chapter 26
BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 26
7:am
Anguwar gangare
Tun bayan ficewar umma hadiza agidan yakumbo take fama da jikin rufaidah wanda Tunda ta farka laulayi kawai takeyi da kyar ma ta Sami tayi sallah tadan kwanta bacci mai Nauyi ya Kara daukarta,Banda juye juye da wangale wangalen cinyoyinta Babu abunda takeyi,har Yau kasarta be dena mata tsami da zugi ba,saidai ata ciki ciki kawai takejin radadin abun, dan Koda taje tsarki ta leka kasarta bata ga komiba sai dan kumburin da wajen yayi,daga Nan bada wani dadewa ba yakumbo ta Sabi mayafin ta itama ta fice ta nufi kasuwa yin musu dan siyayya,dubu sha biyar din da hadizan ta bata ta rabashi gida biyu mai yawan ta boyeshi a gindin setin samiran ta kwalli daya dake tsakar dakin wanda tadanyi jere dashi akas,Wajen masu saida abincin gwari ta nufa direct tadan tarkato musu abunda baza'a rasa ba,yar shinkafar su wanda baifi kwano hudu ba,wake,surfaffen garin masara,da flour,dake ma tanada garin gero da tarkacen sauran ragowar hatsi data samo wajen kale a gida,sai Yan sabulun wanka da wanki da sleepas da Kuma brushi ta hada mata harda man shafawa wanda tasan dai dole Rufaida ta bukace wayannan..
Bayan ta kammala da Nan ta biya har lambun gangare Inda akecema Gidan arha,anan shima ta sissintsinta musu kayan miya da sauran tarkacen su Maggi da manja harda dan kifi da Dan abun sha'awa Abunka da Abincin marar lpya..
Niki Niki ta shigo gidan hannunta dauke da kayan abinci tana tafiya dakyar sabida Nauyi da gajiyar jikin tsufa a kofar daki ta ajesu tayi sallama tare da leka cikin dakin tana mai kallon saman gado,sauke ajiyan xuciya tayi ganin Rufaida Takoma bacci still sai juye juye take da alaman bakin dadin baccin takeyi ba
Kusan minti biyar yakumbo tana tsaye daga wajen cikin rasa ta yadda zata soma tunkarar lamarin rufaida Dan gaba daya yanayin jikin rufaidar na kashe mata jiki..
Abunka da believe irin na tsofaffi already ta riga ta gama sawa aranta cewa Rufaida ta riga ta san da namiji by now,ita Sam bata wani gamsu da labrin cewa attempt bane kawai jinsu takeyi aranta tace Wani irin abu kenan namiji zaiyi da jikin rufaida ace haryanzu bata dena dingisawa ba?yarinyar da akace tayi kusan sati a Asibiti?Ance mata wai shigar karfine toh tayaya kenan rufaida zata kufce batare da ta rasa budurcinta ba?,,ita tun jiya da hadiza ta gaya mata abunda ya afku take saka Idonta sosai akan yanayin tafiyar rufaidar tana Kuma lura da Duk Wani motsawarta Wanda har ayanzu bata gamsu da cewa rufaida ta dawo cikin hayyacinta bama bare ajega samun sauki, Kuma tabbas bata cire tsammanin cewa ba a bawa kasarta da jikinta kulawar daya dace ba,yo meye ma asibiti suka iya?ita dama can bata yarda da maganin asibiti ba tafi gane na gida na zallan itatuwa,yo bakaken fatan ma da suka bijire ma na Allah ai yanzu dawowa sukeyi a Hujajan, inaga Kuma ance turawa dama can sume sukasani banda neman kudi da Suna bare har ace sunyi ma rifaida magani?mita kawai take yi aranta Dan Aganinta ko dingishin da Rufaida takeyi aynzu ya isa ya gamsar da kowa yasan cewa bataji ruwan zafin jinya ba.
Bisaga wannan tunanin data dingayi a xuciyarta ta juya ta shiga debar kayan abincin tana kaisu cikin dakin,sanda ta shiryasu tsaf sannan ta taho a gjiye ta zauna bakin gadon kusa daf da rufaida,kallo tabita dashi sannan ta shafa goshin ta daya jike da zufa jin yadda ko inanta ya dau dumi da alaman zafin zazzabin dake jikin tane yake neman tsanantawa,.
Minti biyu bata kara xaune awajen ba rufaida ta soma bude gajiyayyun idanunta data kullesu gam gam suke mata Wani irin Nauyi da duhu kanta na mata Wani irin Azaban ciwo..
Wani malalaciyar ajiyan xuciya ne ya kufce mata ayayin da taja numfashi me qarfi cikin yanayin da bazata iya banbancewa ba, a hankli ta shiga furta Allah acikin zuciyarta tana kokrin samar wakanta nitsuwa
Batayi aune ba taji an dan tallafo kafadun ta,yakumbo tagani tana ta Kallon ta duk tausayinta ya cike kwayar idanunta na tsufa kallo daya zaka mata kasan ta damu sosai,a nutse rufaidar ta maida mata kallo itama, Jin jiri na shirin debarta yasa ta sulale a kasale ta jingina da jikin yakumbo tare da kankameta tana sauke wasu gajiyayyun numfashi dake saukowa daga can kasar xuciyarta a hankli,sun dade a haka batare dasun cewa juna uffan ba harsaida rufaida taji kamar ta Dan samu nitsuwa,idanunta da sukayi Lui sukayi sanyi ta shiga warasu kadan a hankli ta kamo hannu yakumbo ta hada da nata ta rike, cikin sanyin yanayi ta shiga karema lungu da sako na dakin kallo wanda ya zamto mata tamkar mafarki kasancewarta a raye Kuma a Nan kusa da wanda zata taimaketa sabanin kwana biyuncan daya wuce datake kallon mutuwa da azaba agaban ta karara.
Dan kadan ta motsa jikinta ta Kara lafewa ajikin yakumbo tare da sakar mata jiki tana dada narkewa ajikintan,kanta
yakumbo ta shafo kadan tace rufaida "ya jikin?..Adan takaice ta dago ta kalleta,kallo daya ta mata,sann ta sauke kanta can kasa cikin yar siriyar muryanta dabai Wani fitowa da kyau tace da sauki yakumbo,shiru ne yabiyo baya,can tace yakumbo umma na fa?..karde ..sai Kuma maganan ya dauke mata difff..
Wani Shiru tayi jin yadda maganan ya tokare mata makwaro..."yakumbo dake lura sosai da yanayinta tace 'rufaida ki kwantar da hanklinki,hadiza ta riga ta koma dakin mijinta Amma tace zatayi mana aika daga Nan ma zamuji inkomai ya daidaita ko?"..silent hawayen daya riga ya sauko mata ta shiga sharewa tace Toh Allah yasa haka
"..Allah yasa baba ya yafe,ni bana son umma takasance cikin fargaba saboda ni,..
yakumbo dake Dan shafo gadon bayanta tace Ameen rufaida karki damu karki Saka komi aranki, insha Allah Babu abunda zai same hadixa".Dan shiru tayi snn taja Wani karamin Ajiyan xuciyar tace fitsari nake ji yakumbo kitemaka min inje inyi,tana gama Furta Hakan sai ta kuma sauke hawaye,Nan yakumbo ta dago tana kallon fuskarta canta tallabo habarta tana mai karewa rudaddiyar yanayinta kallo,cike da yanayin lallashi da saukar da murya tace Rufaida ta,ki fadamin gaskiyar yadda kikeji ajikin ki Karki boyemin komi kinji?yaji miki ciwo sosai ko?Da uban sauri rufaida ta sauke kwayar idanun ta kasa tayi shiru,ayayin da kwakwalta ya riga ya fassara mata manufar tambyar da yakumbo tayi, kusan minti biyu ta dauka ahaka bata iya dagowa ba Jin wani uban nauyin furta Wani kalma game da hakan daya gama baibayeta yana cusa mata fargaba
...batare da ta kalleta ba can tace "ummm Anta min jinya a Asibiti fa ykmbo,kawai dai bana jin dadin jikina nane,sai inrika Jin kafana yana min tsamitsami,musamman ma innai fitsari Duk sai inji zafi zafi inajin Wani zugi kamar na kaikayi..
Yakmbo dake kan kallon sunkyayyen Kantan tace "yo a'ina ma Bature yasan yadda ake kulawa da mace dama?kawai sun barki babu isashen jinya,har Wani ciwon ma yaje ya Kara makale miki a gindin mara..tana kaiwa nan Taja numfashi sama cike da saka wasu abubuwa dayawa aranta wanda bata furtasu a fili can tace..nide yanzu ki Dan miqe Muje bayan gida in Gani,tun kafun rufaida ta motsa ta amsa harta dafo kafadunta yanayin lallabi da lallashi tace,insha Allah zaki warke tass rifaida, kibani Nan da kwana biyu zakiga har Kin ware kina takawa akan kafafunki,shiru rufaida tayi batace mata uffan ba ta sunkuyar da kanta Nan yakumbo ta miqe tsaye tabi ta gyara mata kwanciyar ta fice..
Wani bin kofar da Ido tayi A hankli ta sulale ta Jinginar da kanta akan matashin Kan sannan ta lumshe idanunta tsammm can sai kuma ta bude idon firgit Jin muryan yakmbo daga ta bakin kofar tana mata magana
"..tace rifaida kidan jirani kadan bari na zaga Nan baya na dawo,..Ina xuwa..gyada kai tayi tace toh sannan ykumbo ta fice a Gidan cikin sauri ta fantsama jeji..Kara Lumshe idanuntan tayi tayi lamo tana sauke Ajiyan xuciya tuni hotunan Duk Abunda suka afku da Ita ya shiga dawo mata cikin idanun ta,ahnkli ta rinka Jin wanni irin bakon yanayin da bata San dashi ba yana shigarta yana raunana mata xuciya da gangan jiki.
Gaba daya takanji duniyar yyi mata fadi da zafi,Babu Wani takamammen kwanciyar hankli ko Wani digon walwala a zuciyarta da kwakwaltan da already a cike yake da tunani kala kala har bata San Inda zata ajiye xuciyartan taji Dan dama dama ba..
Tunanin yadda zata soma tattara pieces din rayuwarta ta dawo cikin hayyacin ta shiyafi damunta wanda aynzu shi yafi rike mata kwkwalwa da zuciya har aranta take Jin kamar bazata iya sakashi a ranta nan kusa ba..
Tasan nata rayuwar ya riga ya Kare, kimtsatsen rayuwarta data Dorawa kyakkwan buri ya riga yayi Gamo da Wani mummunan tabon da bazai taba gogewa ba,dafe kirjinta tayi zuciyanta na mata Nauyi matuqa,sam Sam bata yarda da cewa zata iya sake leqawa waje bama bare ajega ta soma tunanin leading normal life Irina kowa..
Aranta tariga tasan cewa Komin boye wannan abun da zatayi aranta to tabbas wata rana saiya fito fili,inaga mutane sunji cewa ta kashe mijinta taci naman Mutum?
Wasu maqudan hawayen da suka makale mata ta shiga saukewa Suna saukowa bisa kuncinta da uban yawa kamar an kunna ruwan tamfo,kuka mai sanyi ne ya kufce mata wanda yake saukowa da ciwo bisa makoronta tana fetsar da Wani irin yankakken numfashi mai tafe da wahallen turirin damuwa da kinci,ko Yaya zata tunkare rayuwarta na Nan gaba da wannan muguwar qaddarar nata oho?Ita kanta tasan Gina Wani rayuwar ba abu mai sauki bane musamman ma in xancen abunda ya afku da ita yashiga kunnen magulmatan mutane,"..hawaye ta rinka saukewa wnda Babu adadin su tanajan sheshekar kukanta mai saka tausayi, acikin brain dinta kokri take taga ta daure din,she is alwys trying to put her thoughts behind Amma Ina sai taga kamar bazata taba mancewa ba,she has being trying so hard tun acan Vegas a Asibiti take kkrin dannewa Dan harga Allah bata son tana tuna komi,Sam Sam take son tayi nesa da tuno baqar azaban da ukubar data fuskanta abaya wanda yake azaban tsorota yake rikitata yake bala'in cusa ma xuciyanta da kwakwanta da ruhinta tsananin damuwa.
Around 8am saiga yakumbo ta dawo hannun ta dauke da tarkacen itatuwa da saiwowi Suma a kofar kitchen din ta jibge su,batayi wata wata ba ta shiga kitchen din tadan shashare ta hau hura huta a murhu,dake ma itacen Kara ne bai Wani bata wahala na ya tashi,ruwan kunu ta soma dorawa yanayi tana gefe tana daka kimba da kanufari da masoro,ruwan na tafasa ta Debi kadan ta jikasu sauran ta dama garin geron ta yayi kyau shi baiyi ruwa ba shibaiyi sololo ba Daga nan Cikin Dakin ta nufa dashi ta ajiye agaban rufaidar tana mai umarta ta data miqe ta sha,da kyar Rufaida ta miqe ta zauna qamshin kunun daya Gama bule wajen shi yabata karfin gwiwar Jin kamar zata iya sha,dayawa yakumbo ta zuba a cup ta Mika mata tace mata ta Daure tasha daga Nan bata fice a Dakin ba har sanda taga hakan ya faru,sanda taga kaiwarta baki na uku snn ta fice ta koma kitchen abunta,itama Dan sauran kunun daya rage ta shanye tass sannan ta Kara hada wuta da manyan itatuwar dayake Wajen tuni wutar ya hau ci babban tukunyar ta doraye ta Dora sannan ta cikashi da ruwa mai tsafta..bayan ta Gama hakan taja saiwowin data kawo ta shiga tsince su kowanne da irin mahadin shi ta shiga waresu.
Zama tayi agabann murhun ta rafka uban tagumi Jin Rufaida bata motsa ta ciki ba,hakan yasa ta jefa kanta cikin tunanin umma hadiza,aranta tace "ko Yaya ma take ciki oho?..tagumi tayi cikin yanayin dake Saurin fallasa damuwa taja Wani qarfaffan numfashi,Kan ta Kara nitsawa cikin tunanin can daga cikin daki ta soma jin motsi alaman kakarin amai miqewa tsaye tayi cikin sauri ta nufi dakin, tun kan ta isa baqin kofar saiga rufaida ta wawuso a guje bata zube a koina ba sai a tsakar Gidan rike da cikinta dake Wani irin juyawa,Wani irin zazzafar amai ta shiga fitarwa daga bakinta wanda tamkar hanjin cikinta ne suke shirin yoyewa ta bakintan suyo waje,
Ta Dade tana aman harsanda ya zamto yawun bakinta kawai ake Gani,cikin sauri yakumbo ta kawo ruwan sanyi ta hau wanke mata fuska sauran ta bata tana tayata kurkure bakinta
,wani gagarumin nishi takeja a Duk sanda ruwan ya taba jikinta da alaman zazzabine mai zafi ya shigeta..
Dagota yakumbo tayi a hnkli Suna takawa Sam babu karfi ajiki rufaida layi kawai take tana nishi sama sama
Cikin dakin takaita ta zaunar da Ita abakin gado cikin kulawa tana jera mata sannu,Banda layin Babu abunda takeyi idanunta da jikinta gaba daya sunyi lagwas sunyi sanyi Tanajin kanta kamar ba ita ba,Kar Kar jikinta yake rawan dari kamar wata maijin azaban sanyi Amma Daga Nan basai ma kataba fatar jikinta ba Daga nesa zakai arangama da azaban hucin zafin da jikintan yake fitrwa,a gurguje yakbo ta fice Daga dakin,ganyen RAI DORE data yanko ta tsintsinka ta murkusa sukayi lukwui ayar ludayi sannan tajikashi da ruwa ta kawo mata har dakin,samu tayi harta kwanta,bata Wani tsaya lallabata ba ta tursasa mata shan ruwan wanda tana kammala shansa baifi da minti goma ba Wani uban zufa ya shiga kewaye ta,a hnkli a hnkli sai ta soma jin sauki ajikin ta tuni zazzabin yyi kasa sosai aranta hartana ta shan mamki,itadai tasan ganyen RAI DORE abanza ma zaka gansa a jeji Kai har cikin anguwa Amma bata taba sanin yana maganin zazzabi har haka ba,
Kwanciya tayi kamr mai Jim bacci yakumbo ta koma
Waje ta cigaba da abubuwan datakeyi..
Karfe 10 saura lokacin tana famar jika saiwar magani acikin ruwan wanka saiga aikan umma hadiza,Niki Niki almajiri ya shigo da ghana most go na kaya,kayan rufaida ne acike tam da wasu abubuwan amfani da Karin tarkacen kayan abinci da sauran magungunan rufaidar da Alhj zaidu ya riga ya bayar akan kawo,acikin kayan harda Gidan soro da yar leda guda a gefe na kaza anyankashi angyarashi, takuma rubuta musu wasika akan Duk abunda ake so agaya mata zata kawo,sosai yakumbo taji dadin ganin Hakan,bata bar al'amajirin ba saida yadan jejje mata aika,yajin tafarnuwa da garin kunun jar dawa da alkalama,farar shinkafa da busashen dankli wanda yaji kayan yaji aka Niko mata
Agefe kuwa harta surfe waken suya da garin ridi wanda yyi kyau yana fidda maitar qamshi tsaban yadda shima aka fece shi aka soyashi..
Aranar kawai abubuwa kala kala ta hada Dan Gani take inbatyi Hakan wa jikin rufaida ba toh Babu shakka rufaida bazata taba dawowa sharr da jikinta kamar da chan ba..
Bayan ta Gama da nan ta nufi cikin dakin ta sameta agaba ta sawota sukayo waje da daurin kirji suka nufi bayan gida,already ta riga ta Kai ruwan maganin Adan bahu Banda wanda ta hada mata da helba da Dan gishiri,umartan tayi akan ta tsuguna gaban ruwan sanda ta kifeta da Wani zani ruwan yhau turara ta sannan ta umarceta data zauna aciki,duk jarumtar rufaida haka ta kasa daurewa Ihu ta zage tanayi Jin yadda rufan zafin ke shigarta yna mata zafi da ciwo,tsaban azaba da tsoro daukawa tayi Duk ta kone akasarta,taci kuka ba kadan ba.
Da kyar yakumbo ta maishota daki nanma bata barta ba sanda ta shassafeta da vaseline ta sama mata kaya masu kyau tasaka tuni bacci mai Nauyi ya tafi da Ita...
Nan yakumbo ta fice itama dan watsa ruwar tayi sannan ta Nemi waje tadan huta gajiyarta,sai can bayan azahar ganin Rufaida nata sharar bacci bata farka ba sannan ta koma kitchen din ta shiga shriya musu tuwon masara da miyar kubewa danya da Wani ruwan ganyen maganin wanke hanyoyin jini consisting of tsamiya mai kyau da ganyen mint data jikashi a kwanon sha tun daxu.
_7:30am ABUJA_ _Mayfair hotel,_ _maitama._
Jiya kusan atare jirginsu rufaida da nasu imad suka iso nigeria saidai su basu sauka a kano ba direct akayi dasu abuja bisa umarnin da yaa sheik ya riga ya basu dakema iyalan doc Mehra anan abuja suke da zama ba a kano ba.
Tun kan su sauko already capt muffy yasa mutanen sa Suna jiran sa a filin jirgin,it was his private plane Dan haka Babu ruwan su da hayaniyar yin clearance bare Kuma gogaggya ko gamutsa da sauran mutane...
Sojojin sama ne a jere sunkai su goma acikin shigarsu ta perfect tailored naval uniform dinsu dats so white and clean sunyi matukar kyau bana wasa ba wanda tun ana saura kamar awa guda su imad din su sauko muffy ya umarce su dasu jira isowarsun awajen,tun isowar su wajen suka tsaya bisa layi a tsatsaye Suna gadin Hakan tare da Wasu shegun baqaqen motocin su kirar bentaygas da cullinan Wanda sukenan bakake Kirin convoy yakai motoci takwas wanda banda sheqi Babu abunda sukeyi.
Ana daf da kiran sallan ishai suka iso, Wani sanyin iskar yammacine yake busawa imad na tafiyan yangansa a gefe da doc Mehra wanda yaketa famar danne dariyar sa ganin yadda imad din yasha toka yaketa kallon wajen sama da kasa da Wani irin harara yanata tsame baki, shi kwata kwata baisan meyasa ya tsane dawowar sa Nigerian bama,he just don't like da weather, tsaki yayake sakewa time to time duk dama ayanzu yasan in da xa'ace mai ya koma Vegas da wallhy bazai iya komawa ba,the breeze alone has brought him back to his senses Dan tun shigarsa jirgi bai huta da yawan tunanin rufaida dayakeyi aransa ba,har sai yanzu dayaga sun sauka..
As usual Duk wanda ya gaishe sa baya amsawa saidai yabisu da Ido cos
Rashin ganin mufrad awajen akan lokaci ya sashi Jin kamar bazai bisu ba,sanda suka shafi kusan minti sha biyar tare da Sojojin awajen imad yanata famar kukkukuni aransa,wato mufrad bazai taba sauyawa ba,he is just Neva serious wayasan ma Wani aikin yake ya kyalesu,he tot zaizo shidayansa ne yaxo ya dauke su wato shine za'a hadasa da wasu kurtayen Sojoji ko?shibaice yana son ganin fuskokin kowa ba,yana cikin Sauke bala'in aransa can saiga wata kafurar jeep wrangler ya iso ganin yadda gurds din suka Wani tsime atake suka hau sara mishi hakan yasa imad Jan wata doguwar tsaki doc mehra Banda dariyarsu Babu abunda yake..
Da sauri aka bude ma mufrad kofa ya sakalo kyawawan zaratan kafafunsa waje sanye yake da wata arniyar pure white colour Gucci write my paper shirt da wandonsa ta sojoji camouflage green wacce ta mugun axaban karban hadadde Kuma lafiyayyen dirin jikinsa wanda yake a murde kafafunsa sakale acikin wata camoulage lanvin boot, tafiyar sa yake a hnkli cikin salon takunsa mai mugun tafiya da aji mai kuma cike da kasaita da nitsuwar datake masa muguwaar kyau ayanayin sa na cikakke Kuma gwarzon namiji..
Murdadden fuskan nan Tashi bata sauya ba farinciki ne sosai aransa Amma bazaka taba iya tantacewa ba..
Har ya iso gaban su baiyi Wani kyakkwaran sake fuskar sa ba harsan da suka hade ido da imad daya mugun dore fuskansa yana harar sa ciki ciki yace ,"Dan rainin hankli kawai..Wallhy da baka cika alkwarinka ba da daga Nan wajen komawa garinmu zanyi,"..Furta hakn yasa mufrad sakin yar tsadaddiyar Murmushin sa data zo mai bazata can kasar wuyarsa yace"garinku?saiya juyo ya kalle doc mehra Yace doc kaganshi ko,Wai garin su,shi har yanzu bazai dena yarinta ba?..daga hannun doc Mehra yay yana murmushi alaman Babu ruwansa,kanma ya Gama Sauke hannun yaga harsun rungume juna suna kyakyatawa da dariya kamar wasu sabbin mahaukata Suna ta tsokanar juna,Wani Shiru wajen ya dadayi musamman wajen Sojojin dake tsaye suna kallon ikon Allah Jin dariyar sa abunda basu sabaji ba...cikin dariyar da batayi Wani nisa ba mufrad yace iyeyi kawai ai kasan zanzo din..Imad yana murmushi ya shiga nuna mai agogon sa yana cewa "I mean on time chick...Tunda kabata min lokaci Hakan zaisa ma bazan bika ba Muje gidan ba..,ni Wallhy a hotel zan kwana mu shiga motarka ka kama min Doc mehra yace hotel kuma? Ai ba matsala Muje nawa Gidan kawai,da sauri yace no no doc so nake kaima ka huta,..But u have to tell my small mum cewa awajen ta zan karya gobe',..doc Mehra yanq murmushi yace hakan ma yayi saina ganku duka suka amsa da toh sannan suka rabu...
Sojojin da suka xo daukansu su sukakai doc Mehra har gidan sa dake minister qtrs
,sukuma suka nufi wata haddiyar exclusive hotel da ake cewa Mayfair hotel dake cikin anguwan su ta maitama,it's cost $89.25 us dollars per night,babban daki suka kama su biyu,Babu maijin hirar Wani tsaban surutu kowa na Haba Haba da juna,Nan da nan imad ya shiga basa labaran cases dayayi hndling kala kala har wajajen 3am na dare basuyi bacci ba,sai can bayan sallahn asubah tukunna suka samu suka runtsa..
Basu da farkawa ba sai around 9:30am mufrad yana lullube acikin bargo bai bude idanunshi ba tukuna imad ya dau wayarsa ya kira yaa sheik ganin tun isowarsu jiya basuyi waya dashi ba,dakuma Wani makallalen zimman Jin yadda ake ciki da batun rufaida dayake ta damun zuciyarshi yahanasa sakat.
Ganin yaa sheik baiyi picking call dinba yasa ya aje wayar akan gadon ya nufi bathrum white towel ya dauka ya Dora a kugunsa sannan ya tsaya agaban sink yy brush
Ruwa yahada mai dan uban dumi a bathtube da kyar sabida gajiya ya zuba shower gel nanda nan bayin ya cika dawani irin mugun kamshi ya shiga cikin ruwan ya lumshe ido yanadan tunani, yakai kusan 5min ahaka mufrad yai knocking kofar rike da wayarshi dake ta haske murya chan kasa yace mad your phone is ringing" dan yatsine fuska yayi cikin kasalalliyar murya yace"who is calling?" kallon screen din yi ganin "mi mama" da emojin heart ajiki,a hnkli yace "is grand ma"..imad yace ok talk to her kaji mezatace..Daga can mufrad ya hararesa"
Yace c'mon am serious muff,dan Allah ka amsamin,i know mum is soo desperate to see me yaudararta ne banson inyi, Kuma kaga Yaa sheik yace Kar in yarda inzo kano toni me xance mata?..wayar na daf da tsinkewa muffy ya dauka ya sa a handsfree "gud morning grand ma..
Wani diff ta yanke surutun Daga Jin yankewar sautin muryan tan kasan mamkin Jin muryan mufrad din taji,"..tace ikon Allah
Babban Mutum ka tashi lpya?inashi imad din jasmine tace min bai isa can gida ba,a Ina kenan kuka kwana? Bai Wani amsa ba yadan tsime bayabo Babu fallasa yace grandma muna tare ne dashi,anjima kadan insha Allh zamu taho gida..
Tace to Allah ya kaimu,yace Ameen daf zai katse wayar tace wen he comes around kace yanemi ni..tell him I have a surprise for him yy sauri ya dawo gida..
Mufrd yace copy dat grand ma,baijira jin metaza karacewa ya katsae wayar...
"Kaikuma Saikayi sauri ka fito Muje gidan cos I hate too much calls..
wayasan ma jiya basuyi bacci ba..
Imad dake wasa da ruwan wankan sa yana murmushi yace wow I'm a freaking celebrity can't u feel dat?
Kowa fa so yake yaganni,mufrad Yaja tski baice komi ba ya koma cikin room ya barsa yanatayi baikuwa Gama wankansa Akan lokaci ba saida Shigowar kira kala kala daga gidan ya soma daga musu hankli...
A gurguje suka kimtsa suka fito saidai ba gidan suka nufa Kai tsaye ba,ministers qtrs suka wuce anguwan su doc mehra wanda yakasance musu tamkar God fathern su..sunfi sakewa dashi even fiye da yaa sheik..hakama shima yakejin su acikin aransa tamkar Yaya cikinsa daya haifa.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top