chapter 28


BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 28

Daga kitchen zarah ne kace kace a tsaye agaban su uwani ta Dora hannunta a kugu cikin wani mayyar suturarta dayayi mata mugun kyau ya zauna akan dirin shape din jikinta ya mata cas cas,riga da siket ne fitted ta wani deep blue colour voile lace mai Dan karan tsada,infact komi data sanya ajikinta yau mai uban tsada ne,she was standing tall on an Italian cage pump heels dakema ba Wani tsayi take dashi ba takalmin ne ya temaka ya Kara mata tsaho,Bakinta yaci uwar sa da matte redish brown lippo..

Everything on her face is on fleek nd carefully calculated har Wani sauya kamanni yau tayi..

Masu aiki suyi Nan suyi can sai zagin su takeyi tana hantarar su
"Ke da Allah kiyi Abu da jikinki,ta juya ta kalle uwani ke kuma kiyi sauri ki dauko dump waiter ku sassaka abincin Nan afarayin kasa dasu..mschewww "waiya kuke wani Abune kamar dabbobi?I don't want you to waste anymore time,c'mon  girls,wani maiyyar nishi ta sauke, cak ta dakata daga Furta Wani magana tana Wani irin kallon su kamar taga kashi,Wani kyamataccen numfashi ta ja sannan ta lumshe idanunta at same time ta budeshi tana wani sissine idanunta, tsaban rigima eye brows dinta har wani shaking sukeyi Suna gil gil Suna rawa rawa kamar zasu tsinke daga idon su fado kasa
Cikin wata rigimmmaiyar tune wanda ya fito da kasalliyar sautin muryanta tace,"oh my gosh..my honey is already here,ta Wani Lumshe idanunta tayi tana sauke kakkarfan Ajiyan zuciya like yo she is feeling it,a rigime ta dafe goshin ta,wani hade rai ta karayin tana jinkanta kamar wata hamshakiyar matar gida,tanajin zuciyarta a harzuke daya kasance su uwani basu kammala komi akan lokaci ba,bata ma lura da Shigowar ainau ba tana famar sauke mugun kallonta akan su uwanin wanda iya bare baren da jikinsu keyi kadai ya isa kasan Suna cikin Wani yanayin Jin takaicin ta,biri biri kawai sukeyi sukansu sun kasa tabuka komi duk tabi ta ruda su da tsawa da tsiwa summa rasa Wani oderta zasu soma kulawa

Wani uban tsawa ta daka musu ainau ta karaso ciki cikin sauri fuskarta a Dan dore,a hnkli cikin muryanta mai cike da aji tace pls Enough Zarah please let d girls be"..ta dada matsowa kusa daf da kunnenta tace haba Dan Allah sai kace kece matar gidan?nifa bansan kayan Reni Nikam Muje daki,wats wrong with you..Ta karashe mgn cikin sauri tare da watsa musu uwani kaskantaccen kallo she care less Inba basu Gama akan lokaci ba ita Ina ruwanta?..ba yabo babu fallasa tace "Bunch of useless things,tun daxu ace kuna abu daya?da Allah ni Kuyi sauri ku barnan ppl are already starving..,a hnkli uwani tace Ayi hqri hjya yanzu za'a sauko da sauran abincin,Bata kara kallon su bama bare ta kulasu,cikin sauri ta janye hannun Zarah suka haura can sama dayan dakin tan

"Let go off me'
Zarah ta fauce kafadunta data riko a hatsale da alamun ranta ya mugun baci, Adan zafafe tace wai Meye hakane Aina'u?inai musu magana kin Wani zo kin dakatar Dani mtsew Nidai Karki Kara min haka,ya zaki jawo har masu aikin gidan nan su renani?

Wani juyi Aina'u tayi Tare da  sake yangataccen Rolling  eyes ta juyo tana kallon ta..
"Zarah Raini ya wuce anjima kadan kijisu Suna gulman ki Suna zaginki? A hujajan Zarah ta juyo zatayi magana Aina'u  tayi saurin daga mata hannu fuskarta a matukar daure tace"Hey hey Ki dakata min please,I hope ure not forgetting yestade nazli call u local with her full chest tana refring rawan jikinki da Omo busy body
Zarah waime sa hakane?mesa baki son rike mutuncin kanki ne?..how can I make u understand?

'Zarah dake Jin Wani zafi aranta cikin bacin rai a hnkli ta furta I don't know Kuma ki kyaleni,daga Nan ta dauke kanta tamayar gefe muryanta a matukar shaqe ta shiga tambyarta ciki ciki..."Wai mu yaushe zamuje ne..pls let's go down now,I'm eager to see him..dama abun da ya kawo kenan right? So let me do nd leave dis goddam place abeg,ta karashe da jan tsaki a zuciyar ain tace ai gara ki tafin Dan ji take kamar ta shaketa cikin dauke Kai itama tace Indai a shirye kike let's go..zarah batace mata uffan ba ta wuce fuuu gaban mirror Inda ta aje jakarta ta dauka ta bude ta dauko Wani mayyar sihirtaccen turarenta mai qamshi irin na turaren prince hamdan of Dubai wanda zee zee ne ta bata data karbo musu awajen malami,Dan kadan ta afa ta gogga a jikinta ta mayar ta ajiye sannan suka sauko Suna tafiyar su ta catwalk kowa da abunda yake sakawa aransa

Wani irin takun aji da kakalo girma suke wanda sautinsa yake a hankli Suna Wani irin kamewa cikin bayyana tsarin ajinsu, Nan ma saida ain ta rinka bin Zara da kallon gefe tsabar mamaki ganin yadda lokaci guda zarahn ta Wani dauke wuta ta kuma binne rawan jikinta ta fuske tana Jin kanta tamkar ba itace All desperate ayanzu ba...

Saidai Duk baza takun nan da sukeyi har suka sauko daga steps Babu wanda ya daga Ido ya kallesu,Banda hayaniya da tsaban karfin surutu da aka bude shafinsa a main palon Babu abunda kakeji Duk ahalin gidan sun mamaye shi.

Uhm uhmm Zarah tayi Wani  yangataccen gyaran murya wnda ya fito da Wani Dan uban sautin rigima da Dan karfi tace
"Assalamu alaikum.

Wani Shiru sukayi gabadaya batare da kowanensu yayi yunkurin furta wani Abu ba duka suka juyo suka kare mu su kallo,yaken dole ne ya kufce a fuskar ain ta riko hannun zaran suka karaso ciki da sauri suka hau gaisuwa,wani irin numfashi da ajiyar zuciya Zarah ta dinga saukewa a hakli ganin yadda imad ya dan bata lokacin sa ya kalle su..aransa kallon baisan su ba yake Dan shi harya soma mantawa da kamannin Aina'u dake jinin su bai Wani hadu ba..

Zarah kuwa sai sunkuyar da Kai kasa take tana Wani sake mayyar Murmushi kamar wata amaryan Doki daga ta Dan dago ta kalle fuskar imad shikenan sai ta Lula duniyar gajimare,
Aranta ta dauka Duk haduwarta da ladabin Kule a buhunta ne ya tafi dashi har ya dan kallesu.

Su hjya kuwa tambayar su suke abunda ya tsayar dasu Aina'u take musu bayanin wai sun tsaya kulawa da abinci ne shiyasa basu sauko da wuri ba,a lokacin Aina'un ne kawai take magana dan kwata kwata Zarah ta susuce ta rasa nitsuwarta batama San mezata ce ba sai Wani kirsa take cikin sanyin makirci Tamkar wata budurwan kauye gata da zakewa ahaka sanda tayi jikin kowa ya shiga bashi cewa Duk wa imad take wannan uban murmushin da sadda saddan Kai din.

Aina'u batacewa mufrad komi ba ta dauke kanta  akanshi shima haka yy kamar bai ganta ba dakema hanklin sa nakan wayarsa ne tuntuni yanata kallon Wani video da aka turomai daga can America da wireless earpiece a kunnen sa

Zarah ta dube imad direct tuno da idanunta akwai kwallin sihiri data shafa saita hau murmushi ta daddage ta sinne murya ta kakalo mai zaki da dadin
Tace mai ya hanya?

A hnkli imad ya juyo Jin yadda malak ta dan tsakureshi a boye,Hakan yasa yaki bada hanklin sa akan Zarah suna hade ido da malak ta sauke kanta kasa tana turo mai bakinta a shagwabe
Daga Nan kuma Shikenan ta dauke hanklin sa daga kan su Zarah gida Kuma ya dauka da tsokanar su"..imad na dariya yake cema mahaifiyar sa ai ya samu matar aure anata musu dariya,ahakn saida Zarah taji Wani balain kishi acikin zuciyarta,Duk dama tasan wasa akeyi amma atake atake taji ta tsane malak har makoshi..

Wanda Ko acikin wasan ma Hjy goggo ce kawai take bayansa tace sun dace da malak,tace ai tunda malak takai 15years aita isa aure,hjy adada da hjy jasmine da Anty meera sunata musun cewa batakai ba,hjya saddika kam batacewa komi sai yawan Murmushi Dan ganin fuskar danta ma kawai ya isheta Jin Duk Wani nishadi

Mufrad ne ya tashi ya haura sama da alamn kira zai amsa a hnkli ainau tabi bayansa da kallo tanajin tsananin kewarsa aranta,ji take kamar tayi xcusing dinsu tabi bayansa Amma kuma Ina she can't risk leaving Zara anan wajen bata San Wani irin abun wawanci da zubda mutunci da zata aikata mata ba.

Mufrad yana bacewa nazli ta yunkuro cikin saka baki a  maganan tace "uncle mad kwanan nan fa zakayi aure har yaushe babe din Nan ta girma..kawai kace bakaso muyi asoebi...ta karashe tana langwabar mai da wuya..

Shukra ta shiga washe baki sabida aranta tana mugun son tayi kawance da malak but she can't show it yet sabida Ji take kamar tafi karfin sauke kanta ma wani,a tunaninta malak ce yakamata ta soma mata magana and for the fact dat malak is so gentle,charming educated and classy,yasa take tunanin nasu tafiyar zaizo daya,saidai da kamar wuya dataga malak din bamai son surutu kamar ta bace..ita Kuma bazata taba yadda a raina mata kurwa ba..she love to hate and suspect any one..

Imad ya Dan sake Murmushi was nazli yace.."I wil wait for malak"...hjya jas tace sai mubari ka cuce yarinya ai lokacin ka tsufe  Anty meera tana dariya tace..gwarama kanemi wacce ta dace da Kai dai..
...zai budi baki yay magana Aina'u tayi saurin dakatar dashi tana yaken da baije har kasan wuyarta ba tace Kamar irin sa'ar nazli haka,ta dafo kafadun zaran cikin Kara drawing attention dinsu kanta,tace Zarah I think u're age mates da nazli ko?..Dan dariya akai,nazli ta Kau da kanta slowly cikin jan wata arniyar tsaki,Dan aranta ta Gama raina ajin zarahn ita Sam bata fiye son mutumin da baida class ba,tanajin hjy adada da kininbinta tana ta bayanin cewa ai yafi dacewa da irinsu zarahn
..komi dai acikin wasa akayi shi,Inda Zara ta shiga Jin dadi aranta musammn ma da hjy saddika tazo ta tsoma baki da aka kawo hirar dacewar su akan imad tana ce masa son irinsu nazli sune dai dai Kai ba yar yarinya ba..she knew they were just saying it Amma sosai Hakan yay tasiri aranta tasomajin kamar ma bata shi akayi mai gaba daya..

Hjy jasmine tace shukra jeki kirawo yayanki,I want everyone on d table now,Bari na duba su uwani...Butt Zarah ta miqe tsaye cikin Wani makirtacen salo tana Murmushi tace no maa,kiyi zamanki kawai bari inje in dubosu ..hjy jasmine dake dan Murmushi tace thank you yar albarka..da Wani irin salon tafiyar rigima ta wuce ta haura sama cikin sauri,dai dai lokacin idon nazli da shukra suka ci Karo Wani dariyar raini suka tuntsire dashi
"Wats wrong with u guys?..Aina'u ta hade ranta sabida ta shaqi da waye sukeyi,.bakinsu a hade Sukace nothing...shukra ta miqe da rawan jiki ta haura sama dantaje tayi gulma sannan taga yadda za'a kaya da Zarah da masu aiki a can kitchen..

Wayar hjy goggo ne yay kara aka miko mata ta Kara a kunnen ta suka hau gaisawa da Hajiya mama"..imad ya matsa sai anbashi wayar shima Dan sosai hanklin sa ya koma kano saidai bazaka fahimce Hakan ayanayin sa ba..haka kuwa sukaki su barshi ya amsa wayar kowa na cemasa Babu Inda zaije har sai yaa sheik ya dawo..

daga kitchen kuwa haka shukra tayi cirko cirko daga bakin kofar tana ta kallon su Zarah altho har an riga an kammala komi,Abu dayane kawai ya kwafsa ma Zarah ganin bazata iya musu ihu da ikon data sabayi agaban shukra,itadai har Yau neman gindin zama take bacin bata san shukra ta Gama fahimtar ta tsaf ba.

Tare da masu aiki zarah ta sauko aka hau karasa jera abinci Banda saka Ido irina shukra gaba daya hanklin Zarah baiyya jikinta
Ganin yadda imad da malak suketa hira.

Cikin sauri tasa aka kammala shirya table ta dawo tace musu angama anata yabonta Aina'u kam ko ajikinta duka suka wuce Kan dinning aka zazzauna,ana gama zama saiga mufrad yana saukowa cikin tafiyar sa mai cike da nitsuwa da daukar hankli harya sauya suturar jikin sa zuwa wata
Hadaddiyar Italian white t-shirt ta kamfanin renato balestra hade da lallusan wandonsa Wanda yanayinsa yake kamar sport wear shima fari dogo,kafarsa yay kyau matuka acikin wata convertible loafer sai takunsa yake a kasaitance tamkar halin da ake ciki agidan na zumudi da murna Bai darashi ba

Harya karaso ya zauna kallon sa akeyi,wasu a sace wasu a fili as usual kusa da IMAD ya zauna mahaifyar sa hjiya jasmine tana daga dayan gefen sa kafin Nan ainau da nazli,ata dayan bangaren kuwa zarace daidai setin kujeran dayake kallon na imad tare da sauran mutanen gidan kowa da kalar expression dinsa awajen,hjy jasmine ta miqe tsaye zatayi serving still Zara ta miqe ciki kadadi ta karba Wanda Hakan ya tursasa Ainau mikewa danta tayata har wani Allah Allah take ita tasawa imad din bacin hanklin sa baima wajen tunani dayawa su riga sun cikke masa kwakwalwa mufrad kuwa baice komi ba sanin shi miskiline yasa Babu wanda ya daga hanklin sa akan haka har aka soma cin abinci.

A hnkli malak take  jujjuya spoon dinta acikin abincin at first zaka dauka ta koshi ne but tunani kawai take akan yadda Zara ta tuttula ma kowa abinci kamar wasu mayunwata itama sosai tasoma gane kalar zarar sai taga kamar bata mata ba...

Hirar America shiyabi ya dauke musu hankli kowa najin hirar da ake musamman da aka sako zancen case dinsu da rufaida

Hjy goggo ce ta nace da masa tambaya akan zancen kisar  Kan da akace rufaida tayi,sama Sama yake musu bayani danyariga yay alkwari da zuciyarsa cewa bazai taba bude asirin rufaida awaje ba bare ma dayasan mata da karamin kwakwalwa da son jin gulma shidai saice musu yake self defence ne
Kuma mijin nata shine baida gaskiya

Tuni hirar yaa malam ya Kara zafafa awajen hjy adada da hjy goggo sunata barbada akan halayyar yaa malam da sukaji ance Wai yanayi ma yayan cikinsa auren dole,fade fade Babu abunda basuce akan haka ba,kawai su fito suce akan kwadayin abun duniyane yaa malam ya jefa yarsa acikin ukuba basa iyawa sabida yadda sukaga mufrad da hjya jasmine sun dauke wuta Sam Sam suka ki su bada fuska acikin hirar tuntuni da ake maganan su suka ja bakinsu sukayi shiru sunki suce komi.

Ba Wani cin abincin sukayi ba imad ya fara cewa ya koshi,
Anan ne ma sukaji cewa ai gidan doc mehra yayi breakfast dinshi

Ana kammala komi Aina'u ce ta soma xamewa ta haura can sama tsabar batason ma Zarah ta sata yin Wani aiki

Hakan kuwa Zarah ta zama uwar jagora wa masu aiki har sanda aka kammala tsaftace wajen tas

A Lokacin daidai motar daya kawo kayan imad da Dan tsarabar da yayo musu ya iso,Nan d nan nazli tabi bayan keeyan suka je da masu aiki aka tattaro trolleys dinsa manya guda uku da babban travelling bags trolley kawai yace akai masa sama sauran jakunan haka ya damka ma mahaifiyarsa yace  tsaraba ne,daya jakar nata ne ita daya,sauran kuma yace tasan yadda zatayi dashi araba a tsakanin mutanen gidan,cikin Jin dadi ta rinka saka masa al'barka.

Mufrad ne ya dauke hanklin sa suka haura sama can dakin da aka Kai kayansan cikin masa bayanin yadda yaa sheik ya tsara masa nashi sashen a cikin gidan cewa da akayi saiya kawo mata kafin abashi site din ya rinka sakashi dariya,slowly zakuwarsu akan zancen auren nasa saiya soma shiga zuciyarsa ya soma jin kamar zaiyi tunani akai kawai

Daga falo kuwa Tsabar murnan da akeyi  a babban falon site din hajya adada aka baje kaya aka hau rabawa,Bai Wani dauke su lokaci ba sabida kusan komi yasa anyi packaging dinsa da sunan Duk wani ahalin dake gidan hatta su Anty meera akwai nata sunan saura sauran da suka rage aka bawa malak da su hjya goggo sannan aka debi jewwries da turare aka damka ma Zarah akace taje can su raba da Aina'u.

Komi cikin raha da jin dadi aka gabatar,
Anty meera da hjy jasmine suka koma can daki,aka bar hjy adada da su hjy saddika Wanda har ayanzu hirar case din rufaida kawai sukeyi acikin laluben duhu don kuwa haryanzu harsashe suke basu fahimce asalin abunda ke tafiya ba.

While acikin zuciyar Hjy goggo harda kyashin jikinta da takeyi tanajin mugun zafin rashin kasancewar su da Ita aganinta haryau hasiya itace silar rabata da danta gashi Dan jikarta ma tana shirin janyeshi da jarabar dan tsohon mijinta, Hakan yana matukar cusa mata baqin ciki aranta,
Yo meye mahadin zaidu da Dan cikin hasiya ai ubansu ba daya ba,meyasa za a saka mata jikanta agaba da damuwa..

Tunda akace rufaida ta kashe mijinta take ta mamakin yanayin tarbiyan da aka basu..,anata tunanin aiga mata nan birjik akan musu auren dole Amma bata tabajin ance ga wata ta kashe mijinta ba sukam ma ada can Duk auren dolen aka rinka musu Kuma suka zauna da maxajensu lpya suka hayayyafa
Kawai dai baqin zuciya da muguwar zuria irinna hasiya.

Koda can ma ai ta fahimce kamar ba aslin son dikko hasiya takeyi ba kudi kawai tagani ta biyosa,hira kawai sukeyi hjy goggo tana ta saka wayannan abubuwan aranta hjya Adada kuwa damuwarta baifi taga anyi gaggawan yaface Duk wani zumuncin dake tsakanin zaidu da dayan Dan hasiya ba..

Aganinta basu da mutunci ko darajar da zasu hada xuria dasu sabida matsalar su ta karamcin ilimi da wayewa ga  talauci,sosai da sosai hjya siddika take Goya mata baya itama aranta ko kadan bata son abunda zai hada zuriarta da harkan karanci da zubda mutunci bare ajega karancin ilimi da wayewa,sun Dade suna hira akan lamarin su rufaida Duk dama bawani saninsu ko sanin  rayuwarsu sukayi ba,haka dai suka tayi Suna tofe tofensu aranar Babu abunda basu tofa akansu ba...

Daga cikin babban falo malak ita kadaice a zaune da wayarta a hannu ta daddanawa Duk hanklinta nakan wayar tana famar karanta Wani littafi
Mai taken Ajalin so da surayyahms ta wallafa,daga Ganin yadda take sauke Murmushi kasan book din ya mugun tafiya da Ita..

Da wannan fara'ar akan fusknta ta dago caraf suka hade ido da shukra data shigo tana tafiyar rigima malak batayi kasa a gwiwa ba tace mata "Hi..
Kallo Shukra tabita dashi bata amsa ba sanda ta nemi wajen xama ta zauna a kasaitance ta Wani harde kafafunta Wanda kafin ma ta Gama aikata hakan malak harta bada banza ajiyanta ta dauke kanta ta mayar kan wayarta tanamai cigaba da abunda takeyi, tmakar bata San da halitta awajen ba"..ganin hakan yasa shukra ta rude gaba daya ta rasa yadda zatayi ta soma fidda maganar dake bakinta harga Allah itadai tana son tayi kawance da malak
Sai can ta daure cikin kadadi tace
"ummm Ya Daddy Mehra?Fatan yana lpya,malak batace komi ba itama har tadanja lokaci,batare da kulawa ba ta ce
Lpyar sa lau,ya school?cike da rolling eyes da Jin takaicin Jan ajij malak shukra tace oh dama kinsanni ne?a nitse malak ta juyo ta dasa mata dara daran eye balls dinta dats speaks confident tace "u're yaa sheik dougher I guess..shukra tace yeah,malak ta tabe baki,"he is my dad's best friend nothing wrong in knowing u guys right?..cikin Jin dadin Jin haka shkra tace yeah but har me kenan kika sani akaina?murmushi malak tayi ta Dan Kai da Kai kasar wuyarta tace Nothing..not even your names.
Shukra zatayi magana ta Kara tsareta"..I have Neva been to kano,nd i guess you just moved to abuja right?..cikin rasa kyakkwar amsar da zata bayar tace yes tare da miqa ma malak din hannu a tsaye ta mike tana kallonta "I am khadija zayd matazu..pplarly known as shukra and you?..sanda ta Kare mata kallo sannan ta Mika mata hannun ta sukayi musabaha tace I am malak mehra..da Wani irin salon aji ta karashe Furta hkan Wanda yasa shukra kwace hannun ta cikin sauri so what are you planning to study?..Kai tsaye malak tace information technology,and u? Shukra tace I'm studyn law at nsukka halama gobe na wuce schl daga Nan ta soma zuba tana bayanan da ba a ma tambayeta ba
"Actually We came to meet our grandma sai kuma ga dawowar uncle mad Hakan yasa mu dole muka tsaya tarban sa,so dama uncle mad yasanki ne?dnt tell me u're his pet girlfriend su mama since baki wani girma ba..dariya sukayi atare kowa da yanayin fassarrar sa a takaice malak ta maida mata amsa tace"yes I'm still young for marriage so how old are you?saurin shanye mgnan shukra tayi Dan tambayar bemata ba da kyar ta furta I'm almost 17...malak na shiru batace mata uffan ba,can itama tace am 16..Ashe kusan daya muke,shukra ta tabe baki kasar wuyarta tace nope,nifa har yanzu bana kula guys..u know lokacin Abu ayishi yanzu kuma lokacin karatuna ne I won't spare any minutes Ina cusa kaina wa namiji,Neva,a hnkli malak ta dago Jin ance"cusa Kai wa namiji?abun ya bata dariya,cikin yar muryanta dabaiyi kama da ta damu da zancen ba tace hey,Ba acewa Hakan cos Allah zai iya jarabtarki dabin wani namiji Shukra tace noo noo pls Allah ya sawwake
I can't imagine myself to look like Anty xarah,god forbid,cike da rashin fahimta malak tace "Who is dat?ban fahimce ki ba who is zarah?Aikuwa Nan aka motsi Inda yakeyiwa shukra kaikayi,atakaice sanda sunfi awa guda tana tsinka ma malak labarin Zarah filla filla shafi shafi harsai da takai karshe sannan ta dasa aya..
Mamaki ne ya Gama cikke xuciyar malak tayi shiru tana jinta batace mata uffan ba,she is just wondering yadda akayi shkra tasan dukan wayannan abubuwa,baki ta tabe lallai toh saka idon yakai makura,batun Zarah kuwa bai Wani bata mamaki ba Dan tuni ta soma gane take takenta,wayartane yay kara ganin new number yasata sawa a handfree batakai kunnen ta ba tanayin sallama muryanshi mai dadi da taushi ya tsareta
Yace c'mon taho ta waje Ina jiranki,tunkan ta amsa cikin tsananin mamaki shukra tace uncle mad?atake Malak ta miqe tana mkin yadda akayi ya samo number ta hakan yasa tafice cikin sauri batare data kula shukra ba.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top