chapter 24
BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.
Part1:chapter 24
Bangaren yaa malam kuwa ana sauke shi a kofar gidan sa baiyi wata wata ba ya nufi cikin gidansan ayanayin bacin rai da tsananin fushi wanda tsaban munin sa aransa yasa hatta kwayar idanunsa sanda suka sauya kala sukayi jaajaxur kamar anhura garwashin wuta,tafiya yakeyi gaf gaf gaf kamar wani Doki,yana haki yana huci yana kuma sauri tamkar wanda zai kifu akasa ya ci da bakin sa haka yake jefa kafafun sa,idon sa a rufe take,bai biya dakinsa ba ya wuce direct zauren rubuce rubucen sa na lakanin qur'ani daya sabayi,yana hankade kofar zauren ya fada karkashin gado ya soma fidda wasu Alluna,ruwan tawada na musammn da Wani jimmamen buzu..
Kara lekawa karkashin gadon yayi ya fidda wani abu a lullube da farin kyalle Duk kura da datti ya hau kanta,baidamu ba ya shiga kakkabewa sanda kuran ya ragu sannan ya ajiyeta agabansa,cike da nitsuwa ya yaye kyallen,wata yar madaidaiciyar akwatin gongoro ne ta bayyana agaban sa wanda aka rufe ta kirif da makullin tokos silver colour,key dinta ya dauko ya budeta atake Daga Nan Bai bata lokaci ba ya shiga barbaje abubuwan dake ciki Wani irin qur'ani ne wanda yake brownish_red in colour,anjerasu a falle falle daga Ganin sa kasan jimammen ajiyane wanda bada fasalin hafs akayi rubutun sa ba,an zayyana ayoyin ne da asalin fasalin rubutun warash,Asalin irin rubutun nan na ta da can can wayanda suka matikar kwarewa..
Daukar qur'anin yayi ya ajeshi a gefe sannan ya Kara jefa hannun sa cikin akwatin yana lalube Jim kadan ya fidda Wani sihirtaccen turare,turaren baida wani yawa Dan kwata kwata bazaifi yayi cikin kwalban fiya fiya ba,budewar sa keda wuya Wani azaban qamshi mai ratsa jini da jijiya ruhi da kwakwalwa ta mamaye wajen hartana neman bugar dashi,a kusa da qur'anin ya ajiye turaren ya Kara lalubar akwatin ya fito da Wani ferarren alkalami mai Dan uban kaifi da tsini,gefe yay dasu duka sannan ya rufe akwatin.
Acikin allunan daya fitar yasaka hannu ya dauki na karfen cikinsu wanda yake tamkar takobi,sau daya ma ya taba amfani da Ita arayuwarsa tsaban qarfin sirrinta da muhibbanta a idanun sa, itakanta tawadar ma saida ya zaba daga nan bai bata lokaci ba ya hadata da ruwan Wani magani ya Kuma jefa wancan alkalamin aciki Nan danan ta jike aciki sosai
Miqewa yay ya nufi can sashensa ya bude kofar dakinsa ya shiga ya dauko kwarya da sauran abubuwan bukata kamar ruwa da buta da wasu lakani wanda bansan su ba...
Bai dawo zauren ba sanda ya shiga bayi ya doro sabuwar alwala yanayi yana wasu irin maganganu tamkar zararre da alaman har yanzu wutar dake cin zuciyarsa bata matso kusa da mutuwa ba
Shigarsa zauren keda wuya ya shimfida wata farar buzu ya haukai ya zaune kafafunsa a dungulme,sann ya dauki qur'anin ya shiga bubbudewa daidai Inda yakeso ya jera su falle falle, shafukan da zasuyi mai amfani kaf ya ajiyesu agaban sa
Zaman dirshan yay akan buzun Nan tare da nade hannun garensa yana wasu irin tofin da bansan kansu ba daga Nan Bai kara bata lokaci ba ya dau allon karfen nan da tawadar ya dorata akan cinyarsa ya hau rubuce rubuce Wanda Ako Wani iyakar rubutun dayakeyi saiya shaka dafin tawadar ta numfashinsa wanda yake tayashi jefa sirrin lakanin sa aciki,yanayi yanai ma wasu ayoyin wasali wasu kuma baya saka musu wasali,wasu yakan daure wasu yakan jaaa,ahakn sanda yaci kusan awa hudu yana abu daya.
Kafin ya gama Gabadaya jikin sa yayi tsami ga gajiya ga azaban yunwa ga tsananin fushi da bacin rai daya wuni da shi saidai dukkan wayannan basu hanasa aikata komi ba...
Ana daf za'a kira fajr ya miqe cikin sauri ya Kara komawa bayan gidan sa alwala ya Dora sann ya dawo,rubutun dayayi a allon ya shiga wankewa yana tsilalo ruwan a Dan madaidaicin kwarya,kusan cika kwaryan yay da ruwan rubutu sannan ya ajiyeta Agefe ya nade buzun sa tsaf ya dauko dayan jimammen buxun mai brownish red colour ya shimfida ta ya haura Kai ya tsaya a tsaye kyam kamar tsohon soja tare da kwaryan a hannun sa,daf setin bakin sa ya kawo kwaryan tamkar wanda yake shirin tofa Bismillah sai ya shaisha,,lumshe idanunsa yay ya shiga ambatar wasu irin tawaludun sumbatun karatu wanda ba agane komi sai sunan zaidu daya ke tofawa harda numfashin sa acikin kwarya....
Yana gama tofen tofen sa ya shanye rabin ruwan,sauran ya ajiye acan waje daf setin inda hasken rana zai billo ya dau turaren Nan ya zuba kadan aciki yabarsa awajen,komawa dakin yay ya tattara komi nasa ya maidasu one by one wajen ajiyarsu tamkar da ba ama taba su ba.
Lokacin daya fito ana famar kiraye kirayen sallahn fajr wasu masallatan harma sun shiga Dan haka yay sauri shima ya fita yaje ya kira nashi sallah yana mai jan almajiransa, daga nan bayan sun kammala suka bingire da bitan karatu.
Kowa sai mamakin
Ganin yaa malam yakeyi,cos last Thy know was polisawa sunzo sun daukesa sun tafi dashi Amma Daga Nan ba a Kara Jin sauran zancen ba..
Wato tsabar yadda axaban gulma da makirci da mugun iya saka ido yayi danko yayi kuma katutu a xuciyoyin Yan anguwar acikin Yan kwanakin Nan har comitee suka hada akaje har Gaban dpo domin aji Kan labari saidai basuci nasara ba..
All this while Babu abunda ake yayin gulman sa a anguwar face matsalar gidan yaa malam wanda tun daga auren rufaida basu gane kan komi ba.
Tun ranar da aka kama yaa malam aketa zirya a kofar gidan sun babba da yaro tsoho da tsofuwa,ahaka ma banda makwafta da Yan nesa wayanda sukayi degree a gulma,Kai hatta matar mai anguwar su saida tayi sawu goma shabbiyar a kofar gidan yaa malam Wai Koda ma zataci Karo da umma hadiza taji Kan labari.
Karshenta Acikin duhu suka zauna kowa da yanayin harsashen sa Duk dama dayawan su cewa sukayi yaci kudin sata ne dama ansan sa handamamme mayen kudi,wasu Sukace sayar da yarsa rufaida yayi
Abun ya juya masu
Acikin anguwar kaf aka rasa samun wanda zai masa kyakywan zato shiyasa ayanzu da suka gansa kyam kyam yanai ma almajiransa karatu tamkar wanda Babu abunda ya faru dashi abun sai ya matukar Kara basu mamaki da tsoro.
Babu bata lokaci maganan dawowar sa ya fara karade kunnen mutanen anguwa,saidai komin gulman mutum zaka samu yana matukar Jin shakkar yaa malam danshi mutum ne mai tsananin son girma da daukaka bayason Wani ya dedeta kansa dashi ko yayi abota..
Ya dade yana kallon sa a matsayin Wani katon shehin malami mai kima da tsananin daraja Dan haka alamarin rayuwarsa baya sarara ma kowa.
Duk zumudin Yan anguwar haka suka binne zuciyoyin su Suna jiran karfe 7.30 na safe yay by then ansan ya Sallame almajiran sa
Bangaren su yaa sheik kuwa acikin su babu wanda ya kara samun wani nutsuwa acikin wannan daren,iya bakin kokarin sa yayi dan yaga ya sassaita hjy mama Amma haka takijin shi, takima ta bude masa kofa, haka tayi fafur ta hanasa tunkarar ta da wata magana data shafi yaa malam da su rufaida,while acikin ranta gaba daya hanklinta da tunaninta yana kan jikarta rufaida ne,Wani bin sai taga kamar batayi ma rufaida adalci ba data korata gida saidai tasan in batayi Hakan ba karshenta komi zaizo ya rikice musu ne daga karshe ..
Akan bakarta ta kwana Dan kokadan axuciyarta batajin zata ita sauya ra'ayin ta akansu,zaka kasha mamakin yadda ta raya daren tana Kai ma Allah kukan ta akan yayanta da ahalinta kamar ba tsofuwa ba...
Shikuwa Yaa sheik da taimakon Matarsa yadan samu nitsuwa don tunda ya rabu da hjy maman yakirata sukayi magana kusan rabam daren sukayi tare tana famar kwantar mai hankli da kalamanta masu taushi da tsananin sanyaya zuciya..
Sanadiyar haka yasa bai Wani samu isashen barci ba haka dai ya farka da safe Duk gabobinsa agajiye,ga kansa daketa masa Wani irin azaban ciwo Wanda tun acikin daren ya somajin sa saidai bai dauka zaiyi tsananin da zaina jinshi har yanzu ba..
Kusan da kyar yake iya daga Kan tsaban ciwon dayake masa,he tot he is just stressed,Dan haka kafin yay wanka sanda yaje sasshen motsa jiki Duk da haka baidena Jin komi ba saima jiri jiri dayake kokarin nakasa masa gabobin jiki Wani irin Dan uban kyuiwa da kasala ya rinka ji aransa abu kadan saiyaji ya gaji yananemam wajen lafewa abunda Sam bai saba dashi ba kenan arayuwar sa,Dan tabbas yasan kasala daga shedan take kuma arayuwarsa baya bukatar abunda zai danganta yanayin sa da shedan Dan haka ya ficceke kansa daga yanayin dayakejin ya fada bathrum ya doro wanka tare da alwala,...
Abu kamar wasa haka ya rinka bata lokacin sa a batrum abanza da wofi kwata kwata baisan saibin meyakeyi ba Kan ya hankara kawai ji yay anata sallan fajr a masallatai banda shi da sauri ya zura jallabiyar sa ya fita a gurguje, da kyar yau ya samu raka'ar farko..
A bangaren su rufaida kuwa tun da umma hadiza ta kammala ba ykmbo labari take cikin yanayn sanyin jiki da jimami sai can dai data samu yar nitsuwa sann ta sata agaba ta rinka yi mata nasiha akan yanayin rayuwa....
Sosai umma hadiza ta zubda hawaye anan gaban, Saidai wannan karon zafin kukan ta ba akan matsalar rayuwarta Dana yarta bane kawai,tsantsar tausayin yakumbo ne yake neman ya nakasa mata zuciya.
Tun tasowarta bata San kowa a rayuwarta ba sai yakumbon datace mata tsintar ta tayi a bola acan Wani gari,Kuma tun a lokacin yakumbo bata fiye bude mata labari akan komi ba,takan dai gaya mata gaskiya game da abunda ya shafi rayuwa,saidai gaskiyar dayau ta bude mata yaso yay ma zuciyarta illa da Nauyi Dan saiyau take ganin matukar takaici da tsansar halin damuwar da zuciyar yakumbo yakeciki akan rayuwarta,Wanda tuni ta laka makanta lefin duk wani digon wahalar da take sha danata rayuwan..
Yakumbo bata taba nuna ma umma cewa aranta tana matukar nadamar ganin irin wahalar datake sha a hannun yaa malam ba,yawanci ma saidai tayi bambami ta zageshi,Amma yau saita tsinci kanta cikin bayyana irin tsanar datakeyi masa,babu abunda ta boye ma umma hadiza game da Hakan Wanda yasa umma matukar Jin tausayin yakumbo a xuciyarta bana wasa ba..
Wani irin So,so irinna uwa shi ta bayyana ma umma hadiza a fili,sann ta nemi yafiyarta tana kuka mai ban tausayi,Wanda sanin cewa rufaida zata iya farkawa a ko Wani lokaci ne kadai yasa suka dakata suka Dan samu nitsuwa da kokrin neman kyakkwar mafita agaresu...
Amana umma tabar yarta rufaida a hannun yakumbo domin ta samu kulawa da kwanciyar hankli, ita Hakan ma a fiye mata,rufaida ta zauna anan din sabanin anguwar su data San dolene ayita cakubarsu da gulmace gulmace, Sallahn asubahi sukayi,batare da tsayawa bata lokaci ba ta shiga saka himman komawa dakin Mijinta Wanda har acikin ranta bata son yin hakan,Amma aynzu jitake zata iya aikata komi saboda samun kwanciyar hanklin yarta rufaida..
Sosai yakumbo ta Kara karfafa mata zuciya da nasihohi masu shiga jiki tace mata Allah yana kallon hakurin su kuma shikadai ne Kawai zai iya sassauta musu a lamarin su,tare da mata alkwarin Zata iya bakin kokarinta akan xancen kulawa da lpyar rufaida.
Acikin Kudin da yaa sheik ya basu ta Zara kusan dubu goma shabiyar ta danka ma yakumbo da cewar zata tafi da sauran duk abunda ake ciki zasuji shi ta sako...
Har bakin gadon ta isa ta zauna kusa da yarta data dunkule jikinta waje guda tana Kan bacci,ta dade awajen batare da ta aikata komi ba..
Wani irin kallon ta kawai takeyi da wannan shaukin azaban Nauyi da karayar xuciyar dayake sokiin ta har kashin bayanta
Wanda ya sata soma sauke wasu maraitattun hawaye masu tahowa da turirin dumbin Nauyi da kalaman data binne acikin zuciyarta,gyara mata kwanciyar kawai tayi tare da shafo gefen fuskarta a hankli ta rankwarfo ta sumbace goshinta sannan ta sauke Ajiyan zuciya tayi Sallama da yakumbo ta dau mayafinta ta nufi gida....
Isarta gidan keda wuya ta hange daidaikun almajirai a kofar zaure da alaman har angama karatun safiya,dauke kanta tayi cikin sauri batare da saurarar kowa ba ta shiga cikin gida,it was around 6:59am waje baima gama washewa da maraicen safiya na Dan haka duk Wani motsi da magana da akkeyi a gidan zaka iya jiyoshi....
Tsayuwar cak umma hadiza tayi Jin sautin sa dayaki yaki karewa,tabbas muryan yaa malam takeji kamar yana muzahara,Dan da Wani irin zuciya da karfi yake dukan kirjin sa yana kwada kansa da kwaryan,
atake jikinta ya hau rawa ta somajin tsananin bugun zuciya duk dama nawai fahimtar Abunda yake faruwa tayi ba,umarnin zuciyarta kawai tabi ta wuce sashen yaa malam din,cikin balain sauri take tafiyarta tamkar wanda ake kiranta da gaske,bata koyi Sallama ba sai gata a tsakar filin sashen Inda idanunta suka ci Karo da yaa malam a tube tumbir haihuwar uwarsa yana faman tsinewa rayuwar Dan uwansa zaidu yana cewa "zaidu bazai taba mutuwa ba har saiyayi jahilci ya toxarta mahaifiyar sa,duniya sai sun zagesa sun kirasa azzalumi,uwa uba sai hjy mama ta tsine ma zaidu da bakinta saita masa korar kare...idanun sa gaba daya ya rufe sai fadan Hakan yakeyi da tsananin axaban zakuwa da mugunta
Yana fada yana tofawa harda numfashin nishin sa acikin kwaryan,wanda ruwan already ya riga ya gamutsu da turaren ya dawo Wani irin kalar bakiii
Tamkar duhun dare haka ruwan rubutun nan ya dawo..
Kusan a daskare umma hadiza take tahowa kusa dashi Dan da alamn yayi nisa baima ji shigowartan ba..
Kallon sa da jinsa kawai takeyi sakaka tamkar wata tababbiyar mahaukaciya wanda ta rasa hanklinta,tsoro da mamaki ya riga ya dabaibayeta..
Yana ta tofe tsinuwar acikin kwaryan da alamn xai binne kwaryan ne da maganin a kasa a tsakar gidan Dan saida data matso take ganin ramin daya tuna da yar fatanya agaban sa,Cikin razana da dimauta da karfin balain ta finceko kanta daga kafewar datayi,Wani irin kururuwar axaba mai ratsa dodon kunne da dasa tsoro a zuciyar duk Wani mai sauraro shiya kufce mata,ta tuma a kasa ta wafto da uban gudu tayi kansa ba acikin hayyacin ta ba,ta bangaje kwaryan ya kifu akasa ta daka tsalle akai sanda ta farfasa shi kashi biyu,da ihu da tsawa da Firgita da gigita tace "malam?malam?kasan mekakeyi kuwa?Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun..
Malam kaji tsoron Allah,malam kasan zaka mutu kaje ka gamu da Allah
wa rayuwar Dan uwanka zakayi wa muqun Kulli?
Me yaya zaidu ya taba maka arayuwa?kafada min meya tsare maka?ko yaa zaidu ba Dan uwanka bane baicanci ka masa wannan Abun ba...kasani Allah zai iya tozarta ka kafin ka tozarta shi.. wa iya zubillah malam Allah ya kubutar damu,wayyyoo Allah na ,wayyo Allah na shigga uku wayyo Allah sai rigib ta fado kasa ta sulale a mugun dimauce tana birgima tana kururuwa tanata maganganu tana rabza uban kuka.
Yaa malam bai iyayin ko motsi na Dan shima A mugun razane yake,tunda ya bude idanun sa da suka firfito waje sukayi ja yana kallon ta bai motsa ba,a firgice ta damko kafafun sa tana ta tambayar sa me dam uwan sa yayi masa a duniya dazai saka masa da wannnan baqar muguntar? kururwan datayi ya isa ya sanar dakai takai koluluwar halin dimauta da rikita Dan sosai yaa malam ya bata mamaki yakuma kure mata tunani
Ganin ta rikita tana gagggaya masa maganganu masu tsananin nauyi da raunana zuciya yasa shima ya kakalo dauriya ma xuciyarsa ya soma zaginta yana daka mata tsawa yana cewa "itama bai barta ba,acewar sa yana gamawa da rayuwar zaidu zai komo Kan nata,saiya toxarta su ya muzantu su,suji zafin abunda yaji da suka saka mahaifiyarsa ta Sallame sa...ya rinka zaginta yana dirin masifa akan zubar mai maganin datayo wanda tabbas yaji matikar baqin cikin faruwar Hakan,Dan Koda ya sake Wani baizai to tasiri ba,Dan a shekara sau daya ake amfani da turaren tsabar karfin sirrinsa,kenan Babu halin ya kara daukar mataki cikin gaggawa dole saiya jira Wani shekarar ta zago,ji yake tamkar ya shake hadiza yakaita har lahira,a xuciye yake kallonta yana huci umma bata fasa ba tana ta jefo masa nannauyan kalamai wanda komin bushewar zuciyarsa sanda suka tsagashi suka shiga sunai masa zugi da ciwo,...karshen ta zama tayi dirshan akasa agaban sa tsabar ranta ya baci dan abunda take gudun shiya soma afkuwa dasu..
Ta soma fidda abubuwan dake zuciyarta game dashi,Tana bayyana masa cewa ta tsane zaman gidan sa tace masa saboda kwanciyar hankli da martaban rayuwan yayanta kawai take zama dashi bawai dan ya isa ba .
Tace ta gwammaci tayi karuwanci ta biyashi kudin bashin maganin dayake bin yakumbo akan zaman auren sa..
Ta rinka kuka da zuciyarta tana cewa tana nadama da baqin cikin kasancewar sa uba ga yayanta,tsantsar tsanan datakemai kawai take bayyana masa a furucin ta wanda Hakan ya dame xuciyarsa matika domin kuwa bazai taba iya rabuwa da hadiza ba,Dan kaf cikin matayen daya aura Babu wacce ta taba shiga ransa ta Sami matsiguni da daraja inba hadiza ba,aransa yana matukar kaunar hadixa,yana matukar matukar sonta irin sonda baima San ko so bane ko tabin hankli bane,shidai yasan ko mutuwa hadiza zatayi da tsanar sa saidai ta mutu a dakinsa Amma bazai taba iya rabuwa da hadiza arayuwarsa ba.
Shiyasa ma ayanzun dayake sauraran munana kalaman tsana datake fetsa masa aransa ya shiga jn kamar wuta ake watso waa gangan jikin sa ana qona sa.
Umma hadixa kuwa ba a ma cikin hayyacinta take ba sai magnganu kawai take yi
Tana ce masa gata ta dawo masa saiya kasheta,ya rabata da yayan ta,ya rabata da rufaida alokacin datake bukatar ta matuka
Tace malam ka cuci
Rufaida kamata auren dole ka Dora mata qaddarar kashe mijinta
Ka muzanta rayuwar ta
...malam tsakanina da Kai har mutuwa bazan yafe ba...
Allah ya isa min Allah saiya sakawa rufaida da sauran yayana...
Wani irin damko ta yay ya shakure mata wuya ya shiga dukanta yana kwallo da Ita har suka shiga daki yabi ya jefata akan gadonsa ya kulle kofar dakin da makulli..
Daga kofar gidan kuwa Yan gulma ne makil wayanda suka jiyo kururuwan ummma hadiza maza da mata sunkai su goma Duk an kasa kunne anajin abubuwan da suke fada...
Kan kiftawa da bisimilla har labari y karade anguwar kaf sanda akaji labarin cewa Rufaida yar gidan yaa malam
Ta kashe mijinta...
Wani irin hargitasen gurmi mai tada fence aka bude lungu da sako hirar da aka sunkuya yi kenan,saidai rufin asiri irinna ubangiji yasa iya maganan kisan kawai suketa riritawa ba'aje ga sauran abubuwan da sukajin ba,Dan aganinsu mace ta kashe mijinta ai bakarmin al'amari bane...
A safiyar ranar haka yaa malam ya sauke muguwar azabar jarabar sa datake ciccin sa ajikin umma,ya mata kaca kaca,ya shiga lungu da sako ajikinta yana mai huce haushin tsnar datace tanai masa,bbu gajiyawa sanda ya sauke Duk wata niyyarsa wanda tamkar yau ya soma tarawar aure da Ita,sosai yaci yaji dadi bai sauka akanta ba sanda yaga bata Wani kwakkwarn motsi,yana rikitowa kasa ya saka hannu ya jawo katon garen sa ya saba ya rufe tsaraicin sa yay dayan sashen da uban sauri Jin Wani azaban son hadiza dayake rikita masa tunani da zuciya
Duk da haka ma aransa cewa yake saiya ci uban hadiza saiya sata nadamar rainasa datayi yau..
Saiya raunana mata xuciya...
Da wannan rudaddiyar yanayin ya shiga bayi ya doro wanka,ya dade yana wankar saboda Wani sabuwar nitsuwar dayake dirar masa yanajin nitsuwa,tabbas hadixa mace ce Dan kuwa bai tabajin akwai macen dazatayi masa dadin da hadiza take masa ba har Abada Babu wacce take da baiwa irinta hadiza Dan ita ta musamman ce a duniyan mataye..
Yana kammala wankan sa bai jira uban kowa ba ya koma sashen Inda ya sameta har yanzu akwance cikin tsaraici tanata kuka,kallo daya ya mata ya dauke kansa da zafin hakan aransa Amma saiya basar ya cigaba da abunda yakeyi yana kammala shiryawa ya saka Kai yana Jan mata tsaki yayi fitarsa waje..
Umma dake Jin kamar ta hadiye ranta ta mutu haka ta daddage ta koma sashen ta ta nemi ruwan zafi ta shiga ciki,kafun kace Wani zagowar rabin sa'a harta soma jin daidai ajikinta,cike da dauriya da jarumta irinna mata ta warware cikin tunanin matakin da zata dauka arayuwarta Nan gaba...
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top