chapter 30
BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Please Ana hanquri da yanayin hausa dialect dina i know sometimes my qarin magana is upside down inka gane mena ke nufi shikenan👏🏻🤧
Part1:chapter 30
A tsakiyarsu yakumbo ta tsaya tana dokawa kowannen su harara "tace ke safiya yada haka Kun Wani zo Kun like min agida ashe Dama can hauka kike da har zaki duromin bandaki batare da izini na ba neman a barni da cutan da bansan kanshi ba wato kawai ku tafi kubar mutum da kaikayin gaba shine damuwarku ko?waima meya kawo ku gidana da wannan uban dare Kun wani sha uban dogayen hijabai kamar masu shan jini kun min tsege tsege a tsakar gida kamar wasu mayu.
Juyowa tayi ta kalle maman Abdul dake famar kan washe mata baki sauran matan Duk sun hade rai Amma Banda ita takaicin rashin zuciyarta yasa yakumbo dada harxuka da masifa
Kan Maman Iman ta dawo tace.,"ke hajara yaushe kika soma saka dogon hijabi arayuwarki?
Baki a bude maman Iman ta harxuko zatayi magana da ihu yakumbo tace ke dakata min safiya bana wasa dake,Banda rainin wayo Dan anga bana Nan shine za'azo a jagawalgala min bayan gida?,ai gidan bana ubanku bane, da tsiya na na da arxiki Nan gidan nawa ne ba gidan majazen ku kona mai gari ba,dayan mata da already maganan ya cize ta take taji ta mugun harzuka cikin yar masifa tace Kai yakumbo Kai yakumbo Dan anzo gidankin ne kike haura mana haka kamar wasu Wanda kike so fada ko gaba dasu,yakumbo bata barta ta karasa bama tace yo meyakawo ku?naga baku saba zuwa bane cewa kuke gidana gidan bola Gani mai warin talauci haka kurum sai Kuma in ganku a tsakiyar gidana wata har tana shirin shigemin ban daki da tsakar dare sai in kyaleku?...kufada
min abunda ya kawo ku kokuwa in sauke muku takaici in rakaku dashi har bakin kofa da buhun sa..
Da rawan jiki maman Abdul ta karaso ta matso daf da yakumbon tana famar sauke murya kasa kasa tana narkewa cikin salon lallami Haba yakumbo Haba yakumbo Tsohuwa mai ran karfe Allah ya huci zuciyarki Banda hade wajje irinna maqiya da yan gulma ke yakumbo har kin yarda zamu iyacewa Hakan akanki?
Shiru yakumbo tayi batama kulata ba ta shiga gyara ma kayan data shigo dasu zama tarkacen saiwowi ne da Yan kayan abinci da baza a rasa ba, suna daga tsaye kamar mayu ahakn ma saida suka shiga lelleka ledojin Wani Kallon kallon suka maidawa junan su dayar matan ta Dan tabe baki,Tuni Maman Iman ta danne xuciyarta ta hau murmushi"Cefane kikayi haka ne yakumbo?Haba yakumbo walaknci fa babu kyau Annabi
saw yace ka girmama bakinka ko Yaya suke,yanzu bazaki saurare mu ba kenan?sanda yakumbo ta kammala abunda yake sannan ta juyo tabisu da kallo daddaya tace ke safiya bana son tsugudidi Banda kin maida kanki wata Shashasha Ai knsan Nasan abunda ya ya kawo ku,gulmace sai ku fadeta inji..maganan yay musu zafi Amma dai haka suka shanye atake suka hau dariyar karfin hali Suna yake hmm su yakumbo kenan Ashe dama kina da labarin shine ko ki aiko mana mutayaki jaje, kobabu komi ai hadiza yarki ce duk abunda ya afku da hadiza kema ya Sameki
Da uban yanayin mamaki yakumbo ta kallesu hanklin ta Adan tashe tace Mekenan ya same hadizar?ciwo tayi?maman Iman tace habawa yakumbo A'a, maganan rufaida fa akeyi
dayar matan tayi saurin cewa eh rufaida yar gidan yaa malam ba?shine mukace toh bari muzo muyi muku jaje Ashe Kuma abunda ya faru kenan...
Mammn Abdul caraf ta tsoma baki "nasha Mamkin Jin Wai rufaidace ta kashe mijinta,dama ace murja ce nasan ta akwaita da baqar zuciya Yo Yakumbo mexaisa yarinya kamar rufaida wanda take shiru shiru ta aikata Abu makamancin Hakan fisabilla..
gaskiya abunkam baiyi dadi ba..Wani shiru yakumbo tayi tana Jin kowannen su sai ayanzu ma hankalinta yabi ya koma kan rufaidar data bari a daki kafun ta fice take take ta shiga tambayar zuciyanta shin Ina take Dan tasan wayyanan munafukai dolene su leka daki su dubata,Adam atakaice yakumbo ta Dan dakata da sauraran su tanayi tana yafece mayafinta daga kafadarta datake shirin dorawa akan window sai tayi kamar sudin take sauraro,daf data Kai wajen ta karkace mitsimitsin idanunta da wayo ta leka cikin dakin Ganin Babu kowa yasata juyowa garesu cikin sauri ta tsura musu ido sosai.
maimakon taji Wani sanyi aranta sai taji gaba daya hanklinta ya tashi"..toh Ina rufaida ta shiga?yarinyar da ko wani karfin kirki Babu ajikinta yau mezatace wa hadiza in yarinyar Nan guduwa tayi
Cikin wannan tunanin maman Abdul ta katse ta tana cewa..
"Komi na da duniya yar haquri ne inba ana haquri da juna ba haka yaran mu zasu taso cikin wayanda basada zurfin tunani...
Yanzu abunda rufaida ta aikata dame yayi kama?itama hadiza data kama mijinta da kokowa Duk sai ace ita take koyarwa yayanta rashin uzuri
Arayuwa
Kisan Kai fa Haba wallahy rufaida ta tafka babban kuskure ma rayuwarta,yanzu da wuya in za'a sake samun Wanda zai kwasheta a matsayin matar aure, inba haka ba saidai ta Kare haka a yawo a layi karshenta kiji ance Wani ya danneta ya narka mata cikin shege..
Cikin jin zafin maganar yakumbo ta karkada kai tace iyyyee maman Abdul toh insha Allah saidai hakan ya Kare akan yayank,ai ganan yarki hunaisa ta taso,Fatanki ya sari guntun kashinki,Duk abunda kika Furta akan rufaida saiya Kare akan naki yar amma ba akan rufaida ba..
Kujin min mata da tsugudidi Dadin Abun dai Qaddara ce wacce take Kan kawo Duk wanda yace da ikon wayonsa ko dabarar sa yake rayuwa saiyaje can yaji dashi...
Haba ku baku San Kan labari ba zaku ta tsine ma rayuwar yarinya albarka Allah saiya sakawa rufaida..kuka yakumbo ta fashe da shi,"..munafukai kawai algungumai
Rufaida ta kashe mijin ta saime?
Inadai banaku majazen ta kashe ba .safiya hatke ce zaki dubi tsabar idona kice rufaida zatayi kwantai ta dau cikin shege a layi?Ai Dama can nasan mutunci na kawai kukazo ci...
Toh insha Allah rufaida zata dawo cikin hayyacinta kuma zakusha mamakin mazajen da zasu nan nemanta Inhar muna raye daku bixinillah shekaran Nan bazai Kare ba rufaida zatayi sabon aure ba Yayanki ne zasu Kare a bin layi
Maman Iman taja tsaki"Yo yakumbo daga fadar gaskiya kin kama kokke koke waike mesa bakida fahimta ne
Dayan matar da dama haushin yakbon takeji tace
Tayaya kuwa zata
Fahimce mu kinsan ai gaskiya daci gareta,yarinya dai bata kyauta ba,Kuma mu bazamu dena fadar gaskiya ba..rufaida ta tafka abun kunya Kuma kuskure tayi babba arayuwarta Dan haka dolene mu fada..
Cikin sautin kukan yakumbo ta harxuko
Tace to sannu baqar makira sarauniyar masu gaskiyan karshen zamani Alhamdullhi tunda bake kika haifeta ba,abun kunya bama ke ta jawo ba,hakama banga ta inda kuskurenta ya shafe rayuwarki ba, In zancen kuke so sai kuyi da wanda ya halicceta Kuma ya Dora mata wannan qaddarar Amma ayanzu kam aikin banza kukeyi Wai malam yaki noma Dan zakka..
Dariyar takaici maman Abdul tayi to ke Yakmbo dakika dau abun da zafi cewa akayi Wani abu na cin zarafi kawai fa magana mukeyi na jaje atsakaninmu
Meye amfanin zaman tare in ba'a gaya ma juna gaskiya ba.
Wani gaskiya ne anan safiya?ke kanki kinsani yau
Ko qur'ani na dauko na aje agaban ku akace ku rantse akan abubuwan da kuke furtawa akan rayuwar rufaida wallhy bazaku iya dafawa ba sabida bakusan asalin abunda ya afku ba..
Da sauri dayan matar tace
"Toh aje ahakan me mezai Hana ki fayyace mana yanzu?
Mamn iman tace kwarai kuwa gaskiya ne aisaiki fadama na asalin abunda ke faruwa
Wala Allah in mukaji ata Wani waje ana fadar Hakan saimuma mu fahimtar dasu koya kukace?dukansu suka ce ehh..
Shiru yakumbo tayi sanda ta Dan samu nitsuwa a xuciyarta sannan ta dago ta kallesu"..in a tunanin ku rufaida tayi kisan Kai saboda anmata auren dole ne kuje Allah ya hada yayanku da irin tata qaddarar
Yakumbo wannan wata irin magana ne
A masife yakumbo tace bazakuji gulma abakina ba..
Iya zancen kenan rufaida ta kashe mijinta abisa qaddara in Kun dauka oho in baku dauka ba kune can kuyita kirkiran maganganu Ai Allah ba axxalumin bawansa bane kowa zai gani a kwaryan cin tuwon sa..
Tsabar takaici maman Iman bata bari ta karasa ba a harzuke tace
Toh Ina kika boye ita rufaidar?inku bazaku fadawa mutane abunda ya faru ba ai ita yarinyar tana da hankli zata fada.
Wani irin daure fuska yakbo tayi
Toh ban fada ba uwata ta farar gada,
Inji didim kin hau duka na,..Inta gaya maku mezaku mata Banda ku kirata karuwa ko kuce mata zata Kare abin layi,yafa kamata ku wuce kuban waje inada abubuwan yi agaba na.
Tuni dayar matan taja hijabinta ranta a mugun bace ta fice,maman Iman tana ta surutai ta Inda take shiga bata Nan take fita ba,maman Abdul kam waje ta nema ta zauna Aganinta in aka ja Cece kuce zasu iya Jin Wani abu daga bakin yakumbo Wanda Banda buhun baqar magana ba abunda take saukewa,tana ko dasa aya ta bawa banza ajiyarsu ta wuce gaba ta bude kitchen tana tana Dan dube dube Kan su hankara ganinta sukayi da katoton muciya ta iyo Kansu,aguje suka nade hijabansu suka safce waje.
Wani irin balbalin masifa yakumbo takeyi ta Inda take shiga bata Nan take fita ba"..safiya har gidan mijinki zanzo in Sameki in gurje gandan bakinki,ke kuma hajara saidai inbanga tsohon uban ki ba,Shegu kawai algungumai magulmatan banza
Yaran da ka isa kayi jika dasu swazo gabanka sunai maka iyeyi,..Me kuka sani game da rayuwa harda zaku gayamin rufaida zata Kare abin layi yan Iskan yara kawai daga anyi haihuwa daya biyu a gidan miji shikenan saikuna daukar kanku kamar wasu jakadai..yakumbo tafi minti goma a kofar gidan tana wanke su har Wani rawa rawa jikinta yakeyi tsaban a harzuka.
Sanda ta tabbata sunyi nisa sann ta jawo kafafun tsufanta ta shigo ciki tana tafiya tana mita aranta tana tunanin Inda rufaidar ta shiga har ake wannan hayaniyar bataji duriyarta ba
Da Dan karfi ta bude muryanta da niyar kirar sunanta tana bude bakinta sai caraf suka hade ido da rufaida,wani irin kallon yakumbo tabita dashi ganin yadda ta sunkuyar da kanta can kasa,a lokacin daf ta fito daga bayin kenan jikin ta har na rawa rawa,kallo daya yakumbo tamata tagane Ashe duk tanajin surutun su iya kuka kam rufaida taci duba da yadda jikinta ya sake yay sanyi ta dawo tamkar wata marainiya marar uwa da uba banda uban sheshheka da jan zuciya Babu abunda take saukewa da kyar ma take daga kafafunta tana shirin karasowa dan alokacin ji take kamar ta runtse Idonta taga bata duniyar mai gaba daya.
.
I know wasu xasu tsangwame wannan part din sabida ban haushi,but in gaskiya zamu fadawa kanmu THIS IS THE REAALITY WE ARE INN!!!...ppl love to meddle and backbite,slander,wasu ma kunata xumunci for long amma makiyanka ne a lillube,aransu suna jin dadin suga dik wata muguwar alkabain da xai sameka, MAGULMATA DAIDAI DA JAHILAI KUKE KODA KUWA KUNA DA ILIMIN ARABI DA BOKO.
I fear for rufaida,kunga yadda sharrin xuciya da yanke hukunci cikin fushi irinta hjya mama ya ballo mata da wani matsalar ko?toh be careful how u make desicions in life.no matter how provocked U might be remember there must be a demeaning negative consequences at the end of ur decisions,dole ne akwai innocent souls dinda zai tabu.
Patience is alwys the key....
.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top