chapter 23

VOTE NE KAWAI YA RAGE MUKU YAN ALJANNAH..PLS KU DANNA VOTE BUTTON,PLS BADON KATON GOSHI NA BA😂🤣🤣😂KUYI HKRI KU DANNA.

BISMILLAHIRAHMANIRAHEEM.

Part1:chapter 23

Isar su sashen ke dawuya yaa sheik ya shigo agaggauce tare da yar sallama Suna hade ido da mahaifiyarsa ya ya kau da idanunsa bisa abunda ya tarar baiyi wata wata ba cikin sauri ya dauki zanin mahaifiyar san daga kasa Inda tayi fito dashi cikin gaggawa ya shiga Dora mata tare da janyeta daga kwanciyar kasan datayi ya kuma rungumeta ajikin sa yanata famar rarrashinta cikin tsananin tashin hankli ....
Wani irin kukan haushi kawai takeyi tana girgiza kanta cikin tsananin takaici tace
"Zaidu menayi arayuwata da na cancanci haka daga wajen Dan da na tsuguna na haifa?bukar ya hallaka rayuwar sa,ya hallaka rayuwar yarsa,wallhy ba Dan haihuwar zaure nayi ba da yau saina ce maka zanja min bukar akayi a Wani waje"...ni ciki na bai haife mugu ba,wallhy mahaifata baxata taba rike da mai mummunan baqar xuciya ba,Wai ace abunda ya aikata ma rayuwar yarinyar Nan bai ishesa ishara ba?.
Kace mai ya tafi Duk inda zaije wallhi na yafe sa,bana son in kara ganin sa,in na kallesa Babu abunda nake tunawa sai rayuwar rufaida,bukar sai kaga sakayya akanka,bukar bazan yafe maka ba,kaje Duk Inda zakaje kafita kabarmin gidana,'..kaje duniya ta isheka...cike da razana da kaduwa ya sheik yace Haba Mama, Haba Mama, mama mezai kaiki Furta irin wannan kalaman akan Dan cikin ki,mama yanzu haka zamuyi dake ? Mama idan kikace ma Yaya abbbakar yaje duniya ta ishe sa kinyi masa adalci kenan?wa dukanmu kikayi bakin mama,sabida Duk abunda yagani muma zamu Gani tunda shi Dan cikinki ne,nikuma Dan uwana ne,mama Hakan ne kawai yasa na danne xuciyata na  tsaya masa Kar su kullesa acan,bawai banajin zafin abunda ya afku da yata rufaida ba ne Amma Duk Inda bacin rai tayi tsanani karshen sa nadama ne mama
,Kiyi hakuri kiyafe masa,adduanki yake matukar bukata ba bakinki ba,mama kiyi hakuri ki yafe mai rufin asirinmu ne dukka,dukan mu mudauki ahakan a matsayin qaddarar rayuwar rufaida,wanda bata cancanci mu rarraba kanmu a lokcin datake matukar bukatar kulawarmu ba,mama rufaida tayi ciwon da saida ta rasa hanklinta,yanzu abunda kukeyi Kuna taimakon ta kenan?gata Nan fa acikinmu tana Jin mu tana Kuma fahimtar dukan abunda mukeyi anan,mama kodan rufaida ki yafe ma yaa bukar ki dena tsine masa da kalamanki,kiyi haquri mama dan Allah kiyi hakuri Wasu maqudan Hawaye ne suka shiga saukowa a idanun yaa sheik wanda ya sata yin shiruuu Amma badon taso ba..
Daga nan Wani uban shirune ya dauke wajen harna tsawon minti goma Babu wanda ya iya Kara Furta komi,Umma hadixa dake tsaye can ta shiga kallon yarta data rakube akasa cikin yanayin kife kanta a tsakanin cinyoyinta,Wani irin malaciyar yanayi mai saka tsantsar tausayi shiya debe xuciyartan ta miqe tsaye cikin sauri ta isa gaban ta cikin Kara janyota jikinta ta Kara rungumeta tsammm tana shafa ta,sauke Ajiyan xuciya take tanajin yadda yarta take dada shigar jikinta tana neman Jin dumin ta tako ta halin Yaya wanda Hakan kadai yana kara rikitata,lumshe Idanun ta tayi ta shiga shafo kanta tana sauke hawaye Dan Ko kadan bata so tayi kuka tuno magangaun hjy mama nacewa itama da lefinta hakan yasa kukan ya kufce mata ta shiga neman gafarar rufaida Idonta a rufe tanayi tana rungumeta gwanin ban tausayi,itama rufaidar kuka kawai takeyi,ita bataga laifin ummanta anan ba,har cikin ranta tasan Babu yadda ummanta ta iya ne da tuni ta taemake ta...
Ganin kukan ya tsanan ta yasa rufaidan kwacewa ajikinta ta dago jajayen idanunta ta kalleta muryan ta na rawa tace
"Umma kituna fa ke kika koyamin yarda da qaddara da yin takawallakli game da rayuwata,Ki tuna ke kika ce min Duk abunda ya sameni arayuwata qaddara ne bayin kowa ba,ni na yafe ma kowa umma bana fushi da ku,na dauki Hakan a matsayin qaddara ta..tun bata karashe maganan ba Umma hadiza ta janyota ta kara rungumeta nan hjy mama ta shiga share hawayenta Jin wayannan kalamai na rufaida da suka sanyaya mata xuciya wanda suka kasance tamkar ruwan sanyi a kirjinta dayake ci da wutar fushi da takaici,To inhar rufaida ta yafe ma kowa Kuma ta karbi qaddarar rayuwar ta to lallai suma yakamata su amshi qaddarar ayadda tazo musu sannan su kare martaban familyn su,su hada Kai wajen daidaita rayuwar rufaida,Hakan ya zamto musu jigon gyara kurakuren da suka tafka abaya.

Saidai shi Yaa malam baiji ba, baigani ba,banda sabuwar shafin tsana dayake shirin budesa aransa akan Dan uwansa zaidu ba abunda yakeji aransa,Kawai kallon munafuki yakeyi ma zaidu,wato ya hade Kai da kafurai ya raba sa da yar sa da Matarsa yanzu haka Yana neman ya raba sa da mahaifiyarsa wanda Ita kadai ta rage masa haske acikin xuciyarsa ko?
Wani baqin cikin halayyar yaa sheik yakeji yana Jin Wani irin kaxamin kishin nitsuwa da dattakon sa,har shi za'a nunawa wa iya wa'azi da fadar gaskiya?tab di..Sam shikam bazai iya zama anai masa wannan raini da tsantsar cin fuska ba,..

Yana daga tsayen ya juyo a raunane
Ya dubesu
Yace"..shikenan mama..zanje din,
Nasan dai ko baki Furta ba ansan Ni Da mai yin biyayya ne agareki komin rintsi,tunda ke da bakinki yau kika koreni kika zabi danki zaidu shikenan na barki dashi,ke kuma hadiza saiki zauna anan shi zaidun ya aureki ya hadaki da Matarsa,can dama ba son zama a gidana kikeyi ba burinki ne kiga bayana,Kin hada Kai da yarki Kin rabani da albarkan mahaifiyata Allah ya isa min hadiza

A zafafe cikin bacin rai ya nuna rufaida tsaban ransa a bace yake baima iya maganan ba Sanda  yaci minti biyu ya nunata da yar yatsa
Cikin Wani irin yanayi rufaidar  ma ta narka masa kwayar idanunta da suke mugun jefarsa da nannauyan kalamai Masu rauni dake boye aciki wanda tuni ya karanto su kuma ya fahimce irin kunci da takaicin datakeji aranta game da shi
Duk da haka bai fasa ba yace
"Kije...na barki da su
Tunda akanki xanga tijara arayuwata.. rufaida Allah ya..cikin sauri yaa sheik ya rufe mai baki ya hanasa Furta koma miye zai Furta akan rufaida a mugun fusace ya bangaje hannun sa
Masifa ya shiga masa ya juyo a hatsale ya yo kansa tamkar zai bugesa
"Wai shin ni sa'arka ne zaidu?..inai ma yata magana meye hadina dakai da zaka toshe min baki?..ruwa xaka saka akasa kasha anxabeka a matsayin da nikuma ance canzani akai...
Amma fa Kusani haryau nine da Iko akan rufaida sabida nine na haifeta sannan bazan taba tsine mata ba,.
Niba kamar mahaifiyarka bace datake sallama yayanta ga duniya

Da sauri Yaa sheikk ya kallesa hjy mama ta miqe tsaye,'..tace eh aje ahaka, Dan ka zageni Wani abune?
Rufaida yarka ce Babu wanda ya isa ya canja Hakan shiyasa ma ka samu damar muzanta rayuwarta aida ni uwace agareka da ko auren ma ba'ayi ba.
Amma yarinya bata so bataso sanda akayi, bukar ashe bakama San mawanda ka lika wa yarka ba?Kai a naka tunanin wannan abunda ka aikata wa rayuwar yarka adalci ne?
In adalci ne ka fayyace min yanzu inji...Sabida ni ban gane salon jahilcin dake yawo akan ka ba,wannan ai mugunta ne da rashin sanin darajar Dan adam.
Toh alhamdullhi rufaida da bakinta tace ta yafe maka Amma nidai hasiya bazan sake daukar rashin hanklin ku ba,rayuwar jikata yafimin dukan abunda kake tunani.
Kuma Daga yau zan soma daukan mataki,karka Kuma saka aranka cewa akwai kalamin da zaisa na janye fushi na akanka bukar.
Araunane ta juya ta kalle umma tace
"Ke kuma ai saiki bishi ku barmin gidana,kije can kita masa bauta..karki karban ma yayanki yanci..Daga yau nidai bazan dau nauyin kowa ba duniyar ta ishi kowa riga da wando
,hadixa na bar ki da yar ki rufaida,..kije kisata agaba ki kashe ta kema...inkin ga dama karki tsaya mata har abada, nagaji da ke da jahilin mijin ki.
Duk ku futa kubarmin gidana
Cikin wata hargitsiyar bacin rai ta Kara sake musu tsawar da sukaji shi har tsakar ka tace
Kufita Nace muku ko saina tsine muku albarka ne ? Cikin
Mutuwar jiki da xuciya ya sheik ya gurfana agaban ta,
Tun kan ya fara rokon ta ta hankade sa cikin masifa
"Zaidu ka kiyayeni ko in kaima in faffalaka maka Mari...idan na Kara Jin bakinka akan zancen rufaida Allah ya isa ban yafe maka...tana Kaiwa nan ta fashe da matsancin kuka
Tace kabarsu suje da Ita su kashe ta.
Aiba Kai ka haifa masa yarba,tunda ya tsaneta baya kaunarta saiya tafi da Ita can gidansa ya kashe ta yasha Romo,ke kuma kije can kizauna kita masa kuka bakin cikin mutuwarta ya kashe ki..
"Ni ku futamin a gidana bana son ganin ku,na sallameku arayuwata duniya kaf su zageni,Aje afada Duk abunda za'ace akaina, eh din nazabe Dana xaidu na yafeka ka bukar,Nafada na Kara fada Dan ba tsoronka nakeji ba

A xuciye yaa malam
Yake kallon hjya mama wcce take maganan ta a xuciye Dan ta dade bata tsincin kanta cikin wannan yanayin fushi da bacin rai ba..

Jiki a sanyaye yaa sheik ya sunkuyar da kansa cikin rasa abunda yake masa dadi,yaa malam kuwa kada kansa kawai yayi cikin tsananin fushi ya saka Kansa agaba yay waje baikoyi yunkurin bata hakuri ba..
Da zazzafar fushin hakan ta miqe tsaye cikin masifa ta fatattaki umma hadiza waje datake famar kuka,"..
Haka ta rufe idanun ta tace rufaida maza tabi uwarta suje can..Rufaida batace uffan ba yanayinta ya balain nuna halin karayar da xuciyarta yakeciki,a sadade ta juya a hankli ta bi bayan umman tana takawa a dangale tana goge ruwan hawayenta,Suna fita a falon Hajiya mama tayi sauri ta haura sama ayayin
Da yaa sheik yabi bayan rufaidar da sauri kuka kawai takeyi,ya janyota baya ya Dan rarrasheta yana cewa zaizo har gidan gobe dakansa ya duba lpyarta ya mammata nasiha akan ta kwantar da hanklinta ya Kuma tunashar da Ita adduoin daya kokkoya mata acikin kwanakin Nan,hannu ya saka a aljihun sa ya debo kudin da baisan ma nawa bane ya damka mata yace tayi sauri ta iske ummanta da already ta isa bakin gate ta tsaya Agefe haka tana famar kukan takaici

Yaa mallam kam ko ajikin sa,Koda ya tsare adedeta ce mata yayi karta sake ta biyosa kota shigo masa gidan sa tare da rufaida

Yace mata ai dama tundacan ya fada musu cewa Duk wacce ta kashe auranta bazai Kara daukar nauyinta ba,bare ma rufaida data rabashi da albarkan mahaifiyar sa,yace ma umma ta zaba ko auren ta ko rufaida...

Umma batace mai uffan ba harya gama bambamin sa, ganin har rufaida ta fito tana tsaye tana jin Duk abunda yake cewa yasata dauke kanta daga kanshi ta shiga kallon yartan cikin sauke wata nannauyan Ajiyan xuciya batayi wata wata ba ta sakai ta isa gabanta direct ta rungume ta ajikinta suka tsaya suna ta Kallon sa

Kallon minti biyu ya musu sannan yaja wata arniyar tsaki aransa yana jin tsananin baqin ciki wato hadiza ta zabi rufaida akansa kenan ko,?Wani tsakin ya dada ja yanacema mai keken ya kaisa gida
Babu bata lokaci ya tafi ya barsu a wajen a tsaye...

Ko ajikin umma ta jawo hannun yarta suka fara takawa ganin kamar rufaida bazata iya jure tafiyar ba yasa ta sabata a bayanta har suka isa bakin titi sannan ta sauke ta,da kyar suka samu abun hawa dake dare ne,rufaida ta Ciro kudin take ta miqawa ummanta kudin da kawunta ya damka mata wanda a Ido dai zasu iya finn dubu ashirin sabbin yan dubu dubu,basu tsaya a ko ina ba sai chan anguwar maguzawa inda yakumbo take,dubu daya ta baiwa mai keken ganin dare yay ya tafi yanata godiya,still ta Kuma saba yarta abaya suka nufo cikin gidan Kai tsaye wani Lumshe Ido rufaida tayi abayan uwartan tayi luumui tana sauke numfashi batare da saninta bama har suka iske Wani daki dake shikadai ne ma a cikin gidan
Suna isa daf bakin kofar ta sauketa a  hankli,waje rufaida ta nemi ta zauna ta jingine kanta da bango Jin yadda zazzabi yake ciccinta ata ciki Sam bata jin dadin yanayin ta.
Umma hadiza dake tsaye batayi wata wata ba ta shiga buga kofar tanayi tana juyowa tana lura da rufaida hankalin ta gaba daya yanaga Kan yartan da Dan qarfi take cewa
"Salamu alaikum yakumbo?Dan Allah yakumbo ki taho da sauri ki budemin kofa da ni da rufaida ce kuma batajin dadi...yakumbo
yakumbo...yakum..
Yakumbo dake tsakar da bacci ta somajin maganan kamar a mafarki can dai ta farka da bude idanunta a firgice Jin kamar muryan hadixa ne awaje ana kiran sunanta mamaki ya sata diro kasa Cikin sauri tana famar lalubar dankwaln ta daya salube wajen bacci Batama iya rufe cinyayyen farin kantan da kyau ba ta iso bakin kofar a agaggauce harta saka hannu zata bude kofar sai kuma ta soma tunani kode aljanu ne suka zo mata?inba Hakan ba yo mezai kawo hadiza cikin dare abunda bai taba afkuwa ba,hakan ya sa ta Kara Jin tsoro da dar dat aranta ta Dan dakata kadan na minti daya cikin Kara kasa kunnenta waje,Wani irin ciwo cikin rufaida ya hauyi ta riqe cikin dam cikin sarkafaffen numfashi can da ya murdota ta sake yar Kara tace wayyo Allah ciki na umma
A hanzarce umma hadiza tayo kanta
Tare da tallabota jikintane ya soma bata Hala yunwa ne yake damun rufaida,sake kallon kofar tayi da dan karfi ta nude muryanta tace "yakumbo,yakumbo kirufamin asiri ki bude min kofa Kar yata ta mutu..tun kan ta Kara Furta Wani kalamin sai butt sukaji dorowar mutum a gaban su kamar wanda aka jefota cikin tsananin razanar Jin muryan rufaidar datayi harta hankodo kofar tayi waje batare da saninta ba,a gigice cikin yanayin mamaki ta tsaya akansu tana tafa hannun ta da qarfin shauki mai cike da  mamaki tace
...salawatu sanyi kalau....yau Menake Gani haka?"Menake gani haka hadixa!a Ina kika samo yarki Rufaida?Sai kuma ta fashe da Wani adadannnen kuka Laluben fuskar rufaidar ta hauyi Duk dama acikin duhu suke bai hanata kamota jikinta ba,cikin barkakken kuka mai tafe da rikicewar tsufa da mamaki tace"Rufaida?Allah sarki rufaida,har Ina kika shigane kika bace mana munta nemanki rufaida hankalin Kowa saida ya tashi akanki,oh ni yasu na dauka ma an gudu dake ne rufaida
...ashe da rabon kara saka ki a idona,..Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun
Allah yau mun gode maka,ta karashe Hakan cikin kuka sosai,a lokacin rufaidar ma kuka takeyi sabida ciwon datakeji ajikinta ya fara tsanantawa kanta da cikin ta Duk sun hadu sunai mata zugi ga Wani uban Nauyin da Zuciyarta yake mata,..lura da yanayinta yasa suka  danne zuciyoyin su daga mararin tausayin ta da sukeji suka tallafota suka shiga daki da Ita tare,ba su sauke ta a koina sai Kan gadon yakumbo rufaida ta kwanta a ringingine ta damko cikinta tana Dan murkususu tana sauke Hawaye
,acikin matikar yanayin damuwa umma hadiza ta juya ta kalle yakumbo tace "yakumbo cikin ta ne yake mata ciwo ko akwai abunda zata sha taji Dan sauki? Ga dare ya rufa Duk an kulle shaguna aida sainaje kasuwa in siyo mata magani
..yakumbo bata tsaya Jin ta ba ta juya ta shiga jajjan tsohon ajiyanta na karkashin gado ta hau binciko mata magani,gaba daya umma hadiza ta kasa samun  nitsuwa da sukuni sai juyowa take tana kallon yarta tanajin inama ta karbe wannan zafin ciwon da kuncin ta dorawa kanta Koda yarta data huta,can yakumbo ta dago tare da Wani kullin  maganin gargajiya a hannunta tace yi sauri kijika mata Tasha insha Allah zai mata magani,hannu umma tasa ta karba Amma badon San ranta ba, fita waje tayi ta debo ruwa a randa kusan rabi dan tsaftaciyar mudansa ta jika maganin sannan ta miqawa rufaida ta umarceta da sha,a hnkli take hadiyar maganin tana yamutsa fuskanta warin maganin gaba daya ya hau mata Kai,shanta keda wuya ta rinka kwaxa musu amai,tamkar hanjinta zata amayar haka taketa aman gaba dayansu saida hanklin su ya tashi suka yo kanta,sai can aman ya lafa yakumbo ta jawota ta fitar da ita ta shiga tsaftace ta umma hadiza Kuma ta shiga tattara wajen datayi aman acikin dakin,zama sukayi a yar dakalin dake waje da dan fitilansu a gefen yakumbo na rike da rufaidar a jikinta ta rungumeta tsam tana shafa mata bayanta a hankli
Lafewa tayi sosai ajikin yakumbon ta Dora kanta akan kirjinta ta lumshe idanunta tsam Dan alokacin Babu abunda takeyi sai sauke gajiyayyun Ajiyan xuciya..

Sunfi minti 10 a haka Maganan da yaa malam ya gaya ma umma shiyake dawo mata yana ta damun zuciyarta
gaba daya saita rasa ita din wacce irin baqar mujiyace duba da yadda sanadiyarta ta jawo yau uwa da danta sukayi rabuwar Babu dadi,yan uwan juna suka raunana suka gaya ma juna baqaqen magana,ga mahaifiyata ta jefa kanta a cikin barazanan rasa aurenta sabida ita..
Ta rasa ita wacce irin halitta ce da bata da albarka Sam,mutane basa samun sauki ko sassauci atare da ita saidai ayita samun matsala dominta...

Dada runtse idanunta tayi tsammm cikin tsumayin baqincikin kanta datakeji Ita kanta Kukan daya kufce mata bata San ta Ina ya fito ba
Kawai jitayi yakumbo tana lallashinta da Muryan ta dayake fitowa da mugun tausayi

Itama kukan ta shigayi tana shashhafa fuskarta Koda zata samu ta nitsu Amma Ina abun yakasa dena cizon Zuciyarta,tana mugun mugun jin zafin abunda suke faruwa sabida ita,she just can't hold it anymore,it feels as asif she is just a badluck to anyone's life,a curse to those who loved her,gani take kamar baqin jinintan ne ma yasa baban ta ya kasa Jin tausayin ta,cikin matsanancin kukan da bata shirya masa ba tace..Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, Allah na tuba kayafemin Duk Wani laifin Dana aikata maka wanda nasani da wanda ban sani ba,Allah ka daidaita tsakanin yaa malam da mahaifyarshi da Dan uwansa Allah karka bari auren mahaifiyata ya mutu sanadiyata Allah na tuba kayafeni..sosai take kukan wanda yake fitowa da dukan qarfinsa daga can kuma kasar xuciyarta dayake mata zugi,jikinta ne ya hau rawa cikin tashin hankli da kidima ta rasa yadda zata aje kanta taji sanyi, Jin haka yasa umma barin Duk abunda takeyi ta taho har gabansu ta durkusa a sanyaye tace "yata rufaida me kike fada ne haka?Wani nakasashen Murmushi mai tafe da Hawayene ya kufce mata tanayi  tana kallon fuskarta tana kuma share mata hawayen,cikin tsantsar dauriya da jarumtar iya danne ciwo irinta uwa ta cigaba da lallashinta tana cewa"Haba rufaidata,yar autata Kar ki Kara jefa kanki acikin damuwa kiyi shiru abunki kinji?nasan na aikata Babban kuskure Dana kasa tsaya maki akan burikanki,nayu sakaci wajen Kare ki yata,kiyafe ni,nai miki alkwari baxan Kara maimaita wancan kuskuren danayi ba har Abada.

..dada lumshe ido rufaida tayi ba'a cikin hayyacinta ba ta shiga girgiza kanta sideways cikin tsananin shehshekar kuka Muryan ta a Sarkafe tace...."Umma Dan Allah ki koma wajen baba tunda nice kawai bayason Gani,umma mezan cewa Allah innai sanadiyar mutuwar aurenki?hjy mama ta Sallame shi taci mutunci sa sabida ni wallhy nasan yana Jin haushi na akan haka,Kuma bazai taba yafemin ba Inna rabashi dake kema.
Umma kirufamin asiri ki koma wajen sa Koda Wani abu mai kyau zai faru Dani arayuwata umma rayuwata ta lalace sabida kinbin umarnin sa tun  farko..dagaskiyar baba dayace nice banda gaskiya
Dan Allah karki bari na Kara shiga Wani damuwar a dalilin mutuwar aurenki
..wallah mutuwa zanyi umma, da sauri umma ta rufe mata baki hawayen da bata so ta sauke su suka shiga bulbulowa da qarfi wani Yuuuu suke zubowa daga cikin kwayar idanunta tamkar wacce dama ta boye sune awani waje..."yakumbo ta sunkuyar da kanta kasa bata iya Furta uffan ba tsaban tausayin su,Babu bata lokaci umma ta shiga goge hawayen ta a Duk sanda ta kallo rufaida agaban ta wani sabuwar Murmushin Jin dadin hakan zaka Gani yana haskata
Sanda ta Dan nitsu sannan a hankli ta juyo ta kalleta tace
"Rufaida ki kara hakuri kinji?".insha Allahu zaki cinye jarabawar rayuwar ki,nikaina
Nasan abunda kike tunani,Amma nakasa iya Jin shauqin aikata komi sabida nayi kewarki yata,ayau bana da wata bukata face inga na kula da ke, inaso matukar so in kasance a kusa dake har washe garin gobe,Kuma Koda banason komawa ga mahaifinki ni mai iya aikata Hakan ne saboda ke yata.,kisani
Duk Wani abunda zaisaki farinciki ko Aina yake zanje in Nemo miki shi
,Amma yanzu Ina rokonki da ki kwantar da hanklinki kinji?zanso ace kinci abinci kinyi bacci ki dan huta"..ta shiga shafo kanta cikin yanayina tausayawa tace tun da kika dawo baki ko huta bafa rufaida?..
Karki damu kanki ni nasan menakeyi Kuma insha Allah bazan sake yin kuskuren jefa rayuwarki acikin wata damuwa ba.

Da Hakan suka dinke maganan rufaida taji Dan sauki sauki aranta dake ma maganin da yakumbon ta bata asalin mai kyaune sai tuni taji dama Dama saidai bata iya cin komi ba har bacci mai mugun Nauyi da gajiya ya dauketa.

Rungume a kirjin mahaifiyarta take baccin Inda umma hadiza ta kasa runtsawa Sam ita kadai sai juye juye take tsabagen tunanin dayake yawo a kwakwalnta

Ko kadan bata so ace rufaida ta nemi alfarman ta koma wa yaa malam ba,Dan aranta tagama qudirawa akan zata tsaya ma rayuwar yarta ne komin rintsi komin wuya,saidai fa alkwari ta dauka nacewa Duk abunda rufaida take so shizatai mata musamman in ya shafe farinciki da samun nitsuwarta to koyaya yake tasa aranta kawai shi zatayi..

Can kusan asubahi yakumbo ta farka still taganta azaune ta rafka Wani uban tagumin ta Kure jikon bango da idanu,a lokacin harta Dan shimfede rufaida akan  cinyarta tana Kuma lura da Duk Wani saukar numfashinra sai aikin shafo kanta takeyi tana sauke Ajiyan zuciya mai Nauyi wanda tamkar shekaru dari tayi bata kalle yartan ba.
Dan lumshe ido yakumbo tayi ta Kuma budewa Dan gaba daya tausayi hadiza take bata duba da yadda ta nitse cikin zurfin tunani aganin ta baidace ta kyale ta tana Tara ciwo da takaicin da namiji acikin zuciyarta ba Hakan yasa ta daure ta fincike Dik wani baccin dake cikin idanunta ta miqe ta zauna ta shiga yi mata nasiha masu shiga jiki tana tambayarta labarin yadda sukayi suka samo yarta rufaida?..Duk bazuwar labarin kama yaa malama da akayi yakumbo bata sani ba dake talauci yariga yay mata yawa Kullum yawon jeji take tana neman abinci da abunda zata Dan sayar ta rufa makanta asiri.

Babu Wani boye boye umma hadiza ta zage ta shiga zayyana ma yakumbo Duk abunda ya afku da rufaida da asalin abunda suke ciki ayanzu da mijinta dayace saidai ta zaba tsakanin auren ta da rufaida,wanda za'a iya cewa ko kukan datayi a farko baikai wanda takeyi ayanzu ba sabida sosai abun ya shigeta ya raunana mata ruhi, zuciya, da gangan jiki tanajin zafin abun aranta matuka bana wasa ba.

Ita kanta tasan dan dauriyar datake yi tana tsayuwa da kafafunta ayau Duk sabida rufaidarta ne,Dan ayanzu Sam bata da bukatar Kara mata Wani damuwa

Jikin yakumbo sosai yayi sanyi Dan taci kuka ta gode ma Allah har sanda muryanta ya dauke gaba daya, duk dama aranta taji matukar dadin irin hukuncin da Hajiya mama ta yanke akansu,saidai sabanin ita hajya mama datake ganin kamar lefin umma ne data kasa tsaya ma yayanta,ita kuwa yakumbo Gani take komi lefinta ne.

Aganinta Da can bata nemi maganin jeji awajen bukar ba da babu abunda zaisa ta bashi yar rikon ta hadiza bare har irin wannan mummunan abu ya afku.....surayyahms

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top