin datakeji da Kuma yarda dashi datayi ganin shi bamai saurin fassara bane tana Kuma kyautata zaton bazai tona mata asiri ba.

Malam Abdul jabbar yakasance mutum ne mai rauni da tsananin tausayi,
shima sanda ya zubda hawayen sa sosai agabanta Jin irin ukubar rayuwa da ta fuskanta a hannun mijinta Wanda har ya jawo tayi sanadiyar daukan ransa a wannan yanayi

Saidai shi baiyi mamakin jin yadda tace mutanen anguwan sun juya kan maganan ba,Dan wannan din tamkar da dabiar Dan Adam ne na dindin din,wato ya aibata mummunan qaddarar Wani sannan shi yana mai kafafa da nasa laifukan.

sosai malam ya tausaya mata duba da karancin shekarunta duka duka rufaida batafi sa'ar yar kanwarsa maryam dake karkashinsa ba,tunanin yake ta yadda yarinya karama kamar rufaida zata iya dokar kalubalen dake tattare da irin wannan qaddarar shiyasa yashiga bi da kalamansa cikin hikima yana saukakawa yanamai dangata ko Wani matsalarta da ayoyin alqur'ani da kissosi na manzon Allah saw dan ma kartaji kamar da ra'ayinsa kawai yake furta mata wayannan muhimman shawarwari ko danta ji dadi...

Sunfi minti arbain rufaida tana shiru anajin nasihohin sa wanda Kamar yadda tayi burin samun karfin gwiwan daga gareshi Hakan yakasance har fiye da yadda take zato ma, Dan sosai malam ya nuna mata cewa komi arayuwa mai wucewa ne in har ta dage da addua da karatun qur'ani ta Kuma yarda da Allah tasaka sauki a lumaranta ta mance da maganganun mutane,shida kansa ya mata alkwari cewa muddin ta samu saukin jikinta toh koshi zaina zuwa har gidan yakumbo yana koya mata karatu Dan dama baifi surori kadan ya rage mata ta kammala saukan qur'aninta ta ba.

Sosai rufaida taji sanyi aranta atleast she got sumone else dat totally understand her pain and is ready to help her regain her strngth,basu wani Dade ba malam yace tayi marmaza ta tashi ta koma gida tun kafin gari yay haske mutane su fara tsareta da gulmace gulmace

godiya sosai ta rinka masa Dan har yawan hawayen datakeyi saida taji shaukin yinsa yadan ragu kyawawan kalaman sa masu mugun sanyayawa Wanda taji dirarsu a zuciyarta tamkar saukar ruwan sanyi ta mike tsaye tana famar godiya,shikuwa sai bata haquri yaje yana dadda jadadda mata akan ta dage da kusantar kanta ga Allah.

Cike da godiya tayi masa sallama ta dauki hanya direct ta nufo gida dakema ta Dan killece dskarta bata bude shi dau awaje ba duk da haka daidaikun mutanen dake wajen sai kallonta Suke suna gulmanta, basu dai tunkareta ba dake ma kanta a kasa yake take tafiyarta Kuma cikin sauri da dauke kai bata tsaya kula uban kowa ba harta isa kofar gida

Sallama tayi Jin koina shiru ta fadi tsakar gidan kirjinta ne ya bugga atake ta nemi waje ta dakata Jin sautin muryan yakumbo a daki tanata faman masifa saidai bata San da watakeyi ba.

Kirjinta ne ya buga Duk tunaninta Kar ace mata ummanta tane ta dawo,cikin sanda ta shiga karasowa tana takawa a sace harta ta dafa kofar dakin,Nan da nan ta gane sautin muryan Wanda takeciki,daga Nan ta tsaya itama tana saurarinsu..
Daga ciki taji yakumbo tana masifa tana cewa
Ashe mutum bazai huta da maganan rifaida ba?Fisabaillah da sassafen Allah tun gari Bai Gama waye ba anzo ana tare ka gulmace gulmacen banxa da wofi to wallhi nidai Babu ruwana Allah na Gani nayi wadar da irin wannan rayuwar  taku

Dagata dayan bangaren muryan matar mai anguwane yake tashi cikin isa da iko tana mai dakatar da kalaman yakumbo cikin salon tsananin raina mata wayo

"Ai ke kam dama haka matsalarki take,gaki Nan dai kin manyanta Amma rikicewar tsufan Nan yanaso ya zautar dake kina abu kamar karaman yarinya wacce bata mallake hanklinta ba"Nina ce miki gulma ya kawo ni gidanki?mutanen gari dai da suketa debo matsalar jikarki suna damun mu dashi shine Nace bari inzo dakaina in magance mana komai ..Cikin tsareta da sauri yakumbo tace toh sannu Aminatu yar sarkin yaqi,wato kinxo ki magance mana komi,yat dariya yakumbo tayi da zafin haushin ce mata datayi wai bata mallakin hanklin kanta ba,tace toh sai kuma akayi Yaya Amina?nikam anya kanki daya kuwa?yarinya da uwarta da ubanta araye kyace wani andameki da matsalarta?ko daga cikin iyayen nata akwai Dan uban dayaje gidanki yanemi temakonki ne inda akwai ai saike fito fili ki fayyacemin dan ni bana aikin yaranta
bana kafa hujja da rade raden mutanen anguwa..

Cike da dacin rai da izza tace
"Abun da rufaida tayi Sam bai dace ba Niso nayi ma inzo in sameta a cikin dakin Nan shiyasa ma nayi sammako na taho,yakumbo boyeta da kukeyi bashi ne  fa mafita ba,wannn Abu data aikata na kisan Kai ya shafe mu duka,yarinya tabi ta batama suna Duk garin kano a baredede da damu?  Toh wallhy inku bazaku iya sakata agaba ta amshi kuskurenta ba ta mu zamu iya,ai gamunan muzamu iya ladbtar da kowacce shegiyar yarinya Dan bazamu taba bari ire iren ta Suna yawo anguwa Suna gurbata wa sauran yan matan mu tarbiyan su ba..

Shiru yakumbo tayi aranta tana ta mamakin yadda matar mai anguwa take tada jijiyar wuyarta akan abunda kwata kwata bai shafe ta ba..
Rufaida dake manne da kofar dakin tanajnsu Babu abunda kirjinta yake sai bugawa,gaba daya ta maida hanklin ta wajen son jin kalar amsr da yakumbo zata bayar,Kan ta hankara kawai taji an bankade kofar ta ciki,yakbon ce ta fito waje a harzuke ta debo talkamna matar mai anguwa batare da ta lura da Ita ba ta koma ciki. Dakin ta watsa agaban ta tace

"Ke Amina Kisaka kafafuwanki anan ki kama hanya kibarmin gidana ko in gurje mummunan bakinki..
Matar mai anguwa ta mike tsaye zatayi magana yakumbo ta daka mata tsawa a gigice Wanda yasaka rufaida shigowa cikin dakin a rikice,da sauri ta isa gaban yakumbon tana mai rirrike ta ganin yadda tsaban bacin ranta yake tafarfasa a fili..yatsun hannun ta har Wani rawa rawa suke tana nuna su akan fuskar matar mai anguwa
A zafafe cikin tamfatsen masifa tace"Harke Amina kina da bakin zuwa gidana Dan ubanki kina gaya min baqar magana akan rufaida?yarinya inbaki sani ba da raina aka haifeki,nasan komi akn rayuwarki in kura na maganin zawo to taiyi maknta mama,
karkiga Wai kin auri mai anguwa kina Wani bunkasa kina hura hancin waike kin mallake sa,waye baisan cewa uban ki matsafi bane ne kakanki kuma gasurkumin boka..

Ke Amina Daga yau Na haramce ki da shiga tsabgar rayuwar rufaida inyaso kisa mijinki ya koreni anan anguwar dadin abun harki mutu baxayi gindin haihuwar yar data Kai rufaida ba..

Da Wani irin kukan kura matar mai anguwa ta mike har jikinta na bari,..

"Wani kike gaya ma wayannan maganganun yakumbo?mani like wa gorin haihuwa?
Wasu maqudan hawayen takaici da tsananin zafin maganan yakumbo take suka yanko mata cikin rasa kalar xagn daya dace ta sauke akan yakumbo kawai ta shiga tabe bakinta tana kada kanta araunane...

Can dai ta dauki takalmamta ta riko a hannu tana mai kallon setin rufaida

Tafi minti biyar tana kallon rufaidar da Wani irin mugun Ido a kuma ayanayin daya jefa rufaidar Jin mummunan tashin hankli da fargaba..
Hawayene suka shiga sauka a idanunta Babu kakkautawa,matar mai anguwa ta tabe baki cikin tsananin fushi"Uhm yarinya banga laifinki ba,ace barewa tayi gudu yarta Kuma tayi rarrafe?uwarki ma haka take, mafadaciya makira Wanda tafi kowa salon iya munafurci,hakama wann tsohuwar Wanda kukayi gadon mugun hali da bakin zuciya  awajenta,kinje kin kashe mijinki kina tunanin mu zamu kyaleki anan anguwar kina yawo kina abunda kikaga dama ko?toh wallhy bazata sabu ba saidai in bani bace matar mai anguwa.

Saina saka an ladabtar dake an koya miki tarbiyan da gidanku suka kasa baki,shashar yarinya kawai,da aihuwar irinki gwara in mutu a juya,Allah ya hanani gindin haihuwar Indai irinki zan haifi..
Allah ya raba ni da Mai baqar zuciya irinki Allah wadar da  tarbiyan da aka baki,dangin marasa mutunci, kwadayayyu Kuma dolene agaya muku laifinku ko kunaso koba kwaso..
Da so nayi muyi magana ta fahinta domin ki gaya min mtsalar ki Dana iyayenki Amma harni ce za'acin mutunci ana min gorin haihuwa akanki?toh wallhy saina nuna muku iyakarku a anguwan nan zaman anguwar Nan saiya muku daci..
Tana dasa aya yakumbo ta juyo da ita tana kwallon cikin kwayar idanunta da already a hargitese yake da tsananin bacin rai Dan in akwai abunda ta tsana baifi kamata gorin haihuwa ba

Yakumbo tace
Inkin isa kije ki aikta Duk abunda kika Furta anan Amina
Tsayuwar rana faduwarsa ga fili gamai Doki saura sukuwa,shiru tayi Jin yadda rufaida ta rirriketa da zimman sassaita ta,'..kiyi hakuri umma Amina
Allah ya huci zuciyarki laifin danai muku kuyafemin,abunda ya afku Dani qaddara ce bason raina ba,dan Allah kuyi min adalci kudena zargin iyayena akan Duk abunda ya afku Dani,laifi nawa ne bana su ba,in zaku aibata no zaku aibata basu yakumbo ba kiyi hakuri Dan Allah in ranki ya baci

Cike da isa da izza matar mai anguwa ta juyo a hatsale
Bazan yi haqurin ba
Maqirar banza sai Kun kwaso ma mutane tijara sannan kuzo Kuna makale murya Kuna abun tausayi.

Rufaida kin ban mamaki,to wallhy ki maxa ki kyara halayenki tun wuri Dan kuwa kin aikata mummunn laifin da bazai taba gogewa atarihin rayuwarki Dana anguwar Nan ba.

Cikin dauriya Rufaida tana tare ruwan hawyenta tace Toh kuyi haquri kuyafemin,caraf yakumbo tace karma suyafeki.
Su sakaki a wutar jahannama in su suka halicce ki
In masu kikayi wa laifin su kashe ki mugani,dadin abun kowa zai Gani a kwaryan cin tuwonsa,Kuka ne ya kufce mata tace karya Amina takeyi wallhy dantaga bani da komi ne tazo har gidana tana zagina tana cimin mutunci,suje suyi wa ubanki wannan barazan gulman mana in ba tsoro ba?kawai Dan anrainnin wayo kowa saiya kwaso sharar bakinsa yana watsa min?angani tsohuwa kekuma karamar yarinya toh Duk wanda yake tunani ko yake ikirarin zai kuntata ma rayuwar wani Dan yanaganin yafisa abun duniya karshe shi zai zamto abun tausayi Kuma wallhy saikin tozarta kanki da muguwar halinku Amina.

Abun da ya afko rufaida kwata kwata bai shafeku ba, Yan mata nawa ne a anguwar Nan wayanda suke aikta mugayen abubuwan Allah wadar? Har Yan mata masu siyar da kwaya an kama su,ga karuwai ga yan daudo da gwartaye da Yan luwadi,Amma ai ban tabaji anje har gida ana titsiyesu ba sai Akan nawa da qaddarace ta afka mata tayi kisan kan,dan tsaban Kun raina min wayo?Allah saiya sakamin ya sakama rifaida,yarinyar Nan bata taba muku komi ba sai Allah ya mana sharia akan muzanta da kuke faman yi.

Tsaki matar mai anguwa taja ta kama hanyar ta tayi waje,ita kuwa yakumbo sai sauke hawayen ta take tana jin tsananin zafin abun aranta,
Cike da sanyin jiki rufaida ta juyo tana share kwllar idanunta da suke zubowa daddaya
Muryanta adan dishe tace"kiyi hakuri yakumbo,
Dan..batama karasa ba yakumbo ta tsareta a fusace da yar masifa tace
Ke dalla rufamin baki wani hakuri zaki ban bayan kin kama kinfice waje sassafen nan danki jawo mana masifan mutanen anguwa
Ba kallon ki da sukeyi bane a anguwar yasa suke zuwa nan watsa gulma?Wajen malamin mu naje fa yakumbo?..waye kuma malamin Ku?
Bayan kaf anguwan nan babu mai hankli jahilan banza magulmata wallhy in ba tashi tsaye mukayi ba sai sun binne mu da ranmu.
Masifa yakumbo ta cigaba da yi,rufaida bata kara ce mata uffan ba har sanda ta danyi sanyi,sosai ta fahimce cewa damuwa ne da tsoro take son ya fara damun zuciyar yakumbo,tuno sallan fajr da batayi ba yasata fita waje cikin sauri ta doro alwala tazo ta aiwatar..
Tana idarwa ta cigaba da zama a wajen ayanayin rafka uban tagumi akan sallayar tana mai maida kallonta izuwa bangon dakin

A hnkli take sauke ajiyan zuciya dan Wani irin cunkushewar kwakwala da tunani tarinkaji a zuciyarta hade da tsananin nauyi da bugun da zuciyar Nata yake kanyi Wanda bazata Iya fasalta shi ba

Saidai ata wani bangaren,iya maganganun da sukayi da malam Abduljabbar shiyake kkrin dawo mata kanta yana kuma warware mata wasu damuwowin nata yana Dan sassaita mata yanayinta na daurewar kai da tunani.

Its feel like a waste of time ta zauna tana damuwa da maganan mutanen anguwa,Wanda gaba daya ta lura basuda cikakken masaniya akan asalin abunda yake afkuwa da ita..
Karamar nishi ne ya kufce mata ayayin data dada gyara zamanta cikin nazarin abunda ya dace tayi nan gaba.

Aranta tasan Tabbas komi bazai zo mata da sauki nan gaba ba,duk yadda zataso ta daure akan wasu maganganun tasan bazaiyu ba face sai sun raunanata,in akwai abunda zai takura mata baifi asako maganan iyayenta,runtse idanunta tayi sannan ta bude shi a disashe tanajin wani irin shaukin ganin fuskar mahaifiyarta agaban ta kodama zata danji sauki,kusan minti talatin ta share cikin wannan yanayi sannan ta mike tsaye ta fito ta same yakumbo da har yanzu ba a Dade take ba,Dan kuwa abun ya soma isanta kawai gani take kamar Dan bata da galihu ne yasa ake raina mata kurwa har hakanan.

Iya bakin kkri rufaida tayi dan kawai ta shawo kan yakumbo,wacce itama hakurin kawai take bata akan ta kara daurewa su fuskanci abunda yake gabansu kawai na samun saukin jikinta Ahaka suka bar maganan,kowa ya shiga kkrin binne takaicinsa a zuciyarsa Dan su karfafa ma juna

Da ikon Allah kuwa har yammacin ranan babu Wanda yakara leko su.

Bangaren umma hadiza kuwa fitinan yau daban ta gobe daban,Dan sosai mutanen anguwa suka dau zafi da ita akan tanayi musu tufkar wawa tana nuna musu girman kai,dayawa mata sunsha alwashi akan sai sunga bayan taurin kanta da jiji dakan datake musu Wanda sunsan shiya yakasance musu Katanga dajin mummunan labarin rufaida.

Tsakaninta da yaa malam ma Sam babu dadi,wani irin fushi yakeyi Wanda sam bata fahimce silarsa ba,Dan har abincinta ya dena ci
Wani bin saitaga kamar laifin komi ma akanta ya Dora,ga takurin mutanen anguwa dan rana daddayane bata arangama da rikicin magulmata bacin yaaa malam dayayi makasudin faruwar abun yana rayuwarsa normal tamkar babu ruwansa

Wasu ma tsoron hade ido Sukey dashi bare ajega tunkarar sa da wata gulma,komi akan umma aka jibga anyo gulman anyi baqar maganan har abun yana Neman ya soma raunana mata zuciyarta sosai.

But Daurewa dai ta cigaba dayi sabida yarta tana lazimin rufe bakinta akan maganan lallai zai taimaka awani fannin samun lapyarta da samun cikakken nitsuwarta
By no means bata cire tsammanin rayuwar yarta rufaida zai dawo saiti ba,kaf cikin yayanta tanajin rufaida ta dabance a zuciyarta,dan kuwa rufaida yarinyace data balain yarda da kanta ta kuma yarda da Allah tana mai jingina dukan lamuranta gareshi cikin tsananin yarda dashi,duk da cewa labarin zaman ta A US tare da alhaj bature ya mugun girgizata ya dama mata kwakwala amma wani bangaren zuciyarta bai cire ran sake yarda da cewa rayuwar rufaida zai farfado ya dawo yadda yake dacan ba.

She just cant wait to see dat preety sweet smile on her face filled with enthusiasm and courage to built a better life for heself,that fierceness and boldness in her daya banbance ta zubin dukkan sauran yaya mata.

Kullum fargaban umma baifi yadda rufaida zata amshe qaddarar ta axuciyarta ba.

Rufaida yarinyace karama shin har zata Iya mancewa da komi cikin sauki ta rungume rayuwarta mai cike da burirrika koko hakan zai cigaba da zamtowa wani Katanga ko silar dazai zanca mata tsarin rayuwarta nahar abada?

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top